Duniyata
Irfaan da mahaifinsa jami’an ‘Yan sanda ne. Ƙaddarar rayuwa ta kai su Saulawa inda ya haɗu da Ihsan, wadda ta tsaya mishi a rai ba tare da wani dalili ba. Rashin yin soyayya balle ma batun aure ya sa iyayen Irfaan ke tunanin ko Aljana ce ta aure shi.
Kushewar Badi
Tsawon shekaru Almustapha da matarsa Lajja suna tare, suna matukar so da kaunar junansu, so irin na don Allah. Abubuwa biyu ne kadai ke damunsu a rayuwa; rashin haihuwa, da kuma wani al’amari mai firgitarwa da ke tare da Lajjar. Kwatsam! Wata rana tsaka a cikin ire-iren ranekun babi-babi na rayuwarsu, wani mutum mai suna Alhaji Hammad ya bayyana tare da shaidun cewar Lajja fa matarsa ce. Hujjojin da ya kawo sun tabbatar da abin da ya fada haka yake. Don haka alkali ta karbe Lajjar daga hannun Almustapha aka ba Alhaji Hammad. Shekara daya da faruwar wannan abu Allah ya yi wa Lajja haihuwa. To a wannan lokaci ne kuma wasu hujjojin suka kuma bayyana, kuma suka tabbatar wa duniya Lajja ba matar Alhaji Hammad ba ce! To matar wane ne?
Sanadin Kenan
Engineer Ma’arouf Ji-Ƙas zaɓaɓɓen gwamna ne, yana da ‘ya guda ɗaya mai suna Amina wacce ke fama da ciwon shanyewar ɓarin jiki. Bayan ya lura da cewa matarsa Lailah ba za ta iya kula mishi da ‘yarsa ba sai ya nemi likitar da za ta zo har gida ta kula da ita. A sanadiyar haka ne ya haɗu da Dr. Amina, ko yaya haɗuwar za ta kasance?
Mutuwar Tsaye
Dr. Deeni ƙwararren likita ne a ɓangaren jinyar cututtukan da suka shafi mata kawai. Rana ɗaya kawai ya tsinci kansa da cutar makanta wadda ta zo mishi a yanayi na bazata. Matarshi Deena, wadda ke ɗauke da tsohon ciki ta fi kowa shiga tashin hankali, domin kuwa mahaifiyarta ba son aurenta da shi take yi ba. A gefe kuma ga mahaifiyar su Deeni wacce ita ma ke fama da tata lalurar. Shin za su faɗa mata ne ko kuma za su ɓote? Yaya makomar aikin Deeni? Kuma yaya makomar aurensu da Deena?
Daga Karshe
Fatima budurwa ce ‘yar kimanin shekaru goma sha bakwai. Shiririta, rashin hankali da tsiwa bayyanannu ne daga cikin halayenta. Kowa na ƙorafi da ita game da wannan, domin ko waye mutum za ta iya ɗaga ido ta kalle ka ta faɗa maka duk maganar da ta ga dama. Kafiya, kuwa sai ka ce kuturu. Jamilu ɗan uwan mahaifiyar Fatima ne, kuma shi take so ta aura, Mustafa kuma malamin Fatima ne na Islamiyya. Jamilu ya daɗe yana son Fatima amma bai faɗa wa kowa ba, ita kuma ta ce wa Mustafa ya turo manyan gidansu neman aurenta.
Fudayl
Abbu ya yi wa ‘yarsa Hamna Nuhu Alƙali aure da mijin da ko sunan shi ba ta iya riƙewa ba saboda ba auren soyayya ba ne. Amna za ta bi shawarar Ammi ta zauna da mijinta lafiya ne ko kuma za ta biyewa son zuciya da ra’ayinta?
Rabon A Yi
Farida, wadda aka fi sani da ‘Ferry’ ta yanke shawarar zuwa bikin babbar ƙawarta Jiddah, duk kuwa da cewa mijinta Mukhtar ya tabbatar mata da cewa baya so ta je. Hankalinta ya tashi sosai yayin da ta na gidan bikin aka ce an yi sata, ana cikin rigimar sata kuma aljanun wata suka tashi. Ga kuma Mukhtar yana kiranta a waya.
