Skip to content
Part 40 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Sun mori (honey moon) na tsayin kwana bakwai yadda ya kamata a wannan hotel wanda babu na biyunshi a Nigeria. Sun kara fahimtar juna, so da kaunar junansu ya kara habaka da shaharar da a da, bai yi ba. Sun dinke zukatan junansu cikin na juna sun zama daya. Kowanne ya shiga tababar yadda zai rayu, rayuwa mai inganci ba tare da dan uwansa ba.

A Transcorp suka ajiye tarihin. A can suka baro shi kamar kar su baro, Ma’arouf Ji-kas ya yarda Allah ya sako Amina cikin rayuwarsa SANADIN tashi Ameenar ne don ta gyara ta, ta maye mashi gurbin Aisha, ta wanzar da farin ciki a rayuwarsa wanda ya rasa tun gushewar Aisha. Ta wanke bakin cikin Laila Ji-kas da yake kwana yana tashi da shi. Ta kawo sauyi mai albarka daga rayuwar kadaicin da ya tsinci kansa a ciki tun bayan rashin Aisha. Ita din ALHERI ce, kuma AMANA a gare shi (sunan wasu littattafan Takori.

Isowarsu gida ke da wuya tun kafin su isa dakin barcinsu wani mai share-share ya sanar da Ogan nasa, Anty Laila ta dawo.

Fuskarsa ba ta sauya ba, haka komai nasa bai canza ba. Amma Dr. Amina ta ji faduwar gaba matuka. Sai jin tausasan yatsun Ma’arouf ta yi cikin nata, ya rike ta gam ya ja ta sun fara taka matattakalar (upstairs) tare.

****

Laila na zaune cikin daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falon, ta dora kafa daya kan daya ta harde, ta ci ado da kayan Larabawa har ta gaji. Remote din talabijin ne a hannunta tana sauya tasoshi. Ta dago kai a yangace kamar yadda yake a al’adarta ta dubi masu shigowa.

Sosai ta saki baki tana kallonsu, Ma’arouf ba zai taba kama macen da ba tashi ba, Wannan na nufin…… likitar Ameena wannan ‘yar rainin hankalin ya aura? An tabbatar mata Ma’arouf ya yi aure tana Saudiyyah, amma ba ta taba kawo Amina ba ce. Ta dauka iyakarta kenan sun rabu tunda Ameena ta warke. To yaushe aka kulla soyayyar wadda har ta kai ga aure tana gidan bata sani ba??? Ta tambayi kanta, bata kuma samu amsa daga kowanne sashe na zuciyarta ba.

Har suka zauna a kujera guda hannunsu na cikin na juna, Amina dai a tsorace ta ke ganin kallon kura ta ga nama da Laila ke mata. ta kawo karfin zuciya ta sanya wa ranta, tana murmushi, ta ce,

“Anty Laila, ina wuni? An dawo lafiya?”

Shiru ta yi mata ba ta amsa ba, har yanzu ba ta dauke ido a kansu ba, irin kallon nan na kun ci AMANA TA.

“Wuce dakinki Amina ki huta, zan yi magana da ita”.

Amina ta mike ta nufi dakin nata. Ba ta kai ga isa ba ta ji an shako ta ta baya, an yi mata wani wawan naushi a wuya, an maka mata wani irin abu a tsakar kanta da ya fi kama da kofin gilashi. Ta yi gaba luuu! Ta fadi a kofar dakin nata, tana jin sanda Ma’arouf ya yi magana da karfin gaske da iyakacin sautinsa,

“Lailaaa! Kina hauka ne? Kisa? Wallahi in ta mutu a bakin aurenki!”.

Ya yi kokarin buga waya don kiran likita, amma ya kasa. Ya kuma kasa isa ga Aminan ya bata wani taimako saboda gigicewa. Hannunsa sai rawa yake yi, haka ilahirin jikinsa wayar na subucewa yana sake dauko ta. Ita kanta Laila ta dan tsorata da ganin yawan jinin Amina da ke malala a kasa daga tsakiyar kanta, sai mazari ta ke yi amma ta maze, yadda take jin zuciyarta zata iya kashe Aminan kamar yadda ya fada in yaso itama a kasheta.

