Skip to content
Part 39 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Sujjada ce kadai Ilya bai yi wa Amina saboda girmamawa da kauna lokacin da Goggo ta fayyace masa ko me kenan a washegarin ranar, Ji-kas nasa zai auri Amina. Ya shirya sati mai zuwa zai raka kwamishina Turaki da waliyyan Baban Ameena Shira wajen iyayenta maza a yanke maganar daurin aure.

Allah ne ya yi ba zai hadu da su ba, don da ya sauke Amina bai shigo gidan ba ya kada kan motar ya tafi zance wajen budurwarsa Sadiya. Don bai taba kawowa a ransa sune suka zo a wannan motar ba.

A lokacin ya gaya wa Goggo shi ma yarinyar da yake nema an ba shi, kanwar babban abokinsa ce, an ce ya turo in ya shirya. Yana rokon a yi daurin aurensa rana daya da na Amina, gidan da ta rushe ta sake gine masa, an gama komai. Goggo ta ji dadi, Ilyanta ma zai zama magidanci, Amina da Ilya za su kawo mata jikoki kwanan nan…… Sai godiyar Allah.

Amina a can dakinta bayan fitar Goggo, wayarta ta rike tana jujjuyawa, umarnin Goggo ya yi mata tsauri, ga shi Goggo ta ki karbar uzurinta, ta ce dole ita za ta kira Ma’arouf ta ce ta amince za ta aure shi.

“Goggo kin kasa ganewa, jan aji a wurin diya mace ai wani abu ne mai daraja. Haba Goggo ya ya za ki ba ni wannan umarnin mai zafi?” Abin da ta ke fadi a fili kenan ita kadai kamar zautacciya.

“Maza masu wuyar samu a wannan zamanin irin Ma’arouf Ji-kas a ke ja wa ajin Dr. Amina? Anya ba zai tsitstsinke ba?” Wani sako na zuciyarta ya kawo wannan kalubalen.

“Banda SANADIN ciwon ‘yarsa kina tunanin haduwa da shi ma ko a hanya abu ne mai sauki? Balle har ya yi bad-da-kama ya tako gaban mahaifiyarki da kafafunsa? Zauna nan kina ta jan ajinki Anty Laila ta kwace abinta ya kira ki ya ce ya fasa…” Ita da kanta sai da ta yi wa kanta dariya. “……Baban Ameena ya maida ni zautacciya saboda sonsa da kaunarsa…”

Abin mamaki sai ga kira ya shigo cikin wayar. Da ma kuma wayar na rike a hannunta, ‘JI-QAS’ kamar yadda ta yi ‘saving’ shi ke yawo a madubin wayar.

Shidewa ta yi na wucin-gadi, daga bisani murmushi mai taushi ya bayyana a kan siraran labbanta. At last! Ya cece ta daga umarnin Goggo mai tsauri da hasashe daban-daban da zuciyarta ke kawowa. Ta tabbata Ma’arouf na sonta, ya damu da ita, ya ajiye rawanin Gwamna ya nada na neman aure da neman soyayya. Ita ta fara yin sallama bayan ta amsa, ta san halinsa shiru zai yi mata.

“Kina sha’aninki, Allah ya ja da ranki.”

Murmushi ta yi, “Bana kowanne sha’ani, Allah ya ja da ran Baban Ameena”

“Ina ki ka je har karfe takwas na dare?”

“Mun je Shira ne ni da Ilya gaida Baffannina.”

“Da ma ku ‘yan Shira ne? Kin fi kama da mutanen gabas”

Ya ba ta dariya sosai, “His Excellency kuma mutanen yamma ko?”

“Ni kaina ban san ni dan wane gari ba ne. Amma ki bari wataran mu sa Hajiyan Ji-kas a tsakiya ta ba ni gari daya cikin tarin garuruwana.”

Amina ta tintsire da dariya, “Yanayin rayuwa babu inda ba ya kai mutum. Ka san kuwa Goggo ‘yar Sirrleone ce?”

“Haba! Akwai alamun haka. Dr. Amina, ba ta yi kama da cikakkiyar Hausa/Fulani ba. Wannan tsayin… wannan dogon hancin… wadannan manyan idanun… I’m always assessing daga ina Amina ta samo su?”

Ta kai hannu kamar yana ganinta ta rufe fuskarta tana dariya. Bai taba yi mata kallo uku a lokaci daya ba, amma ashe a kallo dayan yana gama kare mata kallo ne. Yadda ya saki jiki yake magana da ita a yau ya ba ta mamaki, ya kuma faranta ranta. Shi kansa har mamakin kansa yake yi.

“Well, ina cikin wani irin nishadi da ban taba tsintar kaina a cikin irinsa ba Dr. Amina. Kullum zuciya ta a takure ta ke, a kuntace, tun rasuwar matata ta fari. Amma tun daga lokacin da ki ka shigo rayuwarmu ni da Ameena takurar da kuncin suke raguwa a hankali.

