Skip to content
Part 48 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Da safe kafin ya fita suna karya kumallo, a bisa dining-table mara tsayisosaisuke zaune na zallar gilashi (raw glass) kowanne kujerarsa daban tana fuskantar ta dan uwansa, amma can a karkashin table din kafafunsu harde suke dana juna.Ya dauki wayarsa dake gefe ya kira Turaki. Amina na jin sanda Dr. Turaki yace breakfast nakeyi Yaa Maulaya yanzu zan fito, ai takwas din bata idasa cika ba ni bani na kira ka ba, ina sane sai 8:30 zamu fito. yar ka ke son magana da kai Ya mikawa Amina.

Murmushi tayi sosai ta karba Assalamu Alaykum my humble consultant amin waalaikumus-salam a daughter like no other, mun tashi lafiya? sai godiyar Allah! Yaa Maulaya ne yace inyi albishir da sabuwar kujera ta SSG. Zaayi taron kaddamar da kujerar rana ita yau. Allah ya taya ku riko baki daya. Bata tsaya taji reaction dinsa ba ta mikawa Maarouf wayar. Tana ji Maarouf na cewa to menene abin kuka?  You deserve it ne. What are friends for? Beside, kai ne SANADIN haduwa ta da alkahairin dana ke tare dashi a yanzu. Kai ka tsaya da hikimarka da zuciyarka daya saida na mallake ta, na samu kwanciyar hankali kuma kuka samu. Zan iya hakura da kujerar baki daya na bar maka na zama mataimakin ka in ana yin hakan. Im rest assured zaka shugabanci alumma da gaskiya da amana. Don haka naga ba kujerar data kamace ka sai ta SSG. Daga ni har ita bamu cancanci godiyar ka ba.

Ya kashe wayar sa.

Da wannan Amina da Hafsa suka cigaba da zumuncin su ba dare ba rana, zumunci mai tsafta da sanin ciwon kai. Amina na lallaba Hafsa ta koma makaranta ta yo Doctorate Degree ranar da suka dawo gida Nigeria zaiyi mata amfani. Hafsa na kara koyar da ita dabarun sace zuciyar miji ta hanyoyi masu kyau da maana. Ta bar ganin Maarouf baida raayin aure-aure komai dalili takeyi don haka ta tsaya ta kafa kanta yadda ya kamata yadda ko wata ta shigo saidai ta biyo bayanta.

Dr. Zainab Turaki ta kira Amina karo na farko da suka taba gaisawa tayi mata godiya akan kujerar Dr. Turaki. Ta bawa manyan yayanta maza biyu Aadil da Aabid wayar sunyi mata godiya. Amina taji dadi sosai, da wannan sabo ya fara shiga tsakaninsu suke gaisawa sosai don Zainab ta iya takunta bata zaqewa, respect ne da girmamawa tsakaninta da Amina kawai.

Anyi liyafar kaddamar da kujerar SSG, taro na farko na siyasa da Amina ta halarta, suka dumfaro dakin taron itada maigidan ta His Excellency Maarouf Habibu Ji-kas. Tana sanye da kyakkyawar doguwar riga ruwan makuba kirar Dammam ta zagaye fuskarta da mayafin abayar. Takalmin kafarta mai tsayi sosai, ta kama hannun Maarouf ta rike na rashin sabo. Kowa ya mike tsaye don nuna girmamawa yayin da suka shigo dakin taron na (                           ) saida suka zauna sannan kowa ya zauna. Ga Gwamnan da maidakinsa Dr. Amina nanike dashi, ga mataimakinsa Prof. Bugaje da mai dakinsa Zarah, sannan maigirma SSG da mai dakinsa Dr. Zainab da yaran su biyu. A haka aka fara gudanar da liyafar yadda aka tsara bayan mai gabatarwa ya gabatar da abinda ya tara su.

Anyi vedio anyi hotuna iri-iri, yan jarida sun samu babban (cover story) yau kowa ya ga matar Ji-kas da yake boyewa ba Laila Ji-kas ba. Kowa kuma ya bude baki sai masha-Allah. A haka taron ya tashi.

