Skip to content
Part 5 of 10 in the Series Shameekh by Harira Salihu Isah

Ɓangaren su Big Dad kuwa haka suka kwana akan magana ɗaya dan Hajiya Kubura(Mom), akwai son mita a ta yanyana magana guda.

Washe-gari big Dad a ƙurarren lokaci ya tashi, dan haka cikin gaggawa ya shige wanka, yana fitowa kuma ya samu Mom ta farka da magana tun na jiya, da mamaki yake kallonta na irin halinta na riƙe magana, amma sai ya basar ta hanyar cewa, “Hajiya ba na ce miki kar ki damu da wannan magana ba, daughter za ta dawo Insha Allah, mu mata addu’an dawowa lafiya kawai, tun da dai kowa yasan karatu ta tafi bawai wani abun ba.”

Mom cewa tayi, “To shikkenan Alhaji Allah ya dawo da ita lafiya, amma dai kasan halin Sofiya idan ba da rarrashi ba kam, to ba lallai ta dawo yau ba, kuma ni bana son surutun su Hajiya Mama, yanzu sai a ta cewa yarinyata tayi kaza tayi kaza.”

“Ke kam na ce miki kar ki damu, yanzu dai a taso a taya ni shiryawa na samu na fita da wuri, banson na kuma yin wani lattin.”

“To Alhaji”, Mom ta faɗa tare da miƙewa ta fara taya mijin nata shiryawa, suna yi suna hira har ya gama shiryawa.

Agogon da ke maƙale s hannunsa ya duba, ganin lokaci kawai ɗaukan abin da zai ɗauka yayi ya ce, “Hajiya ina jin ba zan staya karyawa ba dan na makara, mu je kawai ki rakani ko.”

Mom ta ce, “Haba Alhaji ban da dai ka fita ba ka karya ba kam, ai ko da ruwan zafi ne ya kamata ka sha”, ta faɗa tana ficewa a ɗakanin tare da kwalawa mai aikinta ƙira.

Mai aikin na zuwa da durƙusa tare da cewa, “Barka da safiya Hajiya.”

“Ba ƙiranki nayi ki gaishe ni ba, maza kiyi sauri ki haɗa wa Alhaji tea”, faɗin Mom fiskan nan ba rahama.

“To Hajiya”, ƴar aikin ta faɗa tana tashuwa, tayi dinning dan yin abin da aka saka ta yi.

Alhaji bayan ya fito a ɗakin, tare suka yi dinning area da Mom, ruwan zafin da aka haɗa masa ta ɗauka ta miƙa masa, shi kuma ya amsa a haka amma sama-sama ya kurɓa kawai, ya tashi tare da ƙara duba agogonsa yana faɗin, “Mu je ko Hajiya.”

Murmushi Mom tayi tare da miƙewa ta bi bayansa dan yayi gaba tuni, har suka isa wajan motansa driver ya buɗe masa ya shiga, jakansa ta miƙa masa ta ce, “Alhaji Allah ya tsare hanya a dawo lafiya.”

Da Ameen ya amsa, driver ya ja mota suka fice a gidan, ita kuma ta juya ta koma cikin gidan.

*****
A ɓangaren gidan Alhaji Isma’il kuwa mahaifin jidderh, wan da suke ƙira da Daddy, zaune yake a kan haɗaɗɗen gadonsa da system a gabansa yana aikinsa, Mummy kuma na zaune daga gefe a gaban dressing mirror tayi wanka ta gyara fiskanta tana ɗaura ɗankwali, sai da ta kammala ta shafa turaruka sannan ta juyo cikin soyayya da biyayya ta ce, “Abu Yusuf a ƙyale aikin haka nan mu karya.”

Daddy dama yana danna system ɗin ne kawai amma rabin hankalinsa, na kan matarsa sanyin idaniyarsa uwar ƴaƴansa, tun da ta juyo garesa kuma ya bar danna system ɗin, ya fara sakar mata murmushi har ta gama zancenta, sannan ya numfasa tare da cewa, “Maman Yusuf anya za ki bari ayi amaryan nan kuwa da irin wannan kwalliya, wa zai ce ke kika haifa mini manyan budurwaye jidderh da Sadeeya, ga kuma Yusuf.”

Murmushi Mummy ta sakar masa tare da cewa, “Idan Allah ya nufa ai yi ya zama dole, addu’ata dai Allah ya bamu tagari wacce za mu zauna lafiya, idan kuma Allah bai nufa ba Allah bamu ikon zama cikin haƙuri da juna.”