Daga jiya zuwa yau kuwa da na yanke shawarar zuwa neman aurenki Goggo ta amsa mani ta bani babu ko kadan, na neme su na rasa a tare da ni. Jin kaina nake kamar ba ni ba, jina nake ‘new Ma’arouf’. Wannan ya tabbatar min ke alkhairi ce a gare ni, wadda za ta tafiyar da dukkan bacin raina ta kawo min farin ciki. In samu rayuwar aure nagartacce kamar kowa.

Amma Amina har yau ban ji daga bakinki kin ce kin amince za ki aure ni don kina sona ba. Ga shi kuma ni din wani irin mutum ne da ba ya tilasta wani don amfanin kansa. Zan so in samu amsa daga bakinki Amina, mai dadi ce ko mara dadi duk a sikelin adalci daya zan dora su. Kin amince za ki aure ni in fito neman aurenki?”

Amina ta samu kanta cikin gigicewa, kunya da rashin tantance abin yi. Da za ta iya da ta ce da shi, “Na dade ina sonka Engnr. Ma’arouf Ji-kas, kawai ina tsayawa a matsayina ne.”

Amina ba ta san cewa kalaman zuciyarta a kunnen Ma’arouf din ta ke zuba su ba.

Ya lumshe ido ya bude a hankali. A cikin zuciyarsa ya ce, “ALHAMDU LILLAH!”. A fili kuwa ya ce, “……Tsayawa a matsayi kamar ya ya Dr. Amina?”

Amina ta ankara da sakin bakin da ta yi. Kunya ta kara lullube ta, ta tuna kanta cikin pillow tana makale da wayar “Ka yi hakuri Baban Amina, zance ne irin na zuciya da mamallakinta.”

Dariya ta ba shi sosai, “Ai ni ne mamallakin zuciyar. Daure ki yi min fashin baki a kan kalaminki. Ina so in dora shi a sikeli ne in yi miki bayani a kansa, wanda zai kwantar da hankalinki.”

Amina ta nisa,

“Your Excellency, ina nufin matsayinmu ba daya ba ne, ni ba ‘yar kowa ba ce, ba jikar kowa ba. Kowa ya ji ka aure ni zai yi mamaki, zai fadi abin da ransa ke so….”

Murmushi ya yi, “Na fahimce ki Amina. Amma ko kin san a da ni malamin makaranta ne? Mahaifina ma haka, babu irin fafutukar rayuwar da ban yi ba. Irin wadda baki taba zato ba. To cut it short, babu wanda aka haifa da arziki, kowa a duniya yake samun rabonsa. Saboda haka kada ki kara yin wannan tunanin ko makamancinsa. Ina sonki, ina kaunarki, na yi wa Goggo alkawarin zan rike ki da soyayya da amana har karshen rayuwarmu!”

Hawayen farin ciki suka zubo wa Amina, ta kai tafin hannunta ta share su. “Na amince Baban Ameena, ko gobe a daura mana aure.”

Runtse idanunsa ya yi yana gode wa Allah cikin zuciyarsa. A fili ya ce,

“Ke ko dan Ji-kas din da ake fada ma ba ki iya ba, you always call me Baban Ameena? This is not my name. It didn’t deserve you. Ki ba ni wani sunan ko ki kira ni da sunan da iyayena suka ba ni, zan fi son hakan, zan fi farin ciki da shi”

Murmushi ta yi, duk da ba ta taba ko da gwada fadar sunan Ma’arouf Ji-kas ba, saboda nauyin da yake mata. A yau zuciyarta ta amince ta fada din tunda ya ce fadar za ta sanya shi farin ciki. Ita kuma burinta kenan, ya kasance cikin farin ciki har karshen rayuwarsa.

“Good night MA’AROUF”. Ta fada da dan sauri, ta yi hanzarin kashe wayarta, ta tura kasan filo, ta bi ta karkashin filon ta tusa fuskarta suka buya tare. Kunyar Dr. Amina yawa ne da ita.

Murmushi ya yi da ya fahimci ta kashe, zuciyarsa ta nutsu sosai, sai godiyar Allah ne fal a cikinta. Ya amince daga kwanaki casa’in masu zuwa zai fara rayuwar aure mai nagarta kamar kowanne dan Adam, ba irin wadda yake yi da Laila Ji-kas ba.

*****

Sati biyu da yin haka ya kara yin bad-da-kama ya zo don jin me Amina ta shirya wa aurensu?

A babban falon Goggo suke, Amina ta cika shi da ababen sha masu sanyi, wadanda ta sarrafa da hannunta daga ‘fruits’. Yana kan kujera tana zaune a kan kilishi. Yanzu kunyarshi da ta ke ji ta ragu sosai, tana iya bude baki ta yi magana a gabansa babu jin nauyi. Sabida yadda yake jan ta da hira sosai a waya, ya maida kansa matashi kamarta.

