Hajiya ta karba ta mika mata. Ta mika hannu biyu ta amsa, ta koma bakin gadon ta zauna ta fara budewa. Sai da ta karance shi tsaf shi da Hajiya suna magana wadda ta shafe su. Ta zari takarda ta yi rubutu a kai. Daidai sanda ya mike tsaye.
Hajiya ta ce,
"Babu sauran wani abin da ki ke bukata?"
Ta mika wa Hajiya takardar da ta yi rubutu yanzun nan,
"Ga wannan magunguna ne da allurai za a sayo."
Hajiya ta karba ta ba shi, ya sanya a aljihu.
"Anything more?" Ya sake tambaya, wannan kai tsaye Aminar yake. . .
Babu ci gaba, bayan babi na sha daya?