Daddy tasowa yayi tare da ƙarisawa gareta ya rungumeta ya ce, “Ameen idan har zuciya kike faɗan hakan, dan ku mata akan kishi sai a hankali.”

“Kishiya ba daɗi Abu Yusuf, amma tun da Allah ne ya halasta to alhamdulillah Allah bamu haƙuri, har zuciyata nake maka wannan addu’a, ina son mijina uban ƴaƴana zan yi haƙuri da shi a ko wani hali Insha Allah.”

“Allah ya miki albarka Maryam, Allah kuma ya raba mu da mummunan ƙaddara.”

Mummy barin jikinsa tayi tana faɗin, “Ameen Abu Yusuf, muje mu karya ko.”

Tare suka fice a ɗakin suna ta zancensu suna dariya, kuma akan maganan kishiya ne Daddy ke stokananta, har suka ƙarasa dinning ɗin, mummy girgiza kai kawai tayi tare da ja wa Daddy kujera ya zauna, ta buɗe baki za ta yi magana sai Daddy ya ce, “Wai ina yaran nan ne suka yi? Babu ko mostinsu.”

“Wannan yara sai dai Allah shiryesu ya musu albarka, wai na tashi nayi aikina na ƙyalesu su huta, amma fitowa su ci ma ya zama aiki, bari na ƙira su”, Mummy ta faɗa tana barin dinning ɗin, ta nufi ɗakin yaran nasu.

Mummy na barin dinning ɗin sai ga Meelat ta iso, ganin Daddy faɗaɗa fara’anta tayi, kujera ta ja ta zauna sanna ta gaishe da Daddy, cikin girmamawa, ya amsa yana faɗin, “Sai yanzu kuka fito?”

Ƙasa da kai Meelat tayi tana sosa ƙeya, ta faɗa masa ita ta jima da fitowa tare suka yi aiki da Mummy, sannan Daddy ya jinjina kai, dan yaran duk sun san shi akwai wasa da raha da yara, amma kuma akan maganan tarbiyansu ko ayyukan gida, to baya musu dariya kuma haka Mummy ma, akan horar da su tarbiya to basa ganin haƙoranta.

Mummy da yake tasan Meelat kam dama tare suka yi aikin ta je wasta ruwa ne, shiyasa bata yi wajanta ba, ta nufi ɗakin Deeyah, tura ƙofan ɗakinnasu Mummy tayi tana surutu, “Wato ku yaran nan ba ku iya samun waje ba ko, kuna ɗaki kaman munanan Amare wai nikam yau ba za ku fito ba ne?”

Deeyah da ke kwance akan ƙatoton gadon nasu ne tayi saurin tashuwa, sai da ta duba gefenta ta ga ba Subby, mostin ruwan da taji a bathroom ne ya tabbatar mata Subby ta tashi, sunkuyar da kan ta tayi ta ce, “Mummy ki yi haƙuri Allah mun yi sallah, baccine ya ɗaukemu.”

Ƙwafa Mummy tayi ta ce, “Zan yi dai-dai da ku ne, maza ku fito ku karya, ke da Subeeya kam sai dai gyaran Allah da  shiryarsa, kuma wallahi idan kuka ci gaba ba ku daina ba mazajen ku na tare da aiki, ko kuwa na ce ku kuna tare da aiki ba ruwana ba ni na muku wannan horarwan ba, dan ba abun da kuka iya”, ta faɗa tana ja musu ƙofan ɗakin ta juya.

Ajiyan zuciya Deeyah tayi, sannan ta sauƙo a gadon, ta wuce bakin ƙofan toilet ɗin ta staya tana faɗin, “Munafuka ki fito tun da an mini faɗa ni kaɗai hankalinki ya kwanta kin ji daɗi.”

Subby fitowa tayi tana dariya ta ce, “Wallahi ni ba munafuka ba ce kema kin sani, zagawa nayi bawai nasan da shigowan Mummy ba ne na zaga, kuma kema da naki da kika zage kina bacci, bayan kin san nan gidan Mummy ne ba na Mom ba balle muyi bacci kaman jakuna.”

Deeyah matsa mata tayi a hanya ta fito, ita kuma ta shige ta wanko baki da ido ta fito tana hararan Subby.

“Sai muje mu karya ai mu samu muje wajan yaya jidderh ko”, Subby ta faɗa tana ficewa a ɗakin tare da maste dariyanta, dan Deeyah na bin ta a baya.

Dinning ɗin suka nufa in da suka samu Mummy, Daddy da Meelat, zaune suna jiran isowan su.

