Skip to content
Part 47 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Wata Sabuwa

Bayan Little ta koma makaranta da sati biyu aka bugowa Babanta waya daga ofishin shugabar makarantarsu cewa ba ta da lafiya. A take ya tsallake abin da ke gabansa ya shirya musu tafiya Lagos shi da Amina. A Clinic din makarantar suka riske ta a kwance ana kula da ita. Ya karasa jikin gadon jikin sa na kyarma ya dafa kanta ya tambaye ta me ke damunta?

Cikin sassanyar muryarta take masa bayani.

Daddy watarana in na zauna ba na iya tashi tsaye sai an daga ni.

Hankalin Amina da na Maarouf ya yi mummunan tashi.

Ameena little ta cigaba da cewa,

Cikin kashin kafata in na tsugunna sai in ji kamar zai tsage, sannan kafafuna suna karkarwa in na dade a tsaye.

A take Amina ta janyo ta ta soma dudduba ta, to babu kayan aiki a tare da ita, don haka ta nemi izinin Maarouf na son yin magana da Dr. Turaki.

Shi ya kira shi da kansa ya hada su. Amina ta gaya masa matsalar da ta biyo bayan warkewar Ameena. Suka yi magana irin tasu ta likitoci. Ta mika wa Maarouf wayar ya ce da shi su zo da ita asibiti a duba ta sosai. Makaranta ta ba da izni suka taho da Ameena Bauchi.

To a binciken su shi da Amina da sauran likitocin bangaren su na ATBU Teaching Hospital sun gano matsala babba a tare da Ameena. Sun gano cewa kashin kafarta na hagu bai gama yin kwari ba, yana bukatar wani irin gashin wanda ba su da injin yinsa sai a waje.

Dr. Usman ya ce ya san wani asibitin da suke irin wannan aikin a Vienna (Austria) wadanda sukawarkar da EFCC Lamido Nasir (Babban Goro)  da kuma wani a Jeddah (Saudi-Arabia).

Maarouf ya zabi na Jeddah, ko ba komai bai karya (patriotism) dinsa na yin alaka da kasashen Turai ba. Ya soma yi musu shirin tafiya Jidda shi da Amina da Ameena.

Ranar wata asabar jirgin KLM ya daga dasu zuwa Saudi-Arabia. Madinatul-Munawwara suka wuce kai tsaye don fara yin umrah musamman akan Allah ya basu saar abin da suka zo nema, daga Madina suka wuto Makkah suka yi cikakkiyar umrah, duk adduoinsu a kan lafiyar Ameena ne na neman nasara a kan aikin da za a yi mata.

Sannan suka isa asibitin da suka zo a Jeddah (Solayman Faqeeh) aka fara yi wa Ameena(Radiotherapy)na musamman. Amina ta ja gefe tana kuka fuskarta cikin mayafinta kawai saboda tausayin Ameena. Yarinya karama tana shan azabar da bata misaltuwa a yan kananan shekarunta da basu kai goma ba.

A duk lokacin da ta ga ana yi wa Little therapy din nan ba ta iya daurewa sai ta yi hawaye kamar ba likita ba. A karan-kanta yanzu in zaa bata trillion ba abinda zata iya kara iya yiwa Ameena. Ba don komai ba sai don tausayi da sarewa. Daga ita har ubanta tausayinsu take ji har batasan wa tafi tausayi ba tsakanin yar da ubanta. Amina keda ciwon a jikinta amma zata iya rantsuwa Maarouf zai fi so a dawo da ciwon jikinsa in har zata samu lafiya. Tana ganin yadda baya iya barci tun saukar su a Saudi. 

A makkah da madinah a masallaci yake kwana. Anan jeddah kuwa bisa dardumarsa. Da gaske Allah ba ya hada maka komai a rayuwa, in  ya baka wannan sai ya jarrabeka da wancan, shi kuma Maarouf  Ji-kas ga ta inda allah yake jarrabarsa (ciwon Da).

Ganin halin da take kasancewa in sunzo asibitin tare sai Maarouf ya daina zuwa asibitin da ita, ya gwammace ya zo shi da wadanda suka rako su (securities) dinsa. A hotel din da suka sauka (Aljamjoum) yake baro ta ya zo asibitin da masu tsaron lafiyarsa.

Ba su fara samun nutsuwa ba sai da manyan likitocin na asibitin (Doctoor Solayman Faqeeh) suka tabbatar musu kafafun Ameena sun samu waraka cikin yardar Ubangiji, amma zai iya yiwuwa wani lokacin ta yi fama da dan ciwon kafa kadan-kadan, da zarar ta yi complain din hakan sun rubuta magungunan da za’a bata ta dinga sha a take ciwon zai daina.

Sai a lokacin ne Maarouf da Amina suka samu lokacin junansu, aka biya bashin soyayyar da aka ci kwana da kwanaki wanda tashin hankalin ciwon Amina ya mantar dasu.