Litinin na zagayowa Dr. Usman Turaki ya shiga sabon ofishinsa. Suka cigaba da gudanar da administration dinsu cikin ilmi da sanin makamar mulki. Talakawa na gamsuwa domin babu handama da cikin mulkinsu sai tsananin jin kai ga alummar su da bullo da hanyoyin kyautata musu. Kullum tunanin su shine, ta yaya zasu kyautata rayuwar alummar jihar su a fannonin rayuwa daban-daban? Ta yaya zasu ciyar da matasa gaba don sune shuwagabannin gobe. Ta yaya alummar karkara zasuji dadin rayuwarsu acan inda suke ba tareda gudowa maraya ba? Ta yaya zaa inganta lafiyar kananan yara daga ciwuwwukan zamani da suka addabe su? Ta yaya zaa samar da ingantattun mgunguna kyauta ga asibitocin gwamnati? Ta yaya malamin makaranta zaiji dadi ya san babu career mai daraja da kima irin tasa? Ta yaya? Ta yaya? Ta yaya Bauchi zata kere sauran jihohin arewacin Nigeria saanninta a fannonin ilmi, kiwon lafiya, infrastructure, aikin yi (employment) sanaoin dogara da kaida sauran alamuran cigaban rayuwa.

Sunan Jikas na kara yin fice a tsakanin gwamnonin Nigeria yan uwansa. He is  ranked asthe best governor inthe North on initiating stabilisation and developmentdaga shugaban kasa na lokacin wanda suke karkashin jamiyya daya.

Anyi wannan taron karramawar a birnin tarayya Abuja inda shugaban kasa ya karrama shi, yayi kira ga gwamnonin arewa dana kudu yan jamiyyarsu (Northern People Congress) da aka fi sani da (NPC)kan suyi koyi dashi a hadu a ciyar da Nigeria gaba, jamiyyar su ta kara karbuwa a wurin alumma duk da cewa itace kan gaba.

Amina ta halarci wannan taron karramawar, karkashin rakiyar Hafsa da mai gidanta Mahmoud wadanda suka kawo mata ziyara daidai lokacin daga birnin Belarus din kasar Russia.Tana gefen damansa inda duk ya sanya kafa nan take mayar da tata. Ta shiga cikin jerin matan gwamnonin Nigeria dake karkashin (Northern People Congress). Dukkansu kuma tafi su zati da ilhama wanda tsarkin riko da addini ke haifarwa mai shi. Sannan kuma jikinta a lullube cikin abayat kirar Oman kai kace daga can tazo ba don kalar fatar jikinta ba.

Lokacin da Ilya ya murdo wa Goggo da Kaka abinda ke faruwa a Birnin Tarayya daidai wannan lokacin (live) a makekiyar plasma din falon Goggon, Goggo Hauwa ta gane Aminanta ce can kusa da matar shugaban kasa, ga Maarouf kamar ya maida ita ciki don kulawa, ya kasa boyewa duniya soyayyar da yake yi mata sabida tsohon cikin dake tareda ita, sai tasa kuka tana yi tana karawa tana yiwa Allah godiya.Kaka da Ilya na rarrashin ta. Ilya na fadin; dariya ai zakiyi Goggo ba kuka ba, kece SANADI. Shi kansa Ilyafarin-ciki kamar yayi yaya. A ganin Hajiya Hawwa, wani farin cikin yafi gaban ayi masa murmushi ko dariya, sai dai kukan. …..Alhamdulillah Alaa niimatihi. Shine abinda Goggo ke ambato har ba adadi.

Waiwaye

Laila ta cika iddarta, ba da jimawa ba zawarawa suka soma damun Dagaci da aike, ciki kuwa har da tsohon (fiance) dinta Mahdi maaikaci a gidan rediyon Jigawa. Dagaci ya zaunar da ita a wani marece ita da mahaifiyarta, ya ce.

Laila, yau wata uku kenan da gama iddarki, babu Maarouf babu aikensa, ga manema Allah ya ba ki tun gama iddarki, don haka na ba ki sati biyu ki fidda gwani a cikinsu, in kuma za ki bi shawarata to ki zabi Mahdi, da sabon gini gwanda yabe.

An sanshi, an san asalinsa, ke kika jawo ya janye auren ki a wancan lokacin, amma ya rage naki. Ni dai na ba ki sati biyu ki kawo min mijin aure cikin mutum hudun nan da suka addabe ni.

Kin san ni sarai bana son rainin hankali, ba don addini ne ya ba ki wannan yancin ba da sai dai ki ji na daura miki aure.

Laila na share hawaye ta tashi ta bar wajen, mahaifiyarta ta yi tsaki ta ce,

Halin mutum ya ja masa ya ishi mutane da koke-koke. Amma abin ki da mahaifiya, can cikin zuciyarta tausayin ta take ji, koda bata amfanuwa da komai a zaman Laila gidan Jikas,tana yi mata fatan komawa.

