Maarouf ya fito daga wanka, bayan shigowarsa cin abincin rana.Amina na jiransa a gefen gado ta mike tana tsane masa jiki da karamin towel, ta fiddo masa kayan da zai sanya bayan ta feshe su da turarensa.
Dawowarsa kenan daga ofis ya shiga wankan ya fito. Sai da ta gama taimaka masa ya shirya ya janyo ta jikinsa yana fada mata, I have a green great giant surprise for you. Ki shirya wani kauye za mu je.
Ta kwantar da kai a kirjinsa tana shakar kamshinbath-gel din da yayi wanka dashi,sannan ta ce, Kana da baki your excellency, ka fara (attending) dinsu sannan mu tafi.
Ya dago fuskarta da tafukan hannayensa biyu ya soma (kissing) dinta lightly cikin wata irin siga har sai da dukkaninsu suka soma fitanutsuwarsu, sannan Amina ta yi karfin halin janyewa ta ce,
Da gaske kana da baki, I would like you to attend to them first, sai mu je duk inda za mu.
Harararta ya yi, sannan yayi tsaki yana saka rigarsa
Wadanne irin baki ne zan je inda suke alhalin ban san ko su waye ba?
Ka yi hakuri dai ka je, ka sani ba zan kawo wadanda za su cuce ka har sassan nan ba, haka (securities) din da ke cike da gidan nan, don Allah ka je.
Da mamakinta ya ce, Suna ina? Ai sai ki wuce mu je tare in dodanni ne su fara cinye ki, haka kawai za ki tura ni wajen wadanda ban sani ba, ban san me ya kawo su ba?
Dariya Amina ta yi ta yi gaba ta zura takalminta marar tsayin dunduniya,
Na yarda, wuce mu je. Ni a gaba kai a baya.
Har ya zauna a kan kujerar hutawar da Amina ta fiya zama a kai lokacin aikinta a gidan bai gane Lailah ba, wadda kanta ke sunkuye. A sabili da abubuwa da yawa ya kasa gane ta. Na farko dai ta yi duhu tunda babu mayukan nan masu tsada na shafe-shafe. Na biyu ta yi lullubi wanda a da ba ta yi, sannan sitturun jikinta duk sun kode. Yana zama Amina ta kama hanyar fita, amma sai ta ji ya riko hannunta ta baya.
Juyowa ta yi ta dube shi da idanuwan nan nata masu kama da zaiba don sheki da kyalli, ta girgiza masa kai alamar ya barta ta tafi. Ita ma tata zuciyar fal da wani irin kishi da bata san tana da shi ba, jin ta tayi ta rikide kamar ba ita batamkar wata mai (multi-personality disorder)amma ta yi kokarin hadiye shi. Ta yi magana ba tareda ta yarda sun hada idanu ba.
Anty Laila ce ta zo ganinka.
Da haka ta kwace hannunta ta fice.
Laila ta sauko daga kan kujera ta rarrafo gabansa ta zube ta rushe da wani irin kuka.
Mikewa tsaye ya yi da hanzari.
Zan fita in zuwa ki ka yi ki tada min hankali. Me aka yi? Haka kawai ki zo min gida ki rusa kuka bayan ba wanda ya mutu cikin gidan?
Laila ta tabbatar in ya fita kyakkyawar damar da ta samu ta ganinsa ta kubuce mata, don ba ta isa ta ganshi a ofis ba ko wani waje, ta yi saurin kama kafarsa ta rike ta soma jero masa ban hakuri masu nuna tsantsar nadamarta.
Tana rokonsa ya yi mata alfarma cikin irin dimbin alfarmominsa ga alumma ya maida ita dakinta, ta yi alkawarin zai same ta mai biyayya a gare shi da zama lafiya da abokiyar zamanta, da kula da yar sa, da guje wa duk abin da ya furta ba ya so.
