Skip to content
Part 8 of 11 in the Series Shameekh by Harira Salihu Isah

Shaameekh ya ce, “Manseer gabaɗaya kai na ya ƙulle, wannan karon bansan uzurin da zan bai wa Alhaji Baba ya ƙyaleni ba, na faɗa maka yacce muka yi da su last meeting da aka yi, kuma ina da tabbacin wannan karon ba zai ɗaga mini ƙafa ba, ni kuma har ga Allah ban shirya yin aure ba tukunna, ina da abubuwan yi da yawa, ba ni da lokacin zama balle kuma lokacin da zan bai wa mace, kuma ka auri yarinya ka kasa bata lokacinka wannan ɗaukan alhaƙi ne, gaskiya ba aure a agender na yanzu Manseer, please idan akwai wata hanyan da zan bi na zillewa Alhaji baba ka faɗa mini.”

Manseer kallon Shaameekh yake yi da mamaki, dan yasan tun da har ya same shi da maganan akan neman shawara, to fa tabbas ba ya buƙatan maganan auren, dan idan ba haka ba Shaameekh da zurfin cikinsa tuni ya haɗiye damuwansa, dan haka shi ma cikin yanayi mai muhimmanci ya ce, “Man to ka bar zuwa family meeting ɗin mana, ai ina ga idan baka je ba shikkenan magana ya ƙare, ga ka da hujjojin kare kan ka, wannan sati za ka duba mara lafiya, wani sati akwai wasa, ka ga sai ka ta yin kwana har su gama su waste.”

Murmushin yaƙe Shaameekh yayi, wan da ke nuni da ba shi da wata mafita, sannan ya numfasa ya ce, “Manseer ko nan da sati uku na ce to Alhaji baba ba ruwansa da kowa ya zo, staf zai ɗage meeting ɗin har sai na gama na koma, dole zai sa ko me ka bari ka zo sai an jira ni kuma nima ba zan so hakan ba, saboda akwai masu muhimman ayyuka ko Ummiy ma marassa lafiya na jiranta, Daddy ma ya baro shungullansa ya zo, infact rashin zuwan ma ba wani mafita bane face na ja wa Ummiy wani damuwa, zuwan dai ya fi gaskiya, kuma ni ɗin ma ina son zuwa dan ina son ganin uncle’s nawa, kawai maganan auren ne bana so”, Shaameekh ya ƙarisa maganan yana dafe goshinsa irin abin ya dame sa sosai ɗin nan.

Yanayin yan da Shaameekh yayi ba ƙaramin dariya ya bai wa Manseer ba, dan haka dariyan ya kama yi, sai da ya gama sannan ya ce, “Man ni fa mamaki kake bani idan kana wannan magana, wai wani irin baka son maganan aure ne kam, to idan baka so maganan aure ba maganan iskanci kake so? Ka fa yi wa kan ka faɗa wallahi, bayan tulin ƴammatan da ke hauka a kan ka, ga kuma Soffy da jidderh a family, duka me kake nufi da su? Kai fa kamata yayi ma ka yi mata huɗu wallahi a lokaci guda, dan Allah kar ka bari jidderh ko Soffy wata ta ji wannan magana naka, dan ba ruwana atou idan aka yi aure amarya ta ƙi ba ka Garage.”

Dogon tsaki Shaameekh ya ja ya ce, “Ka ga damuwanka ba ana magana mai muhimmanci kana kawo wasa a ciki, ko da yake ba laifinka ba ne nine na zo neman shawara wajanka har gidanka shiyasa.”

“Allah ya huci zuciyanka mijin aljana, dan idan ba aljana ce ta aure ka ba, to ba dai za ka ce baka son maganan aure ba.”

“Hmmn!”,kawai Shaameekh ya ce bai tanka wa Manseer ba.

Manseer ajiyan zuciya ya sauƙe ya ce, “Man haƙuri za ka yi, ka yi auren Insha Allah za ta samu lokacinka, ni nasan kai mai adalci ne, kuma duk ƙullewan lamura da yardan Allah, ana yin aure komai ke warware wa, ai aure rahama ne, ba dan ma wannan zamani namu da ta lalace ba, matan da mazan duka sai a hankali sai kawai wanda Allah ya shirya, kawai ka yi haƙuri ka amsa mu sha biki, idan ma ba su jidderhn ba ne a ranka, sai ka kawo musu zaɓinka, Ummiy za ta yi farinciki da hakan, kuma Alhaji baba ma kasan mutuminka ne, damuwansa kada ya mutu bai ga aurenka ba.”

Shaameekh lumshe ido kawai yayi tare da jingina bayansa da kujera, wani iska mai mugun zafi ya furzar a bakinsa, amma bai ce uffan ba dan kan sa ya gama ɗaurewa ne kawai.

“Idan ma ka ƙi auren jidderh ina tunanin baka mata adalci ba, kuma su  Alhaji baba ma ba za su so hakan ba, musamman Hajiya Mama za ta ce ka ƙi takwararta, kawai Man ka yi abin da ya kamata.”

