Wata Sabuwa
Bayan Little ta koma makaranta da sati biyu aka bugowa Babanta waya daga ofishin shugabar makarantarsu cewa ba ta da lafiya. A take ya tsallake abin da ke gabansa ya shirya musu tafiya Lagos shi da Amina. A Clinic din makarantar suka riske ta a kwance ana kula da ita. Ya karasa jikin gadon jikin sa na kyarma ya dafa kanta ya tambaye ta me ke damunta?
Cikin sassanyar muryarta take masa bayani.
Daddy watarana in na zauna ba na iya tashi tsaye sai an daga ni.
Hankalin Amina da na Maarouf ya yi mummunan tashi. . .