Skip to content
Part 10 of 10 in the Series Sharri Kare Ne by Rukayya Ibrahim Lawal

SHA YAƊA

“Ke! Ke ce kika ba wa Amir damar kawo sadakin aurenki a daidai wannan gaɓar?” Na jiyo saukar sautin muryar Abba a kunnuwana. A ɗarare na sunkuyar da kaina ina fadar “Abba ka yi haƙuri na ga cewa ne gara a yi auren nan kowa ma ya huta…” Kafin na dasa aya ya tari numfashina cikin ɗaga murya har kamar zai kawo mini mangara.

“Wai ke ba ki da hankali ne ko mene ne? A’ina kika taɓa jin an yi aure da ciki in dai ba rufa-rufa za a yi ba?”
“Don Allah Abba ka yi haƙuri Allah ya huci zuciyarka.” Na faɗa da raunanniyar murya. Bai sake tamka mini ba ya juya a matuƙar fusace ya nufi hanyar fita daga gidan, sai dai ina jin lokacin da yake ƙwalawa Ali ɗan maƙwaftanmu kira yana ba shi umurnin a gyara falonsa na ƙofar gida, da alama a can za a tari baƙin.
Umma kuwa tun lokacin da baba ya juya ita ma ta shura takalminta a fusace ta bar mini wurin. Sai kawai na miƙe na koma ɗaki ina murnar haƙa ta ta kusa cimma ruwa a kan Amir, ko ba komai na yi farin ciki da barazanata ta yi tasiri a zuciyarsa. Da ma shi ne uban cikin shi ya fi cancanta ya aure ni a yanzu don mu reni cikin a tare, da ma kuma ban daina ƙaunarsa ba shi ne dai yake son zame mini alaƙaƙai ƙadangaren bakin tulu.

Can bayan kamar awa ɗaya Abba ya kunno kai a cikin ɗakin nawa, harara ya wurgo mini tare da kuɗin da ke riƙe a hannunsa. Kauda fuskata na fara ƙoƙarin yi a lokacin da kuɗin suka daki gefen fuskar tawa. Kafin in yi wani yunƙuri ya fara magana da fusatacciyar murya. “Ga sadakin da kika buƙata nan duk da ba ki cancance shi ba, darajarki a yanzu ba ta kai dubu hamsin ba ma ballantana ɗari da hamsin, amma ki tattare su ki ajiye a wurinki da ma haƙƙinki ne.”

Har ya janye daga ƙofar ya juya da zimmar barin wurin ya sake juyowa yana mini wani irin kallo. “Idan na tona asirinki kamar na daɓawa cikina wuƙa ne na dawo ina kirari, wannan ne abin da ya hana ni dakatar da biyan wannan kuɗin, sai dai ki sani muddin ina raye ba zan bari a yi wannan auren cutar ba. Ba za a yi wannan yaudarar da ni ba.”

Yana gama banbanmin faɗansa ya cikawa wandonsa iska ya bar gun, haƙiƙa na san na yi matuƙar ɓata masa rai, to amma ya zan yi? Ba ni da wani zaɓin da ya fi wannan, idan ba Amir ɗin ba waye zai aure ni da cikin wata uku kuma ya rayu da ni bayan yana ganin ɓarnar muraran? Sai dai shi ɗin, da ma kuma tare muka yi ɓarnar don haka mu ya fi cancanta mu rufe ɓarnar da kanmu.

Miƙewa na yi ina sauke ajiyar zuciya na tattare kuɗin da suka gama watsewa a ɗakin, na ɗaga ƙasan adakata na saka su ciki na ajiye kafin na san mafita a kan wannan lamari.

Ƙarar wayata ne ya dawo da hankalina daga tunanin wucin gadi da na je, da hanzarin na ɗauke ta sai na ga ana kira na da baƙuwar lamba ne. Da kamar ba zan ɗaga ba don a lokacin bana buƙatar kowa a kusa da ni saboda na fi sha’awar kaɗaici a kan komai, amma ganin baƙuwar lambar ta waje ce take ra’ayina ya sauya saboda sabon tunanin da ya zo mini. Lokacin dana ɗagan har saura ƙiris ta tsinke don haka ban jira ya yi magana ba na saka ta a speaker tare da yin sallama. A can ƙasan maƙoshinsa ya amsa mini sallama kafin ya ɗora da cewa “Yanzu hankalinki ya kwanta ko?…” Wannan furucin ya saka na yi saurin ɗago muryarsa don haka a hanzarce na cire speaker tare da ƙara ƙulewa can ƙarshen ɗakin na maƙe kamar wacce za ta shige cikin bangon. Lokacin da na ɗora wayar a kunnena ya yi daidai da lokacin da yake cewa