Asabe Reza
Hankalin fitacciyar Karuwa Asabe Reza ya tashi sakamakon cin amanar da ƙawarta Fakriyya ta yi mata na aure mata hamshaƙin masoyinta Hamoudi. Wannan ya sa ta sha alwashin tarwatsa musu farincikin da suke fatar samu.
Mai Daki
Hauwa’u Idris ɗaliba ce mai matuƙar ƙoƙari a fannin karatu. Babban burinta shi ne ta zama malamar jinya yayin da ta kammala karatu. Sai dai kash! Mahaifinta ba shi da ƙarfin ɗaukar ɗawainiyar karatun nata. Hakan ya sa ko da Ishak ya zo neman aurenta kuma ya tabbatar musu da zai barta ta ci gaba da karatu, sai nan da nan suka amince. Abin da ba su sani ba shi ne, Ishak bai da niyyar barin Hauwa’u ta ci gaba da karatu.
Ummu Radiyya
Abakar da matarsa Ummu Radiyya sun gamu tashin hankali mai girma sakamakon kama haya da suka yi a gidan Hajiya Iyami, inda ta hana su cin amarci ta hanyar yin asirin zama mage har zuwa ranar da Abubakar ya buge ta a kai. Gari na wayewa aka kai ta asibiti shi kuma aka ɗaure shi. Shin ko Ummu Radiyya za ta samu mafita a cikin wannan sarƙaƙiya da ta tsinci kanta a ciki?
Halin Rayuwa
Maryam Abubakar ta ga rayuwa a wannan duniya. Duniyarta gaba ɗaya ta fara birkicewa ne tun tana ‘yar shekara tara a duniya. A wannan lokaci ne mahaifiyarta Ramatu ta rasu, ya zamana Baba Sumaye ce ke kula da ita kamar ita ta haife ta. Zaman kaɗaici kawai suke yi ita da mahaifinta.
To sai dai duk wannan ba komai bane a cikin wahalhalun rayuwarta face ‘wasa farin girki.’
Birnin Sahara
Haidar ya farka daga suman da bai san ya yi ba, yayin da ya tsinci kanshi a wani babban birni da duniya kaf ba ta san da wanzuwarsa ba. Abin ya bashi mamaki ƙwarai da gaske da ya ga tsohuwar budurwar da yake so Nadiya ita ce ke mulkin wannan birnin. Sai dai mamakin shi ya ƙara nunkuwa ne bayan ya fahimci cewa yana da alaƙa ta asali da wannan birni, kuma ya zama wajibi a gare shi ya tsallake wasu matakai domin ya zamo sarkin wannan birni matuƙar yana so ya ceci rayuwar ‘yan uwansa.
Launin So
Umma Maryam da yaranta uku, Samir, Abba da Samira suna cikin wani irin mawuyacin hali mai ban tausayi sakamakon talaucin da suke ciki wanda ya jawo musu ƙunci a cikin rayuwarsu. Sai sun yi bara ma suke samun abin da za su ci kuma a bola sukan zauna a mafi yawancin lokaci. Duk da cewa Alhaji Mas’ud ya basu wurin zama a cikin gidansa, shi da matarsa Hajiya Kilishi da babu irin karar tsanar da ba su ɗora musu ba. A cikin wannan yanayi ne kuma kwatsam sai Samir ya kamu da tsananin son Zuhra, shalelen Alhaji Mas’ud. Shin ko za ta karɓi soyayyar tashi?
Kauthar
Kauthar na cikin wani hali na ruɗani, domin kuwa mahaifinta ya yanke shawarar aurar da ita ga Abdulmalik Kwangila bayan sati biyu da kammala jarabawarta. Inda tashin hankalin yake shi ne, Abdulmalik mijin yar’uwarta ne kuma babbar ƙawarta, aminiyar da suke ƙaunar junansu tamkar ciki ɗaya suka fito. Yaya Faheemah wadda aka fi sani da Anty Ummi za ta ɗauki wannan labari na auren babbar ƙawarta da mijinta?
