A hutu na gaba da Amina ta zo, Goggo ta ce ta shirya ta tafi Shira ta gano kawun mahaifinta Bilyaminu, an gaya mata yana kwance ba shi da lafiya, ta kuma karasa ta gaida Baffa Tasi’u shi ma in ta dawo ta je gidan Kawu Sule shi ma ta gaishe shi. Amina ba ta yi wa Goggo musu ba, amma cikin zuciyarta mita ta ke yi, “Na rasa wace iri ce Goggo, sam-sam ba ta yin zuciya da mutanen da ba su damu da mu ba, dan gara-gara ma Baffa Tasi’un shi in an je. . .