Ilyan Goggo da Goggo sun baje kudi a tsakar dakin Goggo suna ta lissafi, Ilya ya ware wasu gefe ya sanya a leda ya mika wa Goggo, “Ajiye wadannan a gefe, kudin makarantar Amina na shekarar karshe, Waec, Neco da Jamb kamar yadda aka ba mu list.”
Goggo ta amsa ta aje a gefe, ita ma ta ware wasu ta mika masa, “Wadannan kuma dubu sittin ga su, ka sayi sabon babur ka dinga amfani da shi, kada ka yi min musu, umarni ne ba shawara ba.”
Ilya ya sanya hannu biyu ya karba, idanunsa suka ciko da kwalla. Abin. . .