LITTAFI NA HUDU
Su Jalan sunyi mamakin daular da suka ga ‘yar uwarsu Hauwa a ciki. Don a saninsu mijin ta bashi da komai har ya rasu, bayan gidan da suke ciki.Da mahaifiyarta ta tambaye ta murmushi ta yi, tace”SANADIN ilmin Amina ne.”
Ranar litinin ita ce ranar da Amina za ta tare a gidan mijinta.
Kamin ranar ta kimtsa komai nata. Har Goggo na yi mata fadan ta ajiye tsofaffin kayan sawarta, ta fiya tsumulmula. Amina tayi murmushi ta ce,
“Goggo ki bar min su. Akowanne canjin rayuwa da na samu ina son in ke sanyayadda nake a baya in memory, kada in shagala, in manta da yadda na taso.”
Goggo ta tabe baki, “Ai falsafa nan ta ganki ta barki.”
Manyan motoci biyar Akilu ya kawo Shira, aka kwaso gaba daya dangin Amina manya da yara da matan Baffanninta kai har da wadanda ba dangin Iya babu na Baba aka dura su sai gidan Gwamnati.
Su Aisata kuwa motoci ne na alfarma daga maigirma Gwamna guda uku don su kadai jamaar Sierraleone.
A cikin gari kuwa dukkan abokan arzikin Goggo, Inna Zulai ita ce kan gaba, su Talatu masu aikin Goggo abu nasu maganin a kwabe su. Makotan Goggo na unguwar da suka baro da na sabuwar unguwa duk haka aka kwashe su Government House.
Sai a wannan lokacin mutane da yawa suka san waye ya auri Dr. Amina. Masu mamaki sun yi, masu gulma sun yi amma masu fatan alkhairi sun fi yawa kasancewar mahaifiyarta mutum ce wadda ta ke zaune lafiya da kowa, kuma ma’abociyar alheri, masoyanta sun rinjayi makiyanta.
Aka bude wa duka ‘yan kawo amaryar guest house aka ce ango ya ce su zauna su huta har tsayin kwana uku. Murna a gurin ‘yan Shira abin sai ya ba ka dariya. Shi kuwa ya sa aka yi ta cika su da liyafa iri-iri, sai da ya kure hadamar kowa, abinci suna gani amma sun kasa ci saboda koshi. Sun manta da wata Amina wadda aka kai ‘upstairs’ shagalinsu kawai suke yi.
Yan Sierraleone kuwa downstairs aka bude musu tareda alummar Hajiyan Jikas. Koda suka sada Amina da dakin aurenta basu ma zauna sun kwana ba suka koma gidan Goggo a motocin da suka kawo su, bayan an gabatar dasu ga Hajiyan Ji-kas.
Anty Laila ba ta kasar, ta je umrah, wannan karon da gaske Saudiyyan ta je ba Dubai bamusamman don ta yi addu’a Allahya ba ta haihuwa tunda likitoci sun kasa tsinana mata komai a Dubai, sai cin kudinta a banza, ta ga gara ta koma ga Allah don ta ji rade-radin Ma’arouf yana neman aure. Hankalinta in yayi dubunnai to ya tashi, sai dai duk kwakkwafinta an kasa gano mata wa zai aura saboda ba’a sa a (media) ba, yau satinta daya a can kuma sati biyu za ta yi.
Hajiyan Ji-kas da jama’arta da suka karbi amarya daga hannun danginta na uwa da uba suna nan a downstairs, washegari za su koma Ji-kas, Hajiya kuma Lagos za ta wuce.
Amina tana kusa da Hajiya lullube cikin laffaya, ta ki yarda ta zauna a dakinta da ke upstairs,self-content ne kamar duka dakunan wanda ke kallon na mai gidan, na Laila kuma yana nesa da nata sai dai duk cikin tafkeken falo daya suke.