Ya samu ya lalubo lambar Dr. Isma’el (personal doctor) dinsa, jikinsa na cigaba da mazari don kuwa Laila ta shammace shi, ko sanda tayi wuf ta mike bai ankara ba balle isar ta ga Amina kamar walkiya.

“…..Ka zo maza-maza har upstairs Isma’el…….”.

Babu tambayar ba’asi Dr. Isma’el ya amsa da; “Ga ni nan ranka ya dade”.

Ya isa inda Amina take a kwance a kofar dakinta magashiyyan ya ciccibe ta ya kwantar a doguwar kujerar falon, bai damu da jinin da ya bi ya bata masa jiki ba. Ya soma yi mata firfita da gefen babbar rigarsa da ya cire babu alamun numfashi a tare da ita. Bai kara bi ta kan Laila ba wadda ke tsaye a kansa tana kuka.

“Allah ya sa ban yi kisa ba zuciya ce, na shiga uku Ma’arouf ka yafe ni…”

Ko kallonta bai yi ba, firfita kawai yake wa Amina idanunsa sun kada sun yi jazur. A haka likitan ya iske su, bayan Ma’arouf ya ba da umarnin a shigo da shi.

Da kayan aikinsa yake tafe don haka a take ya fara bai wa Amina taimakon gaggawa, har ta farfado. Ya cire kwalbar data nitse cikin kanta yayi dressing din wajen da ke fidda jinin ya tsayar da gudunsa ya rufe da plasta. Ya dubi Ma’arouf da Laila mai kuka kashirban, Ma’arouf din ya ki ko kallonta hankalinsa da kulawarsa duk suna kan Ismael dake aiki kan Amina wadda ke kwance ido rufe. Nan ya gano bakin zaren, ya dubi Ma’arouf ya ce,

“Garin yaya? Ya ya haka your Excellency? Wane ne da wannan danyen aikin? Wannan kan dole sai an je asibiti an yi hotonsa don mai yiwuwa akwai (Internal injury) na kwalbar da nake addu’ar Allah ya sa bai taba kwakwalwarta ba”.

Laila ta kara gigicewa, daidai da karuwar fushin Ma’arouf a kanta, ya ce da Doctor din,

“Je ka ka zo da (nurses) ku tafi da ita a ba ta duk kulawar da ta dace”.

Cikin dan lokaci Dr. Isma’el ya yi waya asibitin cikin gidan, nurses biyu suka zo suka tafi da Amina. Aka barshi daga shi sai Laila a falon. Ya zauna cikin kujera ya tallabi fuskarsa da hannu bibbiyu cikin damuwa. Laila ta tsugunna a gabansa, ta kama kafafunsa tana kuka.

“Tunda ba ta mutu ba, don Allah kar ka sake ni, wallahi zuciya ce na tuba, zan zauna lafiya da ita insha Allahu”.

Bai saki fuskarsa ba har yanzu, haka fushinsa bai sauka ba. Da kyar ya yi mata magana cikin muryar bada umarni,

“Hada kayanki Akilu ya kai ki gida Ji-kas sai na neme ki”.

Laila ta rushe da kuka, “Na roke ka da Allah da manzonSa ka bar ni a dakina, in dai Amina ce na yi maka alkawarin za mu zauna lafiya”.

Zuciyarsa ta so ta fara sanyi, sabida irin kukan da ta ke yi mai nuna nadamarta a fili. Amma ya yi rantsuwa cikin zuciyarsa sai ta je gida ko da bai sake ta ba.

“Hakuri na daya ne Laila, ki je gida sai na neme ki, amma ban sake ki ba, in kuma ki ka kara yi min musu raina zai kara baci, shiga ki tattaro kayanki.”

Ba yadda ta iya, ta juya ta yi dakin nata tana share hawaye. Hankalinta a matukar tashe. Shi kuma ya kira Akilu a waya,

“Zo maza, za ka kai matar gidan nan Ji-kas”.

Ta gabansa Laila ta wuce ta yi lullubi da wadataccen mayafi, wanda a da ba ta amfani da irin shi sai raka-ni-gantali. Ta dube shi cikin ido da idanun neman afuwa, ya kauda kai don ba ya son ya ba wa tausayin da ke son rinjayar fushinsa dama ya yi tasiri.