“Ki yi farin ciki na ɗan lokaci, amma ki sani biyan sadaki ba shi ne aure ba, ina nan zan ga wanda zai ɗauran aure da ke ba tare da sahalewata ba.” Jin muryar Amir ta saka na sheƙe da dariyar rainin hankali kafin na ce masa “Mu zuba ni da kai uban ɗana, kada dai ka manta da makaman yaƙina da na tanada, ka yi tunani yanzu a’ina za su iya kasancewa a ƙasa da mintuna biyu idan na so. Kada ka manta ina da number amminka da ta sisternka, ka yi tunani da kyau.”
Ya sheƙe da wata mahaukaciyar dariya kafin ya ce “Kada ki manta ni ma fa ina da makamai masu ƙarfi a hanuna, nawa hujjojin ba haɗin fasahar zamani ba ne na asalin ne, ke ma ki yi tunani idan na so ƙasa da mintuna biyu a’ina za su iya kasancewa.” Ɗif na yi na ‘yan daƙiƙu ina tuno kalaman gargaɗinsa na cikin takardar da ya aiko ranar nan, inda yake yi mini bayanin yana da ɗauka ta tsiraicina da zai iya yaɗawa. Na yi nisa da doron duniyar zahiri ina daɗa zurfafa a birnin tunani kwatsam na tsinto kalamansa da suka yi silar maido ni duniyar zahiri inda yake cewa “Kada ki yi tunanin na aikata yadda kike so ne domin tsoron barazanarki a gare ni, ko kaɗan bana jin tsoro, zahirin gaskiya ma na biya sadakin ne don na tabbatarwa iyayena da naki cikar kamalata ta yadda da waɗannan bidiyoyi sun yaɗu duniya za ta yi amanna da cewa ke kika yaudare ni kika sauka daga layin alƙawarinmu kuma ke za a zarga da lalata alaƙarmu da aurenmu gaba ɗaya.” Yana sauke furucin ya sake sheƙewa da dariyar da ta fi kama da ta mugunta. Zahirin gaskiya kalaman nasa sun firgita duniyata to amma da ke bana so na ba shi koda ƙanƙanuwar dama da zai iya hasaso yanayina ballantana har ya yi galaba a kaina sai kawai ni ma na mayar masa da martanin dariyar ina faɗar “Shi kenan, mu zuba shege ka fasa…”

Daga haka na kashe wayar ina jeranta sauke ajiyar zuciya. Ban kasance tare da Amir ba a lokacin amma na fahimci cewa shi ma yana cikin tashin hankali linkin wanda nake ciki, ba wai don kansa ba sai don barazanar tarwatsa mutuncin ‘yar’uwarsa da nake wanda nake da yaƙinin ko kusa ba zai bari ya faru ba. Zuciyata tana raya mini cewa dukkanin kalamansa barazana ne kawai, ba ma lallai ba ne idan akwai bidiyoyin da yake magana. Sai dai ni duk ba wannan ba ne damuwata, damuwata ita ce a samu a yi auren kafin bayyanar abin da zai dame ni ya sanya duniya ta juyo mini gadon bayanta, tun a yanzu ma na fara hango ƙashin haƙarƙarin baya nata ina ga kuma sauran jama’ar gari sun farga da abin da na aikata?

*****

Gajiya na yi da tsayuwar na fita waje tare da ɗauko tsintsiya bayan na share ɗakina na gyara shi na nufi tsakar gidan ina sharewa, ina zuwa saitin ƙofar umma ta fito daga ɗakin kamar wacce aka yi wa wahayin ƙwace tsintsiyar hannuna, sai ji na yi an fincike tsintsiyar daga hannuna har sai da na yi sartse a babban yatsana.
Harara ta watsa mini kafin ta ce “Daga yau sai yau, bana buƙatar sake ganinki a tsakar gidan nan in bada uzuri mai ƙarfi ba, ballantana ki yi tunanin taya ni aiki.” Tana gama faɗa ta juya ta shige ɗakinta riƙe da tsintsiyar a hannunta.

A nan wurin na ci gaba da tsayuwa sake da baki, har a lokacin na kasa gano dalilin da ya saka ummata ta kasa yarda da ƙaddara. Shin ba ta yi imani da ita ba ne? Shin ina zallar ƙauna da tausayin da take nuna mini a baya? Shin da ma ba a yafiya ne? A iya sanina Ubangiji ma mukan saɓa masa ya yafe mana, wannan laifin ma shi na aikatawa kuma nasan zai iya yafe mini idan ya yi nufin hakan, to ita me ya sa ba za ta yafe ba.?

Ba ni da wani mai amsa mini waɗannan tambayoyin don haka na ja gajiyayyun ƙafafuwana na koma ɗaki ina ci gaba da saƙe-saƙe da kukan zuci.
A wannan ranar ma haka na ƙarasa wunin cikin kunci.
*****

“A’ina ta ajiye su ne? Yi sauri duba mana.” Wannan sautin na ji a lokacin da nake tsakiyar baccina sai kuma na ji kamar motsin mutane a kaina, na fara mutsutsun buɗe idanun da suka yi mini nauyi.


“Kai ta fara motsi ku hanzarta mu fita.” Jin haka ya ba ni karsashin buɗe idanuna gabaɗaya. Ai ko mutum biyu na gani a ɗakin, ɗaya ya nufi akwatita ɗayan kuma yana tsaye a kaina. Na zabura na miƙe zaune ina faɗar “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Sai rarraba ido nake. Ganin na buɗe ido ya sa suka yi hanzarin juyawa za su fita a nan ne na samu damar kurma ihu. “Ɓarayi! Abba Ɓarayi a gida.”

Ai ko suna jin haka suka ƙara wa motar ƙafar su giya suka haura katanga. Daidai lokacin da suke haurewar ne Abba ya fito daga ɗaki har ya kama ƙafar ɗayan amma ya ƙwace ya dure ta waje. Ganin sun gudu ya sa Abba ya nufo ƙofar ɗakin da nake tsaye ina halin tsoro.

“Sun Miki wani abun?” Na girgiza kai alamar a’a, na raɓe ya shige ɗakin ya dudduba yana ƙara tambaya ta “Sun ɗauki wani abun ne?”

“Da alama ba su ɗauki komai ba.” Daga haka abban ya fice ba tare da ya ce mini ci kanki ba. Na koma gefe ina nazari da hasashen abin da zai iya kawo waɗannan mutanen cikin gidanmu. Da a ce satar suka zo yi takanas ba shakka ba za su fita ba tare da sun ɗauki tsinke ba. Zuciyata ce ta sake hasaso mini wani abu Daam! Sautin bugawar ƙirjina na yi hanzarin dafe saitin gun…

<< Sharri Kare Ne 9

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×