Kirkira
A cikin wannan littafi mai suna ‘Ƙirƙira’, shahararren marubuci Bala Anas Babinlata ya zayyane dukkan wani abu da mutum ke buƙata ya sani game da ƙirƙira. Ya kuma bayyana hanyoyin da mutum zai bi domin gano irin tasa baiwar ta ƙirƙira da kuma yadda zai iya sarrafata har ta kai ga yi masa amfani ta kuma amfanar da sauran al’umma.
Kalaman Soyayya
Yayin da zuciya ta kai ƙololuwa a fagen ƙauna, masoya kan rikiɗe su zamo mawaƙa masu zaƙin murya. Muryoyin da kan fitar da zafafan kalaman soyayya masu cike da saƙonnin da ma’abota bege ne kawai ke iya fahimtar su.
Matakan Nasarar Iyali
A irin wannan yanayi da muke ciki da matsalolin iyali da yadda za a tafiyar da su suka yi wa al’ummarmu ɗaurin dema, haziƙi kuma fashihin marubuci Hamza Dawaki ya zo da wannan sabon littafi mai cike da ilimi mai tarin yawan da misalta shi ma ba ƙaramin aiki bane. Karanta wannan littafi zai canja rayuwar mutane da dama tare da hasko musu lungunan da ba su taɓa tsammanin sun wanzu ba a rayuwarsu tare da ba su damar kakkaɓe duk wata ƙura da ke cikinsu.