Skip to content
Part 33 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

An shake katafaren dining-table din da nau’ikan abinci kala daban-daban. Ga wasu greeting cards manya-manya an manna a kowacce kusurwa ta falon. Mutum biyu ne zaune a ‘dining’ din suna cin abinci, a jikin kowanne greeting card an rubuta ‘Welcome to Government House ILYAS’.

Duk suka dago suka dube ta da murmushi, Ilya da Gwamna Ma’arouf Habibu Ji-kas. (Ilyan Goggo). Ta hada ido da Ilya wanda idonsa ya ciko da hawaye ga murmushi yana yi duk a lokaci daya, da gani hawayen farin ciki ne. Ya sha farar shadda kal ‘yar ciki da babbar riga da hula da bata taba ganinsa da su ba, kamar ba Ilya ba.

Ta kama baki da hannun ta tana kallonsu (with astonishment). Baban Ameena murmushi yake yi, yace “karaso mana!” Ilya na kuka da dariya, ya ce,

“Dr. Amina!”

Amina ta ajiye mamakinta a gefe, ta ce, “Ilyan Goggo?”

Ya ce, “Na’am, SANADIN  ilminki, Sanadin ilminki yau ga ni ga Ma’arouf JI-KAS! Ba zan iya kwatanta miki farin cikina ba. Sanadinki na hadu da wanda na fi kauna a rayuwa ta…” Sai kuka

Amina ta karaso inda suke tana turo keken Ameena a hankali, ta zauna a wata lallausar kujera a gefen Ilya, little Ameena na cikin wheel dinta a gabanta.

Ta ce, “To Ilya ai ni ban fada masa ba, ban taba yi masa zancenka ba…”

“Kada ki cika kwakkwafi mana……”. In ji Baban Amina, ya fada yana mikewa tsaye. “Kina zaton zan amince in damka amanar ‘ya ta guda daya ga mutumin da ba ni da cikakken sani a kansa da asalinsa? Wajen ki ya zo ku gaisa, an gaya masa kina ta nemansa kafin ki taho last week.”

Ya fada yana goge hannayen sa da tissue ya wuce su, bayan ya kama hannun little Ameena ya sumbata ya saki ya wuce.

Amina jikinta har rawa yake ta kara matsawa kusa da Ilya.

“Ilya ya aka yi? Last week ya ce in gaishe ka, shine nake ta nemanka in gaya maka, in kuma tambayeka a ina ku ka hadu? Kai ka ba shi account number dina?”

Ilya ya goge idonsa yana dariya, “Wallahi Amina ni ne. Wannan kwamishinan malaminku ya zo har gida bidar account din da kansa, Goggo ta ce in ba shi. Ya tambaye ni, ni ne Ilya? Na ce ni ne, sai kawai ya ce in biyo shi.

Da farko Goggo ta dan ji tsoro kada a ce laifi na yi, na ce mata ta kwantar da hankalinta shi ne wanda ya zabeki ki yi aikin ai. Haka ya dauko ni a mota, bai ajiye ni a ko’ina ba sai ofishin Gwamna, sai ga ni ga JI-QAS ido da ido.

Ya ba ni hannu mukayi musabaha, ya ba ni ruwa na sha. Kwamishina ya gaya masa ni Yayanki ne ba na ciki daya ba, kuma kin gaya masa yadda nake matukar kaunarsa tun kafin ki fara aikin nan, da yadda na ja ku ke da Goggo ku ka je ku ka jefa masa kuri’a. Ya ji dadi sosai, ya gode mini, ya kuma gayyace ni yau in zo mu ci abincin rana tare. Wadannan kayan na jikina shi ya aika mini ya ce nashi ne, in sanya in zan zo….”

Amina ta ce, “Ikon Allah!”

Ya ce, “Ke ce SANADI ai. Ya kuma dauke ni aiki a gidan nan ni ma, ni ne shugaban babban kicin.

