Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria
"Kaiii Ismail tsaya na ce"
Juyowa Ismail yayi yana duban Hajara data masa tsawa, rik'e k'ugunsa yayi yana kallon Hajara kawai.
Wani duba take mai cike da mamakin yaron ta cije baki kamin ta ce "kai dan ubanka, ni ce zan aike ka kaje kayo min shirme?"
"Mama bafa shirme nayo miki ba, haka kike ce na sayo miki Sigari"
Dafe k'irjinta Mama tayi ido a waje take nuna Ismail tana cewa "na shiga uku Sigari?, ni ce nace ka sayo min Sigari?"
Wani irin kuka ta fashe dashi na makirci. . .