A yau Amina ta sauka a mahaifar mahaifiyarta Hajiya Hauwa, kasar Sierrleone birnin (Magburaka), sai rarraba ido ta ke tana kallon ababen mamaki, wato al'adu da suka sha bamban da wadanda ta saba gani. Tsayin shekarun da Hajiya Hawwa ta yi a Nigeria bai sa ta manta hanyar gidan iyayenta ba.
Hajiya Hauwa ta gode wa Allah da ya sada ta da iyaye da 'yan uwanta, ana ta murnar zuwansu amma murnar ta fi karkata ga ganin Amina. Ta samu mahaifinta ya rasu, wasu da yawa a bayanshi ma duk sun rasu. Wasu sun hayayyafa, 'ya'yan sun girma. . .