Kujera suka ja suka zauna, sannan Subby ta ce, “Barka da safiya Daddy.”

Murmushi Daddy yayi ya ce, “Yauwa yarinyar kirki, sai yanzu ake fitowa ko?”

Ƙasa da kai suka yi dukkansu, tun da sun san halin Daddy ma akan irin haka, shi kuma bai kuma cewa komai ba ya amsa gaisuwan Deeyah tayi.

Meelat ta buɗe baki za ta ƙira mai aikinsu sai Mummy ta bi ya da harara, ta ce, “wai meyasa bakwa ji ne ku kam? Za ki ƙirata ta miki me? Ku ba za a more ku ba ko? Common serving na abinci sai an muku? To daga yau ku zaku dinga serving namu, ke Sadeeya tashi ki yi serving namu, ke kuma Subeeya ke za ki haɗa kwanukan bayan an gama ci, Jameela ke kuma ke za ki kai kwanuka kitchen, fatan kun ji ni ai?”

Haɗa baki suka yi wajan cewa, “Eh Mummy.”

Gyaɗa kai Mummy tayi ta ce, “To yayi kyau.”

Deeyah tasowa tayi tare da zubawa kowa nasa abin karin, sannan ta koma ta zauna, dukansu cin abinci suke hankali kwance ba mai magana, sai can Meelat ta ce, “Mummy nikam ban ji mostin yaya jidderh ba.”

Subby da Deeyah kaman su ma jira suke Meelat ta tambaya, suka haɗa baki wajan cewa, “Yaya jidderh bata cin ɗumame.”

Mummy ta ce, “za ku mana shiru ku ci abincin ko kuwa za ku tashi ne ku bita in da taje ɗin?”

Daddy murmushi yayi ya ce, “Yaran kirki uwata na gidan Alhaji baba”, ya ƙarishe faɗa yana ajiye cokalin da ke hanunsa da kuma tea cup, share bakinsa yayi da tissue yana faɗin, “Alhamdulillahi!”

Dukansu suna gama ci Subby ta tashi ta haɗa kwanukan, Meelat kuma ta ɗauka ta yi kitchen da su.

Daddy tashuwa yayi ya koma main palour ya zauna, Mummy da Deeyah da Subby su ma suka koma can, a ƙasa Subby da Deeyah suka zauna kan su a ƙasa, Daddy ne ya kallesu ya ce, “Ya aka yi yaran Daddy kaman da magana a bakinku?”

Subby ta ce, “Daddy am..dama..uhm.”

Kallonta Daddy yayi ya ce, “Ya aka yi ina jin ku.”

“Am..daddy dama ba birthdaynmu ya zo, shi ne..”

Kamun ta ƙarishe magana, Mummy ta tari numfashinta ta ce, “Ku shikkenan iya abin da kuka iya kuma kuka sani kenan, to Alhaji ba abin da yaran nan zasu yi ka barni da su, shi birthday me amfaninsa me abin farinciki a wajan? Raguwan da kwanakinku ke yi a duniya shi ne abin murna? Abu ba lada ba ba komai ba.

Daddy ya mayar da idanuwansa kan su ya ce, “Kun ji abin da Mummynku ta ce ko? To idan kuna son ku yi birthday ku lallaɓata ku yi abin da take so sai ku yi.”

“To Daddy mun gode Allah ya ƙara girma”, suka haɗa baki wajan faɗan haka, duka suka tashi suka wuce ɗaki.

Deeyah kaman mai shirin kuka ta ce, “Wallahi Mummy tana ɓata mana show, amma bakomai yanzu bari nayi wanka, idan na fito kema sai ki shiga, mu wuce wajan yaya Jidderh a gidan baba alhaji, in yaso sai ta taya mu yi wa Daddy magana, nasan Mummy ba za ta ce komai ba indai yaya Jidderh ce tayi magana.”

Subby ta ce, “Ki shiga ki watsa ruwan kamun ni kuma na gyara mana ɗakin, kin ga daganan mun fara yin abinda Mummy ke so.”

Tashuwa Deeyah tayi ta shiga wanka, ita kuma Subby ta gyara ɗakin tsab, Deeyah na fitowa ita ma ta shiga wankan, bayan mintuna ta fito.

Shiryawa suka yi dukkansu cikin Black Abaya wan da yayi mugun amsan su( gaskiya wannan family ba dai kyau ba kam Masha Allah.)

  Sun fito palourn suka samu Meelat ma ta fito ita ma a shirye staf, cewa tayi, “Yaya Subby zan bi ku mu bata haƙuri tare.”

