Skip to content
Part 6 of 10 in the Series Shameekh by Harira Salihu Isah

Subby bayan sun ɗan yi hira da Alhaji baba fitowa suka yi palourn wajan jidderh.

Zaune take a inda suka bar ta sai dai yanzun call take yi, duk zaunawa suka yi a gefenta suka zagayeta, kaman masu neman gafara ko ɗaukan karatu.

Meelat ɗaukan remote tayi ta sanja tasha suna kallo, kamun ta gama wayan.
Sai da Jidderh ta gama call ɗin, ta ajiye wayan sannan ta ce, “To sarakunan surutu sai yanzu kuke dawowa kun je kun dami stoho koh?”

Subby ta ce, “A’a fa yaya Jidderh, shi ya riƙe mu da hira, Hajiya mama ma ta zo ta jona mu, sai da muka gudo yanzun ma, mun ce masa wajan yayarmu muka zo ba wajansa ba.”

Murmushi Jidderh tayi ta ce, “Shikkenan yayi kyau sannun ku da fitowa.”

“Yaya Jidderh wai da Ya Safwan kuke waya ne?” faɗin Deeyah.

Taɓe baki Jidderh tayi ta ce, “Eh Deeyah, shine fa uban ƴan naci da jaraba, mutum ba zai gane ba a son sa ba.”

“Uhmn yaya Jidderh tun da bai gane ba shikkenan ai, nikam dan Allah ki yarda ma gobe ya fitar da ke ɗin, sai ki kawo mana chocolate”, Deeyah ta faɗa tana murmushi dan tasan stokanan Jidderh tayi.

Jidderh hararan Deeyah tayi ta ce, “Za ku fara ko? To ku fita a idona  ba inda za je, ku rufamini asiri na mutu a gida maza su binne ni, kar garin biye muku na kashe aurena.”

Subby caraff tayi ta ce,  “Ai kuwa yaya Jidderh gwanda kam kar ki je ko ina, yacce kowa ke hanyan dawowan nan kar a samu akasi, Ya Shaameekh yayi diran mikiya.”

“Yauwa Subby ke kam kin gane”, faɗin Jidderh tana murmushi.

Murmushi Subby ma tayi ta ce,  “Yauwa yaya Jidderhta, kinsan birthdayn mu ya zo?”

“Au ku ce mun kusa shan shagali, daman kwaɗayin birthday cake nake yi.”

“Eh yaya Jidderh ya zo, cake kam har sai kin ture ma Insha Allah.”

Jidderh ta ce, “Amma ina birthdayn naku sai bayan family meeting da 1 week?”

Deeyah ta ce, “Ƙwarai haka ne yayarmu, kamun lokacin nasan Ya Shaameekh  ya koma ƙasar da ya fito, kada ya mana cikas ya hana mu, tun da bai cika jimawa ba idan ya zo, nasan zai iya komawa kamun ranan, idan ba haka ba kunsan akwai case yin birthday ɗin nan, Ya Shaameekh kaman ba wan da ke zama a ƙasar waje ba, sam baya son irin abubuwan nan.”

Subby ta ce, “yaya Jidderh in ma bai koma ba, ai sai mu je gidan Small Uncle ayi a can, da sauran abubuwan duka ma yi a can hankali kwance ko?”

“Caɓ amma dai Subby an gaishe ki, kin dai san bayan gidan Daddy ba inda yake son zuwa sosai sai gidan Small uncle, tun da suna shiri da aunty Zee sosai,  ke dai mu yi addu’an Allah ya sa zuwa wannan lokacin ya koma akan time kawai”, faɗin Meelat da ke sanya haƙarƙarinta akan kujeran da take zaune.

Jidderh shiru tayi tana sauraransu duka, sai da Meelat ta gama magana sannan ta ce, “To duk ya ishe ku nasan yaya za a yi komai ya tafi dai-dai Insha Allah, amma bana son yayana ya koma da wuri, dan haka ku bar ma addu’an komawansa da wuri, ko yana nan zan yi ƙoƙari komai ya tafi yan da kuke so, kar ku damu ƙannen Jidderh.”

“Ai yaya Jidderh tun da muna da ke mun san komai normal ne, Allah dai ya bar mana ke.”

Da Ameen Jidderh ta amsa tana murmushi, sannan suka ci-gaba da zantawa da ƙannen nata, shikkenan komai ya wuce ta haƙura ta kuma mance, Jidderh na ƙaunar ƙannenta sosai, shiyasa ma ko sun mata reni bata dogon fushi da su take haƙura, halin Jidderh yayi ko ta ina fan’s.

