Haka Amina ta baro gidan Kawu Sule bayan ta yi masa ihsani mai yawan gaske wanda zai dade bai manta ba. Suna tafe a mota suna tattauna al’amuran rayuwar duniya masu ban tsoro. Ta tausaya wa Kawu Sule, ta koka yadda al’umma muka yi watsi da martabar zumunci, kuma a haka wai muna burin shiga aljannah. Bayan duk martabar zumunci da darajja shi da Allah (S.W.T) ya yi, Ya yi mana umarni da mu kyautata shi, yana daga cikin manya-manyan hanyoyin shiga aljannah. Allah ya sa mu dace, amin.
Ba su iso gida ba sai karfe takwas na dare. Wata mota ce ‘yar karama mai duhun gilasai ‘tint’ a kofar gidan Goggo, ta dan fara tsufa duk ta karkarce kuma ba a shaida wadanda suke cikinta saboda bakaken gilassanta.
A daidai sanda Ilya yake kokarin sanya motar a inda ake ajiye ta. Amina ta ce, “Hala Goggo ta yi baki ne?”
Ya ce, “Ko kuma sabon saurayi ki ka yi ba?”
Ta harare shi ta bude kofar bangarenta ta fita. Kanta tsaye ta shiga cikin gida, ta baro Ilya a waje. Ya juya kan motar ya nufi gidansu budurwarsa Sadiya.
Sanya kanta falon Goggo ke da wuya ta ji wani sassanyan kamshi, ya gauraye da sanyin iya kwandishan, wanda a cikin kanta ta dade da saninsa, ta yi (marking) dinsa a matsayin kamshin mutum daya, domin bayan shi ba ta kara jin mai irinsa a ko’ina ba, kai ka ce kamfanin da ya yi shi mutum daya ya yi wa shi, ya kuma gargade shi da kada ya rabar da shi da sauran al’umma.
Gaban Amina ya yi wani irin faduwa, saura kadan dunduniyar dogon takalminta ta kayas da ita garin cirewa. Ba don mutane ukun da ke falon sun dago sun dube ta ba da tabbas ta juya ta bar gidan. Mutum na farko da ba ta taba sanya wa a ranta za ta gani tsakiyar dakin Goggonta ba.
Sanye da kaftan na shadda mai taushi, fara kal. An yi aikin zarenta da zare silver, hular kansa ma fara ce kal, a hannunsa na hagu agogon (rolex) ne mai farar fata. Ya saya kwayar idanunshi cikin farin gilashin ido siriri mai garai-garai wanda ya kara fiddo ilhama da cikar zatinsa. His Excellency Ma’arouf Ji-kas ne.
A kusa da shi kwamishina Dr. Usman Turaki ne. Shi kam ya sha suit ya tsuke abinsa, har da neck-tie. Da shi ta fara hada ido don shi ke fuskantar kofa. Ma’arouf din bayansa ke kallon kofa. sai da ya juyo jin karar takalminta da ya kusa kayar da ita, sannan ta shaida fuskarsa.
Goggo ta sha lullubi da katon mayafinta ta takure can gefe, Dr. Amina ta samu kanta cikin rikicewa, ta rasa me za ta yi? Shiga za ta yi ko fita za ta yi? Jikinta ya hau mazari. Sallamar da ta fara yi ma makalewa ta yi a makogaronta ta hadiye abarta. Ta kasa gasgata abin da ta ke gani; Ma’arouf Habibu Ji-kas shi ne ya tako kafafunsa har dakin Goggonta ya zo neman aurenta.
Dr. Turaki ya fahimci halin da ta ke ciki na razana da rashin sanin abin yi saboda ganinsu unexpected (ba zato). Ya dauko murmushin karfafa gwiwa da sanya (courage) irin na Malami ga dalibinsa ya shimfida a kan fuskarsa.
“Shigo Dr. Amina, shigo mana, ai mu ba baki ba ne. Ko kuwa baki ne?”