“To muje meelatyna.”

Ɗakin mummy suka je suka ce mata za su wuce gidan Baba a Alhaji, a dawo lafiya ta musu suka fice a cikin gidan, za su fita suka haɗu da Uncle Sale, stugunnawa suka yi duka suka gaishesa, ya amsa masu da fara’a yana faɗin, “Yaran Uncle sai ina da safen nan tun rana bai yi ba, kun ci kwalliya haka kaman masu yin gasan kyau.”

Duk murmushi suka yi, Meelat ta ce, “Uncle za mu gidan Alhaji baba ne.”

“Ah to kun kyauta, ku ce za ku je kwacewa uwarmu miji, to ku dawo lafiya, nima bari na shiga wajan yayana”, faɗin Uncle Sale Yana murmushi.

Tashuwa suka yi suka wuce, shi kuma yayi cikin gidan.

Gaishe da baba mai gadi suka yi suka buɗe ƙofan, suka fice suka nufi gidan  Alhaji baba a ƙafa suna tafiya suna hira.

Uncle Sale da sallama ya shiga palourn,  amsawa Mummy tayi tana faɗin, “Maraba da mijin Hajiya.”

Murmushi Uncle Sale yayi ya ce, “a’a fa mummyn yara, matar Alhaji dai ba  mijin Hajiya ba.”

Zolayan juna suka yi kaman ko yaushe, sannan suka gaisa cikin mutuntawa, Uncle Sale ya ce, “Yayana na nan kuwa?”

Dai-dai lokacin da yayi tambayan a lokacin Daddy ya fito a ɗaku, ganin ƙanin nasa sai ya faɗaɗa fara’ar fiskansa.

Mummy ta ce, “To ƙanin Yaya ga yayan naka.”

Murmushi Uncle Sale yayi ya ce, “Barka da fitowa yaya, yau nayi sa’an samunka a gida, bansan ka dawo daga ƙasar da ka je ba, kawai na zo gwada sa’ata ne.”

Daddy waje ya samu ya zauna suka gaisa sannan ya ce, “To ya aka yi ina labari?”

“Yaya babu labari fa yanzu ma takardun can na zo amsa, idan suna kusa a taimake ni da su.”

“Okay ba mastala, amma dai suna office kuma yanzu daman zan fita ne, in yaso sai mu wuce tare ka amsa ko.”

Uncle Sale amsawa yayi, suka miƙe a tare za su fita, Mummy ta ce, “Mijin Hajiya ba za a ci abincin Hajiya ba ne?”

Da murmushi Uncle Sale ya ce, “Kar Hajiya ta damu zan dawo na ci da rana.”

“Allah ya dawo da ku lafiya”, ta faɗa tare da bin bayansu, ta raka su har bakin ƙofan palourn, san da suka ja mota suka fice a gidan, kamun ta koma cikin palourn nata, tana jin gidan ya mata girma shiru, sauran yara sun tafi makaranta ga su Jamila sun yi gidan baba alhaji.

Sai da Mummy tayi duk abin da za ta yi sannan ta wuce ta kwanta, dan ta hutawa rayuwanta.

Jidderh na zaune a ɗaya daga cikin kujerun palourn hajiya Mama tana kallon, hankalinta rabi na kan waya rabi na kan TV.

Sallaman su Subby da taji ne ta amsa tana ɗagowa, su kuma suna shigowa carab suka ga yaya Jidderh, kuma ita ta amsa musu sallaman, da sauri Meelat ta ƙariso wajanta ta rungumeta, tana faɗin, “Babbar Yaya na yi kewanki.”

Jidderh ta ce, “kuna mini rashin kunya kam ba dole na tafi na bar muku gidanku ba.”

“Yaya Jidderh ki yi haƙuri, Allah nikam ban yi magana dan a ɓata miki rai ba, kiyi haƙuri ba zan sake ba”, faɗin Meelat tana kama kunnenta.

Subby da Deeyah ma zuwa suka yi suka rungumeta suna faɗin, “Yaya jidderh tamu ba za mu sake ba ki yi haƙuriiiiii.”

Murmushi jidderh tayi, dan yacce suka ja kalman haƙurin ya ba ta dariya, cewa tayi, “Na yafe muku ai ya wuce kar ku sake, shi ɗan uwanmune kuma yayanmu, bai kamata mu muna ƙannensa kuma muna zaginsa ba.”