Sai da ta dasa aya ya janye kafarsa ya koma gefe ya zauna. Ya sarke hannayensa cikin na juna ya tallafi habar sa dasu. Ya dube ta sosai tana faman share ruwan idanunta. A nitse ya soma yi mata magana irin wadda bai taba gaya mata ba, ba ta kuma taba zaton yana kunshe da su a zuciyarsa ba.
Ta ya ya zan iya kuma ci gaba da zama da ke Laila? Ba kya girmama mahaifiya ta, ba ki damu da ita ba, ba kya kaunar abin da na haifa ko da da tausayi ne, ba kya tausaya min ba kya bani hakkin aure yadda ya kamata alhalin kinsan banida wata matar bayan ke kuma ni ba mazinaci bane, ba kya mutunta aurenki harkar neman kudi kawai ki ka sa a gaba.
Idan na ce ba na son abu ke kuma a lokacin za ki nuna min yanzu ki ka fara sonsa, kin maida ni bankin karbar kudi ba mijin aure ba. Tunda na aure ki ba ki taba girka min abin da zan ci da hannunki, ba ki taba kula da alamarina ba sai alamuran kawaye da buga-bugar karbar kudin siyasa ne kawai a gabanki. Na bi kowacce hanya don in zauna lafiya da ke na kasa billewa.
Na yi aure don in samu nutsuwa da karin zuria kin nuna ke mai iya aikata kisan gilla ce a kan hakan. Ta ina zaman aure zai ci gaba da irin wannan matar a ganinki Lailah?
Ki yi hakuri ki rungumi kaddarar da Allah ya rubuto mana, ta cewa za mu rayu tare na wucin gadi ne amma kowannenmu da tabbataccen abokin rayuwarsa wanda zai samu nutsuwa a tare da shi.
Na yi alkawarin zan yi muku komai na rayuwa ke da mijin da Allah ya ba ki, amma aure a tsakaninmu ya kare. Don ba zan so in tashi a ranar lahira da shanyayyen barin jiki ba na rashin yin adalci a tsakaninki da matata. Laila Im sorry, ki duba (account) dinki zuwa gobe za ki tadda sakona. Na barki lafiya.
Ya fice da hanzari ya bar Laila durkushe tana gursheken kuka. Baya so ya bar tausayin da ya tsirga a zuciyarsa ya yi tasiri. A ganin sa hakan da ya yi shi ne daidai, kuma shi ya fi dacewa da rayuwar kowannensu. Laila ba kaunarsa ta ke ba, kudinsa da kyale-kyalen rayuwar da ke tare da shi ta ke hange. Ya yarda da hakan, yana so ita ma ta yarda.
Ya yi alkawarin ba ta su (kudi da kyale-kyalen) amma ban da Maarouf da gangar jikinsa.
Haka Laila ta baro gidan gwamnati wutsiya a zage amma zuciyarta a dake. Ta tabbata ta bar gidan da mai shi har abada. Ta auna kalamansa a sikeli na hankali da tunani babu wanda ba ta amince gaskiya ya fada ba. Abu daya ne ba ta amince ba da Maarouf ya ce ba ta sonsa, kudinsa ta ke so. Ta amince farkon zuwansa rayuwarta da gaske kudin ta ke so, amma ban da yanzu. Ita kanta ba ta san hakan ba sai da ya bar rayuwarta kwata-kwata.
Ta amince ta hakura da Maarouf har abada, za ta je ta gina sabuwar rayuwa ta manta da shi da duk abin da ya shafe shi, tunda ba shi ne autan maza ba.
A washegarin ranar ta samu (alert) na zunzurutun kudi naira miliyan goma shha biyar cikin asusunta. Amma ga mamakinta ta kasa yin farin ciki da su. Yanzu ne ta gane cewa, SO YA FI KUDI, amma tata soyayyar ta zo (at a wrong time). Da a ce ta san (account number) dinsa mayar masa da su za ta yi.
