Skip to content
Part 1 of 10 in the Series Shameekh by Harira Salihu Isah

DUBAI

Kwance yake a makeken haɗaɗɗen gadonsa wanda ya haɗu ya gaji da haɗuwa, lulluɓe yake da blanket mai shegen laushi ya rufe dukkan ilahirin jikinsa ko ɗan yastansa ba ka hangowa, ba abinda ke tashi a hamshaƙin haɗaɗɗen daƙin nasa sai wani arnen ƙamshi mai sanya nistuwa, da kuma sautin ac wanda ya taimaka wa ƙamshin wajan jefa duk wani halitta da ke cikin ɗakin a yanayi mai daɗin gaske.
Wayansa dake saman bedside drawer ne ya fara ringing, waƙan jimmy na Colorado ne ke tashi yayinda wayan ke kan kukan neman agaji!

My Colorado! You’re my Tonyi my tomato! Me I go take you to Sweeto! You’re my seven my Ronaldo!
Ehh! My gelato!

Ƙiran ne ya tsinke, ba jimawa wani ƙiran ya kuma shigowa, sai lokacin wanda ke cikin blanket ɗin ya ja siririn tsaki tare da mirginawa ya gyara kwanciyan sa hankali kwance ba ko alamun zai bi ta kan wayan balle mai ƙiran ya samu arziƙin a amsa masa.

 Bayan second’s sai wayan ta kuma sanya kukan neman agaji, wannan karon wanda ke cikin blanket ɗin a yangance kaman ba ya so ya miƙo haɗaɗɗiyar hanunsa  ya sanya wayan a silent, hannunsa ya maida cikin blanket nasa dan yasan yanzu kam zai yi bacci hankali kwance.

Bayan kaman mintuna talatin har bacci ya fara awun gaba da shi, kaman a mafarki ya kuma jiyo kukan ɗayan wayansa dake kan gadon a kusa da shi, ringing tone ɗin kawai ya isa ya sanar da kai wanda ke ƙiransa, domin waƙan Simi na Maamaa ne ke tashi, (She’s the angel of my life, I dey call her super woman...)

Wannan karon tunda ko bai duba ba yasan mai ƙiransa, cikin nistuwa ya fito da hannunsa ya ɗau ƙiran tare da sanya wayan a hansakuwa (hands-free), ajiyewa yayi a gefen kansa dake cikin blanket har yanzu, daddaɗan sautin muryan sa na fara jiyowa, cikin ladabi yayi sallama tare da faɗin, “Ummiy naaa!”

Ajiyahn zuciya wacce ya qira da Ummiy ta yi a ɗaya ɓangaren, sannan ta ce, “Allah Ubangijin kowa da komai ga yarona nan Rabbi ka shirya mini shi ka tsare mini shi kayi ma rayuwarsa gaba-ɗaya albarka.”

Ƙasa-ƙasa kaman wani mara gàskiya ya ce, “Ameen ya Hayyu ya Qayyum hajiyarmu.”

“Shameekh wai yaushe za kaji maganata ne? Yaushe za kayi abunda ya kamata? Yaushe za ka girma ne kam?”

“Ummiy kiyi haƙuri Allah ina sane kuma ina shirin zuwa.”

“Au! Ashe kana sane? Tom naji tunda kana sane yaushe ne?”

 “Ummiy zan zo a ƙarshen satin nan Insha Allahu.”

“Ashe dai baka sane tunda ba kasan yaushe bane kuma sai qarshen sati kayi niyan zuwa, zuwan naka ma nasan ba tabbas wataƙila ne, Allah ya shirya ka Shameekh.”

Shagwaɓe murya yayi kaman mace ya ce, “Ayya dai Ummeyh da gaske fa zanzo in Allah ya yarda.”

