Skip to content
Part 45 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Yana sane ya kashe wayoyinsa tsawon kwana uku don ya san dole za a neme shi kan batun Laila. Ba ya zuwa ko’ina a kwanaki ukun nan, wakilai yake turawa. Daga (office) sai gida manne da Aminarsa. Hajiya da ta gaji da nemansa sai ta kira layin Amina, ta ce ta hada ta da shi.

Ba yadda zai yi don yana zaune a wajen. Ya karbi wayar ya soma gaida Hajiya cikin ladabi, ba ta bari sun gama gaisawar ba ta jefo masa tambayar da take dauke da ita.

“Me ya hada ka da Laila? Ta zo wajena ban barta ta karasa wajen iyayenta ba. Nayi-nayi ta gaya min me ya faru ta ki. Sai kuka ta ke tana fadin in nema mata afuwa a wajenku.”

Da ba Hajiya ba ce kashe wayarsa zai yi, amma wannan ita ce mace mai daraja ta farko a gare shi. Ya gaya mata duk abin da ya faru, a yau kuma ya bude baki ya sanar da ita irin zaman da yake yi da ita tun aurensu. Ya ce, saboda rashin kaunarta da tausayinta ga Ameena ya dauko Dr. Amina ya kawo gidan. Don haka ita ce SANADIN aurensa da Amina ko ta ina aka je aka dawo.

Da ta bi yadda yake so su rayu shi da ita da tilon yar sa, shi da ba mai ra’ayin kara aure ba ne. To ta kwashi wasu dabi’u da halaye na kawayen banza  da matan bariki ta daura wa kanta. Shi kam, ya gama aurenta zai aiko mata da takardarta don ko ta ce za ta canza ba zai iya adalci tsakaninta da Amina ba, kuma Annabi (S.A.W) ya ce a zauna da daya, in ba za a iya adalci ba. A karshe ya ce,

“Hajiya ki barta ta tafi gidansu, yanzu ne ta san ke mutum ce da za ta amfane ta? Ta taba zuwa har inda ki ke haka siddan ta gaishe ki tunda na aure ta? A matsayin ki na wadda ta haifa mata miji? 

Ta taba jin kan abin da na haifa a lokacin da take bukatar Uwa mai tausaya mata? Ta taba nuna min kauna ta hakika ban da ta in na ba ta kudi? Laila ba matar zama ba ce Hajiya, don Allah kada ki takura ni in maido ta ta fita daga raina gaba daya. Ki barta ta je gida don Allah na sake ta saki daya…”

“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel… Ma’arouf ni za ka bai wa aiken saki? Ka yi min adalci kenan? In don ta ni ne duk abin da ta yi min na yafe mata, na yi mata uzuri tunda ta yi nadama kuma ta kara jaddada min ba za ta sake duk abin da ba ka so ba, za kuma ta zauna da Amina lafiya.

To na yafe mata duniya da lahira, ko tsoron surutu ba ka yi a ce don ka yi aure ka saki uwargidanka? Ce ne ka maida ita maza-maza tun wani bai ji ba bayan ni.”

“Sai ta ji na sake ta Hajiya wallahi sai ta ji, ba ni ita a wayar.”

Tunda ya rantse jikin Hajiya ya kara yin la’asar, ba ya rantsuwa koda wasa, tabbas yau an kure hakurinsa, ita kanta ta san halin Laila ba mutuniyar kirki bace, ita ma dattaku ne kawai a matsayinta na uwa gyara ne nata ba bin bayan daya ba. Tunda kuma ya rantse ba za ta so shi da kaffara ba.

Lailan ta kuma sabule mata da a yau ta ji bata kaunar jikarta tilo a duniya;Amina diyar Aisha.Daga bakin da bazai yi mata karya ba. A sanyaye ta mika wa Laila wayar wadda ke zaune gabanta dirshan tana tikar kuka, tana kuma jin duk abinda suke tattaunawa tana mai yarda da kuskurenta.

“Ma’arouf don Allah ka yi hakuri na tuba, na bi Allah na bi ka……”

“Na sake ki saki daya. Kije gida kawai. Allah ya hada kowannenmu da Alherinsa.

