Gadan-gadan Ilya ya shiga aiwatar da aikin amanar da Amina ta damka masa. Sai da ya kammala komai, madaidaicin apartment din Goggo mai brown rufi ya kammala, mota kirar (E-Class) ta iso. Matsala daya Ilya ya samu, wato dole Goggo ta je a yi mata fasfot da daukan hoto. Daga baya dabara ta zo masa, ya je ya samu Goggo ya ce ta yi shiri su je wani waje za a yi musu takardar zama 'yan kasa, kuma dole sai an dauki hoto.
Goggo ba ta yi musu ba ta shirya suka je immigration aka yi mata fasfot. . .