Ummiy ta ce, “Za kazo ne kake ƙin ɗaukan ƙiran mutane, to bari na faɗa maka za a ji mu akan maganar nan, kar kazo akan lokaci kuma kasan sauran wajan Hajiya za ku gamu ne ba ruwana tunda dama kai ba baƙon ta bane balle ka ce yanzu kake ji daga bakina.”

“Ummiy ayi haƙuri.”

“Shikkenan bakomi Allah maka albarka ya karemin kai ya kawo ka lafiya.”

 “Ameen Ummiy na.”

“Ka kula sosai, ka daina ganin kai ɗa namiji ne ka kula da kanka ka kare mutuncin ka nasan matan wajen nan wasu sai a hankali.”

“To! Insha Allahu Ummiy, a cigaba da mana addu’a.”

Hira suka ɗan yi kaɗan ta masa faɗa kaman koda yaushe idan suka yi waya, sallama suka yi ta kashe wayanta, shi kuma Shameekh gyara kwanciya yayi da niyan cigaba da baccin sa, me ya tuna kuma sai  ya fasa kwanciyan, yaye blanket ɗin yayi ya tashi ya zauna tare da jingina da kan gadon idanuwansa a lumshe.

Zara-zaran yastun ƙafafuwansa na fara gani wanda suka sha gyara suna yalƙi ga su farare tass kaman na ƙafan jariri, sanye yake da farin pyajams da yayi mugun amsar fatansa kasancewan shi ɗin ma fari ne, daga yanayin yanda yake akan gadon kasan dogo ne shi ko ba’a faɗa ba, yana da ɗan jiki dan baza’a ce masa siriri ba, yana da faffaɗan ƙirji mai cike da haiba, gashin kansa kwance suke luf-luf duk da ba wai tara gashin yake yi ba, amma yayi wani irin aski na zamani ne wanda yayi mugun yi masa kyau.

Fiskansa nabi da kallo wanda idanuwansa suke a lumshe, yana da dogon hanci ga kuma ƙaramin baki me dauke da jajayen lips nasa gashin giransa a cike yake kaman na mace wanda hakan ya qara masa kyau sosai, damatsan hannunsa ma kaɗai abun kallo ne, dan kana gani kasan kaga ingarman namiji jarumi kuma ƙaƙƙarfa.

Hanunsa ya miƙa zuwa bedside drawer yana laluɓa wayansa, jin bai taɓa ba sai ya buɗe idanuwansa a hankali yana kallon wajan da hannunsa yake, idanuwansa madaidaita ne farare tas da su sai dai baƙin cikin yayi kaman brown-brown.

Jawo wayan yayi tare da cire sa a key, call logs ya shiga dan ganin misscalls da aka masa, ganin number ba suna yayi misscall biyu sai ya taɓe baki, ɗayan kuma da yaga numbern Daddynsa ne sai ya bi ƙiran.

Bayan wayan yayi ringing aka ɗauka, muryan babban mutum na jiyo saboda a hamsakuwa ya saka wayan, “Assalamu alaikum son.”

“Waalaikassalam, Na’am Daddy an tashi lafiya?”

“Lafiya Alhamdulillahi! son ya ƙasan mutane ya al’amuran?”

“Ga su nan fa Daddy duka babu daɗi.”

“Masha Allah! yaushe za ka shigo?”

Ɗan sosa ƙeya yayi tare da kawar da wayan a kunnen sa, yana faɗin, “Allah nagode maka”, ƙasa-ƙasa.

Daddy ta ɗaya ɓangaren dariya yayi ya ce, “Wato mun dameka yaushe zaka dawo, hakan na nufin Umminku ta ƙira ka, to Allah shirya ka ya maka albarka.”

Da “Ameen” Shameekh ya amsa, waya suka yi ba jimawa suka yi sallama, yana cewa Insha Allahu zai shigo ba jimawa.

Ɗayan layin ya ƙira, yana shiga ana ɗauka, “Hello Yaya Man ya akayi ya Dubai ɗin?” faɗin wanda ya ƙira ta ɗaya ɓangaren. “Lafiya komai normal.”