*****
Shaameekh zaune yake a arniyar palourn nasa tare da wani Balarabe, fiskansan nan a haɗe gam kaman hadari ya haɗu ta gabas, wan da yanayin fiskansa ke nuni da maganan da suke yi ba sonsa yake ba, dan idan ka ga fiskansa za ka ɗauka jira yake a ce firit ya shaƙe Balaraben.

Balaraben ke magana cikin harshen turanci ya ce,  “Sir ka taimaka mana, majinyacin na cikin mummunan hali, mawuyacin hali na gaske yana jin jiki, wan da idan baka taimaka ka masa wannan aikin ba to zai iya rasa rayuwarsa gaba-daya a ƙanƙanin lokaci, ka taimaka mana Sir dan Allah”, duk da turanci Balaraben yayi wannan magana.

Shaameekh fiskansa har yanzu a haɗe faɗi yake a ransa, “Mutanen nan ba za su gane issues da ke gabana ba, anyway I most help, dan idan Ummiy ta ji ma za ta ce dole nayi.” Mayar da idanuwansa yayi ya lumshe sannan a hankali ya buɗe baki kaman dole ya ce, “Zan yi tunani a kai”, da turanci ya faɗa.

A take fiskan Balaraben nan ya cike da murmushi, dan daman an faɗa masa Shaameekh ba ya ƙin yi wa mara lafiya aiki, kuma idan ya ce zai yi tunani to shiri zai yi, yana washe baki ya ce, “Shukran! Sir Allah ya saka da alheri.”

“Ameen”, Shaameekh ya faɗa a taƙaice.

Tashuwa Balaraben yayi dan tafiya tun da ya samu abin da ya zo nema, sannan ya ajiye masa abubuwa masa wani file akan matslan majinyacin nasu. Shi ma Shaameekh ɗin miƙewa yayi dan ya taka masa.

Suna tafiya Balaraben na cewa, “Yauwa Sir dan Allah idan ka yi tunanin, ka sanar da mu abin da ka yanke akan lokaci, dan mu samu mu shirya komai, duk da daman mu a shirye muke, dan gaskiya muma bama son ayi rashin wannan mara lafiyan, dan da alama mutum ne mai muhimmanci da kuma mastayi a Nigeria duka ba iya iyalansa ba, duk lokacin da ka yanke ko nan da kwana biyu ne a shirye muke, kayan aiki komai da komai akwai, sannan akwai waɗanda za ku yi aikin tare, indai ka gama ka tuntuɓemu akan lokaci dan Allah.”

Shaameekh ko da ya ji wannan Balaraben ya ambaci Nigeria, haka kawai sai ya ji zuciyansa ya tsinke, sai da ya numfasa sannan ya ce, “Insha Allah za ku ji daga gare ni akan lokaci bi’izinillahi.”

Har wajan motansa ya taka masa, suka yi sallama Balaraben ya ja motansa ya tafi, shi kuma gogan ya koma cikin gidansa, yana ƙoƙarin shiga palournsa ya ji ƙira ya shigo wayansa har ya tsinke, wajan wayan ya nufa ya ɗauka dan ganin waye ne, dan shi kam wayansa ya zama hot line ƙira kaman wayan asibiti.

Ganin layin wacce ke ƙiransa sai ya saki wani ƙayataccen murmushi, mai nuni da ƙauna da soyayyan wacce ke ƙiran nasa, Allah ne kaɗai yasan adadin yacce yake jinta a rayuwarsa, yana matuƙar son ƙanwarsa fiye da misali.

Ko da ƙiran nata ya ƙara shigowa rejecting yayi, sannan ya ƙira ta, ƙiran na shiga bugu guda ta ɗauka, sa wayan yayi a speaker ya ajiye a cinyan sa ya jawo system nasa gabansa da wannan file da Balaraben ya kawo, yana sauraronta yana duba su.

“Hello yaya an wuni lafiya? Ya aiki? Ɗazu ka ƙira muna class ne”, baby ta fada a ɗaya ɓangaren, tana jero tambayoyin ko jan numfashi bata yi.

Shaameekh sai da ya staya ta gama magananta yana saurara, sannan ya murmusa tare da cewa, “Assalamu Alaiki”, a taƙaice yayi sallaman.

