Skip to content
Part 5 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Amina an gama aji uku na karamar sakandire suna jiran fitowar sakamako, (double promotion) aka yi mata saboda kokarinta, ta zana (placement) tana shekara sha uku. Jarrabawar ta fito, ta ci makarantar ‘yammata ta gwamnatin tarayya da ke Bajoga, Jihar Gombe.

Amina ba ta samu tafiya makaranta a shekarar ba, saboda ana kashe kudi matuka ba kamar ta gwamnatin jiha inda ta yi ba. Ita ba ta ma san ya akai aka tura Amina wannan makarantar ba, maimakon ta gwamnatin jiha inda ta ke, wannan kuma kokari ne da Malaman Amina suka yi don a cewarsu ba a barin masu (Extraordinary talent) irin Amina su yi ta bata lokaci a kan karatu. Goggo ta daure ta kai ta can din, in har tana da hali.

Goggo da Ilyanta suka zauna suna shawara, Goggo ta ce, “Ka gani fa Ilya, ni fa tarin aure nake mata in na ce wannan makarantar mai tsada zan kai ta me za mu tara? Ga shi da alama ita ma ta makala zuciyarta a kan makarantar.”

Ilya ya ce, “Goggo hakura da tarin auren ki ba ta ilmi, ba abin da ilmin da za ta yi ba zai saya mata ba na auren, ki bar maganar auren a hannun Allah. Ko da mun san Kawu Sule ba zai yi ba, ni na gaya miki Allah zai kawo wata hanyar daban. Sannan ga wata shawara, dazu wani abokina yana da kanti a cikin jami’ar Tafawa Balewa ya gaya min in shawarce ki, ko za ki iya a dinga yin cincin mai nama (meat pie) da kek (cake) mai kyau mu dinga kai wa ‘joints’ na cikin jami’a, kunun Aya da zobo a dinga durawa a tsaftacciyar robar lemuka, in har za a jura wallahi akwai samu sosai. Shi zai rarraba musu in na kai, da an siyar in karbo kudin”.

Goggo ta ce, “Ga shi Amina makarantar kwana za ta tafi balle in samu mai taimaka min”

Ilya ya ce, “Mai aiki za mu dauka babba, ni ma zan shiga cikin aikin, kuma in mun yi mai yawa ba kullum za mu yi ba sai bayan kamar kwana uku-uku in an karbi kudin wanda aka sayar.”

Goggo ta ce, “To ka gaya wa Zulai, (tana nufin mahaifiyarsa) ta cigita mana mai aikin.”

Cikin sati daya Zulai babar Ilya ta samo wa Goggo mai aiki, bazawara ce mijinta ya rasu ya barta da yara hudu sunanta Talatu, neman aikin aikatau ta ke ruwa a jallo, suka hadu suka fara aikin tare, har Ilya shi ma ba a barshi a baya ba, in ka ganshi ya takarkare yana murjin (Meat pie) a injin taliya sai ya ba ka dariya, duk don Aminarsu ta samu ta yi karatu mai kyau.

Baba Talatu na da dadin sha’ani, ga labarai na ban dariya a cikinta, suna aiki tana ba su labarai, Amina na shan dariya, tasu ta zo daya don Amina akwai son jin labarai don haka ba ka raba ta da rediyon Goggo kullum, ta murdo nan ta murdo can, tana jin me duniya ke ciki.

Sana’ar ta Goggo sai sam-barka, ta fara da hannun dama, ba ta ajiyar kudi a gida, adashi ta ke zubawa. Bayan ta fidda hakkin Ilya da Talatu da sauran yaran da Ilya ya samo suke taimaka masa. Amina na kula da Tantabarunta don yanzu aiki ya yi musu sauki, tun bayan samun Baba Talatu. Ita ta ke wanke-wanke da shara, har wankin kayan Goggo da Amina ta ke yi, don haka Amina ta samu isasshen lokacin karatun islamiyyarta, shekara guda ke nan ba ta makarantar boko, Goggo na tarin abin da za ta dauki nauyin karatun da shi.

Amina na son Tantabarunta, don suke debe mata kewar babanta, ko dubu nawa ka ce za ka siya ba za ta sayar maka ba, ga su nan cikin daki guda masha’Allah sai hayayyafa suke.

Ilyan Goggo kan tsokane ta, “Amina da Tantabaru za ki tafi gidan mijinki halan?”