Haɗa baki suka yi suka wajan faɗin sun daina, jidderh kuma ta murmusa ta tare da faɗin, “Yayi kyau to Allah ya muku albarka, sai ku zauna mu sha hira tun da kun zo, daman nima zama shirun ya ishe ni, duk sa’oin nawa maza ne kuma nasan basa nan.”

Miƙewa suka yi duka suna faɗin, bari su je su gaishe da stoho da stohuwa tukunna, suna dawowa.
Palourn Alhaji baba suka nufa da sallama suka shiga,  ba su wani staya ba suka wuce ɗakinsa direct suna ƙwala masa ƙira kaman ya ci bashin su.

Alhaji baba yana kwance yana jan carbinss, jiyo muryan fitinannun jikokinsa sai ya miƙe tare da jawo madubin idonsa ya maƙal, tare da amsa musu sallaman da suka yi.

“Ɗan stoho barka da hutawa”, faɗin Deeyah.

Shi kuma ya ce, “Yauwa stohuwa Halimatu-Sadiya, kun samu shigo kenan.”

“Eh mun shigo angonmu”, suka faɗa tare da gaisar da shi, ya amsa musu dukansu da wasan jika da kaka suka sha hiran su.

Alhaji baba ya ce, “Yauwa Subiya yayar taki tana dawowa yau ɗin ne?”

Subby ta ce, “Ɗan stoho nikam a gidan Daddy na kwana ba a gidanmu ba, banma san ko tana dawowa ba.”

“To Masha Allah, Allah ya muku albarka duka ya ƙara haɗa kawunanku, Allah ya dawo da ita lafiya, ku so junanku ku ci gaba da haɗa kanku iyayen nan naku ne duka Allah raya ku ya baku mazaje nagari jikokina”, faɗin Alhaji baba cikin tsananin ƙaunar jikokin nasa.

Meelat ta ce, “Alhaji kaka nikam ina da kai ai ina da miji nagari.”

dariyan manya Alhaji baba yayi, tare da cewa, “To amaryata amma dai duk da haka, kun ga nikam na tsofe karbna tafi na barku, gwanda kumun abokanayen takara tun da wuri.”

Dariya suka saka dukansu wai wato  Alhaji kaka abokanayen takara za’a maka, ya amsa musu da “eh mana.”

Hajiya Mama ce ta shigo tana faɗin, “Su wanne munanan ƴammatayen ne suke damar mini miji da surutu?”

Alhaji baba ya ce, “A ƙyaleni nayi hira da Amarena ke kam kin stufa yanzu, su ake yayi.”

“Yauwa angon faɗa mata dai mu kake yayi, mu ne na zamani ita kam ta tsufa”,  faɗin Subby, sannan suka ci-gaba da hiransu har da Hajiya Mama cikin nishaɗi.

Shameekh tun da ya koma ya kwanta, yake sharar baccinsa hankali kwance, shi ne bai farka ba sai da agogo ta buga ƙarfe sha ɗaya na safe, sannan ya wara idanuwansa ya wara a hankali, yana mai karanto addu’oinsa, sannan yayi miƙa da salati.

Yaye bargon da ya lulluɓa da shi yayi, ya miƙa hanunsa ya jawo wayansa da ke kan bedside drawer, ( Uwar batoorl na faɗin yau kam ba call ne?) Sai ga Shaameekh ya ja guntun tsaki,  ganin misscalls ɗin da aka tara masa.

Duba ƙiraye-ƙirayen yayi amma babu na Ummiynsa a ciki, dan haka numbernta ya laluɓo wan da yayi saving da  FAVORITE SOUL,  har zai yi dialing sai ya duba time, ganin 11am a Dubai wan da yayi dai-dai da 8am a Nigeria, fasa ƙiran nata yayi dan yasan may be tana asibiti tana fama da patient’s, kada ya ƙira ya shiga haƙƙinsu, dan haka mai da wayansa yayi ya ajiye, bai bi kuma ta kan sauran misscall’s ɗin ba.

Miƙewa yayi ya shige haɗaɗɗen banɗakinsa, brush kawai yayi ya fito ya ɗau wayoyinsa ya wuce dinning dan karyawa.

Yana shiga palourn ya ga komai neat a gyare staff sai ƙamshi da ke tashuwa, taɓe baki kawai Shaameekh yayi, tare da ƙarasawa dinning area ya zauna, yana son ƙiran mai aikin nasa amma ya manta sunanta, dan shi bai da lokacin riƙe sunan mutane, “Heyyyy!” ya faɗa cikin ɗaga murya.

Ma’aikaciyar ta sa da sauri ta ƙaraso tare da ɗan rusunawa, ta ce, “good morning Sir.”

