Skip to content
Part 4 of 10 in the Series Shameekh by Harira Salihu Isah

Ƙwafa Hajiya Mama tayi ta ce, “Ni ban ma san me ya kawo ki ba takwara, kin zo dare-dare kaman mara gaskiya za ki addabi rayuwan mutane.”

Jidderh na daga kwance ta ce, “Ni bansan ma me yake kawo ni gidan stohuwar nan ba, bana iya haƙuri sai na zo, idan nazo kuma ki ta mini gori kaman ɗauke mijin zan yi na tafi da shi, laifi nane ma da nake zuwa ma gidanki ai”, ta ƙarishe zancen muryanta na rawa, kaman mai shirin kuka dan har idanuwanta yayi ƙwalla.

Hajiya Mama haɓa ta kama ganin ikon Allah, ta ce, “Eh samun waje kare da rawa a bakin ramin kura, mai arahan hawaye, yanzu me abin kuka anan? To Allah ya azurtaki da Manzon sauƙi takwara, mutum sai son hawaye da kuka kaman wacce mijinta ya mutu, wai haka za ki dinga yi wa mijin ko nice da kike ganin damana kike min wannan taɓaran? Sai ka ce daman ni na ce ki zo.”  Tura baki tayi ta ce, “Ni dai Hajiya banaso, zan tashi na koma gidanmu, alhamdulillah muma muna da gida.”

Hajiya tana ƙoƙarin miƙewa ta ce, “Na kan ga rasulu idan nayi hali na gari, yanzu ke takwara ni kike faɗa wa kuna da gida? To naji daman nasan kuna da shi ai ba a daji kuke kwana ba, amma a haka kika zo mini gida dan ki takura wa mijina, to kin zo kenan ba in da za ki koma, ke da barin gidan nan ai kuma ba yau ba, abin da ya sanya ki zuwa dare-dare, shi zai zaunar da ke ki kwana dole, dan ƙafan gwoggonki Fatu.”

Jidderh tura baki ta kuma yi, kaman mai shirin yin kuka ta ce, “Nidai ba ruwan gwoggona.”

Murmushi Hajiya Mama tayi ta ce, “To naji masu gwaggo, mu da bamu da su a raye Allah bamu haƙuri, kuma na kowa ma zai tafi indai mutuwar yanzu ne, taso muje mu ci tuwo dan nasan daman kwaɗayi ya kawo ki gidana.”

Jidderh ƴar dariya tayi jin wai kwaɗayi ne ya kawo ta, miƙewa tayi daga kwancen da take tana faɗin, “Eh koma menene dai na zo ne dan na ci tuwo da sakwarata.”

“Sai dai sakwara kam, ni rabani da halinki, bansan abin da ya kai Sama’ila saka miki sunana ba, dan ni ba haka halina yake ba”, Hajiya Mama ta faɗa tana ƙoƙarin ficewa a ɗakin.

Jidderh sauƙowa tayi ta naɗe wa Hajiya Mama sallaya da hijabinta, sannan ta ɗauki wayanta ta bi bayanta a niste, suka fice a ɗakin, palour suka nufa dai-dai Alhaji baba na shigowa shi da wani matashin saurayi.

Stohon da suke cewa Alhaji baba murmushi ya saki ganin jidderh, ya ce, “Ah! Amaryata ce da daren nan.”

Jidderh na murmusawa ta ce, “Nice dai angona mai ran ƙarfe, ka ƙi zuwa hatta ɗaukan amaryan shiyasa na taho abina da naga dare tayi.”

Alhaji baba ya ce, “To Masha Allah! Amaryata ta kyauta, Allah ya miki albarka.”

Amsawa da “Ameen”, jidderh tayi, sannan ta ce, “Yaya Sabeer an wuni lafiya?”

Matashi mai suna ya Sabeer murmushi yayi ya ce, “Lafiya alhamdulillah stohuwa amaryan stoho.”

Jidderh kallon Hajiya Mama tayi, tare da turo baki ta ce, “Allah kuwa sakwara ki ce musu su daina ce mini stohuwa, ƴar gangariyan budurwa da ni haka kawai a rage mini farashi.”   Hajiya Mama haɗe fiska tayi tare da kallon Ya Sabeer ta ce, “A daina faɗa wa takwarata stohuwa, ita ba stohuwa ba kuna ganin yarinya ƴar jinjira da ita, kuna stofar da ita.”