Baby kama baki tayi a ɓangarenta, tare da yin ƙasa da kan ta, murya kaman na mai shirin yin kuka ta ce, “Assalamu’alaikum yaya ka yi haƙuri zan yi sallaman nima.”

“Wa’alaikissalam mara jin magana”, ya faɗa yana murmushi dan baby da shirme take ba kaɗan ba.

“Yaya ya kake? ya aiki ?”

“Alhamdulillahi mun godewa Allah babyna, fatan kuna lafiya duka ku ma, ya kuma makarantar? Ina fatan kina zuwa kuma kina karatu sosai?”

Baby ɗaga kai tayi kaman tana gabansa yana kallonta, ta ɗaga kai kawai bata ce komai ba.”

Tun da tayi shiru yasan tana zuwa, da bata zuwa da ta fara kame-kame, dan haka murmushi ya kuma yi ya ce, “Good ki dage sosai Allah ya taimaka ko.”

“Ameen yaya, ɗazu ma ka ƙira ina..”

Bata ida maganan ba ya dakatar da ita, ta hanyar cewa, “Shiiiiiii! yayi kyau parrot naji ai, kuma daman nayi tunanin hakan, ke dai abin da nake so da ke ki mai da hankali sosai, dan ba zan yi asaran kuɗi ba, kika yi wasa kinsan hukuncinki, fatan kina ji na da kyau?”

“Eh yaya, Insha Allahu zan mayar da hankali na dage, Allah ya ƙara buɗi, Allah ya dawo mana da kai lafiya, Allah kuma ya taimaka yayana”, faɗin baby cikin stantsar soyayyan yayan nata.

Da “Ameen”, Shaameekh ya amsa, sannan ya ce, “Nasan ban saka miki card ba kuma naga kin ƙira ni, ina kika samu?”

Baby saboda ɗaukin ba da amsa, tana washe baki ta ce, “Ai yaya Jidderh ce ta saka mini har na 5k ma yaya.”

“Roƙo ko? Ban hana ki roƙo ba.”

“Allah kuwa yaya ban roƙe ta ba, ita ta tura mini daga kawai ta ƙira Ummiy sun gaisa, da aka bani sai ta tambayi bana ƙiranta na ce kwana biyu ban yi waya da kai ba shi yasa, shi ne fa ta turo mini.”

Shaameekh jinjina kai yayi tare da cewa, “To Allah ya saka mata, Ina Ummiy?”

“Ga ta nan yaya bari na bata wayan”, baby ta faɗa tana miƙa wa Ummiy waya.”

Ummiy amsa tayi tana mai yalwata murmushi a fiskanta, ta amsa sallaman da ya mata tare da cewa, “Babana ya kake?”

Fiskansa da murmushi kuma cikin girmamawa ya ce, “Ina lafiya Alhamdulillahi Ummiyna.”

“To Masha Allah haka nake son ji, ya aikin da kuma shirin dawowa?”

“Ummiyna komai sai godiya”, Shaameekh ya faɗa tare da sauya fiska, irin shagwaɓa ya tashin nan.

Girgiza kai kawai Ummiy tayi tana murmushi, tare da faɗin Allah ya shiryi babanta a zuciyanta, dan yacce ta ji muryansa sarai ta san rigima yake ji, a fili kuma cewa tayi, “To mu dai jibi za mu wuce Yobe Insha Allah, kai kuma sai yaushe za ka shigo?”

“Ayya Ummiyna ba za ku jira ni muje tare ba?”

“Gidanku Shaameekh, ni nasan yaushe zaka dawo ne balle na jira ka, ko so kake mu tsaya jiranka lokaci ya tafi a haɗe mu duka ni da kai ɗin a mana faɗan? Dan nasan halinka ba dawowa da wuri za ka yi ba.”

“A’a fa Ummiyna, Allah nima na so dawowa akan lokaci, abubuwan ne suka taru suka mini yawa, a taya ni da addu’a Ummiy.”

“Menene suka maka yawa?”, Ummiy ta tambaya.

“Ummiy wai akwai wasan da za mu yi next week friday, sannan ɗazun nan aka mini magana zan duba wani patient yana cikin mawuyacin hali.”

Ummiy cikin tausayi ta ce, “Subhanallah! ba matsala Shaameekh kar ka damu ka ji babana, ka tsaya kayi aiki mai kyau ko, kayi aikin lada ina kuma addu’an Allah ya sa kuyi a sa’a, Allah ya tashi kafaɗunsa ya kuma basa lafiya.”