Da fari ya tambaye ni ko na yi karatu? Na ce a’a sai na yaki da jahilci. Ban taba dana sanin rashin tsayawa in yi karatu ba Amina sai yau. Don cewa ya yi, da ya ba ni mai bashi shawara kan harkokin matasa”

Amina ta yi dariya, “Har na hango Ilyan Goggo a office”

Suka sa dariya, ya ce, “Wannan din ma da ofis dina, amma fa da kyar in zan karba, in na bar Goggo ya ya za ta yi da tata sana’ar tunda ni ne karfinta?”

Amina ta girgiza kai “Ka nada wani cikin yaranka masu tayaka wanda ya gane kan sha’anin sosai, amma kai namiji ne iyali za ka tara, dole ka tsaya da kafafunka. Goggo ma za ta fi son haka fiye da a ce saboda tata sana’ar kai ka kasa tsayawa ka gina kanka.”

Ya mike yana sabe hannun babbar riga, “Ke kin faya tsari. Bari dai sai na yi shawara da Goggon. Ni na tafi.”

Ka gaida gida, Goggo da Inna Zulai, Talatuna da tantabaruna.”

“Za su ji! Wannan ce ‘yar taki?” Ya fada yana dafa kan Ameena.

“Ita ce Ameena”

“Allah sarki! Yarinya kamar Babanta ya yi kaki. Allah ya ba ki lafiya Ameena”

Ameena karama ta ce, “Amin”

Suka yi sallama ya tafi, ta tura Ameena suka koma daki.

*****

Haka Amina ta ci gaba da aiki a gidan Gwamnati har ga shi yau ta debi watanni goma tana kula da Ameena da iyakar iyawarta da iya zurfin ilmin da Allah ya hore mata, tana kuma hadawa da addu’a, nafilfili,  tsayuwar dare duk akan lafiyar Ameena Ma’arouf. Kullum kuma yarinya Ameena kara samun lafiya da kuzari ta ke. Hannayenta hagu da dama duk suna motsi, kafar ce guda daya har yau Allah bai ba ta damar takawa ba, Amina ta soma yi mata amfani da karafuna biyu hagu da dama, tana taimaka mata tana koyon takawa da su.

A hankali sabo mai tsanani ya ci gaba da shiga tsakanin Gwamna Ji-kas da Amina, cikin dabara yake janta a jiki yana shiga al’amuran rayuwarta, hali shi ne babban abin da ke sanyawa a so mutum. Kuma Amina tanada hali, hali kuwa mai kyau abin yabo. kullum Ma’arouf Ji-kas cikin (observing) halayen Amina yake, na yau daban, na gobe daban masu yi masa kamanceceniya da na AISHA. A sannu soyayya mai girma ta cigaba da  ginuwa a zuciyarsa ba tare da sanin shi kansa ba. Abin da ya nuna masa son Aminan ya dade da kama shi shi ne, halin kewa da rashin sukunin da yake samun kansa a ciki a duk lokacin da ta je gida, ga damuwa da al’amuranta. Ga son ganinta akai-akai, ga son jin sassanyar muryarta.

Goggo da Ilya wanda yanzu ya zama na hannun daman Ma’arouf kuma babban (officer) na (catering) a gidan gwamnati sun dade da gane His Excellency son Amina yake yi, amma ita wawiyar har gobe ta sanya Baban Ameena a matsayin wani mutum mai son ci gabanta, mai kula da al’amuranta, mai darajja iyayenta da ‘yan uwanta. Hatta Talatu da Zulai Jikas ya san da zamansu. Don haka itama a gare ta Ma’arouf Habibu Ji-kas mutum ne mai daraja da kima a gare ta da bata ajiye matsayin sa nan kusa a zuciyar ta ba, irin matsayin nan da kake baiwa babban Yayanka da kuke ciki daya.