“Haka akeso, ya yaushe ne za ka shigo kuma?”

“Ba zai jima ba Insha Allah, za ku ganni” faɗin Shameekh.

“Ko dai kuna da wasa ne?”

“No babu fa kai dai na kusa shigowan in Allah ya yarda.”

“To Allah ya amince, Allah ya kawo la lafiya, Yauwa na ƙiraka da wani number ma ba ka ɗauka ba, ko da yake ma ba ka ɗau layina ba balle wani layin.”

 Shameekh shafa kansa yayi yana murmushi ya ce, “Kai ma dai ka so neman magana Sadeeq, kasan bana ɗaukan baƙon layi.”

“To sannu ɗan wasa” cewan Sadeeq a ɗaya ɓangaren yana dariya.

Shameekh murmushi yayi wanda ya ƙara masa kyau sosai, sai ya ce, “Afuwan  Sadeeq.” “Ba mastala Man sai mun ganka.”

“To ka gaidamin su Abba su Baba duka.”

Sallama sukayi, ya kashe wayan ya ajiye a kan drawer dake gefen gadon, sauqa yayi a gadon yana miƙa wanda hakan ya bani daman ƙare masa kallo, zubinsa na jarumai ne jaruman ma jaruman gaske, jikinsa a mummurɗe ga ƙwanji mai ɗaukan hankali.

Cikin takunsa na ƙasaita ya shige haɗaɗɗen toilet nasa, bayan shigansa da mintuna wata baturiya ta shigo ɗakin ta gyara shi tsaff ta gama komi cikin mintunan da basu haura ishirin ba, tana gamawa ta fice dan dama ta gyara palourn da sauran ɗakunan gidan.

Bayan fitan baturiyan da kusan mintuna arba’in ya fito a toilet ɗin, sanye da rigan wanka a jikinsa, fari ne tass rigan wankan ma, gaban dressing mirror ya wuce direct, bayan ya share jikinsa da ƙaramin farin towel dake hanunsa, sai ya jawo mansa ya shafa, ƙamshin wannan mannasa yafi wani turare.

Bushar da suman kansa da ba yawa yayi, ya ɗauko mayukan da sukafi kala biyar ya haɗa ya shafa a gashin kansa, sheƙi gashin ya keyi dan daman baƙi ne gashin, ya kuma taje kan nasa, sai da ya ɓata kusan 1 hour kamun ya wuce wajan ma’adanan kayansa wanda yake babba sosai wani waje kaman switch  ya danna a take ma’ajin kayan ya buɗe, ganin kayan nasa sai ya yamusta fiska, dan har kaman zai juya ya fasa ɗaukan kayan sai kuma mai ya tuna ya juyo, ƙananun kaya ya ciro , farar riga da baƙin wando sai P-cap black.

Kayan ya fesawa turaruka kusan guda shida, sannan ya ajiye kayan a wani waje wanda musamman na ajiye kaya ne a gefen dressing mirror, angogon maƙalwa a hanny ya ɗauko, baƙi designer mai stadan gaske, sannan ya ciro  takalminsa baƙi sau ciki, ƙirar Dubai wanda kuɗinsa ya kai 750k.

Sai da ya ciro komai da zai buƙata sannan ya fara warware rigan wankam da ke jikinsa, kwantattun gashi ne a jikinsa mai tafiya da hankali gami da imanin duk mai kallonsu, dan sosai gashin jikin yayi masa kyau kasancewan sa fari kuma farinsa mai yellow-yellow ne.

Short da vest nasa duka farare ya saka, wannan baturiyan ce bayan ta gama gyara dinning tayi komai ta zo ta ƙwanƙwasa masa ƙofa, ya gama shiryawa kenan yana taje sajensa da gemunsa da yake dai-dai da fiskansa, amsawa baturiyan yayi ta hanyar bata izinin shigowa,  turo ƙofan tayi ta shigo ta ɗan rusuna ta ce, “Sir your breakfast is ready.”