Wayyo Allah Maarouf ka yimin rai, ina son ka, ina kake so insa raina…?

Sai a lokacin ta lura ya dade da kashe wayar hannunsa.

Hajiya ta rasa kuzari, ta kasa yin komai akai, a karshe da Laila ta yi kuka ta gaji ta umarce ta data yi hakuri taje gidan nasu kawai kafin tayi tunanin yadda zata shawo kansa.

*****

An sallami Amina ta koma gida amma baa kwance bandejin kanta ba, Amina zata iya rantsuwa cewa ciwon nan a jikin ta yake amma Maarouf ne yake jin zafin sa.

Har dakinta nurse ke zuwa tayi mata dressing din ciwon kullum.

Sai kasancewarsu su kadai cikin makeken gidan mai rassa daban-daban ya zama wata hanya ta kara dankon soyayya da fahintar juna, aminci da kauna mai karfi a tsakaninsu. Amina ya zamanto bata da damuwa, koyaushe idanMaarouf ya shiga office zama take ta kira Goggonta da yan uwanta na gida dana kauye dana Sierraleone su sha hira ko ta tura mota a dauko su su wuni tare, duk wanda ke da nasaba da Amina komai kankantar ta to kuwa yana shan inuwar data ke ciki, wannan a fili yake, hannunta a bude yake kullum cikin bayarwa take da yiwa alummar data shafe ta hanyar cin abinci.

Hatta Yayanta Hafiz kuma tsohon masoyinta Amina tasa Maarouf ya dauke shi daga kamfanin mtn da yake aiki ya maida shi bankin GT. In ma tanada damuwa to na rashin practising aikinta ne.Ta taba yiwa Maarouf zancen tanaso ta koma aiki don bata iya zama waje daya ba ta komai ba, kuma ba ta son tsoma hannunta cikin siyasa.

“Ina matar Jikasda zuwa aiki? Kin taba jin wata matar gwamna na aiki a Nigeria? Ko zan amince da komawarki asibiti sai ranar da bani da nauyin kowa a kaina muka bar wannan gidan na aro muka koma gidana na Fati Mu’azu”

Dole Amina ta hakura ba don ta so ba, ta maida hankali ga bautar aurenta, domin neman dacewa wajen Ubangiji, don a duniya kam ta yarda ta gama dacewa. Alfarmar auren miji na gari irin Ma’arouf Habibu Ji-kas ba karamin dace ba ne. Ta kowanne fanni da diya mace ke buri.

Duk da an ce kowanne dan Adam tara yake bai cika goma ba, a wurinta ita nata mijin ya cika har ya wuce ya isa goma sha tara!!!Matsalarta da Maarouf bazai wuce yawan tafiye-tafiye ba wanda ba yadda zatayi da hakan yanayin rayuwarsa kenan a haka ta ganshi ta aure shi, ba kuma kowacce tafiya ce yake iya yi da ita ba wata tafiyar bata bukatar rakiyar ta.

Kullum Tana kitchen,safe, rana da dare tana girka masa abinda zai ci da hannunta, tafi gamsuwa da hakan, bata ga amfanin ta ba in zata harde kafa a gefe gardi ya shigo ya shiryawa mijinta abin ci ya gama kalle kwalliyar ta ta gefen ido,ta fannin His Excellencyfadar farin cikinsa da hakan bazai misaltu ba. Kullum zaka ganta da littafi da biro tana tsara time-table na abinda zata dafawa maigidan nata, ko ka ganta gaban talbijin tana murdo tasoshin girke-girke na kasashen duniya tana jotting.

*****

Laila ta isa gidansu yamma lis almajiri dauke da katuwar akwatunta, mahaifinta ta fara arba dashi a kofar gida ya shimfida tabarma yana kishingide yana sauraron radio, tun daga nesa ya hango ta tana tafe amma ya sawa ransa ba ita bace mai kama da ita ce, ina Laila ina tafiyar kasa da dirkeken akwati haka kamar mai barin gari?

Bai tabbatar itace ba saida ta tsugunna a gabanshi tana gaishe shi tana share hawaye da gefen gyalenta. Muryarta ba ta fita sosai saboda kukan da ta ci. Dagaci ya ce, Laila ce?