A hankali Shaameekh ya ce, “Okay!”

Dariya Manseer yayi ya ce, “ƙaton gardin gauro kai ma kana so kake wani basarwa, hhhh duk bogi ne wallahi wuyan dai a yi ne, idan ba mu gan ta da ciki ba to mun tabbatar baka so ɗin.”

Shaameekh miƙewa yayi ya ɗau keyn motansa da wayansa, zura hannunsa ɗaya yayi a aljihun jallabiyansa ya nufi ƙofan ficewa a palourn yana faɗin, “Idan na ƙara zuwa gunka da wata magana a sauya mini suna.”

Manseer yana dariya ya miƙe ya rufa masa baya, yana ta magana amma Shaameekh yayi banza da shi, har ya fice a gidan ya shiga motansa ya mata key yayi gaba, bai ko kalli Manseer ba balle ya ce masa wani abu, shi kuma Manseer cikin gidan ya koma yana dariya da halin Shaameekh, idan yana wani abun sai ka ce mai shafan aljanu, wai mutum ya ce baya son maganan aure, ka yi lokacin shiga fili ka yi dambe ma, balle lokacin soyayya da matarka.

Shaameekh direct gidansa ya wuce, yana isa ya samu baturiyar ƴar aikinsa ta jera masa komai, kallo ɗaya ya yiwa dinning ɗin ya ja guntun staki ya shige ɗakinsa, dan baya jin ma zai iya saka abu a cikinsa, haka kawai ana son a laƙaba masa mannau, idan baka kula da mace ba ko baka son ta aka aura maka ita to alhaƙi na wuyanka, mata da musulunci ya darajasu ya martaba su, ai sai mara ilimi da tunani ke ƙuntatawa mace, duk da matan ma dai wani zubin da mastalansu kaman gidan haya, “mstww!”, Shaameekh ya ja guntun staki, tare da kwaɓe jallabiyansa ya shige toilet, yana wasta ruwa ya fito ba ɓata lokaci, kayan baccinsa ya saka tare da fesa turare ya kashe wutan ɗakin ya kwanta, dan yacce yake jin yanayinsa ko ya ce yayi aikin ma, ba wani abin kirki zai stinana ba, sai dai ƙarshe ya fama da ciwon kan da yake gudu, dan jimawa zai yi yana damunsa.

*****

Ci-Gari

Wani Ƙauye ne a yankin Adamawa, ƙauye ne wanda ba shi da rata sosai da cikin Yola town, wannan ƙauyen dai ba za’a ƙira sa da ruga ba, sakamakon ba iya fulanine ke rayuwa a cikinsa ba a yanzun, sannan ƙauyen ya samu ci-gaban samun makarantun zamani(boko), kasuwa, asibitoci da sauransu.

Akwai gine-gine dai-dai gwargwado, amma dai kana ganin yanayin ginunnukan kasan tabbas ƙauye ne, ga kuma yanayin mutanen gari, suna kasuwancinsu sannan suna harkan kiwon dabbobin su.

Kutsa kai nayi a ɗaya daga cikin gidajen da ke a jerin na masu rufin asiri, ko in ce na masu kuɗi a wannan ƙauyen, domin gidan ba laifi Masha Allah, gidan ginin bulo da bulo ne ba ginin ƙasa ba, sannan yana ɗauke da madaidaicin palour ɗaya da kuma ɗakuna biyu, ginin dai irin wanda ake ƙiransa da mu haɗu a palour ne, sai staftaccen banɗakinsu da ke a cikin gida, ga madafi(kitchen) a gefe, faɗin gidan ɗan dai-dai a share tas-tas, sai daga ɗaya ɓangaren gidan kuma wani ƙaton fili ne a kewaye, wanda zai iya ɗaukan arnun plat guda biyar, wannan fili kuma cike yake da dabbobi, shanaye da tinkiyoyi da awakai, daga gefe ma akwai zabbi da kaji, a dai taƙaice dabbobi ne a wajan.

Wannan gida kana shigowa cikinsa kasan na masu stafta ne, duk da kuwa dabbobin da ke a kewayen gidan, hakan ba zai sa ka ga ko da kashin dabba ɗaya a ɓangaren masu gidan ba.

Ganin ƙofan palourn nasu a garƙame(a kulle), sai hakan ya sanya ni tunanin ko masu gidan basa nan, sai dai murya-muryan da na dinga jiyowa daga bandaƙi, shi ya ja hankali na dan zuwa na saurara, muryan babbar mace bafulatana naji tana magana da yaren fillanci, cewa take, “Wai Kulu ba za ki gyara na wanke miki ƙafan da kyau ba, ni fa shiyasa nafi son wanke miki ƙafa a stakar gida, idan yaso wankan sai muyi a banɗaki, amma da yake yau halin ya mosta kin saka mu zuwa banɗaki, kuma kin ƙi stayawa na miki na huta kema ki huta.”

