Amina da Goggo suna hira a yau, Goggo ta dubi Amina cikin damuwa, “Har yanzu lokaci bai yi ba da za ki kawo min miji Aminatu? Sai na fadi na mutu ban ga ‘ya’yanki ba Amina? Me ki ke nema a rayuwa haka? Na bi ki, na bi ki da duk abin da ki ke so da burikanki, sai yaushe ni za ki faranta min, ki cika min nawa burin a kanki?”
Hankalin Amina in ya yi dubu to ya tashi, ganin Goggo tana share hawaye. Ba ta san sanda ita ma idanunta suka yi rau-rau ba, ta gurfana tana bai wa Goggo hakuri,
“Na yi miki alkawari Goggo, duk wanda ya fara zuwa yanzu zan ba shi dama ya fito ba zan kara korar kowa ba.”
Sai a sannan ne Goggo ta sauko, ta daga hannu sama ta ce,
“Ya Allah ka kawo wa Aminatu miji na gari alfarmar Alqur’ani”.
Wani ikon Allah kuma sai dif! Maneman suka dauke kafa, babu su babu alamarsu, har Amina ta tafi hidimar kasa jihar Gombe..
To duk wanda ya zo, in ya ji cewa Amina cikakkiyar likita ce, sai ya ga ta fi karfinsa ya cika bujensa da iska.
*****
Bayan Amina ta kammala hidimar kasa, an rarraba su asibitoci da dama, da taimakon Dr. Turaki aka bar Amina a ATBU Teaching Hospital, Dr. Amina Mas’ud Shira ta fara aiki a ‘physiotherapy department’ cikin kawarewa da sanin makamar aikinta.
*****
Maballan ‘suit’ din da ta sanya masa ta ke ballewa, a tausashe kuma tana yi masa hira, ta dauko ‘necktie’ mai ruwan makuba ta zarga masa ta ja ta matse tana fadin,
“Ba ka ga yadda ash (ruwan toka) ke karbarka ba Baban Amina, ya kamata mu shiga gasar (handsomes) ta duniya, saboda har tafiyarsu ka iya, matsalarka daya rashin fara’a, kullum handsome fuskar nan a cikin seriousness, zan yi rantsuwa ban yi kaffara ba, idan nace ban da Amina ba wanda ke ganin dariyarka, ko ni albarka……”
Bai san sanda ya yi dariyar ba, Aisha will never cease to amuse him (Aisha ba za ta bar sa shi dariya ba kullum), mace ce ta gari da kowanne namiji ke burin samu, idan har samun mace ta gari shi ne cikar rabin addini yana da yakinin cikar nasa rabin addinin. Ya kama karan hancinta ya ja kadan,
“Kin ga malama yi sauri ba na son shirme, flight dina to Abuja karfe sha daya na safe zai tashi, don ba ni da yadda zan yi da ke ne zan barki da Ameena ku taho a mota. Ni rasa me ye abin tsoro a jirgi, matsoraciya kawai.”
Aisha ba ta yi magana ba, ta dauko masa (briefcase) dinsa. Ita dai tunda Ubangiji ya halicce ta ta ke tsoron hawa jirgi, ga ta dai ba haihuwar kauye ba, ko wani abu makamancin haka, it happens by nature.
Akwai lokacin da maigidan ya takura mata don ya zama dole, umrah za su je bayan aurensu, zuwa dakin Allah ya kori komai ga kowanne musulmi, don haka Aisha ta yi shahada ta hau jirgi, suka nabba’a a mazauninsu, bayan sun sanya ‘belt’. Da jirgin ya yi kururuwa ya karci kasa ya luluka sama, Aisha ta rungume mijinta ta runtse idonta, sai jini ya kece kamar an yanka rago, cikin watanni uku ya fice.
Tun daga lokacin bai kara takurawa Aisha wajen hawa jirgi ba. Shi zai bi jirgin, ita ta bi mota su hade a inda za su je. Fita kasar waje kuwa ba ya daga cikin al’adun rayuwarsa, ba ya zuwa kowacce kasa duk da arzikin da Allah ya yi masa ban da Saudi-Arebia. A cewarsa bai ga me zai je ya yo ba ban da asarar dukiya, duk abin da muke nema na jin dadin rayuwa muna da shi a kasarmu mai dumbin albarka.