Shirin Allah
Wanda Allah Ya so da shiriya, babu wanda ya isa ya sauya shi. Duk da irin ƙalubale na rayuwa da Hamida ta fuskanta har zuwa aurenta da Abdurrashid, da kuma harin da babban amininsa Usman kai mata tare da nuna sha’awarsa akanta basu canza ta ba. Shin ko Hamida za ta ba wa Usman dama wajen saɓa wa Allah, me zai faru idan Abdurrashid ya gane Usman na neman matarsa?
Bakar Kaddara
Wasu lokutan ba sai ka aikata mummunan aiki ba kafin baƙar ƙaddara ta afko maka. A wasu lokutan kuma, halayen mutane ne ke kaisu ga faɗawa cikin bala’i.
Wa Gari Ya Waya?
Tahir yana cikin matsananciyar damuwa, ba komai ya jawo mishi wannan damuwa ba kuwa face matansa guda huɗu. Basma na fama da ciwon ƙwaƙwalwa, Halima na da yawan cin bashi, Latifa amarya kuma yawon bin malamai. Ummul Khair ce kawai mutuniyar kirki a cikinsu. Shin ko Tahir zai iya magance matsalolin da ke ci gaba da tashi a gidansa?
Soyayya Da Rayuwa
Safina da Nabila matan Hassan Hassan ne da Hussaini. Suna zaman lafiya tare da nuna wa juna tsantsar soyayya. Kwatsam rana guda sai Hassan da Hussaini ke faɗa wa matansu cewa za su ƙara aure nan da wata uku. Shin ko matan za su ɗauki wannan labari da sauƙi kuwa?
Mijin Ta Ce
Humaira, mahaifiyarta da ƙannenta na fuskantar baƙin kishi da mugunta iri-iri a wurin matar mahaifinsu Alhaji Surajo. Hajiya Majadan ta mallake gidan, sai abin da ta ce a yi ake yi. Shi kuwa Alhaji Surajo babu abin da ya fi ƙi fiye da ganin ɓacin ranta. Hakan ne ma ya sa ta ƙwace girki daga wurin Inna ta kuma hana shi kwana a ɗakinta. Rigimar gidan ta kai ƙololuwa ne yayin da Hajiya Majadan ta ga Inna da cikin wata bakwai kwatsam da rana tsaka.
Wace Ce Ni?
A gidan Alhaji Bello Mustapha, Rabi’atu (Adawiyya) ta zamewa kowa jalli-joga. Shagwaɓarta da ta da tsiyarta take tsulawa irin yadda duk ta ga dama sangarta da son jiki kuwa ba a magana. Dawowar Yaya Almu daga makaranta ce ta sauya komai na gidan, ciki kuwa har da yadda ya zuba wa Adawiyya ido abinda take so babu kwaɓa. Ita kuwa Adawiyya gani take duk abinda yaya Almu yake yi mata ƙiyayya ce da kuma ‘yan’ubanci.
Cikin Baure
Auren Asma’u da Abbas ya kusa, sai dai ko kaɗan ba ta son shi. Hankalinta na kan wani matashin mai kuɗi da ake kira Alhaji Nas, alhali kuwa shi bai san ma tana yi ba. A haka dai aka ɗaura auren ba don tana so ba. Kwaɗayin dukiyar Alhaji Nas da fafutukar ganin ta shiga rayuwar daula suka sa soyayya ta makantar da ita har sai da ta kashe aurenta ta fito domin ta auri Alhaji Nas. Burinta ya cika ta aure shi, sai dai irin halin da ta tsinci kanta a rayuwar zaman gidan ko a mafarki ba ta hango wa kanta hakan ba.
Rayuwata
Zuwan ‘Yan Bindiga rugar su Naja’atu ya yi sanadiyar mutuwar mafi yawa daga cikin ‘yan’uwanta. Yayin da ita kuma garin gudun neman ceton rai ta faɗa hannunsu har shugaban ‘Yan Bindigar ya mayar da ita tamkar matarsa.
Meenal
Kyakkyawar matashiya mai taƙama da kyau, kuɗi da kuma ilimi wadda ake kira Meenal ta sha alwashin cewa ba za ta taɓa yin soyayya ba ballantana ta yi aure, domin ita a nata tunanin, babu wani sauran abu kuma da za ta yi sha’awa a wurin ɗa namiji da har zai kai ta ga yin aure. Me ya sa Meenal ta tsani maza? Me ya sa ba ta da ƙawaye?