“Shirye-shirye na su ne, bana son a sanar da daurin aurenmu a kowacce kafar sadarwa, a dauro a Shira, zan yi walima a nan gidanmu don ‘yan uwa, iyaye, abokan karatu, na aiki da duk wasu abokan arziki. These are my programme of events your Excellency, please don’t say no!”

Murmushi Ma’arouf Ji-kas ya yi, “A kan me zan ce NO? Bayan kowa da irin yadda yake tafiyar da rayuwarsa? Wanda ya tafiyar da rayuwarsa da sauki shi ya huta. Ina da irin ra’ayinki a wasu bangarorin Amina, ina sonki, ina yinki, ana mugun tare!”

Amina ta kyalkyale da dariya shi ma ya taya ta. Goggo na daki tana jiyowa, da ma a kan sallayarta ta ke ta idar da sallar isha, sai ta dungura ta yi wa Allah sujjadah ta gode maSa da ya share mata hawayenta, Ya bai wa Aminanta irin mijin da kullum ta ke mata addu’ar samu kafin Ya dau ranta. Tsarki ya tabbata ga Allah!

******

Don haka Amina bata koma aiki asibiti ba, ta kara jingine aikin don Ma’arouf ya gaya mata bazai yiwu ba, matarsa sa da aikin asibiti. Yana da shirin da yake yi mata a ransa don bazai bar ilmin data nema ya bi iska ba dole al’umma ta cigaba da amfana da shi.  Shi dai ta kasance cikin yi masa biyayya akan ra’ayinsa shine burinsa kuma ta amince.

Sun cigaba da fahimtar juna, bai fasa bad da kama yazo gidan Goggo ba, soyayya kamar a birnin Hindu,  mai ma’ana kuma tsabtatacciya. Amina da Goggo na cigaba da shirye shiryensu a hankali. Ma’arouf ma na nasa.

Ance rana bata karya saidai uwar diya ta ji kunya. Irin kudin da Amina taga Goggo na zarowa tana mata saye-saye sun bata mamaki, ta kuma yarda ba’a raina sana’a, ka ji tsoron koda mai sayarda allura wanda ya tsaya sosai akan sana’ar tasa.

Ranar wata juma’a aka daura auren Engnr. Ma’arouf Habibu Ji-kas da Amina Mas’ud Shira. A kan sadaki mafi albarka wato mafi kankanta.

Hajiyan Ji-kas sai kukan farin ciki ta ke yi tana mika godiyarta ga Allah.

Da yamma kuma bayan an sauko daga masallaci aka daura na Ilyas da Sa’adiyya. Washegari asabar da yamma aka gabatar da kasaitacciyar walimar kamar yadda Amina ta tsara, ba abin da ba a ci ba, ba irin abincin da ba a yi guzurinsa ba bayan an ci an koshi, anyi guzurinsa, kowa sai sanya wa auren albarka yake yi.

Wasu kan tambayi junansu wane irin miji ne haka Amina ta aura? Su dai ba su taba zuwa walima mai wadatar abinci da abin sha irin wannan ba.

Akilu ya kawo akwatuna guda goma sha biya shake da kayan lefe na fita hankali, ya ce da Goggo Yallabai ne ya turo shi a baiwa Ilyas, sai mukullin mota sienna dalleliya duk na Ilyas ne.

Goggo ta kawo tukwici mai yawa ta baiwa Malam Akilu ya tafi yana godiya. Da ango Ilya ya zo har da taka rawa don murna. Yana tsokanar Amina, wai Yallabai ya fi sonsa a kanta. Ita ko dankwali bai bata ba. Bayan ya san Goggo ce ta roki Hajiyan Ji-kas kada a kawo komai, in ta tare ya bata. Ita ba ta son ‘yan tsegumi su cika mata gida. Ita da jama’arta suka dauka suka kai gidan su matar Ilya.

An sanya tarewar Amina sati mai zuwa, don ta roki Hajiyan Ji-kas alfarmar a barta ta kimtsa a hankali ta yi sallama da danginta na Shira, ta raka Goggo kasarta Sirrleone kamar yadda ta dade da burin sai ta aurar da Amina zata koma, za su yi kwana uku a can. Da fari hankalin angon na Amina ya tashi a kan tafiya Sirrleone din nan. Amma daga baya da Hajiya ta gaya masa shekaru talatin da doriya kenan rabon Goggon da kasarta ta haihuwa da iyaye da ‘yan uwanta, kuma Amina ba za ta iya barin Goggo ta tafi ita kadai ba, a cewarta don kada ta ki dawowa, sai ya amince. Ya yi musu booking jirgin kasar Sirrleone.

<< Sanadin Kenan 37Sanadin Kenan 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×