Jin maganan matar ya sanya ni leƙawa har cikin banɗakin, dan duk a tunanina da ƙaramar yarinya take wannan magana, duba da yanayin maganganun nata, amma abun da ya bani mamaki ba yarinya ce ƙarama ba, babbar budurwa ce da za ta kai shekaru 17 zaune a kan wani ɗan duste wanda shi ne kujeran banɗakin, sai matar kuma tana riƙe da ƙafanta tana goge mata shi da abin goge ƙafa, har suka gama wanke ƙafa suka yi wanka suka fito, matar nan sai kan mita take, hannunta riƙe da na mastashiyar budurwan suka nufi cikin palourn nasu, direct ɗakin da yake mallakin budurwan suka shiga, matar da sallama ta shiga, ita kuma budurwan laɓɓan bakinta ne kawai suka mosta alaman tayi sallaman, amma na tabbata ko kunnenka ka kai kusa da bakinta ba za ka jiyo sautin sallaman ba.

A bakin madaidaicin gadonta ta zaunar da ita, ɗakin staf-staf da shi sai ƙamshin ke tashi, daga gadonta ɗan dai-dai mai ɗaukan mutum ɗaya, sai akwatin kayanta a gefe, manyan akwatuna uku da kit, ga kayan kwalliyanta a wani kwando, ɗakin dai a taƙaice ya haɗu kuma yayi kyau sosai, kana gani kasan na ƴar gata ce.

Wannan matar cewa tayi, “Kulu kin ga rana nayi zan ɗaura sanwa, ki yi maza ki shirya kamun kawunki ya dawo, ni sam ba son abin da kike yin nan nake ba.”

Har wannan mata ta gama zancenta ta fice a ɗakin, Kulu ko mostawa bata yi ba balle a sa ran za ta miƙe ta saka wani abu a jikinta, a haka tana zaune shiru ta sturawa waje guda ido ko giftawa bata yi, a hankali-hankali take lumshe kyawawan idanuwanta masu ɗauke da zara-zaran gashi kaman wacce tayi ƙari (eye lashe’s), tana kullesu tana buɗe su har ta kullesu gaba ɗaya tana zaune bata mosta ba, can ta fara yin gaba da baya kaman za ta faɗi a zaune, saboda gyangyaɗin bacci da take yi.

Kulu ta ɗau stawon lokaci tana gyangyaɗi a zaune, kuma ta kasa kwanciya har sai da baccin ya ci ƙarfinta ta yi gaba ta kifu da fiska kuma a yanda take a zaunen, gashinta da yake a kunce ya barbaje ya rufe kan ta ba’a ganinta, a taƙaice dai Kulu bacci tayi a zaune, daga ita sai ɗan ɓingilen ɗanlwalin da wannan matar ta ɗaura mata, suka fito wanka da shi.

A ɓangaren matan da nake kyautata zaton mahaifiyar Kulu ce, duk da kuwa ƙaramin ruwa da take da shi, idan ka kallesu tare ka ɗauka Kulu ƙanwarta ce, sai dai kawai dan fiskan girma da idan ka kalleta kasan ma ba yarinya bace, duk dai yacce aka yi ita ce mahaifiyar Kulu.

Tana ficewa a ɗakin Kulu tayi cikin gidan, madafinsu ta shige wanda yake da ɗan girma, daga gefe can ga buhuhhunan hasti, sannan ga wajan da yake ɗauke da murhunan girki, da su randa da kwandon kwanuka.

Wuta ta haɗa ta ɗaura girki, tana nan zaune ita kaɗai a madafin sai surutu take da fillanci, sallaman da ta jiyo shi ya sanyata miƙewa ta fice tana amsa sallaman, da murmushi ta ce, “Ah! gwaggon Kulu ku ne a gidan namu, sannunku da shigowa.”

Wannan mata wacce da alama za su yi sa’a da matar gidan cewa tayi, “Wallahi nice Hajjo, zan wuce ne na ce bari na iso mu gaisa, nasan kawu kam yana kasuwa ko.”

Hajjo(Maman Kulu), cewa tayi, “Ku iso mana gwaggon Kulu.”

“A’a Hajjo a kan ƙafata nake, ina Kulun fa take?”

Hajjo ta ce, “Kulu na can ɗakinta hali ya mosta, ko na ƙira miki ita nasan sai dai ta biki da ido.”

“To Allah kyauta ya bata lafiya, nikam zan wuce idan kawun Kulu ya dawo a ce na gaishesa”, wannan matan da ta shigo ta faɗa tana juyawa.

Hajjo rakata tayi tana faɗin, “Insha Allah zai ji gaisuwa, Allah kai ku lafiya a gaishe da mutanen Gurin(sunan wani ƙauye ne shi ma).”