Ya Sabeer dariya yayi tare da riƙe bakinsa, da kunnensa alaman yaji ya daina, ita kuma jidderh murmushi tayi ta ce, “Yauwa Hajiya Mama ta.” Alhaji baba ne ya ce, “To azo aci tuwo kubar shirmen nan, dan Hauwa’u rigimanta ya mata yawa.” Duk akan centre carpet suka zauna, Jidderh ce tayi serving nasu, ta saka wa alhaji baba tuwon biski da miyar zogale da ya ji kifi kasancewan yana da ciwon sugar, Hajiya Mama kuma ta saka mata tuwon shinkafa da miyar zogale da kifin ita ma, ta saka wa Ya Sabeer tuwon shinkafa da miyar kuɓewan da yaji man shanu ga namomi, sannan ta saka wa kanta tuwon doya(sakwara) da miyar egusi shi ma ya ji bushashshen nama.

Abincin suke ci wajan shiru ba ka jin ƙaran komai, sai na taunan abincin nasu,  jidderh bata wani ci sosai ba ta cire hanunta, ɗiban ruwan zafi tayi ta haɗa black tea ta sha, gefe ta matsa tana duba wayanta hankali kwance ciki ya ɗauka.

Hajiya Mama kallon jidderh tayi tare da girgiza kai, ta ce, “Ke dai takwara Allah ya yaye miki rashin cin abincin nan, watarana har gwanda mai sunan Alhaji da ke kam.”

Murmushi kawai jidderh tayi ba ta ce komai ba. Ya Sabeer ya ce, “Ai Hajiya Mama dai-dai kenan, kin ga an haɗa su perfect match, amma dai nikam ina namiji ban ci ba wa zai ci? Ni fa na nemo abincin, ai gwanda ace mace bata ci sosai akan a ce namiji ne baya ci sosai, don ita mace hakan ma ado ne gare ta.”  “Kubar damar mini amarya da surutu, tun da ta ƙoshi to a ƙyale ta”, faɗin alhaji baba.

Jidderh murmushi tayi tare da cewa, “Yauwa mijin ka gama ci kai ma sai muyi fira”, ta faɗa tana komawa kan kujera ta zauna. Alhaji Baba ne ya mayar da dubansa kan Ya Sabeer ya ce, “Nikam yaushe ƙanwarka za ta dawo ne? Ko ita ma ta fara ɗaukan huɗuban wancan mara jin maganan ne eyye?”

Ya Sabeer ya ce, “Alhaji baba wannan yarinya kam me mutum ma zai ce ne, su Mom sun jima da sakalta ta, kawai ka ƙira Dad ka tambayesa, dan nikam ban san ko tana hanya ko bata hanya ba, ba ma magana take mini ba tana jin yanzu ta girma ta fitsare.”

Ƙwafa Hajiya Mama tayi kawai, amma ba ta ce komai ba, shi ma Alhaji baba bai kuma cewa komai ba, har suka kammala cin abincin, baba larai ta zo ta gyara wajan tass.

Alhaji Baba sai da ya gyara zamansa har da kishingiɗa, sannan ya ce, “Amaryata ɗauko mini ƴar salulata (waya) a ɗaki, ki zo ki mini ƙira dan naga iyayennaku sai an saɓa musu za su yi abin da ya kamata, su kuma kula da tarbiyyanku, idan ba ma lalacewan zamani ba duk cikin yaran nan akwai mai yara irin yacce na haife su ne, ni ban kasa tarbiyyansu su kusan goma sha ba, amma ni za su wasta mini kasa a ido su kasa yi wa jikokina tarbiya, daga mai uku sai mai huɗu, ba mai yaran da suka wuce biyar, sun ɗau rayuwan yahudawa sun ɗaura wa kan su, basu san yahudawan la’ana ce ke bin su ba, da akwai wan da ya kai yahudu auran mata da yawa da haihuwa ne, addu’an Annabi ne ya sa yanzu suke zama da mata ɗaya kuma yara biyu mace da namiji, ai Annabi Dawuda yahudu ne kuma matansa sun kai ɗari, Annabi sulaiman ma yahudu ne matansa sun bai wa ɗari baya, yanzu Allah ya rahamce mu muke auren mata har huɗu sannan mu hayayyafa, yacce Annabi SAW zai yi alfahari da mu ranan ƙiyama, kuma sai ga shi mun ɗauko al’adan yahudu mun iza a kawunanmu, to zan kuwa saɓawa iyayenku.”