Ta ce cikin dusasshiyar murya, Ni ce Baba.

Ya ce, Lafiya kwaram-kwaram da yammacin nan kamar korarriya?

Da farko Laila ta so ta boye wa mahaifinta gaskiyar cewa, Maarouf ya sake ta, sai kuma ta yi tunanin gara ta gaya masa ko ba komai Maarouf na ganin girmansa idan ya nemi alfarmar ya maida ta dakinta zai yi masa. Don haka ta bude baki ta ce, na dade a garin nan, ina gidan mahaifiyarsa, mun samu sabani ne. Jiya kuma ya sake ni. Amma saki daya ne. Don Allah Baba ka je ka ba shi hakuri.

Dagaci ya gyada kai cikin matsanancin takaici, Ya yi kyau. Na tabbata halin naki na tsiya da ki ke shukawa a gidan da giggiwarki ce ta ishe shi. Ga gidan nan tunda zamansa ki ke shaawa kafada daya da uwarki sai ki shiga ki yi ta zama ki ji in zaman gidan dadi ne.

Amma ni ko sawuna ba zai taka inda Maarouf yake ba balle in wani ba shi hakuri alhalin ban san me ki ka shuka masa ba. Haka siddan yaron nan yaron kirki ba zai sallamo ki ba, da ma ina jin wai-wai a kan wulakancin da ki ke wa yan uwanki saboda Allah ya rufa miki asiri. Duniya ta fi bagaruwa iya jima Laila, ga gidan nan ki zauna haka kawai ba za ki zo ki daga min hankali ba ina zaman-zamana lafiya.

Ya nuna mata hanyar cikin gida, ya ce, Wuce ciki.

Sabon kuka Laila ta sakar wa Babanta, fadi ta ke,

Wallahi ba abin da na yi masa Baba, sabon aure ya yi shi ya sa ya sake ni.

Maigari ya ce, Yanzu na ji magana. Ya yi sabon aure kin yi masa tashin hankali ko? Saboda gidanku ba mata uku ris ki ka tashi ki ka gani ba. To madallah wuce ciki na ce ki gama idda ki auri wanda ba shi da mata. Kada in kifta ido in bude in sake ganinki a wajen nan duka za ki sha wallahi.

Tana kuka ta ja akwatinta mai tayoyi ta shige cikin gidansu kamar ta dora hannu a ka ta zabga ihu.

Matan gidan uku duka suna tsakar gida har mahaifiyarta, kowacce da sabgar da ta ke yi. Mahaifiyarta ce mai girki, don haka talgen tuwo ta ke yi, mai bi mata Larai tana tankaden garin kuka.

Sai amarya Laminde ita kuma tirken awaki ta ke sharewa. Ga kannenta nan matasa da kanana kowa abin da yake yi daban. Jin karar akwatunta duksuka juyo suka dubi hanyar shigowarta.

Babar Laila Inna Saade ta washe baki amma ganin yanayin Lailan sai gabanta ya fadi ta bar abin da ta ke yi ta shige daki, ta fi so ko ma mene ne ta ji shi a daki ita kadai ba gaban wadannan masu son ganin hanjin nata ba.

Kai tsaye kuwa Laila dakin mahaifiyar tata ta wuce. Ta jefar da akwatin gefe ta samu waje ta hada kai da gwiwa ta ci gaba da kuka. Inna Saa ta ce,

Ke lafiya? Mutuwa aka yi?

Laila ba ta amsa ba sai hadiyar zuciya.

Tambayar duniyar nan Innar ta yi Laila ta ki gaya mata komai har ta fusata ta fita ta kyale ta. Kishiyoyin kuwa abin nema ya samu tattaunawa suka shiga yi tsakanin Larai da Laminde.

Wannan akwatin dai ko saki ko yaji. In ji Larai.

Laminde ta ce, Ko kuma an nado mata dankaren duka ba, an koro ta. Ahayye!

Ita dai Inna Saa ba ta tanka musu ba ta wuce murhunta ta ci gaba da tukin tuwonta zuciyarta a jagule.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 44Sanadin Kenan 46 >>

1 thought on “Sanadin Kenan 45”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×