Duk lokacin da ya ce mata hakan ba za su kara shiri ba sai an yi kwanaki, don inda abin da Amina ta tsana a rayuwarta to a yi mata zancen aure ko miji, don ta dauke su ‘as an obstacle’ (matsayin shinge) ga ci gaban rayuwarta da kudirin da ta ke da shi a zuciyarta.

Akwai wata rana da wani dan unguwarsu Danladi ya biyo ta tana tafiya ta dawo daga ajin haddarta, ba ta san ita yake bi ba sai da ya yi mata magana.

“Aminatu, dan tsaya mana, magana nake so mu yi”.

Amina ta tsaya cak! Sannan ta juyo da manyan idanunta ta galla masa harara.

“Amina kin dade kina burge ni, don Allah ki ba ni dama mu shirya kanmu in nemi aurenki, don Allah Aminatu”.

Su Amina aka yi wani irin tsaki kamar tsaka, “Na yi kama da ire-iren ‘yammatan da za ka aura ne? ko na yi kama da matar karen mota mara arabi da boko? Ahir dinka da kula ni, wallahi ka kara tare ni a hanya sai na tula maka kasa, ba kai ba ni ka ji na gaya maka, ba kai kadai ba mai aurena ba a haife shi ba wallahi, don haka ka fita hanya ta ka ji na gaya maka”.

Kalamanta sun yi wa Danladi ciwo, “Ashe ba ki da mutunci? Don kin samu an so ki? Banza! Wadda ubanta bai bar mata gadon komai ba sai Tattabara, kin yi kadan ki ci min mutunci, insha Allahu sai mijin aure ya gagare ki, da ni ki ke zancen”.

Amina ta murguda baki ta yi wucewarta ta rabu da shi yana ta masifa, har da kumfar baki. A ranta ta ce, ‘Ai gara in rasa mijin auren. Ni ina ruwana da wani aure? Duk abin da zai raba ni da Goggona neman tsari nake da shi’.

Can kuma ta yi kwafa, ta girgiza kai, “Wai ubana bai bar min komai ba sai Tattabaru, ya bar min komai kuwa tunda ya sanya ni a turbar neman ilimi, Tantabaru kuma arziki ne na gode wa Allah, na gode wa Babana da ya bar min su a matsayin gado, wani me nasa uban ya bar masa?”

Tana nufin Danladin, Amina fa akwai tsiwa ta rashin arziqi in dai a kan za a ce ana sonta ne. in ban da wannan za ku zauna lafiya cikin kwanciyar hankali. Ko Goggo ba ta gaya wa yadda suka yi da Danladi ba, don ta san fada za ta yi mata.

*****

A yau Goggo ta dau adashinta na kudi naira dubu dari da hamsin. Ta soma sayayyar kayan abinci wanda dan makarantar kwana ke bukata, ta shake (Ghana Must Go), Amina ta shirya kayanta, Ilya ya yo musu shatar taxi su uku har da shi, wadda za ta kai su har cikin FGGC Bajoga.

Da suka shiga suka nemi ofishin Principal ta lokacin, Hajiya Aishatu Dukku. Suka mika takardun Amina, aka ba su bill na komai da komai har (uniform) da (house wear), Sandal da cambos, littattafai (text books) da sauran abubuwan da daliban makaranta ke bukata. A take Amina Mas’ud ta zama cikakkiyar ‘yar makaranta aka ba ta aji da hostel.

Inda ake yinta shi ne rabuwar Amina da Goggo, ta makalkale Goggo tana kuka ita ta fasa karatun. Wata malama ta kamata tana lallashinta. Wata kyakkyawar yarinya da za ta yi tsarar Aminan ta zo za ta wuce, malamar ta yi kiranta, “Hafsa kama hannun Amina ki kai ta hostel dinku, ku yi wanka kafin lokacin fitowa (prep)”.

Hafsa ta zo ta kama hannun Amina, “Ki yi hakuri mu je, kwana kadan za ki saba, ki yi hakuri.”

Haka Amina ta saki Goggo tana kuka suka tafi. Goggon kam ta yi jarunta ko hawaye ba ta yi ba, sai murmushi ta ke yi, sai dai fa kada ka so ka tona zuciyarta, ko na kwana daya ba ta taba raba gado da Amina ba, shekara goma sha uku, da yake a J.S.S je-ka-ka-dawo ta yi.