A ranar ta tabbatar wa mahaifinta ta zabi Mahdi a matsayin mijin aure. Ta yi aniyar gyara zuciyarta ta koyi yin komai saboda Allah, ta daura aniyar yin amfani da damarta a lokacin da ta zo mata ba za ta kara wasa da ita ba, ta koyi girmama iyayen miji da yan uwanta da duk dan Adam din da rayuwa ta hada su tare. Za ta koyi daukar duniya da sauki ta rage (high taste) domin ba ya amfanar da kai komai. Ubangiji ya dankwafar da shaidan ne saboda girman kansa.
Ta yarda da duk laifuffukanta da Maarouf ya zano, wadanda ba za su bari ya iya ci gaba da rayuwar aure da ita ba. Tana rokon Allah ya sa yadda ta yi aniyar gyara halayen nan nata halayen su gyaru a rayuwar aurenta na gaba. Zuciyarta ta gyaru ta koma yin komai saboda Allah.
*****
An daura auren Laila da Mahdi ranar wata asabar. Da sati ya zagayo ta yi walima ta tare a gidansa da ke cikin garin Dutse. Kudin da Maarouf ya ba ta da su ta yi amfani ta yi wa kanta komai ta kuma taimaka wa Mahdi ya kara gyara gidan ya fito fes! Ta sayi mota ta ja jari ta koma makarantar da Maarouf ke ta goranta mata. Komai na Maarouf ya zama bygone a gare ta, ba ta ko son tuno rayuwarsu ta baya, ta dumfari sabuwar rayuwarta da ikhlasi.
*****
Hannunta kawai yake ja har zuwa falo na karshe, wanda daga shi za su tadda motocin da zasu shiga da masu mara musu baya. A nan ne ta daddage ta kwace hannunta ganin ba shi da damuwa don maaikatansa sun gansu a hakan. Wani irin kallo ya bi ta da shi wanda ita kadai ta san maanar sa.
Ya lura a cike take idanunta sun juye kamar ba ita ba. Wannan balai har ina? Yana zaman-zamansa ta daukeshi ta kaishi yanzu kuma zata yi masaprotestmara dalili, shi meye laifinsa?
Bayan fitowarsa daga wajen Laila yazo ya sametadon su tafi inda yace zasu tafi, budar bakinta sai cewa tayi ita ba inda zata, su tafi shi da Anty Lailah.
Da farko abin haushi ya bashi sai kuma ya koma bashi dariya. Ya fincikota yana fadin wallahi sai kin je, bana niyyar fita in fasa kan wani abu marasa tushe da madafa. Shine ya janyo ta tana turjewa amma karfin ba daya ba, a haka suka fito. Inda ta gode Allah basu hadu da kowanne maaikaci ba.
Suka fada mota yana dama tana hagu, mai tsaron lafiyarsa a gaba (securities) suka biyo su a baya. Sai da suka dauki hanyar barin gari ta ji ya ce da direban Shira za su je.
Suna tafe ba mai magana da dan uwansa, hadiyar zuciya kawai takeyi alhalin ba kuka tayi ba. Yayi banza da ita yana amfani da wayar hannunsa har suka isa.
A can bayan gari tsakiyar gonaki Amina ta ga an yi parking a daidai wani katon gate. Motocin suka tsaya, a nan duk suka firfito. Sanye ta ke cikin riga da zani na atamfa ta yi lullubi da wadataccen mayafi launin adon atamfar jikinta. Ta yi kyau kamar koyaushe. Don ita ba sai ta bata lokaci wajen yin kwalliya ba, kullum kyakkyawa ce ahalittar Ubangiji mara yawan kyalekyale. Kowanne kalar kaya ta sanya karbarta suke su amsheta su dace da zubin halittarta. Physiotherapist Amina Masud kenan.