Shaameekh lumshe ido yayi yana mai jin ƙaunan mahaifiyar tasa a ransa ba adadi, halayyanta a ko yaushe ƙara stumasa suke yi, fatan samun mace mai irin halinta yake yi, ga tausayi ya haƙuri ga uzuri ga kawar da kai, ga kuma sanin ya kamata, cewa yayi, “To Ummiy Insha Allah zan yi aikin, a kuma taya mu da addu’a, sannan zan yi iya bakin ƙoƙarina a ranan da muka yi wasan, idan zai yiwu to zan biyo hanya Insha Allah.”

“Duk yacce ya yiwu kai dai ka kula sosai ka ji Babana, idan ma ka gaji to ka bari sai Saturday ka taso kawai, yau da gobe duk ɗaya ne a wajan Allah.”

“Shikkenan Allah ya ƙara girma da nisan kwana Ummiyna, Allah ya kai ku lafiya ya tsare hanya.”

“Ameen ya Rabbi Baban Ummiynsa, Allah ya maka albarka ya taimaka.”

Cike da farinciki suka yi sallama, ya ajiye wayansa yana faɗin, “Allah ya saka maka da Aljanna Abiy da ka zaɓa mini uwa tagari irin Ummiyna”, Yana  maganan kuma sai a take murmushin fiskansa ya ɓace, sai wani irin ɓacin rai ne ya mamaye fiskan nasa, wan da a take har colorn idonsa sai da suka sauya, wan da ni kai na ban san dalilin hakan ba.

Buɗe system ɗin nasa yayi yana dube-dube akan ciwon da patient ɗin ke fama da shi, ƙira ne ya kuma shigowa wayansa, ganin layin Manseer ne sai ya haɗe fiska kamun yayi picking, cewa yayi, “Me kuma ka ƙira ka ce mini dan uban mutum.”

Dariya Manseer ya kwashe dashi a ɗayan ɓangaren, ya ce, “Haɗa fiskanka a banza ko a kwalan rigana, ɗan iska dama an ce maka akwai mutumin da bai da uba ne? Sai dai ko ace shi na shege ne na gaba da fatiha, amma bayan ɗan starkakakkiya Nana Maryama AS, to ba ɗan da za a haifa a duniya kuma ba uba, wa lau mutum wa lau aljan.”

“Me ka ƙira ka ce min?” Shaameekh ya ƙara tambayansa cikin dakewa.

“Nasan ka huce yaron Ummiynmu shiyasa na ƙira ka, am yauwa na ce ba yaya kuka yi da Balaraben?”

Guntun tsaki Shaameekh ya ja tare da cewa, “Man kar ka bari mu haɗu, dan zan iya karya ƙashushuwan ka, uban wa ya ce maka na huce?”

Dariya Manseer ya ƙara yi tare da cewa, “Ba matsala ƊAN DAMBE  kuma angon kulu mai jidda, yanzu dai please ni damuwata na ji ya kuka yi da su, ka amsa musu za ka yi kuwa, dan nasan halinka imani ya maka ƙaranci.”

“Hmnn! Ba ka gama haɗa mini case ba, ai dole ka tambayeni me na ce musu, kuma kasan dai duk rashin imanina, ba ƙin attending patient zan yi ba, tun da dan haka na ɓata lokaci wajan yin karatun, kuma ko na ƙi yi ma Ummiy za ta saka ni yi dole, ban dai ba shi amsa ba kam, amma na ce ya bani lokaci zan yi tunani, kuma kasan tunanin kawai ina son duba wasu abubuwan ne, dan tun tafiyansa abin da nake yi kenan, ya ce patient ɗin na cikin halin rayuwa ko mutuwa idan ba’a yi gaggawan yin aikin ba, ya taho mini da abubuwa masu muhimmanci dangane da ciwon patient ɗin, kuma daman ko baka ƙira ni ba ni zan ƙira ka, yanzu abin da nake so kai ma ka turo mini file record na patient, dan nasan ta in da za mu fara, saboda a yi aikin a kan lokaci.”

“Okay Man ba mastala za a turo maka yanzu Insha Allah, Allah kuma ya ba da sa’a, amma yaushe ne za ku yi aikin?”