Jidderh tashuwa tayi ta tafi ɗauko wayan da sauri, dan kowa yasan Alhaji baba bai da mastala amma idan aka taɓo sa, ransa ya ɓaci to fa jam’i yake haɗawa, stoho mai ran ƙarfe.

Ya Sabeer ma tuni ya miƙe ya musu sallama, yayi gaba abinsa kamun Alhaji baba ya haɗa da shi, a basa kasonsa, gidansu ya wuce a ƙafa kasancewan gidansu yafi kusa da na su Alhaji baba.

Jidderh ta ɗauko waya tana ƙoƙarin zama, sai ƙira ya shigo wayanta ita ɗin ma.

Baby ce zaune a dinning area ita da Ummiy suna cin tuwo, kuma tuwon da Ummiy ta fi so, tuwon shinkafa da miyar kuka da man shanu.

Da Ummiy ta gaji da surutun baby, sai ta ƙwalawa Talatu mai aiki ƙira, zuwa tayi cikin ladabi ta ɗan durƙusa ta ce, “Hajiya gani nan.”

Ummiy na murmushi ta ce, “Yauwa Talatu yarinyar nan ta dameni, tun ɗazu yarinya taƙi barina na ci tuwo, cikin kwanciyan hankali sai fitinata take, wai sam ita ce tayi miyan ba ke ba, dan taji na ce yayi daɗi, gaskiya ne ita tayi ko kuwa fitinane irin na Baby?”

Talatu murmusawa tayi ta ce, “Hajiya ai wallahi dai ita ce tayi, dan taƙi ƙyaleni na saka ko hannu na taya ta, ita tayi har da tuwon ma.”

Ummiy na washe baki cikin jin daɗi ta ce, “Inyee ki ce mini babyn Ummiy ta girma saura aure, amma wannan iya girkin dai kyawunsa na aurar da ita a ƙauye, dan ta wuce auren birni da wannan girkin.”

Talatu dariya ta fara yi, da yake daman sun saba raha da Ummiy, ba ruwan Ummiy da kana mata aiki ko wani abu, bata wulaƙanta ɗan Adam sam-sam, wasa da raha duk idan ta kama tana yi da masu aikinta, kuma ita ɗin ce ta ce su dinga shiga kitchen da baby dan ta koya aiki, tun da ita asibiti na cinye mata lokaci, kuma kada ta ɗau alhaƙin yarinya irin tarbiyan yaran masu kuɗi a yau, yarinya ta girma ta kai aure amma ba abin da ta iya, komai sai mai aiki ta mata, idan tayi aure to ita kawai kwanciya da miji ta sani, masu kuɗi ku gyara tarbiyan yaranku saboda halin rayuwa shawara ce.

Talatu tana dariya ta ce, “Haba dai Hajiya wannan ai matar drivern jirgi ce, ba in da aure ba ya kai mutum, amma Insha Allah ko a ƙauye Saudiyya ba za ta zauna ba.”

Baby murmushi tayi ta ce, “Yauwa aunty Talatu na, faɗa wa Ummiy ko a Makka ne to a babban birnin zan zauna in Allah ya yarda, shiyasa nake yin ki auntyna.”

Ummiy ta buɗe baki za ta yi magana sai wayan baby ya fara ihun neman agaji, Ummiy da yake wayan na kusa da ita, ɗauka tayi ta miƙawa baby tana faɗin, “Duba mana ko ƙiran kuɗaɗe ne za su shigo Mu fara shiri, amaryan ɗan ƙauye.”

Baby amsan wayan tayi tana tura baki wai bata so, ganin saƙo ne ba ƙira ba buɗewa tayi, ai ba shiri ta waro ido akan wayan tana gani da kyau, ai miƙewa tayi ta ɗan yi tsalle har da juyi tana faɗin, “Wayyo Allah na! Ina son ki yaya jidderh, Allah ya bar mini ke, Allah ya mallaka miki Yaya ke kaɗai ba kishiya, Ummiy ga shi ki gani yaya jidderh ta saka mini card.”