Sai da  matar da Hajjo ta ƙira da gwaggon Kulu ta ɓace wa ganinta, sannan ta juyo ta koma madafi ta ci-gaba da ayyukanta, wan da ta ɗan ɗau lokaci kamun ta kammala, a hakan ma wai tana yi da sauri dan lokacin dawowan kawun Kulu yayi, tun da kasuwa ya je ci ba wani jimawa yake yi ba.

Hajjo na gamawa ta haɗa komai sannan ta ja ƙofan madafin ta kulle, sai da tayi wanka sannan ta shiga ciki, kayanta ta saka riga da zani masu kyau, sai dai yanayin ɗinkin ne kawai sai a hankali, ɗinki ne nasu na Fulani, kuma a kan rigan ta ɗaura zani, ta kuma ɗaura ɗankwalinta daban irin ɗanlwalin mutanen da ɗin nan, ta fesa turare, sannan ta fito ta nufi ɗakin Kulu, da sallama ta shiga ɗakin, amma ganin yacce Kulu take sai ya sanya ta maƙale sauran sallaman a maƙoshinta, mamaki ya sanyata tafa hannu kawai ta tana salati, tare da cewa, “Yanzu fisabilillahi Kulu wani ya shigo ba sai ya kwasa a guje ba, kin baje gashi kaman na ƴaƴan aljanu ga ki ba kaya, yarinya kullum abu guda ɗaya kaman ba dama, baccinma a ce ba za ki iya kwanciya ba sai an kwantar da ke, wannan wace irin damuwa ne ni Hajjo”, ta faɗa tana ƙarisawa gaban gadon Kulu.

Tun shigowan Hajjo tuni Kulu ta farka, amma a yacce take ko mostawa bata yi ba, kuma a hakan ita ma ta gaji da wannan kwanciyan dan wuyanta da kunkuminta ciwo suke mata, amma kuma ko mosti bata yi ba balle ta gyara kwanciyan.

Hajjo zama tayi a gefe tare da tattare gashin Kulu ta tafke mata shi kaman donut, tan faɗin, “Nasan sarai kin farka kina ji na Kulu, bansan meyasa wani lokaci bakya ƙoƙari wajan ganin kin yaƙi wannan halin naki ba, sam-sam bana jin daɗinsa wallahi, wannan idan ma ba mu mahaifanki ba wa zai iya da ke, tun da kin kasa saka kayan kin zaɓi kwanciya stirara shikkenan ai, amma a ce ki gyara ki kwanta mai kyau ma ya gagareki, wannan ai ba adalci kike wa kanki ba, kinsan da kawunki ne ya shigo ya ganki a haka ai yau ci-gari ta mini kaɗan da masifansa.”

Har Hajjo ta gama zancenta Kulu bata mosta ba, balle ta ce wani abu, sai da Hajjo ta gaji ta sanya hannunta ta ɗagota ta jinginata da jikinta, ajiyan zuciya kawai Hajjo ta sauƙe ganin yacce fiskan Kulu ya kumbura yayi jajir, duk da kuwa ita baƙa ce amma sai da ya nuna jan, a hankali cikin muryan lallami ta ce, “Beben Kawunta bana jin daɗin wannan shirun naki sam, kwata-kwata na kasa sabawa da hakan, abin baya mini daɗi, sai zuciyata ta dinga stinkewa ina ganin kaman daga haka za ki kurunmce ki daina yin magana, kiyi haƙuri ko da kanki ki dinga mosti alaman kina amsa mini, hankalina zai fi kwanciya na samu nistuwa, amma a ce idan shirunki ya zo shikkenan kaman kin zama mutum-mutumi.”

Kulu lumshe idanuwanta ta kuma yi bata ko mosta ba, sai numfashi da take yi a niste.

Suna zaune haka shiru, kaman daga sama Hajjo ta jiyo sallaman kawun Kulu, kamun tayi yunƙurin mostawa tuni ya shigo ɗakin cikin fara’a yana faɗin, “Ina Kulun Kawu take?”

Hajjo miƙewa tayi tare da amsa sallaman cikin fara’a, da fillanci ta masa sannu da dawowa ya amsa yana kallonta yana kallon Kulu, ya buɗe baki zai yi magana amma tuni Hajjo ta rigasa magana, kamun ya faɗa abin da zai faɗa ta ce, “Kawun Kulu wallahi kasan halin yarinyar nan sai a hankali, wanka na mata na ce ta saka kaya kamun na gama abinci ka kusa dawowa, shi ne yarinyar nan ta kwanta a haka kaman aljana, yanzu na shigo kenan zan saka mata kayan.”

Kawu ɓata fiska yayi tare da cewa, “To maza ki saka mata kayan kafin ta huta, ta zo ta amshi starabanta na kasuwa”, ya faɗa tare da ficewa a ɗakin.

Hajjo cikin gaggawa ta ciro kayan Kulu ta sanya mata, kaya ne na kanti mai shegen kyau da kuɗi, kana gani kasan a birni aka sayo sa, dogon riga ne mai hannun vest kuma yana da falmara, sanya mata tayi ta tufke mata gashin kan ta, ta yafa mata ɗankwalin kayan mai kaman net, sosai Kulu tayi kyau fan’s.

