Duk shawarwarin da suka yi ita da Ilya haka suka aiwatar da su. Goggo ta budi ido ta ganta a wani dankareren gida mai hawa daya (flat house). Ga dalleliyar mota a rufe cikin tamfol an ce ta kai ta unguwa ce. Duk tarkacenta Amina ta bai wa Inna Zulai ta zuba mata sabo. An karo mata mai aiki sun zama biyu sunanta Rabi, suna ci gaba da yin sana'ar ta Goggo, ita kam nata umarni ne da taimakawa yanzu, ga samari maza uku masu (barrow) da suke aiki tare da Ilya tuntuni sun tsaya madadinsa.
Goggo ba. . .