Hajiya da ‘yan uwanta da kishiyarta Lami hira suke, har dare ya soma yi. Hajiya ta lura Amina ta fara gyangyadi, ga dare ya yi wajen karfe goma sha daya na dare, ta ce,
“Tashi haka Amina, mu je in raka ki dakinki dare ya yi.”
Amina ta turo baki cikin shagwaba, yadda ta ke yi wa Goggonta don ba ta bambanta Hajiya da Goggo, tana fadin,
“Don Allah Hajiya ki bar ni in kwana cikin mutane. Ni wallahi tsoro nake ji gidan yana da girma sosai, na yi miki alkawarin gobe zan koma.”
Hajiya ta rasa yadda za ta yi da ita don ba ta so ta takura mata ta koma kukan nan da ta yi musu sanda suka banbaro ta daga jikin Goggonta. Kafin ta bata amsa ma Amina ta gyara waje a gadon ta yi kwanciyarta, barci ya sure ta.
*****
Sanda angon ya shigo gidan, karfe goma sha biyu na dare ya yi. Wajen Hajiya ya fara dosa da takunsa mara amo, wanda yake yi cikin nutsuwa, ya shiga ne don ya yi mata sai da safe ya wuce wurin amarya.
Duk jama’ar dakin sun yi bacci, wasu a gado wasu a kasa, Hajiya ce kadai ido biyu, makure ta ke a can kusurwar dakin kan sallaya tana lazimi, ba komai Hajiya Saude ke roka ba daga wurin Ubangijinta face nema wa danta Ma’arouf dacewa a cikin wannan auren da zuri’a dayyiba, Allah ya kare mata shi daga duk mai nufinsa da sharri, ya ba shi alherin da ke tare da Amina ya nesanta shi daga rashin alhairanta. Ya sanya ta zamo marufar asirinsa kamar Aisha, ya kade dukkannin fitintinu daga cikin aurensu.
Jin murda kofarsa da sallamarsa ya sanya ta yi fatiha ta shafa. Bai shigo ba saboda mutane, daga bakin kofar ya tsaya rike da marikin kofar. Hajiya ta amsa sallamarsa fuskarta cike da yalwa. Ya ce,
“Hajiya ba ki kwanta ba?”
“Yanzu dai nake shiri, don gobe sammako za mu yi, zan je ganin Ameena a makaranta (an kai Ameena wata makarantar kwana ta yara ‘yan firamare a Lagos) sannan na wuce Jikas.”
“Ai booking din naki na rana ne Hajiya, ba sai kin yi sammako ba.”
“A’ah, gara dai in yin don ta ji dadi.”
Ya juya zai fita,
“Allah ya ba mu alkhairi Hajiya.”
“Amin. Ga Aminar a nan ma bacci ya dauke ta.”
Cak! ya tsaya kamar bai ji daidai ba. Hajiya ta yi murmushi.
“Na yi-na yi ta zauna a dakinta ta ki, wai tsoro take ji, abu kuma da gajiya ba ta san sanda bacci ya dauke ta ba.”
Saura kadan ya ce,
Taso ta Hajiya, wannan wane irin abu ne? An taba yin haka?Amarya a ranar aurenta ta kwana da ‘yan biki? To ni kuma fa? Hajiya kin daina sona da alama!”
Dariya ta kusa kwace wa Hajiya Saude ganin ya kasa tafiya, ya kuma kasa magana. Sannan ya kasa juyowa. Ta yi niyyar tashinta wata zuciyar ta ce, ‘kyale ta yau daya dai ta huta da gajiyar biki, yadda Maarouf yake rawar kafar nan da kyar zai barta ta runtsa, gobe mu bar muku gidanku ku karata.’
“Ka ce sai da safe kuma ka tsaya, ko in taso ta ne?”
Ya yi gaba yana fadin, “A’ah, Allah ya ba mu alkhairi.”
