Ta bude ido ne ta ganta tsakiyar wani ni'imtaccen gado, rufe ruf da lallausar (duvet).Da ta kara bude idon, ta juya sosai, a can gefe bisa wata yar kujera da dan tebir a gaban kujerar Ma'arouf ne yake cin abinci. Sanye yake da karamar t/shirt deep-bluesamfurin DKNY da bakin dogon wando samfurin Armani. Sosai yayi mata kyau irin na ranar nan data ganshi cikin kananan kaya, yau fiye da waccan ranar saboda harda hasken amarci tareda shi.Yayi wani fresh dashi (wanke hannu ka taba) inji zuciyar Amina. Suka kalli juna na 'yan sakanni tana. . .
Shukran jazeelan