Mahdi tsohon saurayin Laila ne, har an sa musu ranar aure, ya aiko ya karbi kayanshi ya ce ya fasa, a sabili da har lokacin da aka yi musu baikon Laila ba ta daina sauraron sauran samarinta ba, shi kuma ga shi da kishi, ya yi ya yi ta bari ta ki, shi ya sa ya aiko ya ce ya fasa, ya karbi kayansa.

Iyayenta duka a lokacin babu wanda ya ga laifinsa don su ma shaida ne, sun kuma tsawatar mata a lokacin ta ki ji sabida giggiwarta. Don haka yanzu da ya dawo ya ce zai aure ta a bazawararta shi ko auren fari bai yi ba, duk suka hadu suka yi naam da shi. Amma har kwanakin da Baban ya diba mata suka cika Laila ta ki cewa uffan. Har kullum tunaninta na ba ta cewa, Maarouf zai dawo gare ta ko ba dade ko ba-jima.

To amma haka za ta yi ta zama tana jiran tsammanin warabbuka? (inji Mairon ABARI YA HUCE) Don haka ta yanke wa zuciyarta zuwa kai tsaye har inda Maarouf yake ta roke shi gafara, ta gaya masa ta yi nadama za ta rayu da shi da duk abin da ya yi mata umarni, yake kuma son ya rayu tare da shi. Don ta lura Hajiya Saude a wannan karon duk kawaicinta sai abin da Dan nata yake so za ta bi.

Ta yi shiri tsaf ta ce da mahaifiyarta za ta je Gwaram wajen wata tsohuwar aminiyarta, Innar ba ta hana ta ba, don ta san yadda suke da Hannatun. Amma data samu rayuwa yadda take so ai watsar da Hannatun tayi,Lailah kenan.

Tana zuwa tasha ta yi shatar karamar mota har Bauchi don bata son bata lokaci, tasan lokacin da yake dawowa daga ofis zata isa in a karamar motarta ne da yake akwai isassun kudi a tareda ita.

Sojojin da ke gadin gidan gwamnatin duk sun san fuskar Laila a matsayin matar mai girma gwamna, babu kuma wanda ya san ya sake ta a cikinsu sun dauka tafiya tayi kamar yadda ta saba duk da cewa wannan karon ta dade fiyeda tsammani, ko kuma sun samu sabani ne a dalilin sabon auren da yayi, don haka sun yi mamakin ganin a yadda ta zo yau da motar da ta kawo ta, sai suka ki yarda su barta ta shiga, suka ce ta jira sai sun yi bincike tukunna.

Waya suka yi ta bugawa har suka samu yin magana da Amina. Suka fada mata ko wace ce ta zo, kuma wai tana son a barta ta shigo. Amina ta yi musu iznin su barta ta shigo su kawo ta har downstairs.

A dakin Amina na da aka sauki Laila. Ta zuba uban tagumi, ta tsura wa hoton Maarouf da Amina da yarsu Ameena ido, suna manne da juna sun yi kyau, sun yi kyan har sun gaji. Katon hoto ne da ya kusan cinye bango guda, sun dauke shi ne a hotel dinsu na birnin Jeddah bayan Amina ta samu lafiyar kafafunta a karo na biyu.

“Duniya juyi”

Laila ta ce a zuciyarta, da ta tuna yadda ta ke zuba mulki a gidan nan rana daya duniya ta yi mata gwatson mage. Amina ta hambare gwamnatinta, ta maida ta kauye.

Tsanar Amina ta kara ninkuwa a zuciyar Laila, ji ta ke da da hali da ta danne ta da filo ta mutu ta huta. Amma ta yi amanna da cewa in har tana son ci gaba da zama da Maarouf dole ta koyi kissa wadda ada bata iya ba, take abubuwanta keke-da-keke, dole ta yakice wa kanta kishin Amina, ko ta ki ko ta so. Ta tusawa ranta kaunar wannan gawa ta ki ramin yar tasa.

Ta nisa, ta ja dogon numfashi, daidai lokacin da mai aiki ta shigo da trolleydin abincin rana, ta jere mata su a diningta gaishe ta ta fita. Babu wani girmamawa ko jin tsoro irin yadda suke mata a baya, kamar ma ba su ji dadin ganinta ba, sun tuno yadda ta ke cin zarafinsu ne ga shi yau ita da su an zama daya.

Sai da umarni za a ga uwargidan gwamna mai mutumta su da karrama su. Har gara ma su, sun fi ta tsafta da kyan gani a yadda ta koma din nan.

<< Sanadin Kenan 47           Sanadin Kenan 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.