Hajiya ta ce, “Amin”
Washegari da safe su Hajiya suka yi shiri suka wuce. Bayan ta raka Amina dakinta ta yi mata nasihohi a kan ta zauna lafiya da Laila, ta yi hakuri da ita kamar zamansu na baya. Ta yi musu addu’a suka tafi.
Gida ya saura ‘yan Shira a sassan baki suna ta sha’aninsu. Ba wanda ya damu da ya zo inda amaryar ta ke ban da Ramma matar Baffa Bilya, ita kam ta zo taya Amina hira.
His Excellency bai shigo gidan ba saboda ayyuka masu yawa da suka tsare shi a office. Tunda aka fara hidimar auren bai dauki hutu ba sai yau. Wajejen karfe uku na yamma ya samu ya kira Amina a waya.
“Shirya kayanki da abubuwan amfaninki da za su yi miki kwana bakwai, za mu tafi Abuja.”
Amina ta ajiye wayarta a gefe, twna mita cikin ranta, wace irin tafiya ce saboda Allah daga kawo ta jiya ko ‘yan biki ba su watse ba? Sai kuma su nemesu a gidan su rasa? Abin da ta ke fadi a ranta kenan. Bata san shi yan bikin yakeson gujewa ba. Sun isheshi sun dameshi, yana son samun privacy hakannan da matarsa. Rabon da ya ganta tun kafin daurin aure. Hakan kuma bai hana ta bin umarninsa ba, ta samu babbar jaka ta shirya duk abin da ta san za ta bukata. Ya fi karfin ya yi hukunci, ta ce, a’ah! Ya fi karfin komai a gare ta!!
Ya sake kiranta a karo na biyu bayan ta idar da sallar la’asar. A gurguje yake fadin,
“Ki fito, direbana yana bakin falon karshe yana jiranki, zai taho da ke filin jirgi. Ba za mu hadu ba sai a jirgi, ina tare da jama’a sosai. Ina rokon kada hakan ya bata ranki, sai kin yi hakuri Amina, yanayin rayuwar tawa kenan. Are you o.k?”
Ta gyada kai kamar yana ganinta.
“I’m o.k, zan fito yanzu.”
Da kanta ta turo jakar tata waje, bayan ta nade jikinta cikin wata lallausar laffaya fara mai ratsin shudi mai hasken sararin samaniya. Ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin kamshi. Kamin ta isa downstairs wani ma’aikacin gidan ya zo don fita da jakarta, direban na jiransu ya karbi jakar ya sanya a bayan motar kirar ‘porsche’ ta shiga suka kama hanya tare da security dinta mace a gidan gaban motar.
A takaice Ma’arouf da Amina, ba su hadu ba sai a first class seats na jirgin Azman mai zuwa Abuja daga Bauchi.
Kar ki so ki tona zuciyar kowannensu a yayin da suka yi arba da juna domin ba za ki iya kididdige adadin farin cikin da ke cikinta ba.A lokacin da Amina ta zauna a kujerar dake daf dataangon nata. Karo na farko a tarihin rayuwarsu da ya kama hannunta ya rike cikin nasa.
Ji tayi tamkar magnet ya manne hanuwan nasu. Kanta ta sunkuyar,ta kasa hada ido da shi, tana mai karbar sababbin sakonnin farin-cikin dake shigowa zuciyarta, ba ta iya ta dube shi ba, amma wata rahma taji ta sauka aruhin ta.
Shi kuwa ajiyar zuciya ya ke saukewa da sauri-da-sauri, cikin ransa yana godiya ga mai tsarkin mulki, da ya nuna masa wannan ranar, wanda ya mallaka masaAminar nan da ya dadeyana so da kauna lokaci mai tsawo ba don isarsa ko mulkinsa ba.
Sun sauka a hotel din TRANSCORP HILTON da misalin karfe takwas na daren ranar. Gajiya ba ta bar Amina ta tsinana komai ba. Ta yi alwala ta yi sallar magriba da isha da ta riske su a hanya, a nan kan sallayar barci mai nauyi ya dauke ta.
NYC story