Kulu yarinyace kyakkyawa ta gaske, kalan fatarta kalan wanda ake ƙiransu da black beauty ne, baƙinta mai asalin kyau da sheƙi ne, tana da gashin kai shi ba baƙi wuluk ba shi ba ja ba har gadon bayanta, ga stayi ga sulɓi amma babu cika sosai, kana ganinta dai ka ga kyakkyawar bafulatana, hancinta ƙarami mai ɗan stayi dai-dai ƙaramin fiskanta, baƙinta ma ɗan cukul da shi, ga idanuwanta madaidaita, giranta ma ba irin cikakku sosai bane ɗan siriri dai-dai, tana da goshi wanda ya zama wani sirri na daban a kyawunta, fiskanta na da ɗan stayi da gemunta abinta, Kulu cikakkiyar budurwa ce, domin ta kai shekaru goma sha bakwai da haihuwa, ƙirjinta Masha Allah, ɗauke da ƴan madaidaitan cikakkun na fulaninta, ƙugunta ma Masha Allah kaman na wacce ta kai shekaru ishirin da ɗori, bata da wani jiki sosai kuma ba za’a ƙirata siririya ba, yanayin jikinta yanayin stayinta, shape nata kuma ya tafi da jikin nata duka, Hauwa’u kenan wacce aka fi ƙira da Kulu ko kuma Kuluwa, ƴar gatan iyayenta ta gaban bugawa a jarida,

Hajjo kamo hannun Kulu tayi suka fito palourn nasu, zaunar da ita tayi akan kujeransu madaidaita wan da duk an saye su ne saboda Kulu, saboda duk wani abun zamani na birni mai kyau, idan ka gansa a gidan to Kulu ce ta cewa Kawunta ya saya musu, sannan Hajjo ta ce mata, “Ina zuwa ko Beben Kawunta”, ta faɗa tare da shigewa ɗaki wajan Kawun Kulu.

Da sallama Hajjo ta shiga ɗakin wajan Kawu, cikin girmamawa ta ce, “Ka yi haƙuri Kawun Kulu Insha Allah ba za’a kuma ba.”

Kawu rai a ɓace ya ce, “Hajjo kullum magananki guda kenan ba za’a kuma ba, amma kina kumawa, wai idan mu iyayen da muka haifeta muka mata haka, idan wasu suka mata ai bai kamata ya dame mu ba, yarinyar nan sanin kanki kyautar Allah ce, ba ita kaɗai muka haifa ba amma kuma ita kaɗai Allah ya bar mana, meyasa ba za mu riƙe ta hannu bibbiyu ba, kinsan idan ba lalura ba da yanzu haka Kuluwa na babban makaranta a birni, ko kuwa tana gidan mijinta, dan haka bana son irin abubuwan nan na faruwa, ki daina barinta haka, kuma ki daina haɗa mini yarinya da aljanu, mu bi ta yacce take Insha Allah komai zai wuce, za ta samu lafiya kuma.”

“Insha Allah ba za’a ƙara ba Kawun Kulu, Allah kuma ya bata lafiya.”

“Ameen Hajjona ko ke fa”, Kawu ya faɗa tare da yalwata murmushi a fiskansa, dan sai lokacin ya sake mata fiska, saboda Kawu sosai yake ƙaunar Kulu, shi ne ya shagwaɓata ya sankaltata ya sangartata, akan Kulu ba irin kuɗin da ba zai iya kashewa ba, kuma akan Kulu yana iya ɓatawa da kowa ba ruwansa da ya kake a wajansa, sosai yake ƙaunarta wanda ba dan rashin lafiyarta ba da abin ya fi haka kuma, ya ci alwashin muddin ta samu lafiya da ransa da lafiyansa, to ko dako sai yayi tayi karatu, kuma aure ba zai mata na wuri ba sai lokaci yayi, tun ana masa magana akan hakan har aka gaji aka ƙyalesa.

Sai da Kawu ya gama sannan suka fito da Hajjo, zama yayi a kujeran da Kulu ke zaune, ya masto da ita jikinsa, cikin soyayya da tausayi ya ce, “Kuluwan Kawu na kawo miki starabanki kuma kin ƙi kulani tun dawowana.”

A hankali ta lumshe idanuwanta tare da mosta laɓɓanta ta ce, “Na go de”, da zazzaƙar muryanta, na ce dole Kulu tayi rowan yin magana.

Hajjo murmushi tayi ta ce, “Shikkenan an gama maganan yau kuma, sai na wani lokaci idan mai duka ya kai mu, tun da ba mai ɓacuwa bane a ajiye mata.”