Amnah
Amnah nutsattsiyar matashiya ce mai kyau da kamala, domin har sauka ta yi. Sai dai mummunan halin da ta tsinci kanta a ciki ne ya sa ta shiga harkar karuwanci, a harkar karuwancin ma har tarihi take ƙoƙarin kafawa na ganin cewa duk mutumin da ya yi tarayya da shi ba ta ƙarawa. To sai dai kuma ta kamu da soyayyar matashi Taufiq. Shin ko za ta samu cikar burinta?
Ya'yanmu
Rayuwar zaman marina ake yi a Unguwar Hayin Talaka. Unguwa ce ta talakawan da basu san ciwon kansu ba ballanta na ‘ya’yansu. Rayuwa ce ake yi cikin rashin tsafta, nutsuwa da sanin yakamata. Ko yaya rayuwar yara masu tasowa a wannan Unguwar za ta kasance a gaba? Shin ko za su samu mafita?
Fadime
Bayan Uwale ta yi wa ‘yar mijinta Faɗime asiri ta haukace,’ yarta Hainsai na ganin cewa ta fidda ita kawai daga ƙauyen kowa ya huta. Sai dai Uwale ba za ta iya ba saboda sharuɗɗan da aka gindaya mata. Kuma a shirye take ta bi takan ko waye domin cikar burinta. Sai dai ƙaddarar da ke cikin rayuwarsu duka mai girma ce.
Rumfar Kara
Malam Iliyasu shahararren malamin addinin Musulunci ne da ke da kima da daraja a idon jama’a. Sai da sai dai ɗansa Sidi bai biyo halinsa ba. Hakan ya ƙara fitowa ne bayan ya yi wa tsohuwar budurwarsa Hanan ciki, ita kuma ta je ta sanarwa mahaifinsa. A gefe kuma ga Halima, wadda ta biyewa su Gwaska da Hayat wajen neman abin duniya ta gurɓata rayuwarta.
Tsakaninmu
Sa’adatu yar gidan Abida da Habibu wacce ‘ya ce da ta shiga ran iyayenta da kuma ‘yanuwanta sosai musamman ma yayanta Abdallah, duk dai ba uwa daya ce ta haife su ba. Amma duk da wannan soyayyar bai hana Sa’adatu gamuwa da kaddarori na rayuwa da suka wuce shekarunta ba, shin Sa’adatu za ta ga karshen matsalolinta?
Marigayiya
Bayan tarin wahalhalu da kuma ƙalubalen da suka fuskanta kafin su yi aure, Rumy ta yanke shawarar yin amfani da kayan amfanin yau da kullum ɗin mijinta domin ita ma ta kamu da irin cutar da ke damun shi, wato cuta mai karya garkuwar jiki.
Rigar Siliki
Mujahid da Binta ‘yan dangi ɗaya ne. Akwai kyakkyawar fahimtar juna sosai a tsakanin su, domin ya zamo mai share mata kukanta a kowane lokaci. Abinda ba ta sani ba shi ne, Mujahid na matuƙar ƙaunarta fiye da komai na duniya. Sai dai kuma ta zaɓi Shukuranu a matsayin miji ba tare da ta san yana da wata gagarumar matsala ba.
Lokaci
Alhaji Yusuf na kwance yana barci sai ga kiran ƙaninsa Khamis cewa ya zo ofishin C.I.D cikin gaggawa ya fitar da shi daga komar wata azababbiyar mace da ta jawo mishi jarfar da bai san yadda zai yi da ita ba. Wace ce ita? Kuma wanene mai gaskiya a cikinsu?
Kishiyar Katsina
Tataburza ta fara wakana a gidan Khamis tun bayan da matarsa ta farko, Aisha ta ji cewa zai mata kishiya, kuma ‘yar Katsina ce. Wannan dalili ne ya sa ta ɗau aniyar ajiye kyawawan halayenta da aka sani tare da ɗaukar sabbi bisa shawarar ƙawarta Zuzee domin tabbatar da cewa Maryam, wato amarya ba ta samu sararin yin numfashin kirki gidan ba. Duk wannan saboda dalili ɗaya: ‘Wai an ce mata ‘yan Katsina suna da asiri.