“Ranan litinin dai nake so in Allah ya so ya kuma amince, so sai ka sanar da su, a zama ready sauran doctor’s ɗin ma duk za mu yi magana da su, idan ma aikin bai yi ranan Litinin ba to ko zuwa  Laraba haka dai, kada ya wuce Monday to Wednesday.”

Manseer cike da neman magana ya ce, “Man why not ku yi ranan Asabar?”

Dafe kai Shaameekh yayi ya ce, “Kai fa ƙaramin ɗan iska ne ba ka san abubuwan da ke a gabana ba.”

Manseer Dariya yayi a ɗayan ɓangaren ya ce, “Me kuwa a gabanka Man idan ba kayan aikin Jidderh ba.”

Ƙwafa Shaameekh yayi ya ce, “Alhamdulillahi! Wa Jidderh ce kawai ba na rabawa yaran turawa ba, ɗan iska kawai, kada ka ji storon Allah ka shiryu sai ka rasa mai auranka.”

“Oho dai ka ce komai ma kai yaro ne Man ba ka san daɗin mace ba tukunna, sannan idan Allah ya bani ta aure sai ka hana idan ka isa”, Manseer ya faɗa yana dariya.

Shaameekh ɗage kafaɗa yayi irin ta rage masa tun da yayi nisa baya jin ƙira, sannan ya ce, “Wannan kuma matsalarka ce, ni dai ina da abubuwan yi sosai, dan haka ban da lokacin shirme, ga wannan issue na aikin patient ɗin nan, ga kuma muna da wasa next week Friday, so this weekend you know i will be busy having training, shiyasa ma sai Monday zan je asibitin nasu.”

“To Man all the best, Allah ya taimaka ya sa ku yi komai a sa’a likita ɗan dambe.”

“Ameen kai kuma ɗan iska mai zaman banza”, Shaameekh ya faɗa tare da kashe wayansa ya ajiye, gaba ɗaya ma a silent ya saka wayan, dan kar a dame sa da ƙira.

Yana kan bincike-bincikensa da system nasa ba jimawa saƙo ya shigo masa a system ɗin, kaman yan da yayi stammani yana duba wa ya ga Manseer ne ya turo masa, abin da suka yi magana akan game da mara lafiyan.

Ba tare da ɓata lokaci ba ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kai, ya duba abin da ya kamata yayi arranging na komai, har sai da lokacin sallah yayi sannan ya kashe system ɗin ya rufe, ya mai da sa ma’ajiyar sa, shi kuma ya wuce ya ɗauro alwala ya fito ya ja motansa ya nufi masallaci.

*****
Ɓangaren su Ummiy suna gama waya da Shaameekh, ta miƙa wa baby wayanta tare da cewa, “Yanzu da kika yi waya da shi ɗin ya dakeki ne a wayan? Ko kuma ya ce miki wani abu? Ki daina yi wa babana sharri a ga kaman musguna miki yake yi.”

Tura baki baby tayi ta ce, “Uhmn! Ummiy ai shikkenan ya wuce, yauwa ma Ummiy wai Daddy kam yaushe zai dawo ne?”

“Ni fa baby bansan amfanin wayanki ba, a haka kuma kike cewa a sauya miki wani sabo, kina da waya ki ƙira mutane amma kya saka ni a gaba da tambaya, tom tun da kina da waya kina da kati kuma kina da layinsa to maza ki ƙirasa, ki bar damuna da tambaya ko na ƙwace wayan naki, yarinya kaman wata kanari sai son surutun stiya.”

Baby dariya take tana faɗin wai idan Ummiy ta stufa, jikokin Ummiy sun ga ta kan su, ta ƙarishe tare da yin dialing layin Daddy, yana shiga aka kashe aka ƙira ta, tana murmushi ta ɗauka da sauri, sai da ta shagwaɓe murya da fiska kaman Daddyn na kallonta, sannan ta ce, “Assalamu alaikum Daddyna.”

“Babyn Daddy yaya kuke? Ya Ummiynku?”

“Duk muna lafiya alhamdulillah Daddy, amma ni ce nake kewanka Daddy, yaushe za ka dawo.”

Murmushi yayi a ɗaya ɓangaren na rigiman baby, sannan cikin stigar rarrashi ya ce, “babyn Daddy kar ki damu ko, Daddy na hanya Insha Allah ba jimawa zan dawo.”

Idanuwan baby har sun tara ƙwalla, murya na rawa ta ce, “Daddy ayya dai ka dawo da wuri ka ji.”