“morning”, kawai ya amsa a taƙaice bai ƙara cewa komai ba.

Ganin haka tasan ba zai wuce zuba masa abinci ya ƙira tayi ba, dan haka ta masto cikin girmama ogan nata, ta haɗa masa tea kaman yacce yake so, ganin yau bai fita ba ta saka masa da wani abincinsu ta ƙasar, wan da kuma favorite nasa ne a lokacin breakfast da safe.

Bayan ta gama sawa ta koma gefe ta tsaya tana jiran wani umurnin, shi kuwa gogan ba tare da ya ɗago idonsa ya ko kalleta ba ya ce, “Ok you can leave.”

Jin abin da ya faɗa da wuri ta bar wajan ta koma ta cigaba da aikin da take yi.

Bismillah yayi tare da fara cin abincin kaman ba ya so, wayansa ya ɗauka yana dannawa, sannan ya ɗau cup na tea ɗin ya kurɓa, a wayansa kuma contacts nasa ya shiga tare da laluɓo numbern da ya raɗawa  MY BABY, yayi dialing na layin kuma cikin sa’a ya shiga, amma har ya gama ringing ba’a ɗauka ba, a hankali ya ce, “May be babyna tana school ita ma, all the best sweetheart”, ya faɗi haka yana ci-gaba da karyawansa, sai da ya gama sannan ya tashi ya koma palourn ya zauna ya kunna TV, amma rabin hankalinsa na kan wayansa, da yake dannawa da alama charting yake kuma serious magana yake yi, can ya rufe datan nasa yana mai busar da iska a bakinsa wani number yai dialing.

Ƙiran na shiga bugu ɗaya aka ɗauka, “Hello Man”, abin da aka faɗa a ɗaya ɓangaren.

Shaameekh ba tare da ya amsa ba ya ce, “Wai abin da nake gani gaske ne?” Ya faɗa hakan a taƙaice.

Mutumin ɗayan ɓangaren ya ce, “Capital Yes ma kuwa Man, da gaske ne muna da wasa next week.”

“Amma meyasa za su mana haka? Tun-tuni muna zaune for nothing ba su yi maganan wasa ba, sai yanzu da ƙarshen wata ya zo, ni ba wai wasan ne nake jin ba zan yi ba ko wani abun, ina da zuwa Nigeria ne, kuma idan ban je akan time ba, Ummiy kaɗai ta ishe ni tuwo da miya, mutanen nan suna da renin hankali”, Shaameekh ya faɗa rai a ɓace.

“Man kuma ba yacce zamu yi dole fa ayi wasan nan da kai, kasan ma ba za su taɓa yarda ba, haƙuri kawai za ka yi kuma ka faɗa wa Ummiy”, mutumin ɗaya ɓangaren ya faɗa cikin stigar rarrashi.

Staki Shaameekh ya ja ya ce, “Okay  zan duba naga ya za a yi, amma gaskiya bana tunanin za a yi wasan nan da ni, ba zan ɓata wa Ummiy rai ba akan common kuɗaɗen da suke bai wa mutane, wan da bai taka kara ya karya ba.”

Dariya mutumin yayi a ɓangarensa ya ce, “Idan mutum bai godewa rahamar Allah ba, zai godewa azabansa dan dolensa, Man ka ji storon mai sama, duk uban kuɗin da ake baka ne bai taka kara ya karya ba, amma kasan kuɗin da kake samu ko wani mai babban muƙami, a siyasan gwamnatin Nigeria ba ya samun haka, to ka faɗi gaskiya dan kai kuɗinka ai sai riƙe baki, Allah sa jidderh ta fara da haifa maka yara maza ƴan huɗu, idan ya so kana mutuwa su ci gado hankalinta kwance.”

Murmushi Shaameekh yayi ya ce, “Ɗan iska ba zan mutu yanzu ba sai naga jikokina.”

A haka suka yi sallama cikin raha, Shaameekh yana kashe wayansa ya dafe kan sa tare da faɗin, “Shiiiiiitttt! Why? Meyasa sai da zan je gida ne za a wani ce akwai wasa, mutanennan suna wasa da hankalin mutane sosai gaskiya”, maganan da yake yi ne ya kaste jin ƙira ya shigo wayansa.

Duba layin mai ƙiran yayi, sai ya ga Sabeer ne, ɗauka yayi suka gaisa ya tambayesa ya kowa da kowa a gida, da kuma jikin baba alhaji, Sabeer a ɓangaren ya amsa da, “Baba Alhaji ya warke da sauƙi, kowa kuma na lafiya, amma yaushe za ka shigo ne Man?”