Ta girgiza kai, sannan cikin sanyin jiki ta cira kafa kamar wadda kwai ya fashewa a ciki rike da takalmanta a hannu ta shiga falon. Ta tsugunna gaban Dr. Turaki ta gaishe shi, abin mamaki ta kasa isa inda Ma’arouf yake balle shima ta gaisheshi, sai ta wuce dakinta wanda ke kusa da dakin baccin Goggo mai ban sha’awa. Abinda ta kashe wa dakin baccin Goggo bai kai wanda ta kashe wa nata dakin ba.
Wannan abu da Amina ta yi, ta gaida Turaki ba ta gaida Ji-kas ba ya fusata Goggo, har kunya sai da ta ji. Ya kuma tabbatar mata da abin da suka fada mata, wato akwai kauna da soyayya a tsakaninta da mai girma Gwamna, wanda ita da ma tuni ta sanya wa zuciyarta akwai din. Ta dauka Aminan ce ba ta sani ba, ko ba ta fahimta ba, ashe ita Amina ke wa kallon sakarai, Allah ya ba ta mijin da ta ke hana idonta bacci tana roka mata har a dakin Allah, ta tattara maganar ta zuba a kwandon shara yadda ta saba.
Bayan alkawarin da ta yi mata kafin ta barta ta fara aikin nan, na cewa, duk wanda ya zo na farko za ta bar komai ta yi aure, yau me raba ta da Amina sai Allah.
Sun dau tsawon lokaci tare da Goggo, har karfe goma na dare. Amina ba za ta ce ga abin da suke tattaunawa ba. Ta kwanta lamau ta yi rigingine a gadonta ta ja bargo mai laushi ta rufe jikinta, kirjinta in ban da dukan tara-tara ba abin da yake yi. Shi kenan ta faru ta kare, wai an yi wa mai dami daya sata, tunda zance ya zo kunnen Goggo, ta lissafa kanta cikin AMAREN BANA (in ji Aziza Idris Gombe). An zuba wa Goggo magani a kan ciwon da ya addabe ta.
Ba ta san yaushe suka tafi ba, ta dai bude ido ta ga Goggo tsaye a kanta tana bubbuga ta sabida barci ne ya dauke ta ba da saninta ba, mai cike da mafarkai marasa kan-gado, wai Goggo na zane ta da wayar rediyo. Tana bude ido kuma ta ga Goggon tsaye a kanta tana huci.
Da sauri ta mike zaune, ta koma bakin gadon ta takure ta sunkuyar da kai.
“Sannu, sannunki likiciyar duniya.”
Amina ta yi shiru, kai a kasa.
Goggo ta ce, “Alkawarin da muka yi da ke kenan? Yaushe ki ka koma boye min sirrikan rayuwarki Amina?”
Amina ta soma hawaye, “Wallahi Goggo ba abin da na boye miki.”
“Daina rantsuwa, kin gaya min Baban Amina ya yi miki maganar aure? Kin gaya min ya ba ki kwanaki uku ki yi shawara da ni?”
Amina ta yi shiru tana share hawaye.
Goggo ta ce, “Ba da ke nake magana ba Amina?”
Ta saki kukan sosai, “Goggo na kasa ne, maganar ta yi min nauyi a baki, sannan ina gudun kada kice soyayya mukeyi tuntuni wallahi ba haka bane, bansan ya zanyi miki bayani ki fahimta ba ba, abin is mysterious (wanda ya gagara fahimta)”
Goggo ta ji zuciyarta ta fara hucewa. Ta zauna gefen gadon itama,
“Amma kin san burina ki yi aure ko Amina? Duka naki burikan na lamunce miki kin cika su, ni me ya sa ba za ki cika min nawa ba in samu cikon nawa farin cikin? Bayan na haihuwar ‘ya ta gari da Allah Ya ba ni, idan na mutu ban ga aurenki ba alhalin Allah ya ba ki mijin auren, ke ce ki ka sa kafa kika shure, ba zan yafe miki ba Amina.”
Ita ma ta soma kuka, ta sanya fuska cikin mayafinta.
