Skip to content
Part 3 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Asalin Labarin

Goggo Hauwa na zaune a madafi tana kullin zobo da kunun Aya, wanda ya kasance sana’a a gare ta mai albarka. Ta kwala wa Amina kira daga nan inda ta ke zaune a kujera ‘yar tsugune cikin tsaftataccen madafinta.

“Me ki ke yi wa tantabarun nan ne haka Amina? Ki fito ki sa hannu mu yi mu gama kullin nan”

Daga can dakin tantabarun Amina ta amsa,

“Dan bebina ne ba lafiya, ya kasa cin abinci shi ne nake dura masa dawar. Amma ga ni nan”

Ta ajiye dan tattabarar a cikin tukunyarsa, ta fito ta tadda Goggo.

Wata kujerar ta jawo ta zauna tana fuskantar Goggon, suka ci gaba da aikin; in Goggo ta zuba sai ta bata ta kulla. Suna yi suna hira irin ta Da da mahaifi.

“Goggo in kin dauki adashen wannan watan ne zan koma makaranta ko?”

Amina ta fada cikin murya mai ban tausayi, wadda daga ji za ka fahimci rashin komawa makarantar yana damunta. Cikin muryar tausasawa Goggo Hauwa ta ce,

“Insha Allahu Aminatu, saura kwana biyar ma in dauki dashin. Insha Allahu in dai ina raye Allah zai nuna min cikar burinki. Ga ki can na hango ki cikin farar rigar likitoci kina tsira wa mutane allura…”

Nan da nan Amina ta washe baki, farin ciki mara misaltuwa ya bayyana a kyakkyawar fuskarta.

“Da yardar Allah kina raye Goggo, kuma da na fara daukar albashi kin bar sana’ar lemon Aya da Zobo, Cincin da meat pie. Ni zan saya miki duk abinda kike so, in kai ki Makkah, in saya miki mota, ki kwanta a gida ki huta.

Allah ya jikan Baba, da yana raye da karfinsa kafin ciwo ya kwantar da shi ina za ki rinka wannan wahalar? Dubi fa in kin tashi da asuba bakya kara komawa bacci, sannan in dare ya yi ba za ki kwanta a kan lokaci ba sai kin gama hada kayan aikin gobe.

Ina tausaya miki Goggo, har wani lokacin in ji bana son komawa makaranta saboda wahalar da nake barinki a ciki.”

Goggo Hauwa ta yi murmushi.

“Amina ke nan, ko Babanki yana raye ba na zama babu sana’a, ba don komai ba sai don in tallafa masa, kasancewarsa mai karamin karfi. Da kuma ciwo ya kwantar da shi dole na ci gaba da sana’a saboda kudaden magani.

Rayuwa ta canza yanzu kowa ya dogara da kansa shi ya fi, kada ki yi la’akari da abin da ki ka yi wa mutane ki ce za su rama miki. Dubi dai yadda kanne da yayyen mahaifinki suka yasar da mu saboda kasa ta rufe idanunsa. Don haka Amina na hore ki da sana’a komai kankantarta, ko da ta kiwon Tantabarun nan da ki ka kwallafa wa rai ne watarana za su yi miki amfani”

Amina ta girgiza kai, “Abin yana ba ni mamaki Goggo, wai har Kawu Sule shi ma ya watsar da mu, duk irin taimakon da Baba ya yi masa, ya dauko shi daga kauye ya rike ya samar masa sana’a, dubi albarkar da ya samu a ciki, amma wai ko (school fees) ba zai iya biya min ba.”

Goggo ta ce, “Kada ki kullace shi, duk lalacewar shi ubanki ne. ba ki da wanda ya fi shi, kuma ba dolensa ba ne ya dauki nauyin karatunki don babu mahaifinki, kada ki dogara da kowa ki dogara ga Allah sai Ya iya miki.”

Amina ta girgiza kai, “To ke Goggo ba ki da dangi ne? tunda na taso na yi wayo ban taba ganin wani ya ziyarce ki da sunan dan uwanki na jini ba sai abokan arziki”.

Goggo ta yi murmushi, “Ba irin dangin da ba ni da su Amina. Ba zan je ko’ina ba ne sai ranar da Allah ya cika miki burinki, na aurar da ke a hannu na gari, sannan ne zan koma gare su Amina”

Aminan ba ta kara magana ba, saboda sun gama aikin. Can kuma ta ce,

“Allah ya yarda Goggo”

Ta mike ta jawo manyan kuloli tana shirya lemukan a ciki. Ta bude (freezer) dinsu ta soma ciro kankara tana zubawa a kai.

Daga can soro suka tsinkayi sallamar Ilya mai kura, wanda ke daukan kayan sana’ar yana kai wa makarantu da asibitoci, kura uku suka shigo da ita da samari biyu a bayansa bayan Goggo ta amsa sallamarsu, ta kuma yi musu izinin shigowa. Suka dauki manyan kulolin da bokitan da aka shirya meat pie da cake suka zuzzuba a kura suka yi waje kamar kullum.