A gefe ga kaunar da Hajiya ke mata kamar ta hadiye ta, kusan kullum sai sun yi waya.Amma bata cika zuwa ba. Hajiya na da wannan dadadden burin a zuciyarta na Allah ya hada zuciyoyin Ma’arouf da Amina, amma idan ta tuna tsarin da a kullum yake fadin ya yi wa rayuwarsa sai jikinta ya yi sanyi. Duk da haka tana addu’a idan Allah ya tashi sauya zuciyar Ma’arouf daga kan tsarinsa na auren mata daya kacal, Ya sanya Amina ce. Ita ba za ta tilasta masa ya kara aure ba, ko ta tallata masa Amina ya zo ya ce a’ah ta zubar mata da martaba a banza a idanunsa.

A daya gefen zamansa da Laila na kara tabarbarewa. Kullum ba ta gida, in kuma tana nan za ka tadda falonta cike da kawaye da women leaders. Idonta ya bude sosai da harkar siyasa ta yadda har ba ta da lokacinsa. Ko tafiya ce ta kama shi ya nemi rakiyarta ba ya samu, yanzu za ta ce tana da biki, ko gayyatar taro ya je abinsa.

Tafiya ta yi tafiya aka gangara watanni goma sha daya, Ma’arouf Ji-kas ya soma ganewa, wato bayan ilmin likitancin tada mataccen kashi da Allah ya baiwa Amina, ita din fasiha ce, tana da sani a fannonin rayuwa daban-daban. A hankali zuciyarsa ta cigaba da afuwa ga soyayyar Amina mai girman gaske.

A karshen wata na goma sha daya ne Amina ta duba asusunta. Kudin ciki sun ba ta tsoro, sai ta ga lokacin da ya dace ta cika burinta a kan Goggonta ya yi.

A wani yammaci ta kira Ilya kafin ya wuce gida, bayan ya tashi daga aiki. Suka zuna a wani karamin falo, ta ce, “Ilya ka taimaka mani, na samu abin da zai ishe ni cika burina. So nake Goggo ta ji dadi a wannan siradin na rayuwarta. Ta daina wannan wahalalliyar sana’ar, shekarunta sun ja. Tana bukatar hutu.

Inaso Goggo na ta daina shiga motar haya, ta je ta sauke farali. A rushe gidanmu a yi mata na zamani. Ga abin da nake da shi, gaba daya na damka wannan hidimar a hannunka. Ina kuma rokonka kada ka gaya mata sai ka kammala komai. Aikin hajji kuwa sai an sa musu ranar tashi za ka gaya mata”

Ilya ya dubi Amina, sai ya ga tana share hawaye.

“To kukan na mene ne kuma? Allah ya yi miki albarka Amina, Allah ya ba ki miji na gari da zuri’a mai albarka masu jin kan mahaifa. Hakika ni ma na yi wannan tunanin, lokaci ya yi da Goggo za ta huta haka a rayuwarta tunda dukkanmu ni da ke yanzu mun tsaya da kafafunmu mun kawo karfi.”

Amina ta yi sharbe,

“Ba komai ya sa ni kuka ba Ilya, illa tuna Baba da na yi. How I wish shi ma yana raye? Ya shigo cikin inuwar ilmin da suka dora ni a kai? Allah ya yi masa rahama!”

“Daina kukan haka, ya isa. Ki ba ni wata guda, komai zai kammala a gabanta insha Allah. Amma maganar gini ki ba ni wata uku, ba nata za a rushe ba, sabo za a yi. In aka ce sai an rushe dole sai ta fito daga gidan, kuma sai ta tambayi ba’asi.

Sabon fili za a saya a gaba kadan. Aikin hajj kuwa an kusa gama biyan na wannan shekarar, don haka zan hanzarta. Mota kuwa har Kwatano za ni na auno mai kyau, Allah ya yi miki albarka.”

Amina ta ce, “Ameen. Sai abu na biyu. So nake Goggo ta daina wannan sana’ar wahalar kwata-kwata daga lokacin da za ta tare a sabon gidanta, zan dinga raba albashina biyu duk wata ina bata rabi”

Ilya ya dan girgiza kai,

“Da kyar za ta yarda da wannan. Zan dai dauki ma’aikata a dinga biyansu su ci gaba da komai, nata ya zamo umarni.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 31Sanadin Kenan 33 >>

2 thoughts on “Sanadin Kenan 32”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×