Kawu ya jinjina kai tare da shafa kan ta ya ce, “Allah ya miki albarka ya kuma baki lafiya Kuluwan Kawu”, ya ƙarishe maganan tare da kwantar da ita a jikinsa, yana faɗin, “Ga shi ita ta san kan abun kallon bamu sani ba balle a kunna mata ko karatu ne.”

“Sai ka ci abinci ka mata na kan ka dan nasan bacci za ta koma ba jimawa indai Kulu ce”, Hajjo ta faɗa tare da miƙewa ta fice, madafi taje ta ɗauko abincin Kawu ta kawo masa ta ijiye a gabansa a kan tebur, zuba masa komai tayi, ya wanke hannu da bismillah ya fara cin tuwon da yaji namomi, loma ɗaya ya kai bakin Kulu amma sai ta ƙara yin gum da baki taƙi buɗewa, dan dole Kawu ya ƙyaleta ya ci ya cika cikinsa, ya gama Hajjo ta tattare, sannan ya kwantar da kan Kulu a cinyarsa, yana karanto mata surorin da ya haddace yana shafa kan ta har ba jimawa bacci yayi gaba da ita, sannan ya gyara mata kwanciya a kujeran ya miƙe ya fice, dan yin sallah ya kuma yin sauran shungullolinsa.

Hajjo kuma sallah tayi sannan ta samu waje ta kwanta ita ma, dan huce gajiya tun da kayan kallon Kulu ce ta iya kunna su, kuma babu abokin hira dole sai dai tayi baccin.

Su ne basu farka ba sai da lokaci ya ja sosai, Hajjo kama hannun Kulu tayi suka je banɗaki ta gama suka fito, alwala ta mata suka koma ciki ta saka mata hijabi ta zaunar da ita, sai da yayi kusan mintuna goma sannan Hajjo ta zo ta ɗaga ta.

Har dare tayi Kulu haka ta wuni kaman mutum-mutumi, komai sai Hajjo ta mata ko Kawu, dan ko da Kawu ya dawo kama hannunta yayi suka tafi sashin dabbobi, sai nuna mata yake ya ce wannan nata ne, wannan na jikokinsa da za ta haifa masa ne, shi kaɗai idan yayi magana sai yayi dariya domin yasan da bakinta na buɗe da yanzu tana amsawa, har sai da Magrib yayi sannan ya mayarta cikin gida ya wuce masallaci, bai dawo ba sai da yayi sallahn isha’i.

Abincin dare suka ci dukkansu, amma Kulu kam Kawu ne ya haɗa shayi mai kauri da kansa ya dinga bata, da ƙyar ta yarda ta buɗe baki tana amsa, a hakan ma wani na zuba a jikinta, kaɗan ke shigewa maƙoshinta, ko Hajjo tayi magana sai Kawu ya ce gwanda hakan, da a barta ba komai a cikinta gwanda ko kaɗan ne ta taɓa, sai da suka gama sannan ya koma ɓarin dabbobinsa, Hajjo kuma ta wasta mata ruwa a nan cikin gida da yake waje yayi duhu, suka gama ta saka mata kayanta mara nauyi riga da wando mai kyau, wan da yayi matuƙar amsan jikinta, don kuwa Kulu ba dai kayaki ba, Kawu jimeta yake shiga ya sayo mata kayakin ƴan gayu, da wuya ka ganta da riga da zani, balle kuma a kai ga ta saka ɗinkin ƙauyen nasu.

Sai da Kawu ya kai ta ɗakinta ya mata addu’a, sannan ya ja mata ƙofa ya fito ya koma ɗakinsu, kaman kullum sai da yayi sallahn nafila sannan ya kwanta gefen matarsa cikin damuwa, Hajjo ita ta dinga rarrashinsa tana basa haƙuri, faɗi take, “Kawun Kulu yanzu idan baka cire wannan damuwa a ran ka ba mai kake so ya sameka? Idan fa wani abun ya sameka Kulu ka sanya cikin mastalan rayuwa, abu guda shekara da shekaru, yanzu shekara goma sha biyu ake nema kullum abu guda, dan Allah ka lallaɓa lafiyanka ko dan yarinyarmu.”

Kawu ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa, “Hajjo dole abin ya dameni, ina haƙuri ina kawar da kai kuma na ɗau ƙaddara, amma jama’a basa gajiya da ka-ce-na-ce, amma ba komai Insha Allah watarana sai labari, Allah ya bai wa Kuluwa lafiya ya kuma bata miji nagari.”

“Ameen Kawun Kulu”, Hajjo ta faɗa tana murmushi, daganan suka kwanta bacci.

Kulu a ɓangarenta bacci ta kasa yi, domin haka abin yake mata idan dare yayi to bata iya runstawa, shiyasa daga gari ya waye to duk ƙarancin mintunan da ta kwanta sai tayi bacci, dan biyan bashin na daren da bata yi ba, haka idanuwanta biyu har sai da asuba ya kawo kai sannan bacci yayi gaba da ita, ba jimawa kuma ana ƙiran sallah Kawu ya shigo ya tayar da ita, Hajjo ta kai ta banɗaki da alwala da komai, gari na haske kowa ya kama ayyukansa, Kawu ya shirya ya tafi kasuwa bayan ya karya ya kuma duba dabbobinsa, Kulu kuma bacci ta dinga yi hankalinta kwance.