Karɓan wayan Ummiy tayi ta duba, ganin yawan katin sai ta murmusa ta ce, “Allah ya mata albarka ya ƙara buɗi, Allah bata miji nagari”, ta faɗs tare da miƙa wa baby wayanta.

Baby ya amsa wayan tana cewa, “Ai Insha Allah Yaya ne mijin, shi ne nagari kuma na alkairi, kai idan yaya ya kuskura zai yi wa yaya jidderh kishiya ko yaudara, to ni kaɗai na ishe sa tuwo da miya dan ba zan bari ba ma hakan ta faru.”

Ummiy haɗe fiska tayi ta ce, “Sannu addarsa, Allah zan saɓa miki akan manyancenki baby, shi shameekh ɗin sa’anki ne, to ki yarda ya ji abin da kike cewa, addu’an alkairi kawai shi za ki yi ba surutu ba, kuma maza ki ƙirata yanzu ki gode mata, bana son surutunkin nan mara kai.”

Cunna baki baby tayi wai dan Ummiy ta mata faɗa, Ummiy kuwa ko kallonta ma bata yi ba ta ci-gaba da abin da take yi, sai da Talatu ta bai wa Ummiy haƙuri Allah ya huci zuciyanta, sannan ta bar dinning ɗin, baby kuma layin yaya jidderh ta laluɓo tayi dialing kaman yan da Ummiy ta faɗa.

Wani haɗaɗɗen club ne a ƙasar Dubai, club ɗin da sai wane da wane ke zuwa, don classic club ne, Shameekh ne zaune a wani table da wani matashin saurayi wan da za su yi sa’an juna a shekaru, matashin kyakkyawa ne Masha Allah, amma fa bai kama ƙafan Shameekh ba, duba da yacce suka mai da hankalinsu akan juna, to kasan tabbas abu mai muhimmanci suke tattaunawa a kai, wannan matashin ne ya ce, “Man yanzu to ya za’a ɓullowa abun?”

Shameekh ya buɗe baki zai yi magana sai haɗaɗɗiyan stadaddiyar wayansa, tayi flash ta kawo haske da vibrating alaman ƙira ne ya shigo, fasa maganan yayi tare da saka wayan a silent, yana gani har ƙiran ya kaste.

Wannan matashin ƙwafa yayi ya ce, “Gaskiya idan aka ce maka kana kyautawa to ƙarya aka maka Man, kai fa ka laƙantu da wulaƙanci da iyayi kaman wani Garage gare ka ba dick ba, haba mata masu Garage su ya kamata su yi wannan iyayin, ba gardi irinka mai Banana ba, tun ɗazu wannan baiwar Allah sai ƙiranka take yi, amma ka ƙi ɗauka, wai meyasa ne kake mata haka?”

Shameekh haɗe fiska yayi tare da aikawa matashin da wani kallo ya ce, “Manseer please let’s talk about what brought us here, kabar maganan wani dick wani Garage ne ko me, kasan ba son maganan banza nake ba, dan ba shi bane a gabana.”

Manseer dariya yayi ya ce, “A faɗawa kaji da agwagi mu zabbi firewa muke yi, magana kake nema wai an ce da gauro ya iyali, kai ɗin ne baka son maganan banza? Hhhhh ko da yake daman ai nasan ba shi ne a gabanka ba cucumbern jidderh ne a gabanka, so please idan za ka bar wulaƙanta ƴar mutane ka bari idan ba haka ba za ka sha mamaki.”

Wani kallo Shameekh ya yiwa Manseer tare da haɗe fiska ya ce, “Yanzu idan da yara a nan ba sai ka ja su renamu ba, ni na faɗa maka ina da issue da mace balle wani ka ɗosana mini wani shirme.”

Murmushi Manseer yayi ya ce, “Eh lallai a yanzu kam ba ka issue da mace, amma ka guji haɗuwanka da ita, Allah ya sa ta dinga ƙarar maka da ruwan jiki za ka dawo hanya.”

“Abar wannan magana”, faɗin Shameekh rai a haɗe.