Ko da suka koma gida Ilya ya gane jikin Goggo a sanyaye yake, washegari ma da ya zo su yi aikin (meat pie) da ya kare da wuri, cewa ta yi da su ta ba wa kowa hutun kwana biyu ba ta jin dadi.

Amina A Kwaleji

Da taimakon Hafsa Datti, Amina ta gane komai na zamantakewar makarantarsu cikin kwana bakwai. Ba abin da ke burge ta irin yadda duka daliban turanci suke yi, kabilu da hausawa. Hafsa na son Amina, sai dai ita Aminar ba ta saba da yin kawance da kowa ba bayan Goggonta, don haka ba ta bawa Hafsa hankalinta su yi kawancen yadda ya kamata, in ba ita Hafsan ce ta neme ta ba, ita ba za ta neme ta ba sai in tana neman ta warware mata wani abun da ya shige mata duhu. Amma halayen kirki irin na Hafsa Datti ya sa dole Amina ta mika wuya ga kawancensu.

Amina na mamakin kyau irin na Hafsa kamar Balarabiya, ta taba tambayarta su wane yare ne? Ta ce su fulanin Jama’are ne. abin da Amina ba ta sani ba, behind (karkashin) kyawun Hafsa Datti shi ne hutun rayuwa da ta ke ciki, ‘yar manyan mutane ce, ga ta nan kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba, sumul-sumul da ita kamar da ka taba jini zai yi tsartuwa.

Wasu cimakar gwangwani iri-iri da ke cikin kayan abincin Hafsa, Amina ba ta taba ganinsu ba. Sai dai ba ta da kauyanci, ba ta tambaya, kuma ba ta da kwadayi, abin da Goggonta ta kulla mata kadai ta ke amfani da shi. Ko da Hafsa ta yi mata tayin cin ire-iren cimakarta cewa ta ke yi, “Ban iya ci ba”.

In Hafsa ta turza ta ce, “In ki ka takura ni na ci cikina zai baci”.

Dole Hafsa ke kyale ta.

Karatu ya kankama gadan-gadan, su Amina ana ta kwasar ilmi babu dare babu rana. Amina sai ta ga ashe a da ba karatu ta ke yi a Bauchi ba, wasan yara ne. Amina tana ajin (science) kamar yadda ta zaba, don haka ta kama wadannan darussan (subjects) ta rike gam (Mathematics, Biology, Chemistry, Physics), ba ta wasa da su. An ce, ‘talent never hides’, wato hazaka ba ta buya, cikin dan lokaci malamansu sun fara gane kokarin Amina.

Sun samu hutu bayan watanni uku, Goggo ita kadai ta zo daukar Amina ta bar hidimominta a hannun Ilya da Talatu.

Tsallen da Amina ke yi a jikin Goggo kamar yarinyar goye, Hafsa ta zo ta tadda su a inda suke ta gaida Goggo cikin girmamawa. Goggo ta amsa da fara’a, don ta gane ta, ita ce aka hada da Amina a ranar da aka kawo ta.

Suka zuba kayan Amina a taxi din da Goggo ta yo shata, suka yi sallama da Hafsa wadda ita ba a zo daukarta ba tukunna, don a nesa suke, daga Abuja ta zo.

Wajejen la’asar suka iso gida, Goggo ta sallami mai taxi, da gudu Amina ta fada  gida tana kiran Talatu, a soro suka yi mugun karo da goshin kowaccensu. Dukkansu suka dafe goshi kafin Talatu ta rungume ta, “Sannu da zuwa uwardakina, shalelen Baba Talatu”

“Sannu da gida ta wajena, na same ku lafiya? Ya ya su Balki (‘Ya’yan Talatu)?”

Haka dai suka ganganda suka yi cikin gida.

Amina na ta ganin sauye-sauye wanda ke nuna lallai sana’ar Goggo na tafiya yanda ake so, da karin albarka, cimarsu kanta ta sauya kullum girkin Goggo da nama zuku-zuku na Saniya ko na kaza ko kifi. Asabar na zagayowa ta koma Tahfiz dinta.

Haka Amina ta kare hutunta lafiya ta koma makaranta, wannan karon babu kuka.

<< Sanadin Kenan 4Sanadin Kenan 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×