Skip to content
Part 35 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Ta daura hannu a kan Ameena tana shafawa a hankali. Daga bisani ta ture akwatin gefe ta rungume ta, kuka sosai ya kwace mata.

An yi (knocking) har sau biyu Ameena da Ameena ba su ji ba dukkaninsu kuka kawai suke yi. Ameena Ma’arouf ta gane Antinta barinta za ta yi, in tayi duba da yadda tayi parking komai nata, ita kuma ba za ta iya zama a gidannan babu Antinta ba.

Cikin kuka ta ke fadin, “Aunty ni bin ki zan yi, wallahi ba zan zauna da Anty Laila ba!”

Amina ta ce, “Cool down Ameena, da Daddy za ki zauna ai ba da Anty Laila ba…”

“Kullum ba ya nan, Aunty ni ma ba zan zauna ba…” Sai kuka.

Amina ta rasa abin da za ta ce mata, sai ta biye mata suka dunkule wuri guda suna ta rera abinsu. Sabo turken wawa!

Alamu Dr. Amina ta ji na an zauna a gefensu. Ta yi saurin bude ido, ta juya inda ta ji alamun zaman mutum din da kamshin turarensa na koyaushe ya gaya mata  MA’AROUF JI-KAS ne.

Hadiye kukan ta yi baki dayansa ta saki Ameena ta ba shi baya. Bata so ya ga hawaye a idonta ba kada ya yi zargin tana kuka ne don za ta bar Government House.

“Kukan naku ya yi yawa…” Ya fada a hankali.

Ba ta ce komai ba, ya koma kan diyarsa.

“Kukan me ki ke yi haka Ameena?”

Ta share hawayenta da tafukanta biyu, kafin cikin shessheka ta ce, “Aunty ce take hada kaya za ta koma gida yau, wai saboda na warke. Daddy ni ma ba zan zauna ba, Aunty zan bi daddy…”

Ya janyo ta jikinsa, ya aza a gefen gefen kafadarsa yana lallashinta, “Ameena makaranta zan sanya ki, wadda ake kwana acan, Dr. Amina ta gama aikinki za ta koma asibiti, za ta yi aure ta haifa maki kanne. Ba kya son wadannan ci gaban ga Auntyn taki?”

Ta yi sheshsheka “Ina so Daddy. Amma ita zan bi, bana son makarantar kwanan…”

Rigima sosai Ameena ta ke yi, ta birkice musu, hatta Dr. Amina ta tsorata da borin da yarinyar ke yi, ta juyo ta kamo ta tana nata lallashin. Amma Ameena ta fizge ta tubure.

Ya kai hannu ya cire hular kansa ya ajiye a gefe, sai gumi yake duk da na’urar sanyaya daki da ke aiki ba kakkautawa. Idanunsa sun kada don ko fushin Ameena ba ya so balle kukanta, shi ma ya san zamanta da Laila ba zai yiwu ba, Ji-kas ne waje na farko da ya yi tunanin maida ita ta zauna wajen Hajiya.

Amma lokacin shiga makarantarta ya yi har ya wuce, ya kamata a ce tana Primary 1 amma ko nursery ba ta fara ba, shekarunta shidda. Abin da ba ta sani ba shi ne, ya fi ta jin tafiyar Dr. Amina.

Wata mace guda daya tal a duniya da ta shigo cikin rayuwarsa ta sauya ta. Rana daya ta yi fatali da bulullukan da ya gina rayuwarsa a kai na falsafar auren mace daya. Ya dade yana nazarin kansa akan Amina kafin wadannan bulullukan su ruguzo. Bai taba haduwa da mace mai kyawawan halayenta da nasibobinta ba, (he’s sorry to say) hatta A’ISHA.

Amina Mas’ud Shira, ta dade da canza wannan tunanin, ta kawo sabo fil ta gina, kullum kwana yake ya  tashi da tunanin ta inda zai tunkare ta kai tsaye ya kasa. Ba wai ba zai iya gaya mata ya yanke shawarar hada rayuwa da ita ba ne, a’ah! Azancin fadar hakan ne babu, tunda ya gama cika duniya da furucinsa na mace daya ta ishe shi rayuwa, a talabijin ne, a jaridu ne, a radiyo ne da sauransu. Shi ya sa ba a so mutum ya ce ya tsara wa kansa rayuwa, muna namu Allah na naSa, rayuwarmu tun haihuwar mu tana rubuce ne a allon lauhul mahfuz. Ya nisa a hankali ya dan saci kallon Dr. Aminah.

“Ki daure ki kara kwana biyar, ban gama sallamarki ba ai, kokari kike ki sallami kanki, albashin wannan watan bai shiga account dinki ba,  tun jiya ban zauna ba.”

Ta girgiza kai, “Na riga na yi waya da Goggo, na fadi mata yau zan koma, already nace ina hanya…”

Ya bude idanu sosai ya dube ta daga kankance su da yake yi a baya.

“Da iznin wa kika yi hakan? Sai ki fadi yadda za a yi da Ameena……”.