“Ok” shi ne kawai abinda Shameekh ya faɗa, sai ta miƙe ta fice, turarukansa ya ɗauka ya feshe jikinsa ba abinda ke tashi a jikinsa ko ta ina sai ƙamshi kawai, keyn motansa da ke kan mirrow ya ɗauka, yaje wajan gadonsa wanda ke a gyare nit, kallon bedsheet ɗin da aka saka masa brown colour ne yasa shi jan tsaki ya ɗauki wayoyinsa ya juya ya fice a ɗakin fiskan nan a haɗe.

Baturiyan ya samu tsaye a wajan dinning tana jiran zuwansa dan ta yi saving nasa, wucewa yayi ya zauna yana huci cikin harshen turanci ya ce, “Hey you!”

Zuwa tayi da sauri ta staya daga gefe jikinta har yana ɗan rawa saboda yanayin da ya mata maganan, shi kuma kallon sama da ƙasa ya mata sannan ya ce, “Are you out of your sense or you are okay with the work you want to leave? Okay! then am paying you now so that you can leave cuz i can’t take this nonsense for no reason.” Jikin baturiyan na rawa tana faɗin, “Am sorry Sir³.”

Harara ya dalla mata ya ce, “Sorry for your self, if you want ur work again go and remove that useless bedsheet you use for my bed ,and this should be first and last don’t you ever use this colour for my bed again, infact not even bedsheet anything in this house is either you use white, blue or black hope you get me?”

“Am sorry Sir! Abinda kake so shi zan yi, yau ma stautsayi ne” faɗin baturiyan da turanci dan kana ganinta kasan hankalinta har ya tashi jin zai sallameta.

A gadarance ba tare da ya ƙara kallon inda take tsaye ba ya ce, “Oyah! Go and take a look again to my rules for being a maid in this house” ya faɗa yana wucewa dinning ɗin ya ja kujera ya zauna.

Biyosa baturiyan tayi dan tayi saving nasa, kallon da ya mata ne ya sanya ta saurin juyawa, shi kuma staki yaja tare da mayar da kallonsa kan dinning ɗin ya ciro wayansa yana lastawa.

Bedroom nasa ta wuce direct ta cire wannan bedsheet en tare da blanket ɗin duka, White bedsheet ta ɗauko ta shimfiɗa kaman yacce yake so, ta ɗauko black blanket me laushin gaske shima ta shumfiɗe sa, sannan ta ƙara gyara ɗakin, daman ya hanata shiga masa bathroom shiyasa ba ta bi ko hanyan ba, ba ta ma san inane bathroom ɗin ba, tana gama abinda ya kamata tayi ta fice ta samesa zaune yana danna wayansa, coffee ta haɗa masa dan shine abincin sa da safe sai dai sometimes yakan buƙaci chip’s, ta buɗe baki za tayi magana kenan ya ɗaga mata hanu alaman baya son jin komai daga bakinta, shiru tayi abinta tare da juyawa tabar dinning ɗin tunda tasan baya son yana cin abu a staya a kansa.

Shanye coffee ɗin yayi duka ya ɗau tissue ya goge bakinsa ya ɗauki keyn motansa ya fice a palourn, wajan haɗaɗɗiyar motansa mai shegen kuɗi ya nufa, yana shiga ya mata key, baturiyan kuma tana jin mostin sa ta fito da sauri ta bisa har wajan motansa ta ce, “Sir what should i cook for lunch?”

Shameekh bai ko kalleta ba ya taɓe baki ya ce kar ma tayi girkin komai da shi, in za tayi to ta yi nata da gate man, yana gama magana ya ja motansa ya fice da mugun gudu, baturiyan jiki na rawa ta juya ta koma ciki, gyara dinning ɗin tayi ta kuma gyara palourn sannan ta tattara ta wuce kitchen, duk da ya ce banda shi amma za tayi ta ajiye ko dan visitor’s tunda ya kan yi baƙi lokaci zuwa lokaci.