“Soon Insha Allah ina hanya”, ya faɗa a taƙaice.

“Allah ya kawo ka lafiya, please Man ka ƙira Sofiya ka ce ta dawo yau nasan za ta ji magananka, ka ga Mom da big Dad duka sun ƙira ta, ta ce za ta dawo amma har yanzu shiru, kuma Hajiya mama da masifa kasan halinta”, faɗin Sabeer cikin magiya.

Shaameekh guntun staki ya ja ya ce, “Ni ma gani da nawa ƙuran a gabana gwanda ita ma, kuma in dai masifan wancan masifatun stohuwan ce, to nima ban stallake ba, gwanda ita ba abin da take yi, ni kuwa abu ne ya riƙe ni.”

Sabeer a ɓangarensa ya ce, “Bangane ba Man, ba ka ce kana hanya ba? To wani ƙuran kuma?”

“Hmmn wani hanya Sabeer, yau nake jin labarin muna da wasa, ba hau Thursday ba to ban da fridayn gobe, Friday na sama za mu yi wasan.”

“Whatt!!” Sabeer ya faɗa yana kwashewa da dariya, ya ce, “Man ka ce akwai buga wani wasan kuma a gidan Baba Alhaji kai da Hajiya Mama, kana gama na Dubai kuma na Yobe a anguwan Shagari na jiranka” ya faɗa yana dariya.

Dafe kai yayi ya ce, “Wato kai kam ka ɗaukesa abin dariya ba? kasan ban cika son surutu da stohuwar nan ba, ina ji zan ce musu ba zan yi wasan ba kawai, inyaso sai su nemi wani yayi replacing na.”

“Okay Man, Allah dai ya taimaka ya kuma tabbatar da alkairi, Allah ya kawo ka lafiya.”

“Ameen Sabeer ka gaishe da kowa”, Shaameekh ya faɗa cikin yanayin gajiya da surutun.

Sabeer ya ce, “Kowa zai ji Insha Allah, am please Man give her a call nasan za ta dawo idan kai ne.”

“Okay I will call her.” ya faɗa tare da kashe wayansa.

Guntun tsaki ya ja ya ce, “Ina ta kai na nima, idan taga dama ta shekara can bata dawo ba, is none of my business dan abin da ya dame ni daban”, ɗaga kafaɗa yayi tare da kuma cewa, “An not fucking care”, ya ci gaba da kallon sa.

*****
A can Adamawa kuwa, baby fitowanta daga class kenan, lokacin dai-dai ƙarfe 4:30pm na yamma, jerawa suka yi da ƙawayenta  biyu suna tafiya.

Wayanta ɗayar ta miƙa mata ta ce, “Babe tun ɗazu muna class ake ƙiranki.”

Baby amsan wayan tayi tana faɗin, “Allah sarki, wataƙila ma Ummiyna ce ta ƙirani”, ta faɗa tana shiga duba call logs ɗin, kamun ta ga numbern da ya ƙirata sai ga ƙira ya shigo wayan, murmushi tayi ganin layin Ummiy, dan daman tasan Ummiy ce ta mata misscall’s ɗin.

Ɗauka tayi tare da yin sallama, tana faɗin, ,”Ummiyna Allah sai yanxu muka fito daga class, duk ma na gaji nikam.”

Shiru tayi alaman Ummiy na magana a  ɗayan ɓangaren, can ta kuma cewa, “To Ummiy, please ya zo da wuri, okay Ummiyna sai na dawo byee”, ta kashe wayan ta mai da shi jaka bata duba misscall ɗin ba, takawa suke da freinds nata har suka Bar wajajan classes nasu,  sun iso wajan da suke parking, duka freinds ɗin nata ko wacce ta shiga motanta.

Wacce ta ɓata waya ɗazun ne ta ce, “Babe ki zo nayi dropping naki sai na wuce.”

“Noo batoorl ki bari mun yi waya da Ummiy driver na zuwa.”

Ɗayar ma ta ce, “Ai kuwa ma batoorl kika je dropping nata za ki sha faɗan Ummiy, wai mu dena driving da kan mu.”

“Yauwa Bea faɗa mata dai”,  inji baby.

Suna cikin magana ba jimawa sai ga driver ɗin ya iso, shiga motan tayi tare da ɗaga musu hannu ta ce, “Babe’s see you tomorrow ko kuma may be sai na dawo daga Yobe.”