Da sauri ta dago ta dube shi, jin yadda yayi maganar fada-fada, bata ga laifi cikin abinda tayi ba, shi ya kamata ya fadi wannan ai, ita ya za a yi ta sani, shi da ‘yar sa?

Ya karanci abin da idanunta suka fadi, ya kara janyo Ameena jikinsa suka hadu suka narke mata, duk sai suka ba ta tausayi. Ba ta san lokacin da ta bude baki ta yi magana ba.

“In za ka ba ni ina so, da ma Goggo ba ta da wadatar ‘ya’ya. I’m sure za ta hada mu ta rike da amana.”

Murmushi ya yi, domin iya gaskiyarta ta yi furucinta, cike da wauta da gabunta irin na ‘yan fari zai ce ko auta?

“Ku kuma ‘physiotherapists’ haka ku ke zama gaban Goggonninku ba kwa ko tunanin yin aure? Al’adar ku ne yin hakan? Dube ki don Allah (close to 26) amma ko kunyar ambatar Goggo za ta rike ku ba kya yi bayan ke ma kin isa zama Goggon wasu irin su Ameenata. Amina Mas’ud Shira, in kin amince ki maye min gurbin Babar Ameena. Ina nufin, ina sonki, ina  kaunarki ina ra’ayin aurenki ba don Ameena ba, I just love you, so do I since….. Amma fa idan har ban yi miki tsufa ba.

Ina son dukkan halayenki Ameena wadanda su suka ja ni ga kwadayin ki  zamo cikin iyalina. Wannan sakona ne gare ki da Goggo, na ba ki kwana uku ki yi tunani da nazari ki kuma yi shawara da Goggo. Kwana uku bai yi kadan ba? Dr. Amina ki ba ni amsa!”

Amina wadda ta mutu a zaune, tun daga farkon furucinsa, ‘In kin amince ki maye min gurbin Babar Ameena…’ ta daskare ta kasa motsawa, sai dai abin da ya ba ta mamaki shi ne, jin can wani lungu na zuciyarta ya yi sanyi daga azabtar da yake yi na rabuwa da Ameena da Babanta, “…….. Amma fa in har ban yi miki tsufa ba…’

Ta tuno jimlarsa ta gaba. A wannan karon sai ta yi murmushi. At 41, kwarai zai yi wa ‘yammata da yawa tsufa, to ita mai 26 ta ce me? Kada dai sake-saken zuciyar nan yana nufin tuni zuciyarta ta aminta da soyayya da kaunar Baban Ameena? Mutumin da duniya ke so ba abin mamaki ba ne in itama ta so shi. Sai dai fa nata feelings din daban suke da na sauran al’umma irin su Yayanta Ilya, natan are extraordinary. Ba na citizen ga shugaban sa bane, bata taba jin irinsu a kan kowa a duniya ba. Kamar da ma suna ajiye a wani sako na zuciyarta ne, jira suke a sanya kara a zunguro su. Kuma yanzun aka zunguro sun. Kamar tun da ma can an halicce su a cikin kirjinta ne.

Ta yi nisa a duniyar sake-saken nan, ta sunkuyar da kai ta kasa dagowa. Ba ta san sanda ya mike ya nufi kofa ba. Sai da ya murda marikin kofar ya dan ba da kara Amina ta dawo daga duniyar tunaninta. A tsakiyar kanta ta tsinkayi sautinsa yana fadin.

“In kin gama kintsawa Akilu na jiranki. Ameena za mu wuce Ji-kas da ita, ki gaida Ilyas!”. Ya fice.

Ta mike cikin sanyin jiki ta ci gaba da harhada yanata-yanata da kayan amfaninta. Ameena ta yi kuka ta gaji, ta bingire ta yi bacci a wajen. Wannan damar ta samu ta silale da akwatinta biyu. Duk kayan sanyawar da ta tarar a gidan ta yi amfani da su a nan ta barsu, ba ta dauki ko daya ba.

A cikin mota suna tafe suna gaisawa da direba Akilu, ta ji shigowar sako a wayarta. Ta dauko ta duba, sakon shigowar kudi (Alert) ne daga Kwamishina Usman Turaki. Adadin kudin sun ba ta tsoro kamar na baya, sun tada hankalinta. Da hanzari ta danna wa malamin nata kira.

Dr. Turaki ya san za a yi haka, kuma tuni ya shirya karbar kiranta, don haka tana kira ya yi murmushi ya dauka.

“Dr. Amina ya aka yi?”

Amina ta feso ajiyar zuciya. Ta tsane gumin da ya tsatstsafo mata a goshi da hankicin ta.

“Doctor wannan kudin sun fi karfina, me na sayar muku? Me na yi muku na wahala haka? Doctor na fi son iya cikon albashina, Goggo za ta yi zargi, wanda dama kullum cikinsa nake a gurinta”. Ta jero maganganun a jere babu shan numfashi, amma cikin taushin murya mai nuna damuwar da take ciki a fili.

Dr. Turaki ya yi magana cikin muryar kwantar da hankali.

