Gurbi K'aramar Hukumar Jibia Katsina State Nigeria
"Ance wai ana sallama da Babansu Auta"
Inna dake tsakar gida ta dubi yaron daya shigo ta ce "kaje kace gashi nan zuwa"
Juyawa yaron yayi ya fice daga gidan.
Inna ta kalli Nanah dake cin abinci ta ce "Nanah shiga d'akin Babanku kice ana sallama dashi k'ofar gida"
Tashi kawai Nanah tayi ta shiga d'akin Baba ta sanar dashi.
Ba'a jima ba Baba ya fito ya fice daga gidan ya nufi waje.
Nanah ta kalli Inna ta ce "wallahi Inna gidan su D'an Liti mai shigo. . .