Manseer ya ce, “Ai dole ka ce abar maganan tun da kasan kwanan zancen, Man nifa idan ba ka yi ka bani waje, ka masta na shige layin masu nema ayi da ni, wannan haɗaɗɗiyar wa zai so ta wuce sa, irin su idan ka ajiye su a gida ko ba komai ka dinga farinciki idan ka kallesu, mace har mace ga….”, wani irin kallon da Shameekh ya yiwa Manseer, shi ya sanya shi haɗiye sauran maganan da zai yi yana dariya, dan Shameekh ɗin ya san dole maganan banza zai faɗa.

Tsaki Shameekh ya ja rai a ɓace ya miƙe ya kama hanyan ficewa a club ɗin, dan daman a takure yake da kallon da ƴammatan club ɗin ke masa.

Yana ficewa waje yayi wajan motansa, fiskan nan a haɗe rai a ɓace ya buɗe motan ya shiga, yana ƙoƙarin tayar da motan sai Manseer ya fito daga club ɗin shi ma dan dama bayansa ya biyo tun fitowansu, kallonsa ya sashi saurin tayar da motan yayi gaba, yana driving ya ja wayansa ya duba lokaci, ganin mid-night ne yanzu a wajensu suna fin agogon Nigeria da 4 to 6 hours, wanda hakan ke nufin yanzu bai wuce 9 zuwa 10 na dare ba.

Yana isowa gidan nasa yayi horn, mai gadi ne ya taso ya leƙa duk da dare ne amma ya gane mai gidannasa ne, tun da daman ya sani yana iya kai ire-iren wannan lokacin a waje, buɗe masa gate yayi ya shigo da motan, parking yayi ya fito mai gadi ya masa sannu da dawowa,  hannu kawai Shameekh ya ɗaga masa alaman ya amsa, ya shige cikin gidansa.

Bai tsaya yin komai ba a palourn ya wuce ɗakinsa, yana shiga ya cire kayan jikinsa ya rage daga shi sai white short nasa, sanin idan ya shiga toilet ɗin zai iya jimawa, shiyasa ya fasa shigan ya koma ya zauna a kujeran da ke cikin ɗakin nasa, wayansa ya ɗauka ya kalli misscall’s da aka masa, scrolling na number’s ɗin yayi, da ya zo dai-dai layinta sai ya tsaya kaman ya ƙira kaman kar ya ƙira, sai ga wani ƙiran ya shigo wayansa kuma new number ba suna, kasancewan ya gane numbern sai ya ɗauka dan misscall na numbern da yawa, yana ɗauka yayi shiru bai ce komai ba, a ɗaya ɓangaren kuma cewa aka yi, “Hello! Ya Shameekh ya kake?”

A taƙaice ya ce, “Lafiya, ƙira da daren nan lafiya? Wacece?”

Wani numfashi aka sauƙe a ɗayan bangaren wan da zai tabbatar maka da na haushi ne, amma ba’a ce komai ba.

Shameekh kuwa jin shiru ba a ce masa komai ba, sai kawai ya kashe wayansa yana taɓe baki, amma fa ya gane  wacce ta ƙira ɗin dan true caller ya nuna sunanta ɓaro-ɓaro, kuma daman ya gane layin da take addabansa da shi, damuwane baya so shiyasa yayi hakan kawai, guntun staki ya ja a fili ya ce, “Ke kika sani.”

Shameekh bai gama rufe baki ba wani ƙiran ya kuma shigowa, kuma da wannan numbern ne na ɗazu, yanzu kam ransa a ɓace yayi picking, dan ba abin da Shameekh ya stana kaman yawan ƙira kuma da number mara suna ko ɓoyayyen layi, a harzuƙe ya kara wayan a kunnensa tare da cewa…

Jidderh ganin ƙira ya shigo wayanta fasa miƙawa Alhaji baba wayansa tayi, cikin zaƙuwa ta duba dan duk a tunaninta shi ne ya ƙirata, amma sai ganin layin baby tayi wan da tayi saving da “Lil Sis”, ɗauka tayi tana murmushi ta ce, “Assalamu alaikum Babyn Aunty jidderh ya aka yi?”

Baby a ɗaya ɓangaren cewa tayi, “Na’am yaya jidderhta, lafiya lau naga kati nagode sosai, Allah ya ƙara buɗi, Allah ya bar mana ke yayarmu.”

Sansanyar murmushi Jidderh ta yi ta ce, “Ameen ya Rabbi babynmu, ki gaishe da Ummiy ko sai da safe.”