Daddy jin muryanta girgiza kai yayi kawai, tare da tausasa murya ya lallashi autansa, sai da ya tabbatar tayi dariya sosai, sannan suka yi sallama ya kashe wa’yansa, baby kuwa sai murmushi take yi abin ta, (da alama Daddynta ne ya sakalta ta).

Ummiy dai tana daga gefe tana kallon su, da ta gaji ma miƙewa tayi ta koma ɗakinta dan tasan, yana gama waya da baby kuma zai ƙirata ne, kaman wani ana musgunawa babyn, yarinya goɗoɗuwar budurwa da ita tana abu kaman jinjira.

*****
Shaameekh yana dawowa masallacin ya parker motansa ya shigo ciki, da sallama ya shigo cikin gidan nasa duk da ya san ba wai a kwai mai amsawan ba ne, sai dai hakan ma wani stari ne da mutum ke samu daga mugaye, da kuma rahama daga Allah.

Ɗakinsa ya wuce direct, kayan jikinsa ya cire ya rage daga shi sai short, faffaɗan ƙirjin sa mai cike da haiba da kuma kwantattun gashi, ga ƙiran jarumta kaman wani “Salman Khan”, Shaameekh namiji ne wan da ko wacce mace za ta yi addu’ar mallaka a matsayin abokin rayuwa kuma uban ƴaƴanta.( Dole Soffy tayi hauka a kan sa), don wata macen ma in raguwa ce ta kallesa to sai ta storita dan ba makawa zai iya hallaka ta, ba ko wacce mace bace zata iya ɗaukan sa.

Zama yayi a kan kujeran da ke cikin ɗakin, ya ɗau waya yayi dialing layinta yana haɗe fiska, wayan na yin ringing ɗaya aka ɗauka, sai da ya ja tsaki kamun ya ce, “Assalamu alaikum.”

A ɗaya ɓangaren ba tare da ta amsa sallaman ba ta ce, “Sweetheart ya kake?”

Tsaki ya kuma ja ya ce, “Simple sallama ma ba za ki iya amsawa ba kaman ba ƴar Musulmai ba, sannan kina buɗe baki kina faɗan wani nonsence name, look Safiya am not ur mate! ba na son raini, maza-maza ki shirya ki koma gida yau ɗin nan, if not kin san sauran muddin na koma baki koma ba, shashasha kawai”, ya faɗa yana kashe wayansa, haushinta yake ji sosai yarinya ko class ba ta da shi, daga ƙira sai ɗauka, “mtssww useless girl”,  ya tashi ya shige bathroom.

*****
A India kuwa Soffy suna gama waya da Shaameekh ta miƙe cikin farin ciki, dan tsaban farin cikin ganin shi ne da kansa ya ƙirata ko tsakin da ya ja bai dameta ba, balle kashe wayansa, tashuwa tayi akan gadon da tsalle daga ita sai ɗan guntun shimi iya cinyanta tana tsalle.

Wasu ƴammataye biyu da ke gefen ta kwance suka lasan junansu( lesbians) ne suka ɗaga, tare da zuba mata rinannun idanunsu da feelings ya cika su, suka haɗa baki wajan cewa, “Babe lafiya muka ga kina farin ciki haka kaman ba staki muka ji anja miki ba?”

Harara ta aika musu da shi tare da cewa, “Mtswwwww wato ma bakwa so ku ga ina farin ciki? Har da wani tambayan ko lafiya, so what dan kun ji an ja staki, ai dai ni ce mai waya kuma ni aka ƙira ba wata ba, to ni ban ji ba sai ku tashi ku ƙara wuta, ku je can ku ci gaba da fasiƙancin naku dan kulle ɗaki zan yi, Nigeria zan koma yanzu.”

“What! Nigeria yanzu babe?” Ki duba time fa is almost mid night a Nigeria lokacin da zaki isa, tun da kin san ba yau za ki samu isa ba.”

“Look ko da ƙarfe nawan dare na isa ba ruwan mutum, so mind your business bana son shishshigi, kuma ku yi gaggawan tashuwa ku bar ɗakin nan, sannan ku gyara mini bed, wahalallu kawai mene a jikin yar uwarki mace idan ba tsabar jaraba ba, “mtswwwww!” ta kuma jan tsaki ta wuce banɗaki tare da banko musu ƙofa da mugun ƙara.

*****

<< Shameekh 5Shameekh 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×