Hankalin Amina ya yi kololuwar tashi, ta sauko da hanzari ta durkusa a gaban Goggo, ta dora hannu a kan cinyoyinta. Hawaye na zuba daga idonta.
“Don Allah ki yi hakuri Goggo, wallahi ko gobe ki ka ce na yi aure zan yi. Na tuba na bi Allah na bi ki…”
Sai da Goggo ta yi kukanta mai isarta, cikin dalilin kukanta har dana rashin marigayi mijinta, ta san da yana nan da ko kusa Amina bata kawo wannan lokacin ba a dakin aure ba, sannan ta kai hannu ta daga Amina daga durkuson da ta yi a gabanta tana neman gafara.
“Na yafe miki duniya da lahira. Kin amince za ki iya auren Baban Amina saboda Allah ba don wani dalili ba, ko don ‘yarsa Amina?”
A hankali Amina ta daga kai ta kalli Goggo.
“Goggo duk da ina jin nauyinki, amma a yau zan gaya miki, na dade ina son Baban Amina. Amma Goggo ba kya tunanin jama’a za su ce kwadayi ne ya kai mu ga aurensa, ko wani abu makamancin hakan? Ga kuma matarsa wata irin halitta mai mugun hali da in ba mutum mai tsananin hakuri da kauda kai ba ne kamar shi (Ji-kas) babu mai iya zama da ita.”
Goggo ta yi murmushi, “Amina in ki ka ce za ki daka ta mutane ko abin da za su ce a kanki, ba za ki taba kulla wa rayuwarki wani abin alheri ba. Ke dai komai za ki yi, to ki yi shi don Allah da neman yardarSa. Ki tsarkake niyya da zuciya. Ki yi don neman falalar Ubangiji, ki rabu da mutum wanda ko Ubangijinsa ba ya iya masa. Maganar matarsa, ki nemi da ya raba muku gida…”
“Hakan ba zai yiwu ba Goggo, har sai ya sauka daga kujerarsa, ma’ana sai (tenure) dinsa ta cika, saboda tsaro”
Goggo ta ce, “To ai ni ban san yaushe ki ka koyi tsoro ba. Aminata da na sani mai dabarun zamantakewa ce. Duk da halin nata da ki ke kokawa kin taba ko musayar yawu tare da ita?”
Da sauri Amina ta girgiza kai, “Ko sau daya ban taba ba. Mafiya yawan lokuta ma ni dariya ta ke ba ni, saboda abubuwan da ta ke yi na marasa hankali da tsinkaye ne”
“Madallah!” In ji goggo, “Ci gaba da zama da ita yadda ki ka zauna da ita tun farko. Na tabbatar miki ranar da ta gaji da kanta za ta neme ki da ku zauna lafiya”
Amina ta ce a sanyaye, “Toh Goggo”
Hajiya Hauwa ta kawo murmushin lallashi kan fuskarta, “To tunda mun yi shawarar da ya ba ki kwana uku mu yi, ba ki gaya min ba sai yau, bayan kwana goma sha hudu da ya gaya min da bakinsa. Mun kuma tsaida shawarar, kin amince wa auren bawan Allah irin Baban Ameena, sai ki kira shi ki gaya masa amincewarki, saboda yana cikin damuwa na rashin ji daga gare ki. Ki kuma yi masa gaisuwar da dazun ba ki yi masa ba ki ka wuce shi kai a sama…”
Amina ta turo baki, kamar kankanuwar yarinya, “Don Allah Goggo ki bari sai in shi ya kira, na yi miki alkawarin zan dauka. Ai sai ya ga kamar neman kai ki ke yi da ni.”
Goggo ta danna mata harara, “Da me nake yi ba neman kan da ke ba? Kin ga bana son iya shege, ta bakinki suke jira Ilya ya raka Turaki Shira, da wajen Sule. Cikin watanni uku suke so a gama komai ki tare a dakinki.”
Ta yi ficewarta ta bar Amina tana kakabi da sambatu ita kadai,