Sun yi honey-moon mai tsayawa a zucci fiye da na farkon aurensu a Transcorp. Wata guda da rabi suka kwashe a Saudi-Arabia sannan suka tattaro suka dawo gida Nigeria.

Daga airport kai tsaye direban da ya kwaso su Ji-kas ya wuce da su. Maarouf bai kwana ba ya koma Bauchi su kuwa suna tare da Hajiya har tsayin kwana uku. A nan ne Amina ke yi mata bayanin matsalar da ta fidda su Jeddah. Hajiya Saude ta ce, Kai! Wato dan Adam har ya mutu ba zai huta da kaddarorinsa ba, Allah ka kara mana lafiya baki daya, Allah ya kara miki lafiya mai dorewa Amina.

Da suka koma Bauchi da wata daya aka mayar da Ameena makaranta bayan ta kara samun kyakkyawar kulawa a hannun Antynta.

******

Watarana Amina na gyaran tsofaffin takardun ta na makarantar sakandire wani karamin littafi ya fado, ta dauka ta goge shi tana dubawa, a ciki ta ga lambar waya a kasa an rubuta Hafsa Datti. A take ta tuno kawarta ta makaranta Hafsa. Murmushi tayi tareda yin hamdala ta roki Allah ya sa ta samu Hafsa a wannan lambar wayar, bazata taba mancewa da Hafsa ba, ta dade tana fado mata a rai batasan ya zatayi ta riske ta ba, abinda ta sani kawai shine a Abuja take. Da gudu ta dauko wayarta ta shigar da lambobin.

Sai da ta gama abincin ranan His Excellency ta shirya komai a inda yake cin abincin tayi wanka ta kintsa a lokacin bai dawo daga office ba ta harde a hakimar kujerar falon ta ta soma kiran lambar.

Kira na daya, na biyu ta ji lambar ta shiga, ta fara ruri. Addua kawai take Allah ya hada ta da Hafsa Datti a wannan gabar na rayuwarta. Wata mutum daya cikin masoyan ta na hakika da bazata manta gudummuwar da suka bata a rayuwarta ba. Sannan tana bukatar aboki bayan yan uwa da dangi, aboki saanta wanda zata ke tattauna wasu alamuran dashi bayan Goggo.

Assalamu Alaykum

Taji muryar wata kamilalliyar dattijuwa ta amsa.

Amin waalaikumus-salam . Ina yi ni?

lafiya lau yammata, daga ina? Ban dau muryar ba kuma bansan lambar ba.

Sunana Amina Masud, daga Bauchi nake magana, ni kawar Hafsa ce da mukayi makarantar sakandire tare. Don Allah ko zan iya samun magana da ita?

Allah sarki, Amina ke ce! Yau Allah ya hada Hafsa da Aminar ta. Kullum tana zancen ki, tana rokon Alla ya sada ku watarana kun rabu ba tare da karbar adireshin juna ba kullum cikin zancen take. Allah Rahim, ni mahaifiyarta ce, zan turo miki lambarta yanzu. Bata kasar nan tana aure a kasar Russia. Yanzu na gama magana da ita.

Amina tayi godiya sosai dadi fal ranta.

A take maman ta turo mata lambar Hafsa ta kasar Russia. Amina ta kira Hafsa Sunana Dr. Amina Masud Shira.

Tsalle Hafsa tayi ta dire akan mijinta. Amina! Dr. Amina? Ashe Allah ya cika buri?

Ya cika Hafsa. Im a proffessional physiotherapist, married to Maarouf Ji-Kas.

Maarouf Ji-kas wanne? Hafsa ta tambaya cikin mamaki. Murmushi Amina ta yi, ta daga ido tana kallon sa yana shigowa, idanunsu suka sarke dana juna bayan ya zare farin gilashin sa. Babbar rigarshi ya cire ya jefeta da shi ya wuce bedroom yana fadinnaji ana cewa Maarouf Ji-kas, ke da waye? murmushi tayi, tace wanda kika sani, I think shikadai ne me wannan sunan a Arewa. Yaya bayan saduwa? Mama ta gayamin kina Russia. Yaranki nawa? Don nasan bakya son karatu, Hafsa tayi ajiyar zuciya. Amina, tun farko na fahimci ke yar baiwa ce kuma mai saa a rayuwa, kina daga cikin mutanen dake cimma burirrikan rayuwarsu yadda sukayi fata. Na jinjina miki, na kuma sara miki ta yadda kika yi nasarar auren mutum irin Maarouf Habibu Ji-kas. Na sanshi a jaridu tun yana dan majalisa, na san sanda matarsa tayi accident ta rasu ta barshi da ya ba lafiya. Kada dai ince SANADIN KENAN?

Bakin Amina dai ya kasa rabo da murmushin SANADIN KENAN Hafsa, paralysed Amina. Kuma alhamdulillah ta samu lafiya. Baki bani amsar tambayoyi na ba.