Mutum ne mai girmama kasarsa da son yankinsa (Arewa) kwarai da gaske. Bai yi kowanne irin karatunsa a kasar waje ba. Bayan kammala sakandirensa a (Science College D/Tofa) ya wuce jami’ar Ahmadu Bello, inda ya nazarci ‘Civil Engineering’.
Ya fita da digiri mai daraja ta farko, bayan kammala hidimar kasa bai bata lokaci ba ya koma jami’ar ya hado digiri na biyu.
Bai fito daga gidan masu hannu da shuni ba, ko gidan wasu masu fada-a-ji, dan talakawa ne likis, mahaifinsa Malamin makaranta ne, inda mahaifiyarsa ta kasance mai sana’ar kiwon dabbobi. A haka ya rayu cikin wahalar karatu. Da ta abin amfani har Allah ya sa ya kammala.
A wancan lokacin, karatun boko bai zama yadda ya zama yanzu ba, gwamnati neman masu zuciyar yin karatun ta ke kawai ta tallafa musu. Don haka zai iya cewa matsalolin da ya ci karo da su a zamanin karatunsa ba masu yawa ba ne, ban da nisan gari da gari da yake a tsakani. Amma har alawus na abinci iyaye ba su faya wahala a kai ba, gwamnati na yi musu.
Yana dan shekaru uku mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa, a dalilin ya auro wata, don haka ba ta barshi a hannun matar Babansa ba ta dauke shi ta tafi da shi wani kauye a Jihar Jigawa, inda kanwar mahaifiyarta ke aure. A can ya yi firamare ya gama, da ya isa shiga sakandire ta samu miji a can ta yi aure, shi kuma ta maido shi hannun mahaifinsa, ya dauke shi ya kai shi makarantar sakandire ta kimiyya da ke Dawakin Tofa, daga wancan lokacin ya ci gaba da zama hannun mahaifinsa har ya shiga jami’a.
Matar da yake aure din mai suna Luba, ta dauki tsangwamar duniya ta dora masa saboda ita Allah bai ba ta haihuwa ba, tana kishin kaunar da mahaifinsa ke yi masa, komai ya samo a kansa yake karewa.
To zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana ga muzuru, ana ga shaho sai ya yi. Bayan kammala digirinsa na biyu ya ci gaba da zama da mahaifinsa, har ya samar masa aikin koyarwa a sakandiren da yake aiki.
Watarana da yamma yana karanta jaridar Daily Trust ya ga wani kamfani na cigiyar Civil Engineers masu matakin digiri na biyu. Kamfani ne da ke karbar kwangilar ginin tituna, gidaje, asibitoci, gadoji, Dam, titin jirgin kasa da sauransu. Ya dauki adireshinsu na (Fax) da (post office) wadanda da su ne ake amfani wajen sadarwa a wancan lokacin. Ya rubuta (application) ya hada da photocopy na takardunsa ya aika musu. Ya ci gaba da harkar koyarwarsa bai kara tunawa da zancen ba.
Kusa da gidansu da ke unguwar Yelwa gidan Alh. Mansur Maifata ne, mutumin yana da rufin asiri sosai, don duk unguwar babu mai sukuninsa, duk ‘ya’yansa mata ne ta ukun ita ce Aisha, ya sha ganinta tana wucewa in yana kofar gida yana karatun jaridar da ya zame masa taba, in bai karanta ‘Daily Trust’ kullum ba, ya ji halin da kasarsa ke ciki ba, jinsa yake kamar mara lafiya.
Kullum yarinyar ta wuce sai ya bi ta da kallo, shi ba ma’abocin kula mata ba ne duk da dalibai mata yake koyarwa, amma bai san me ya sa duk ranar da bai ga wucewar Aisha ta gabansa ba, sai ya ji wata irin kewa. Ya kura wa kofar gidansu ido ya yi ta Allah-Allah ya ga giftawarta.