Muradin Rai
Alhaji Kasim Banazir ƙasurgumin ɗan kasuwa ne a fili, a ɓoye kuma gogaggen ɗan safarar miyagun ƙwayoyi. Yana da wata kyakkyawar ‘ya guda ɗaya da yake matuƙar ji da ita, sunanta Nooreyn. Nooreyn da Ekram tare da Saleym sun je River Kaduna domin yin wani shagali, kwatsam sai ta ci karo da wani mutum ruwa ya jawo shi daga wani wuri, jikinsa duk tabbai.
Kuskuren Wasu
Khadija ta yi kuskure mai girma a rayuwarta, ciki kuwa har da na rabuwa da ‘yarta. Maryam ita ma ta yi kuskure mai girma, musamman na auren mijin da bai san daraja da kimarta ba. Fatima kuwa da-na-sani ne ya kamata yayin da mijinta Kabir ya fara nuna mata asalin halinsa. Alawiyya na matuƙar son mijinta, sai dai kuma wata ƙawarta na neman jefa ta cikin bala’i.
Yini Sittin Da Daya
A fadar sarkin namun dawa, wato Zaki. Dabbobin dawa, manya da ƙanana kan zo masa da labarai iri-iri domin tattaunawa da samo mafita a cikin al’amuran yau da kullum irin nasu na dabbobi wanda yake kamanceceniya da namu na mutane.
Inuwa Daya
Fadila ta shirya tsaf domin ganin ta auri Uban riƙonta ko da kuwa duniya za ta yi Allah-wadai da ita, matuƙar dai za ta samu damar zama inuwa ɗaya da mai tarin arziƙi. Alhaji ya dage kan cewa lallai zai ƙara aure, kuma budurwa zai aura. Wannan dalili ne ya Hajiya Amina ta kasa zaune ta kasa tsaye wajen ganin ta samu mafita dangane da wannan ɗanyen aikin da yake ƙoƙarin jawo mata. A gefe kuma, babbar aminyarta Hajiya Baratu ba ta da burin da ya wuce ita ma ta aure mata miji. Tsakanin Fadila da Baratu wa zai yi nasarar aure Alhaji?
Labarin Asiya
Ba tare da tunanin komai ba Asiya A Baba ta shiga asibiti domin karɓar sakamakon gwajin da ta yi ranar Larabar da ta wuce. Sai dai hankalinta ya yi matuƙar tashi da jin cewa tana ɗauke da cutar ƙanjamau. Hakan ya sa ita da mijinta Hassan zuwa wani asibitin suka yi wani gwajin, sai dai a nan ɗin ma dai sakamakon iri ɗaya ne, ita da shi duka suna ɗauke da cutar. Babban tashin hankalin Asiya shi ne ba ta taɓa zina ba, don haka kai tsaye ta fara tunanin Hassan ne ya saka mata cutar.
I Am Not Your Punching Bag
I Am Not Your Punching Bag And Other Stories is a collection of short moral and interesting stories depicting the daily struggles of African woman.
Rai Da Kaddara
Shin ko Daada za ta iya riƙe amanar Nawfal da Madina kamar yadda ta yi alƙawari? Sai zuwa yaushe ne Nawfal zai samu sauƙin halin kaɗaicin da ya riga ya saba da shi a gidan Julde? Matuƙar da rai, to ƙaddara za ta biyo baya. Yadda za su yi da wannan ƙaddara kuwa zaɓinsu ne.
A Daren Farko
Duk da cewa Dr. Jidda Abubakar Aliyu ƙwararriyar likita ce a fannin cututtukan mata da yara, hakan baya nufin ita ma ba ta da damuwar da ke damunta. Musamman wani mafarki da ya nace mata, wanda kuma duk in ta yi shi sai ta ji ta a sususce. Shi kuwa Dr. Sani, soyayya ce ta rabo shi da Kaduna ta kawo shi Katsina neman Jidda ba tare da ya taɓa ganin ta balle ya san inda zai same ta.
Kuskuren Waye?