Kwana biyu masu kyau aka kwashe a irin wannan yanayi, tun magana da tayi rannan sau ɗaya ta ce ta gode, to bata kuma cewa komai ba, kuma daman ƙa’ida ne idan tayi magana ɗaya shikkenan, kuma komai sai Hajjo sun yi wa Kulu, yan da aka ajiyeta haka za’a same ta a zaune a wajan, kuma Kawu alƙawari ne kullum ya je kasuwa zai kawo mata staraba, haka za’a ta ajiyewa wai ba mai ɓacuwa ba ne, dan bata cin komai, ko shayin ma wataran bata buɗe baki sai anci sa’a yake karɓa, rabi da kwata na zuba bai wuce kwata ke shiga maƙoshinta ba.

A kwana na uku kuwa tun cikin wannan dare Kulu ta sha baccinta lumui har da juyi, kaman wacce ke shirin faɗowa daga ƙaramin gadon nata, asuba nayi kuma akan kunnenta dan ana ƙiran farko ta wara dara-daran idanuwanta a hankali, tare da sakin wani irin murmushi mai ƙayatarwa, duk da akwai duhun asuba amma hakan ba zai hanaka hango kyawawan fararen haƙoranta ba, wan da ke dandashe da haɗaɗɗen wushiryanta, ga dimple nata mai shegen kyau, wanda a duk tsawon kwanki ukun nan ko alamansu baka gani, amma da mamaki ga Kulu da murmushi yau ko me dalili sai Allah.

***
Ummiy tana shiga ɗakinta ta kwanta dan ta huta, sai dai abin da tayi tunanin shi ya faru, dan ƙiran Daddy ne ya shigo wayannata, sai da ya kusa stinkewa ta ɗauka tare da yin sallama da tattausar muryanta.

Daddy ajiyan zuciya ya sauƙe a ɓangarensa tare da cewa, “Allah ya ja kwanan Uwar gidan Shu’aibu, Ummiyn Shaameekh da baby.”

Ummiy a taƙaice ta ce, “Tare da kai”, sannan ta gaishesa ya amsa.

“Lafiya kuwa naji muryan Ummiyn Shaameekh cikin fushi, wani laifi nayi na bada haƙuri”, Daddy ya faɗa cikin zolaya.

Ummiy shiru ta masa bata ce komai ba, sai da ya dage da tambaya sannan ta ce, “Ba ka kyautawa Daddyn Shaameekh, kai fa kasan da maganan meeting ɗin nan duk bayan wata uku, amma kullum sai hanya-hanya kake baka son zuwa, kuma hakan ba daɗi yake yiwa Alhaji baba ba sam, tun da dai kasan anriga da an zama ɗaya, su Yaya Sulaiman suna magana har sun gaji sun yi shiru.”

Daddy da yake yasan ba shi da gaskiya a wannan magana, haƙuri ya dinga bai wa Ummiy, yana mai tabbatar mata yanzu ma wani shungulla ne ya riƙe sa, idan ba haka ba ya so musu ba zata, sai dai kawai su gansa a gida, da ƙyar da lallami ya shawo kan Ummiy ta haƙura, amma da tabbacin Insha Allah wani jiƙon da shi za’a yi, in dai da rai da kuma lafiya, sannan Ummiy ta saki ranta, yana murmushi ya ce, “To yanzu goben ne za ku tafi ko kuwa jibi?”

“Insha Allah jibi za mu wuce, ga baby ma da rigimarta wai ita ba za’a je a mota ba, kuma naga duk abin ɗaya ne, inma ba’a je a motan ba, dole jirgin a Maiduguri zai ajiye mu, sannan mu bi mota zuwa Yobe”, faɗin Ummiy cikin jajanta nacin baby da son jirgi.

Dariya Daddy yayi nasu na manya sannan ya ce, “Ayi haƙuri ayi wa uwata yacce take so, inaga dole mu nemi private jet ko dan baby.”

“Amman kam da ya kamata.”

“To Allah ya tsare hanya ya kai ku lafiya, sai kun isa za ki haɗa ni da su Baba da Mama na basu haƙuri da bakina, kamun yarona ya isa shi ma ya taya ni basu haƙuri”, Daddy ya faɗa yana murmushi.

Ummiy ma murmushi tayi ta ce, “Insha Allah zan haɗa ku, shi Shaameekh ɗin ma ai aiki ya same sa a can Dubai ɗin, zai duba wani mara lafiya kuma wannan aikin nasu na wasa da rai ɗin za su yi shi.”