Batoorl ta ce, “Deejerh mu faɗa mata gaskiya ko mu bar ta?”

Dariya wacce aka ƙira da Deejerh tayi ya ce, ” Nop Babe ƙyaleta dai a dawo lafiya.”

Baby hararansu tayi tana tambayan me suke nufi, su kuma gunste dariyansu suke yi suka ce mata ba komai, idan bata zo ba Allah tsare hanya, ya kai su lafiya ta gai da Ummiy, da handsome brothernta.

Baby amsawa tayi suka yi wa juna sallama, kowa ya figi mota, drivernta ma ya ja mota, sun ɗau hanyan gida ta gaishesa, ya amsa cikin fara’a.

Wayanta ta ciro tana dannawa har suka isa gida, ɗakinta ta wuce direct ta shige bathroom nata, ta watsa ruwa bayan fitowanta ta saka simple gown, tayi sallah da ta iɗar ta ɗau wayanta ta yo palour, ganin Ummiy ba ta palourn ɗakinta ta wuce dan ta san ba za ta wuce tana can ba.

Da sallama baby ta shiga ɗakin ta samu Ummiy na call, kuma da alama da Daddy take waya, zaunawa tayi ta jira Ummiynnata.

Bayan Ummiy ta gama wayan juyowa tayi ta ce, “Mutanen school har andawo ne?”

“Eh Ummiy na dawo, na wuce nayi sallah ne shiyasa sai yanzu na shigo.”

“Bakomai babyn Ummiy”, faɗin Ummiy tana murmushi.

Murmushin ita ma baby tayi, ta gaishe da Ummiy da gajiyan asibiti, Ummiy ta amsa tare da cewa, “Soon Ai kema za ki fara gajiyan.”

“Noo Ummiy ni dai kam ba zan dinga jimawa har haka ba.”

Murmushi kawai Ummiy tayi ba ta ce komai ba, sai da ta numfasa ta ce, “Gobe Friday sai ki ƙoƙarta ki shirya komai naki, dan Saturday mu samu mu shiga da wuri.”

“Insha Allah Ummiy, kuma nikam ma ko gobe mu tafi a shirye nake ba za ni school ba.”

“Akan me ba za ki school ba?” Ummiy ta tambayeta.

“Ban ce muna da lectures ba gobe.”

“Ok shikkenan, amma fa ban yarda ba sai na tambayi doters na, in ma ba ku da shi to asibiti za mu tafi tare.”

“A a nikam, Ummiy gobe ƙunshi zan je yi.”

“Ko ma menene Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya babyn Ummiy.”

“Ɗazu ma kika ƙira muna class ban ma sani ba Ummiy, da  wayan na hanun batoorl.”

“A a baby ban da ƙarya, nikam ban ƙira ki ba sai da naga time na fitowanku yayi, saboda driver kar ya ɓata miki lokaci.”

“Au wai Ummiy ba ke ba ce kika ƙira ni ba? To bari na duba naga waye ne, dan ni ban duba ba tun da naga ƙiranki na ɗauka ke ce”, ta ƙarishe faɗa tare da jawo wayanta ta buɗe, ganin wan da ya ƙira ta ɗin ai zaro idanuwa tayi ta ce, Yau ni baby na shige su Ummiy.”

Ummiy kallonta tayi ta ce, “Da kika yi me? Waye ne ya ƙira ki bana son shirme.

Baby kalan tausayi tayo ta ce, “Ummiy yaya ne fa ya ƙira ni wallahi, na shiga magana a garin Adamawa ƙasar na Nigeria, yanzu yaya zan yi Ummiy? Zai ce ya ƙira ban ɗauki ƙiransa ba, kuma du ban bi bayan ƙiran nasa akan lokaci ba.”

Ummiy ta ce, “Bana son shiriritar kinnan fa baby, wai kam shi yayan naki dodo ya zama ne, ko kuwa shi azara’ilu ne? Abu mai sauƙi ki faɗa masa kina class ne lokacin da ya ƙira, amma kin staya kina damun mutane da surutun nan kaman kanari, ai yasan ba ki masa ƙarya, dan haka bana son shirme maza ki ƙirasa yanzu.”

Baby dialing na layin yayan nata ta yi, yana ringing ƙirjinta ma yana ringing na storo, amma har ya gama ringing ɗin ba’a ɗauka ba, hamdala tayi za ta ajiye wayan, Ummiy ta saka ta sai ta sake ƙira, tura baki tayi tare da yin dialing again, yanzun ma ya shiga.

*****

<< Shameekh 3Shameekh 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×