Wannan karon ya yi aniyar daidaita mata sahu in har tana son ci gaba da zama da shi, to dole ta bar duk abin da ba ya so ta kuma zauna lafiya da zabin ransa. Ba ita dake cin alfarmar zabin iyaye ba.

Zaman hakurin da yake yi da ita inda tana da hankali adalci ne ya yi mata. Yaushe ta fara sonshi so na gaskiya da har ta san ta yi kishi a kansa? Kishin ma na jahilai da rashin hankali.

Bayan tafiyarta ya kasa zaune ya kasa tsaye, yana son jin halin da Amina ke ciki wayar Dr. Isma’el na kashe alamar yana bakin aiki. Shi ba abun ya fita da kansa ya je asibitin ba.

Ya daure ya shiga (master bedroom) dinsa ya yi wanka da alwala, ya yi sallah nafila ya roki Allah matsalar Amina ta zo da sauki.

Yana kan sallayar bai sauka ba bayan awa daya, sai ga kiran Dr. Isma’el. Da mugun sauri ya amsa wayar.

“Ya ya Isma’eel, is she o.k?”

“Eh, toh, she’s conscious now, amma mun samu internal injury, bayan na wajen, dole za’ayi minor surgery akwai bukatar ka sanya hannu, zan kawo maka takardun yanzu kayi signing.

Amma ranka ya dade ya kamata a dinga kula a kuma dinga tsawatarwa iyali idan sun aikata ba daidai ba irin wannan, this is sheer rudeness, don dai matsalar ta cikin gida ce, amma da ba za mu barta ta tsaya a haka ba”.

“Kada ka damu Isma’el, it’s o.k, za a kiyaye za’a dau mataki. Yanzu ina Aminan? Ya ya yanayin jikin nata?”

“Alhamdulillahi ta farfado, amma za mu rike ta har muyi aikin ya warke, bari in kawo takardun maza”.

Har Dr. Isma’el ya iso gumi kawai yake yi a zaune. Bai san yana son Amina har haka ba sai yanzu da take cikin wani hali da yake ji da zai yiwu da ya maido da ciwon jikinsa. Laila zata dandana kudarta yadda gobe ko da kyauta aka ce ta kwatanta rashin hankali irin wannan cikin gidannan bazata soma ba.

Ya yiwa Isma’el umarnin shigowa, ya kawo takardun har inda yake cikin girmamawa ya karba ya rattaba hannu. Mintuna talatin suka dauka suna zare kwalbar data nitse cikin kan Amina amma alhamdulillahi bai tabi kwakwalwar ta ba.

Karfe takwas na dare sukayi waya da Ismael ya tabbatar masa zai iya zuwa ya ganta yanzu. Asibitin nan cikin gidan gwamnati yake don haka akwai tsaro sosai.

Amina na kwance lamo a gado Ma’arouf ya murdo kofar ya shigo, idanunsu suka sarke dana juna hawaye ya cicciko idon Ameena. Ya karasa jikin gadon ya kama hannun ta ya ja farar kujera ya zauna a saitin kanta.

Zaiyi magana ta kai tafin hannunta ta rufe masa baki ta san hakuri ne zai bata akan laifin da ba nasa ba.

“Don Allah kada ka sake ta na ji sauki wallahi na ji sauki. Kaima ka yi laifi da tuntuni baka fada mata ba da bazata dauki al’amarin da zafi haka ba.”

Ido ya zuba mata ya kasa cewa komai, wace irin mutum ce Amina? Wace irin kyakkyawar zuciya gareta? Yake tambayar kansa.

“Me kike so yanzu?  Me zaki iya ci?” Ya kawar da maganar data yi masa don bashi da amsar da zai bata, babu bayanin da zai yi mata ta fahimci irin zaman auren da yake yi da Laila Jikas wanda babu emotion ko affection a cikin sa da har za’a zauna ana tattauna muhimman al’amura da suka shafi rayuwar juna, zaman auren kawai akeyi don ya zama dole. “Ba abinda nake so, Goggo kawai nake so a dauko min don Allah” ya dan fiddo ido damuwarsa ta karu “kina so a tayar mata da hankali Amina?” “Ba kankanin abu ke tada hankalin Goggo ba, tanada juriya, idan bata zo ba bazan iya cin komai ba”. Bai yi musu ba wannan karon, ya fiddo waya yana magana da daya daga cikin direbobinsa tunda Akilu ya tafi da  Laila Ji-kas.