Shi Ilyasu dan makotansu ne da yake kula da sana’ar Goggon cikin amana, tana biyansa duk wata. Katangarsu daya da gidan Goggon. Amma yanzu a dakin soron gidan yake zaune tun bayan tashin Sule kanin Baban Amina.

Amina ta cire hitar ruwan zafi daga bokiti da ta jona don ruwan wankanta ya yi zafi, ta dauka ta nufi bayan gida. Saboda dadi da tsaftar lemon Goggo Hauwa, da an fita da shi karfe takwas zuwa la’asar sai kudinta a hannu. Wasu kuwa gida suke zuwa saya, sana’ar Goggon sai masha’Allahu domin tana da nasibi a ciki.

Gidan marigayi Malam Mas’udu gini ne na talakawa masu rufin asiri. Dakali biyu sun sa kofar gidan a tsakiya, da ka sanya kai zaure (soro) za ka tadda, a cikin soron akwai daki falle daya wanda marigayin ya mayar dakin hutawarsa da karbar bakinsa masu zuwa daga kauyensu wyin kwanaki a wajensu. Daga baya da ya dauko kaninsa Sule a dakin ya zauna ya yi samartakarsa har ya yi masa aure.

A halin yanzu Ilya dan makotansu shi ke zaune a dakin wanda ya zama kamar Da ga Goggo, saboda maraya ne kamar Amina shi ma mahaifinsa ya rasu tun yana karami.

Da ka wuce zauren za ka tadda tsakar gida madaidaici. A tsakar gidan, dakuna ciki dai-dai ne guda uku, madafi a gabas, bayan gida a kudu. A tsakiyar filin tsakar gidan bishiyar umbrella ce wacce ta bude ganyayyakinta sosai ta ba da duhuwa mai sanyi.

Daki falle daya na maigidan ne Malam Mas’ud, kafin Allah ya dau ransa, daya na Goggo da Aminatu, tare suke kwana ba sa raba shimfida, yayin da daya dakin Tantabaru ne fal kala-kala maza da mata, sabuwar haihuwa da masu tashi, kowanne aure cikin tukunyarsa.

Sana’ar Baban Amina kenan, ya kiwata Tattabaru in sun girma ya kai kasuwa ya sayar. Wani zubin kananan ma ana saye. Da wannan sana’ar ya rike iyalinsa, suka rayu cikin rufin asirin Allah. Duk da matarsa Hauwa tana gwada sana’o’in hannu iri-iri.

Garin Bauchin Yakubu shi ne asalin garin Malam Mas’ud na haihuwa, sun fito daga kauyen Shira. A kauyensu tun yana yaro kiwon Tattabaru yake yi, wani ne ya ba shi shawarar ya dinga shigo da su maraya ana sayensu da daraja, da haka ya fara, ya yi keji babba ya zuba su a kasuwar Wunti, Allah kuma ya sanya masa albarka a ciki, ya koma gida Shira ya sayar da katuwar gonarsa ta gado ya dawo ya sayi gidan da suke ciki a yanzun.

Hauwa’u mahaifiyar Amina, asalinsu ‘yan kasar Sirrleone ne. Kasuwanci ne ya kawo iyayenta Bauchi har ta zame musu gida. Rannan ta shiga kasuwar Wunti wajen Babanta kai masa abinci kamar yadda ta saba kullum karfe biyu na rana, tana ‘yar shekara goma sha uku, ta ga Tantabaru guda biyu a hannun wani abokin cinikin Babanta. Cikin sha’awa ta soma tattaba su, ta ce, “Baba, don Allah ni ma ka sayo min in yi kiwonsu, ina son Tantabaru.”

Babanta Malam Hadi wanda shi kuma sana’ar saida kaji yake yi ba su da nisa da Mas’ud, wanda a lokacin saurayi ne mai tashen kuruciya, ya yi dariya ya ce, “Ba na son rigima Hauwa’u, ina za ki iya wani kiwon Tattabaru ke da ko kajin da nake bari a gida ba iya kula da su ki ke yi ba, ina za ki iya wani kiwon Tantabaru?”

“Wallahi Baba zan iya, don Allah ka saya mani.”

Hauwa ta dage, Malam Hadi yana matukar son Hauwa, don ita kadai Allah ya ba shi, tare da maidakinsa Aishatu.

Ya ce, “Tunda kin dage bari in sallami wannan mu je in saya miki wajen Masa’udu, amma lallai in kina barinsu da yunwa zan dawo masa da su.”

Hauwa ta amince da sharadin Babanta.

Masa’udu yana zaune ya zuba tagumi, yau tun safe bai yi cinikin ko Tattabara daya ba, Hauwa da Babanta suka yi masa sallama, ya dago da sauri idonsa bai fada a ko’ina ba sai cikin na Hauwa, ya kuwa zuba mata ido ya kasa daukewa. Yarinya kyakkyawa, doguwa kalar mutanen Sierleone, wani abu ya ji ya fizgi zuciyarsa a kanta, sai da Malam Hadi ya yi gyaran murya ya yi firgigit ya maida hankali kansa, tukunna ya fara gaishe shi, Malam Hadi ya dube shi cikin kulawa.