Masu gadin gidan suka bude wawakeken gate din. Nan Amina ta yi arba da kasaitaccen gidan gona na kiwon tsuntsayen gida, amma tantabaru farare sun fi yawa. Bude baki ta yi tana kallonsa bakinta kamar zai tsage, ya wani kawar da fuska ya tamke ta, ta karasa inda yake ta manta ba su kadai bane ta kamo hannunsa, ta russuna saitin kunensa tace Maarouf Jikas! Im dying for you, my heart is itching da tamkewar fuskarka. Waiwayawa yayi da sauri don ba ahankali ta fada ba, babu wanda hankalinsa yake kansu cikin yan rakiyar nasu sun yi gefe sun samar da space sosai a tsakaninsu. Yayi ajiyar zuciya. Kai wannan yarinyar sai a barta. Ya kwace hannunsa ta kara rikowa ….. na tuba, na bi Allah na bi ka! Tayi conclusion da marairaice idanunta cikin nasa.
Bashi da katabus a duk lokacin da ta kira yi sunansa na ainihi, wanda ba kasafai take yi ba tun sanda ta fahimci fadar hakan na sanya shi a wani hali, tafi cewa (Your Excellency)a gaban kowa don ya zauna lafiya. Sai in sun kebe ne take kiranshi da duk yadda taga dama.
A take ya sassauto, hannunta dake cikin nashi ya bi da kallo yana murmushi infront of them Ameenah? Hawaye suka cicciko idanunta kayi hakuri in nayi laifi, bazan iya sakin hannun bane. Ta fada cikin emotion (shauki). Da gaske ya bata a very big giant surprise kamar yadda yace which she didnt expect. Tantabarunta ne fa sukayi wannan bunkasar. A mahaifar mahaifinta SHIRA.
Sai ya kara damke hannun nata sosai cikin tafin hannunshi, ya jata suka shiga zagaye gidan gonar lungu da sako. Sun kasa cewa juna uffan zuciyoyi kawai ke aiki, farin cikin Amina heighteneda lokacin da ta gane dukyawan tantabarun da ke ciki nata ne suka hayayyafa.
Sai da suka gama shirunsuka tsaya cikin dakin tantabarun suna fuskantar juna, ta mika hannu ta kamo aure daya ta dora akan tafukanta, suka tashi firrr!Suka koma tukwanensu alamun sun manta da ita, dada ne bazasu tashi ba. Zama zasuyi sai ta maida su da kanta. Ta dubeshi ya dubeta ya daga mata kafada alamun ita ta jawo sai sukayi dariya, anan ya gaya mata cewa duka wannan gidan gonar nata ne, mallakinta ne.
Ya hayo kwararru a kiwon tsuntsayen gida ne suna kiwata mata su. Tunda yanzu bata da lokacin hakan. Tantabarunta da ya amsa ne suka yi wannan albarkar bayan nan kuma ya kwaso nata na gida da iznin Goggo ya hade. Surprise din da ya ce zai mata kenan.
Tukuici ne ya ba ta for bringing happiness to his life, for her sacrifice to hisdaughters life(na kawo farin ciki a rayuwarsa da ta yi, da sadaukarwarta kan rayuwar diyarsa). To sai ta rasa me zata ce masa. Shi kuma me ya kawo cikin tata rayuwar?
Contentment, love,affection, devotion, family tie, and everything!Ita bata da abinda zata bayar tukwicin, banda mallaka masa kanta da komai nata wanda dama nasa ne. Kawai sai ji ya yi ta yi azama ta rungume shi tsam-tsam tana hawaye.
Ubangijin da Ya halicceta Shi Ya sanya mata kaunar tantabarun mahaifinta. Kwarai ta ke sonsu, ta maida su wani bangare na rayuwarta. Su ne kadai take kalla ta tuna ya bar mata wani abu na rayuwarsa.
Ta dade tana tunanin yadda za ta habaka kiwonta yau ga Maarouf ya cika mata burinta, ya hutar da ita, kuma a kasar mahaifinta (Shira).
Damka mata takardun gidan gonar ya yi, ya gabatar mata da maaikatanta, ya kuma gaya musu ita da su cewa, yanzu hakkin kula da gidan gonar da hakkin mallakarsa ya koma karkashin ikonta.