Amina na ganin Goggo ta shigo sai kuka, Ma’arouf yayi kasa da kai ya russuna ya gaida Goggon ya fita, zuciyarsa cike da damuwa, kukan Amina na tada tsigogin jikinsa. Ga nauyin Hajiya Hawwa da yazo ya baibayeshi, a ce matarsa ce ta aikata wannan ta’addancin yana zaune ma ai sai a ga sakacinsa. Ba kuma yadda zaiyi ya hana Amina fadawa Goggonta tunda ta riga tazo.

Cikin nutsuwa Hajiya Hawwa ta zauna a kujerar da Ma’arouf ya tashi, ko hankalinta ya tashi babu alamun hakan akan kamilalliyar fuskarta. Ta kai hannu ta dafa kafadun Amina don an nade kan da bandeji, “yi hakuri ki gayamin me ya faru daku? Kun yi hatsari ne a hanyar Abujan?” Amina ta girgiza kai “Goggo ai na gaya miki, Anty Laila ce, kofin gilashi ta kwantsa mini a ka”. Goggo ta girgiza kai “babu mummunan rauni to?” “akwai goggo amma an cire” “kiyi hakuri nasan zai dauki mataki Hajiyarsa ma haka, Allah ya kiyaye gaba Allah ya baki lafiya. Tun yaushe rabon ki da abinci?” “Wallahi Goggo tun a Abuja don a jirgi ma ban ci komai ba. Ni sai da na ganki ma na ji yunwa”

Goggo tayi murmushi “bansan yaushe zaki girma ba Amina,  me kikeso ki ci?” “meat pie da cake da kunun ayarki” murmushi Goggo ta sake yi ta ciro wayarta ta kira Ilya ta gaya masa Amina na asibiti wai zata ci meat pie da cake, zobo da kunun Ayansu, ya jajanta ya kuma tabbatarwa Goggo yanzu zai kawo dama yana cikin gari.

Cikin dan lokaci Ilya ya kawo cikin bokiti, Amina ta shiga ci hannu baka hannu kwarya. Ya tambayi Goggo abinda ya faru ta sanar dashi. Ilya yana tsokanarta wai raguwa mai tsoron kishiya don me bata bude kwanji ta rama ba?” Amina bata kula shi ba, a ranta fadi take baka san Anty Laila ba, labarinta kake ji ina ni ina gwada ‘yar kashi da ita ta karairayani a banza. Sai da ta koshi ta rufe ragowar tace.

“Goggo na ragewa Baban Ameena nasan shima tunda muka dawo bai ci komai ba” Goggo tace “to Amina!” sai kuma taji kunya ta rufe fuska tana dariya. Goggo tace “ah toh mutum yayi rashin kunyarsa ya nade kayarsa shikadai ba!”

Kwanan Goggo uku a asibitin gidan gwamnati tana jinyar Amina, ka’ida ne Ma’arouf ya zo duba jikin nata sau uku a rana, da safe kafin ya shiga ofis, da rana in ya dawo da kuma da daddare kafin ya shiga barci, tun Goggo Hauwa na jin kunyar surukin nata har ta sake dashi, ta lura yanada saukin kai matuka kuma bai aje Amina nan kusa a zuciyarsa ba, don haka bata jure ganin su tare yana shigowa zasu gaisa ta nemi wurin fakewa don Ma’arouf ba ya jin kunyar kama Amina a gabanta da nuna mata tsantsar kulawa mai nuna soyayyar sa gareta ba kadan bace.

Goggo ta kasance koyaushe cikin godewa Allah akan hakan,  ta kuma amince wani jinkirin alheri ne, inta tuno yadda ta matsawa amina akan aure ashe kyakkyawan rabon ta na gaba. Goggo kan daga hannu ta godewa Ubangijin ta.

<< Sanadin Kenan 38Sanadin Kenan 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×