“Take it easy Amina. Me na gaya miki sanda za ki fara aikin nan? In ban manta ba na ce da ke, ‘Allah ya sa ta hannunki za ta samu lafiyar, ina addu’ar tukwicin hakan ya zamo naki ne’. Kin yi kokari a kan Ameena, ta samu lafiya a hannunki, idan Ma’arouf ya mallaka miki rabin abin da ya mallaka ba zai ji komai ba fa. Sai bai yi hakan ba, ya yi daidai hankali da tunani don kada ya razana ki. Ina so ki sani, wane ne gwamna kuma Engnr. Ma’arouf Ji-kas, wannan tukwicin da ya ba ki kwatantawa ne ba kankat ba a kan son da yake yi wa ‘yarsa Ameena. Ki sanya a ranki ilminki ne ya ba ki ba Ma’arouf ba. SANADIN KENAN! Ki yi wa mahaifiyarki bayani kada ta damu, ilmin da ta tsaya miki ki ka yi ne ya ba ki, babu matsayin da ilmi ba ya bai wa mutum a rayuwa. Sannan a wajen His Excellency wannan kamar an fitar da allura daga kogi ne (so relax please, say thanks to almight Allah, not Ji-kas).”

Amina ta yi murmushi ta sauke wayar daga kunnen ta. Tunda ya kashe tasa alamar bai son (anymore word from her) karin wata kalma daga gare ta. A kalla ta samu peace of mind yanzun (kwanciyar hankali). Ta shiga tunanin ta zama attajira mai zaman kanta sanadin ilminta, ta samu zuciyar mutum irin Ma’arouf Habibu Ji-Kas SANADIN ILMINta.  Dadin-dadawa ta samu (exposure) na rayuwa kala daban-daban a gidan gwamnati, wanda za su taimaka mata wajen tafiyar da zamantakewarta har karshen rayuwarta.

Har Akilu ya yi fakin a kofar gidansu tana wadannan tunanninkan. Sai da ta ji motar ta daina motsi ta farga.

“Sai watarana Akilu, sai watarana!  Daga yau an gama.”

Murmushi ya yi, a ransa yace yanzu aka fara dai, a fili kuma ya ce,

“Ranki ya dade, Allah ya kyautata rayuwarki da ki ka kawo karshen matsalar ubangidanmu. Mun gode, Allah ya kara wa Ameena lafiya.”

“Amin Baba Akilu, sai watarana”. Ta fadi tana ‘waving’ dinsa ta shige gida tana jan kafarta, sakamakon wasu tawagar hawayen sabo da suka shimfido mata, zuciyar ta na gaya mata ta rabu dasu fa kenan ta bar gidan gwamnati har abada! Alfarmar ubangidan nasu ba mai yiwuwa ba ce agareta, ba shine irin mijin da ya dace da ita ba, ina ita ina kishi da Anty Laila?

Aka ce yaro tsaya matsayin ka kada zancen ‘yan duniya ya rude ka!  Kwarya ta bi kwarya in tabi akushi sai ta fashe. Jikas mijin mata da yawa ne ba shine Mr. Right dinta ba, tunaninta yafi karfi ga cewa the best is yet to come….. A ra’ayin ta data tsara a zuciyarta tun lokacin da ta soma mallakar hankalin kanta: Tanaso ta auri mijinta ita kadai ne don tanada tsananin kishi, yaro matashi daidai ita wanda bai mallaki komai ba sai kwalin ilmin boko, wanda bai taba yin aure ba, akanta zai fara, wanda zasuyi fafutukar rayuwa tare su gudu tare su fadi tare su tashi tare, amma Jikas ai mijin mace hudu ne.

A lokacin da ta tuna alkawarin data yiwa Goggo kafin ta barta ta fara aikin sai hankalinta yayi mugun tashi.

“Duk mijin da ya fara zuwa ko waye zata bar aikin tayi aure…..”. Akan haka suka tsaya itada Goggo, kafin ta amince mata zuwa gidan gwamnati. Ta tuno da maganganun Zainab Alkali inda take cewa.

“Dreams are conceived, but not all dreams are born alive, some are aborted. Others are stillborn”. (Mafarkai kamar ‘ya’ya suke, ana yin cikin su, amma ba duka ake sa’ar haifesu a raye ba, wasu tun suna ciki ake zubar dasu, wasu kuwa a mace ake haifarsu). In hakane ba lallai ka samu duk abinda kake so ba a rayuwa kuma ka zauna lafiya?

Akilu direba sai bada kayanta ya yi aka shigo mata da su don ya lura kwata-kwata bata cikin hayyacinta har ta shige gida. Abin ya wuce ace kewa ce kadai ta sanya ta a wannan halin, ga dukkan alamu akwai abin da ke damunta. Jikin sa ba laka ya ja motar ya tafi shima cikin kewar Amina. Yarinya ce mai matukar kirki da shiga zuciya da ba zuciyar Jikas kadai ta shige ba har ta wadanda ke zagaye dashi sabida halayenta ababen so.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 33Sanadin Kenan 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×