Halima da Zarah maƙwafta ne kuma ƙawaye. Makarantarsu ma ɗaya. Suna tsaka da rayuwarsu mahaifin Zahra ya ba da ita ga Hafiz. Babbar matsalar ita ce, mahaifiyar Hafiz ba ta son wannan haɗi da za a yi duk kuwa da cewa su yaran sun fara kamuwa da son juna. Ko ya za ta kaya a tsakaninsu?
Siradin Rayuwa
Karatu ne ya zama sanadin haɗuwar Al’Ameen Bello Maƙarfi da Ihsan a America. Bayan sun sheƙe ayarsu na wani lokaci sai suka yi aure ba tare da sanin iyayensu ba. Yanzu shekaru kusan goma kenan, rashin nutsuwa ya sa dole sun dawo gida Nijeriya. Babbar matsalar da ke gabansu ita ce, ba su san da wani ido za su kalli iyayensu ba.
Hakabiyya
Yayin da fafutukar nemawa mijinta magani ya kai Zawwa zuwa ga tone kabarin wata budurwa mai ciki, hakan ya zamo matakin farko na cukurkuɗewar rayuwar Haƙabiyya tun kafin ta fito duniya. Hameedu, wanda ya canza sunan shi zuwa Huzaif yana ɗauke shi ma da wani ɓoyayyen sirri wanda ka iya fayyace komai ko ruguza komsi. Makirci ya haɗu da makirci, tsafi ya haɗu da mugunta, sirri ya ci karo da sirri, shin ko gaskiya ita kuma za ta yi halinta daga ƙarshe?
Fitsarin Fako
A daren tarewar auren Lantana ne ‘yan ta’adda suka je ƙauyen da aka kai ta suka watsa jama’a tare da yi mata fyaɗe kuma suka kashe mijinta. Yayanta Kamalu, shi ma sun yanke masa hannu ɗaya a wani hari da suka kawo daga baya a ƙauyen Namu-Ya-Samu bayan sun kashe mahaifin Lantana. Sai dai kuma mutuwar Lantana ta bar baya da ƙura, musamman da wasu hujjoji suka fara nuna wa Kamala ɗan yatsa.
Na Kamu Da Kaunar Matacce
Rayuwar Munaya ta birkice tare da wuntsulawa wata duniyar sabuwa tun daga lokacin da ta ga hoton tsohon mijin Zuwaira, wato Zayyad Muhammad Hashim. Tafiyar da ta yi zuwa garin Kaduna da nufin shiga makarantar KASU domin ta ɗora karatun gaba da Sakandare sai ga shi yana neman komawa karatun binciken rayuwar matacce.
Sakacin Waye?
Ummatin Mambila ta yi matuƙar ƙoƙarin gaske wajen ganin ta raini ‘ya’yanta maza uku a bisa nagarta da kamala. Ta kuma ci nasarar yin hakan har zuwa lokacin da manyan guda biyu suka yi aure. Sai dai rayuwa ta zo mata da bazata, inda mutuwa ta ɗauke matayen ‘ya’yan nata ta bar abin da suka haifa mace da namiji. Bayan zama na tsawon lokaci ba tare da aure ba, Giɗaɗo ya Auro Jaru, abinda bai sani ba shi ne, ita kuma a zuciyarta babu wanda take so sama da ƙaninsa Muhamman.
Rikon Sakaina
Ammi na so ta karɓi shawarar juma na tura Zubaida bara, sai dai tana tunanin yadda za su ƙare da Maqsood domin kuwa ya sha nuna mata rashin amincewarsa game da hakan. Ita kuwa Zubaida sai murnar lashe jarabawar da suka yi take yi ba tare da ta san abinda ake kitsawa ba.
Mu'azzam
Irin biyayya da kuma soyayya da Mu’azzam ke yiwa mahaifiyarsa, Goggo, ya sa duniya ke kallon shi a matsayin da nagartacce. To amma a badini kuma yana da wata rayuwa da ko makiyinsa ne ba zai yi farin ciki da ganin sha a ciki ba. Wannan ya hada da rashin adalcin da yake tafkawa a tsanin matansa uku. A hakan kuma Goggo ta umurce shi da kara auren Husna, wacce ta ke kamar kanwa a gare shi, adalilin wani mummunar kaddara da ta fada ciki. Shin ko rikicikin da ke cikin gidan Mu’azzam zai barshi ya zauna lafiya?