“Masa’udu tunanin me ka ke yi haka? Ko yau ba kasuwa ne?”

Masa’uudu ya yi dan murmushi, don a halittarsa ba shi da yawan magana. Malam Hadi ya ce.

“Kada ka damu, ai kasuwa ta gaji haka, wataran kaf mutum ya rasa ciniki, idan Allah ya koro cinikin kuma sai ka ganshi fiye da tunani, Allah ya ba mu kasuwa mai albarka”

“Amin”. In ji Mas’ud.

Ya maida hankalinsa kan Hauwa, ya ce, “Kanwarka ke son Tattabaru aure daya, nawa suke?”

Masa’udu bai san sanda ya sanya hannu cikin kejin ya zaro wadanda suka fi sauran kyau ba ya mika wa Hauwa, ta karba kowacce a hannu daya tana ta murna.

“Nawa suke?” Malam Hadi ya sake tambaya.

“Naira Maitan, amma ita kyauta na ba ta”

“A yi haka Mas’udu?” In ji Malam Hadi yana murmushi.

“Har fin haka za a yi, tunda kanwata ce kamar yadda ka ce”

Malam Hadi zai ja da nisa Mas’udu ya katse shi, “Idan har da gaske ka ke kanwar tawa ce, to don Allah ka barshi haka”

Malam Hadi ya ce, “Shi ke nan Masa’udu, Allah ya kawo kasuwa mai albarka”.

Masa’udu ya ce, “Amin”

Hauwa ta rusuna ta ce, “Na gode”

Kai ya daga mata, Babanta ya wuce gaba, ta bi shi a baya.

Masa’udu tun ganinsa da Hauwa ya kasa sukuni, kwana uku bayan nan ban da tunaninta ba abin da yake yi, daga baya ya gane kaunar Hauwa’u ce ta shige shi farat daya. Ya kuma yanke shawarar kai kukansa ga mahaifinta ko da ba zai ba shi ba a kalla ya samu sukuni cikin zuciyarsa.

Washegari ya tadda Malam Hadi a nasa kejin, ya sunkuyar da kai, Malam Hadi ya ce, “Ya aka yi ne Mas’udu? Mun gaisa ka yi shiru bayan da ganin bakin nan naka akwai motsi a cikinsa”

Mas’ud ya muskuta ya daure ya ce.

“So nake ka ba ni izinin shiga cikin maneman Hauwa’u Malam, in har ba an yi mata miji ba”

Malam Hadi ya yi murmushi, a ransa ya ce, “Na san za a yi haka”. A fili kuma ya ce, “Ka zo sau uku ku shirya, in ta amince ni da ma a shirye nake da in aurar da ita”

Zuwan Mas’udu biyu wajen Hauwa suka shirya kansu. Ya tattara ya tafi Shira don turo danginsa. Iyayensa sun dade da rasuwa, sai kannen Babansa guda biyu Malam Bilya, da Malam Tasi’u. sai kaninsa Sulaiman wanda a lokacin yaro ne. Ko da ya kai maganar ga kawunsa Bilya sai cewa ya yi, “Ni nan ai na riga na yi maka mata, kanwarka Talle. Jira nake ka zo da ma in yi maka zancen”

Masa’udu ya ce, “Ba zan iya auren zumunci ba Kawu, don Allah ka amshi zancen Hauwa’u, ita ma iyayenta mutanen kirki ne”

Malam Bilya ya danne bacin ransa na kin amsar ‘yarsa da Masa’udu ya yi, ya ce zai zo marayar ya sauka gidan amininsa ya yi bincike a kan yarinyar da iyayenta, kafin ya yarda ya shige masa gaba kan aurenta. Ya je ya dawo bayan sati daya.

Masa’udu ya kasa barin satin ya cika, kwana shida ya yi ya dawo Shira wajen kawunsa, sai da ya gama sha masa kamshi sannan suka zauna.

“Na gama bincike na tare da aminina Malam Dahiru, abin ikon Allah ma makota suke da iyayen yarinyar da ka ke nema din. Bincike ya nuna iyayenta bakin haure ne daga can wata kasa da ban taba ji ba wai Saliyo. Don haka ni ba zan shige maka gaba kan auren wadda ban san asalinta ba. In ba za ka auri kanwarka ba, to ka nemo wata ‘yar asali amma ba na cikin auren bakin haure’

Masa’udu bai hakura ba, sai ya koma kan daya kawun nasa Tasi’u, don shi kam mai ilimin addini ne, limami ne guda a shiyyarsu, shi kam ya karbi maganar da muhimmanci, da ya yi nasa binciken ya nuna ban da kasancewarsu baki iyayenta mutanen kirki ne da aka yi musu kyakkyawar shaida, yarinya kuma ta samu tarbiyya da ilmin addinin islama har alqur’ani ta sauke.

<< Sanadin Kenan 2Sanadin Kenan 4 >>

1 thought on “Sanadin Kenan 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×