“To Yaya jidderh Insha Allah Ummiy ta ji gaisuwa”, baby ta faɗa suka yi sallama  sannan jidderh ta kashe wayanta.    Jidderh ta ce, “Mijin ga wayan naka wa za’a ƙira maka?”

“Yauwa Hauwa’u dubo mini layin babanku Sulaiman.”

Jidderh amsawa tayi tare da shiga numbonin wayan, ta laluɓo layin big Dad ta aika da ƙira, yana shiga ringing ɗaya yayi aka ɗauka, ana ɗaukan ƙiran ta miƙa wa baba alhaji wayan ta ce, “Ga shi nan an ɗauka stoho.”

Amsan wayan yayi tare da karawa a kunnensa, ya amsa sallaman da big Dad ke masa a ɗaya ɓangaren, gaisawa suka yi big Dad ya ce, “Baba ya jiki ya kuma su Hajiya?”

“Duk muna lafiya sulaimanu, na ce yaushe Safiya za ta dawo?” Faɗin Alhaji baba fiska a haɗe.

Big Dad a ɓangarensa sai da ya ƙai-ƙaya kan sa sannan ya ce, “Ammmm baba tana dawowa Insha Allahu.”

Alhaji Baba da faɗa ya ce, “Kai Sulaimanu ungo naka, na ce ungo naka ɗan ƙaniya, daman na ce maka ba ta dawowa ne?  Ka fa shiga hankalinka Sulaimanu, ita Safiya fa yarinya macece kar ka ɗaure mata baya ka lalata mini jika, dan bazan yafe maka ba muddin tarbiyan jikata ya lalace, maza-maza indai na isa da kai ka ce ta dawo goben nan, ba zai yiwu ƴa mace da ita ta zauna a ƙasar marassa ishashshen tarbiya ba, tun da rai na ba za ku ƙonani ba, yarana basu yi wannan abun ba to jikoki na baku isa ku ce za ku sanya su a wata bidi’ar rayuwan ba.”

Hajiya Mama rai a ɓace ta ce, “Alhaji ka bani wayan.”

Alhaji baba miƙa mata wayan yayi, big Dad na ƙoƙarin gaisheta ta ce, “Sulaimanu ka riƙe gaisuwanka, ina fatan ka ji abin da babanku ya ce ko? To sayfiya ta dawo goben nan kuma duka zan haɗu da ku ne mutanen banza mutanen wofi kawai.”

Haƙuri big Dad yake bayarwa amma ba wan da ya saurare sa, dan baba alhaji ma karɓan wayansa yayi ya kashe.

Jidderh cikin girmamawa ta ce, “Ayi haƙuri mijin, a dinga mana addu’a Allah ya shiryamu, ke ma kinji Hajiya sakwaralle ta, Insha Allah ba abin da zai samu tarbiyanmu duka.”

Alhaji baba murmushi yayi ya ce, “Allah ya sa, Allah kuma ya kare ku a duk in da kuke, Allah ya muki albarka Hauwa’u.”

Jidderh ta ce, “Ameen mijin, saura ke ma sakwaralle ki saka mana albarka indai ba kishi kike ba”, ta faɗa tana yiwa Hajiya Mama dariya.

Dan-ƙwalo Hajiya Mama ta yi wa jidderh ta ce, “Ungo naki ke da ƴan uwan naki, Allah ya shiryaku.”

Jidderh na dariya ta amsa da Ameen, ta miƙe ta nufi ɗakin Hajiya Mama tana faɗin, “To abar mini kallon kishi sakwaralle dan yau da ni ke da miji”, ta faɗa dai-dai tana shigewa ɗakin.

Hajiya Mama girgiza kai kawai tayi ta ce, “Wannan takwara tawa sai addu’an shiriya.”

Alhaji Baba murmushi yayi ya ce, “Allah Ya shirya mana su duka, amma da ace duka yaran nan irin halin Hauwa’u gare su, ai da hankalin kowa a kwance, wannan yarinya dai Allah ya mata albarka, Allah ya nuna mana ƙarshen watan nan lafiya, kowa ya halarta nasan hukuncin da zan zantar, dan dole na yiwa abin tufkar hanci.”

Hajiya Mama ta ce, “Ameen, Allah ya kai mu da rai da lafiya ya kuma tabbatar da alkairi.”

*****

<< Shameekh 4Shameekh 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×