Aisha Mansur, ba wata kyakkyawa ba ce fiye da ‘yan uwanta ba, amma duk ta fi su nutsuwa da kwarjini. Bai taba ganin ta tsaya da wani namiji a kofar gidansu ba kamar sauran ‘yan uwanta, abin da bai sani ba shi ne, ko an aika ba ta fitowa sai dai saurayi ya gaji da tsayuwarsa ya tafi.
Baban su Aisha na matukar kokari a kan tarbiyyarsu. Shi dai bai taba yi mata magana ba, haka ita ma. Amma ya lura in ta dawo daga islamiyya ta wuce shi, ya bi ta da kallon da ya saba binta da shi, in ta kai kofar gidansu sai ta juyo cikin dabara ta kalle shi, sannan ta wuce. Sai ya yi murmushi ya maida kai ga jaridarsa.
Ranar da ta lura ya kamata tana kallon inda yake, da gudu ta shige gidansu.
Murmushi ya yi, ya ci gaba da karatun jaridarsa, ya rasa me ya sa yake jin yarinyar a ransa. Ko sunanta bai sani ba.
Ranar wata juma’a suna zaune a kan tabarma a kofar gida shi da Babansa, suna cin tuwon dare a kwano daya, daya daga cikin ma’aikatan gidan Alh. Mansur ya zo ya gaida Baban, ya kuma sanar da shi Alh. Mansur ne ya aiko shi ya sanar da shi zai zo ganinsa karfe tara na dare.
Baban ya ce, “Allah ya kawo shi lafiya”.
Bayan sun gama cin abinci sun wanke hannu da ruwan butar alwala, Baban yake janshi da hira, don ya san in ta dan nasa ne, to a zauna a haka awa uku baki a rufe, ko kowa ya dauki jarida ya karanta.
“Ni wai cewa nake wata mai zuwa za ka cika shekaru ashirin da bakwai ne?”
Ya yi dan lissafi, ya ce, “Eh, Fabrairu insha Allahu”.
“Kuma ba ka da niyyar aure ko? A da in an yi magana ka ce karatu, hidimar kasa, aiki, yanzu wanne ne ya saura?”
Ya yi dan murmushi bai ce komai ba.
“Daidai gwargwado Allah ya rufa mana asiri, ba za mu kasa rike mata ba. Albashinka ya isa ka ciyar da iyali, ga gidan nan babba ne na ja maka katanga na ware maka muhalli, me kuma ya rage?”
Ya yi ‘yan mutsu-mutsu na rashin abin cewa, domin ba shi da hujjar da zai bayar, kuma ba zai iya fada wa Babansa abin da ke ransa ba, ganin abin ba mai yiwuwa ba ne.
Inda Allah ya kwace shi daga titsiyen Baba shi ne, isowar Alhaji Mansur Maifata. Turarensa mai dadin kamshi ya baibaye su, shaddarsa har walkiya ta ke. Ga damanga ya kafa, wadda a da babu masu sanya ta sai masu hannu da shuni. Ya ba su hannu dukkaninsu, Baba ya ba shi wurin zama, shi kuma ya yi musu sallama ya tashi ya ba su waje.
Bayan gaisuwa da tambayar iyali, Alhaji Mansur ya gyara murya,
“Wato Malam Habibu, abin da ya kawo ni neman alfarma ne, na neman iri. A zaman shekaru ashirin da muka yi tare na yaba da halayenka, da tarbiyyar da ka ba wa yaron wajenka. Ga ilimi mai kyau da ka tsaya tsayin daka ya samu, ban taba jin an ce yau ga abokin fadansa ko ga wani hali na banza da aka same shi da shi ba. Wannan ne ya kawadaitar da ni in neme ka mu hada iri, in har ka amince.
Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ya hore mu da mu nema wa ‘ya’yanmu mazan aure na gari a aurensu na fari. Duka yarana na ba su dama su zabi mazan aure da kansu su uku manyan, Aisha ce kadai ban bai wa wannan damar ba, a dalilin ita marainiya ce, mahaifiyarta ta rasu wajen haihuwarta, ta sha wahala a hannun matana, ina so ta samu kwanciyar hankali da sukunin zuciya a gidan aurenta