Dariya Daddy yayi sosai jin Ummiy ta ce wai dambe wasa da rai ne, sai da ya stagaita sannan ya ce, “To Allah taimaka ya basu sa’a, da duba mara lafiyan da wasan da yake da shi ɗin duka Allah sa yayi a sa’a.”

“Ameen dan isar Annabi SAW”, Ummiy ta faɗa, sannan suka ci-gaba da hiransu na mata da miji, Daddy sai zolayanta yake yayi kewanta, Ummiy kuwa ta ce ai zance yake so wai an ce da gauro ya iyali, da yayi kewanta ai da ya dawo, a haka dai har suka yi sallama da fara’a, kuma cike da shauƙin juna, musamman Daddy da yake matuƙar kewan matar tasa da ƴar sa gudan jininsa.

Ummiy tana kashe waya ta jawo ayyukanta ta hau yi, sai da aka yi sallahn Magrib sannan ta tashi tayi sallah, bata bar kan darduma ba sai da tayi isha’i, tana idarwa ta fito palourn, suka ci tuwon dare da baby sannan ta koma ɗakinta dan bacci take son yi da wuri yau, sakamakon washe-gari juma’a kuma yana da kyau ga dukkan ɗan Adam, ko da kuwa a sauran darare baya samun tashuwa yayi nafila, to wannan dare ta alhamis wacce washe-garinta juma’a ne, ana son mutum ya tashi ko raka’a biyu ne yayi, yana mai yawaita salati ga Annabi SAW, sannan ya kai buƙatunsa wajan mahaliccinsa, musamman yanzu da duniya sai dai mu ce Allah ya sa mu cika da Imani, to mutum ya yawaita lazumtar YA RABBI INNAKA AFUWWU TU HIBBUL AFWA FA AFU’ANNA, domin ruwaya ce ta hadisi guda daga Nana A’isha AS, ta tambayi Manzon Allah SAW idan Allah ya ƙaddara mata ganin lailatul-ƙadr, wani abu za ta yawaita faɗa, sai Annabi stira da amincin Allah su tabbata a gare sa ya faɗa mata wannan addu’a, wanda kuma ba ana nufin iya daran lailatul-ƙadr ba, a stawon rayuwanmu ake so mu yawaita lazumtar wannan addu’a, Allah Ubangiji ya yafe mu ya mana afuwa, Allah sa mu gama da duniya lafiya, wadanda suka riganye mu tafiya kuma Allah kai musu rahama da haske makwancinsu.

Wannan dare haka Ummiy ta raya sa yacce addini ya so, ana ƙiran farko ta je ta tayar da baby, ita ma tayi nata nafilan, ko da suka yi sallahn asuba duk ba wan da ya tashi sai da ya karanta Suratul-Kahfi da kuma salatin Annabi SAW.

Baby taya mai aikinsu Talatu tayi suka staftace gidan saƙo da lungu, wanda daman duk ranan juma’a hakan suke yi, ba su suka kammala ayyukan ba sai wajan ƙarfe goma, kuma lokacin Ummiy ta tashi bacci, sannnan suka karya, baby ta wuce ta wasta ruwa ta shirya tafiya ƙunshi dan basu da class sai yamma, a yau za ta yi ƙunshi da gyaran kai, dan kisto kam sai sun je Yobe jidderh za ta mata.

Ummiy shirin tafiya asibiti tayi, ta fito suka fice tare da baby, tana mai jaddada mata kada ta yarda bata je makaranta ba, baby ta amsa suka sauƙeta a inda za ta yi abubuwan, driver ya wuce da Ummiy asibiti.

Baby ƙiran ƙawarta Deejerh tayi ta zo ta ɗauke ta suka tafi gidan ƙunshi, ba su wani jima a can ba aka gama mata mai shegen kyau, sannan suka wuce saloon aka wanke mata kai, sai da ta ƙira Ummiy ta sanar mata ta amince, sannan suka wuce gidan su batoorl, a can suka baje kolin hiransu, baby kam har da bacci tayi, sai da yamma tayi lokacin class sannan suka tashe ta, duk suka shirya suka yi school, class ɗin bai wani jima ba aka tashi, dai-dai lokacin Ummiy ma za ta koma gida, suka biyo da driver suka ɗauki baby, Deejerh da Batoorl suka gaishe da Ummiy ta amsa tana fara’a, tare da musu sannu da karatu.

Deejerh ta ce, “Ummiy a kawo mana tsaraban Yobe.”

Murmushi Ummiy tayi ta ce, “Insha Allah khadija, ku gaishe da gida ko, Allah muku albarka.”

Suka haɗa baki wajan amsawa da Ameen, da kuma yi wa su Ummiy addu’an a dawo lafiya, sannan driver ya ja mota suka tafi, Deejerh ta aje Batoorl a gidansu, ita ma ta wuce nasu gidan..

Kada ku manta daga wannan sai last free page, garaɓasa ta ƙare daga wannan page ɗin, kina son a cigaba da tafiya da ke to maza hanzarta ki biya.

*****

<< Shameekh 7Shameekh 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×