Hafsa ta yi murmushi Eh, karatu kam bana son sa amma Baban Iman bai kyaleni ba saida nayi shi anan Russia na karanta (education) yanzun haka (lecturing) nake university din dana yi. Shi maaikacin embassy ne kwanannan zamuzo hutu zan iskoki a Bauchi insha Allah idan zamu samu ganin Her Excellency da sauki ta karashe cikin dariya. Amina tace Hafsa ho! Kina nan yadda na sanki. Nace yarana nawa? Hafsa ta yi murmushi Iman, Imam da Amina, nayi miki takwara don kar in manta dake. Hawayen kauna suka cicciko idanun Amina.

Bansan kin dauke ni da muhimmanci har haka ba Hafsa da ban kai wannan lokacin ban binciko ki ba ko da da taimakon Yallabai ne. Na gode Hafsa, ki shafa min kansu, ina duban hanyar ku zuwa Bauchi, gaisuwa ta musamman ga Mahmoud.

A bedroom ta iske shi ya fito daga wanka kenan ruwa yana bin fresh fatar jikinsa. Kafin Maarouf ya juyo sai yaji Amina ta rungume shi ta baya. Sosai take cikin farin cikin da ya dade bai ganta ciki ba, sai ya taya ta farin cikin ta hanyar datafi  kowacce sanya farin cikin. Sun farantawa juna yadda ya kamata da soyayya mai tsayawa a zuci. Suna kwance take bashi labarin samun Hafsa, ga mamakinta sai taga ya dakata yana yi mata kallo na rashin gamsuwa da labarin nata.

Amina bana son ki da kawa, bana so.

Gaban Amina ya fadi me yasa Maarouf?

“Abinda nakeso ki tambaye ni kenan. Muna zaman mu lafiya nida ke, banida matsala dake ta kowanne fanni haka kema, in ma akwai muna tattauna ta a junanmu mu magance ta ba tareda kowa ya ji ba, amma kinyi aminiya duk sirrin aurenmu zai zama a kunnenta. Kada ki dauka wayon ku daya ita budadden ido gareta tarbiyyar turai, ina tsoron ta canza maki tunani.

Amina ta kwantar da kai bisa kirjin mijinta jikinta yayi sanyi.

Believe me Maarouf Hafsa ta gari ce, ba yau na santa ba. Amma ka fada min abinda zan kiyaye a kawancena da ita insha Allah zan kiyaye.

kinyi alkawari?

Wallahi nayi, in ma kace in rabu da ita kwata-kwata zan yi hakan amma zan kasance cikin kewar ta.

Murmushi yayi wato dai bazaki iya rabuwa da ita din ba kenan shine zaki yimin wayo, irin wayon ku na likitoci da kikayo course wajen su Turaki.

Murmushi tayi mai sauti ni kam na rasa me Baban nan nawa yake maka daka sako shi gaba, don baka san yadda yake son ka ba, ga yi maka campaign a fakaice, ga wanke laifin ka, ga-ga…… alherin Turaki mai yawa ne akan ka.

Dariya ta bashi sosai ya bubbugi bayanta kin ganki! To shikenan, albarkacin ki an daga kujerarsa daga yau daga matsayin commissioner zuwa na SSG. Kuma ke zakiyi masa wannan albishir din.Wata sumba da Amina tayi super ta mannawa Maarouf dinta,ta tabbatar masa tafi malamin nata godewa. Saboda kunyarta mai yawa ce,sau-tari sai ta kai zuciya nesa take iya kissing dinsa.

Bata bashi bashi damar yin commenting ba domin ta rufe bakinsa gabadaya da tausasan labbanta. Sai a washegari ne da yake cikin nutsuwar sa yayi mata conclusion na zancen Hafsa Datti. Yace ya amince suyi kawancen su amma, bai yarda ba bai amince ba,not in anyway, tayi zancen sa kowanne iri ne da Hafsa. Su cigaba da magance abinda ya shafe su a tsakaninsu yadda suka faro. Ko Goggo ta zama third-party. Amina ta amince da umarnin mijinta,ko dama can kullum cikin umarnin sa take. Zata iya sadaukar da komai akan Maarouf  Jikas. Wani kwayan mutum guda daya da ruhinta ke so, zuciyarta ke kauna, gangar jikinta ke bege.

Allah kuma ya dauko yaya bata ba tare da tsimi ko dabararta ba. Yaya kuwa zaayi bazata zamto mai biyayya ga umarninsa ba? Da son duk abinda yake so tana so ko bata so,in cewa yayi ta gutsuro masa naman jikinta, shell do so willingly, without feeling any hurt,balle wannan kankanuwar biyayya? Wadda ko da bai fada ba ai tanada hankalin kanta. A abubuwa da dama sunna da raayi daya.Itama ba mai raayin hakan bace. Bazata taba iyatona sirrin sa ga kowa ba koda kuwa ga GOGGON data haife ta. Don haka da gudu ta amince da sharadin sa akan alaqarta da Hafsa Datti.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 46Sanadin Kenan 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×