NIGERIA

Damaturu-yobe State.

Anguwan Shagari, anguwa ne na masu abin hannu, akwai gidajen masu rufin asiri amma akwai manya-manyan gidaje na masu kuɗin gaske, wani ɓari na anguwan kuwa wasu manyan gidaje ne wanda kusan duk yanayin ginin iri ɗaya ne, sai dai amma ko wani gida da gate nasa, gidajen suna jere kusan guda tara, ɗaya na kallon ɗaya, kuma duka gidajen ba ƙaramin girma ne da su ba, gidan da yake na uku a jeri shi na kusta kai ciki, gida ne haɗaɗɗe ya haɗu iya haɗuwa, dan tsayawa tsara irin haɗuwan gidan zai cinye mana page guda, cigaba da kusta kai na nayi har dai na tsaya dai-dai gefen wani ƙofa da na ke iya jiyo sautin mutane a ciki, ɗakin na tunkara, ina buɗe ƙofa nayi arba da wasu stala-tsalan kyawawan ƴammataye  guda shida 6 zaune a cikin ɗakin.

Guda uku na zaune a kan gado, ɗaya na zaune a kan mirrow sai kuma sauran biyun da ko wacce ke zaune akan stool nata daban, da alama duka ƴammatayen shekarunsu zai yi kusan dai-dai, kana ganinsu kasan sa’annin juna ne, ba za su wuce 22year’s to 23year’s ba, ko waccen su da waya a hanunta qirar i phone, ƴammatayen dukkansu farare ne tass kaman larabawa, sannan kyawawa ne dai-dai gwargwado Masha Allah!

Ɗaya wacce ke zaune akan stool ne tayi magana ta ce, “Guys wallahi na mastu yaya Soffy ta dawo, nasan akwai show a gidan nan, wannan karon stoho zai yi shara.”

Ɗayar da ke zaune a ɗayan stool ɗinne ta ja siririn tsaki tare da aikawa wacce ta fara magana harara ta ce,  “Amma dai Meelat da gangan da neman magana kika yi wannan maganar, kinsan dai ba wani shiri muke da yaya Soffy ba, duk idan ta zo sai tabi ta addabi rayuwan mutane akan wannan ɗan gidan masu ji da kai ɗin” matashiyar budurwan ta ƙarisa magana tana ɓata fiska.

 Wacce ke zaune a bakin mirrow ce tayi magana, kuma da alama ta ɗan fi su shekaru dan zata yi iya kai 25year’s, wayan hanunta ma yafi nasu dan ita iphone 14pro ne a hanunta saɓanin su da yawancin su iphone X ne sai kuma 11pro a hanunsu, a zuciye da kuma tsawa-tsawa ta ce, “Subby can you plss close ur mouth, mai ya miki? mai ruwanki da shi? So karki kuma faɗa masa mai ji da kai, infact idan ba raini da ke damunku ba, ai ko Ya Sabeer ma ya girme shi, amma kina ƙanwar bayansa kina rena sa, so wannan ne last warning da zan muku akan sa, you guy’s should watch your tongue’s idan har kuna so mu shirya.”

Wacce da alama ita ce  Subby sai ta tura baki tare da kawar da kai irin bata so faɗan da aka mata ba.

Waɗanda suke zaune a kan gadon me za suyi idan ba dariya ba, duk dariyan Subby suke yi har dai suka stagaita, sannan ɗaya a cikinsu ta ce, “Ke ma Subby wa ya aike ki yin wannan magana? kinsani fa sarai yaya Jidderh ma tana ciki kuma dai ita ce sarauniyar” faɗin Deeyah tana murmushi.

Wacce ke kan mirrown tashuwa tayi ta nufi hanyan ficewa a ɗakin tana danna wayanta tare da faɗin, “Zama a cikinku ya fara ja mini reni, tunda kun kalli kan mu ɗaya yanzu duk kun kamo ni tsayi”, ta ƙarisa maganan tare da ficewa a ɗakin ta turo musu ƙofa.

 Meelat ce tayi fiskan tausayi tare da cewa “Dee, Leemah da Deeyah meyasa kukayi dariya bayan kunsan yaya Jidderh da saurin fushi, yanzu ga shi kun ja ta ɓata rai, kuma dai kunsan gwanda ita a kan yaya Soffy, ita ke zama a cikinmu ba ruwanta da mu ƙannenta ta yi wasa da dariya da mu, in dai hauka ne da a gaban yaya Soffy kuka yi wannan maganan ai da tuni kun gansa, da an bawa kowa sadakan bugu a baki.”

Meelat ta ƙara mai da idonta kan Subby ta ce, “Kinsan halin yaya Soffy sarai a kan shi, ni kuma duk ba dan komai nace na matsu ta dawo ba, wallahi nayi kewanta ne kawai, kunsan muna shiri da ita nikam.”

 Subby taɓe baki tayi ta ce, “Ku kuka sani yanzu kuma” ta tashi ta shige toilet.

Wacce aka ƙira da Dee ta ce, “Ai kuwa nikam anjima zan dangana da gidan stoho na bawa yaya Jidderh haƙuri dan nasan yanzu haka can ta wuce, bawa yaya Jidderh haƙuri ya zama mini farilla ni da nake dakon wayan hanunta, naji wai wancan wahalallen saurayin nata zai sauya mata kuma fa kunsan ba amsan na hanun nata zai yi ba.”

Leemah ta ce, “Nima zan biki mu bata haƙuri dan gaskiya banason fushin yaya Jidderh tamu.”

Deeyah jin abinda suka faɗa sai ta kwashe da dariya ta ce, “Ke ma Leemah nasan abu kika gani kike so tabaki, kunsan yaya Jidderh da kyauta, anyway ni banson komai amma nima zan bata haƙuri.”

Meelat murmushi tayi ta ce, “Da ya fi muku kam, kunsan dai yaya Jeeddeerh ita ce idonmu a gidan nan, serious bai kamata muna ɓata mata rai ba, Subby ce kawai da ba ta ji da ƙaton kan ta.”

Subby da fitowanta kenan daga toilet, jin abinda Meelat ta ce sai ta aika mata da harara.”

Meelat ta ce, “ki harareni da kyau, amma ko menene dai ke ce kika fara maganan da ya ɓata mata rai.”

Dee ta ce, “Yanzu dai a matsayina na Auntynku in absence of yaya Jeeddeerh ni yaya Fadeela na ce case close.”

Dukkansu biyar ɗin dariya suka saka har da ita Dee ɗin da tayi maganan, Deeyah ce ta fara hararanta ta ce, Waye sa’anki a nan? dan kawai kin ga ba kya ce mana yaya shi ne har da reni, wai yaushe ma kika cika 21year’s ne Dee?”

Tura baki Dee tayi tare da faɗin, “To nidai naji ko nice ƙarama na ɗau matsayin manya na ce a rufe babin maganan ya wuce.”

Subby murmushi tayi ta ce, “Nikamma Deeyah kin tuna mini birthdayn mu ya kusa, akwai cin kuɗi, kaiii gaskiya dole ma na bawa yaya Jidderh haƙuri nima.”

Leemah ta ce, “za ma ki dawo hanya ai wallahi, indai yaya Jidderh ce ko wa ma yasan yana cin albarkacinta kuma tana yi wa kowa kirki.”

 Meelat miƙewa tayi tare da buga stalle kaman ƙaramar yarinya ta ce, “kowa ya tuba dan wuya ba lada, sai da ke yaya Jidderh tamu.”

Shameekh 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×