KU’U
Ba a Yabon Ɗankuturu….
Har abin hawan ya fara tafiya a kan shimfiɗaɗɗiyar kwalta razananniyar zuciyata ta yi tsalle ta tuna mini da murya mai gargaɗi da na jiyo a safiyar ranar da ta gabata a asibitin.
Nan fa fargaba ta ziyarce ni ‘Wai waye mai yi mini gargaɗin nan? Taya yasan abin da na aikata?’
‘Aljani ne.’ wani sashi na zuciyata ya kawo mini gulma wanda kuma a take na amince da hakan, don kuwa idan ba aljani ba ba wanda zai iya wannan aikin.
Sai kuma na ji ba na sha’awar komawa asibitin saboda fargabar sake yin katari da aljanar murya mai gargaɗi. Sai a lokacin ma na tuna cewa na kashe ɗarin da Abbana ya ba ni wurin sayen awarar da ba ta ma samu muhalli a tumbina ba.
“Ɗan dakata bawan Allah.” Na tsayar da matuƙin abin hawar tare da sauka sannan na fuskance shi ina yi masa bayani tare da ba shi haƙuri.
“Mtsww!” Ya ja dogon tsaki kana ya ɗora da faɗar “Aikin banza kin san ke faƙiriya ce shi ne kika ɓatan lokaci?”
Ban damu da kalamansa ba sai ma wani busasshen murmushi da na yi masa, ya ja abin hawansa ya ƙara gaba. A galabaice na sake takowa na dawo daga baya sannan na durfafi cikin unguwa don tafiya gida jiki duk a sanyaye.
Umma ta yi mamakin dawowa ta alhali lokacin tashi daga makaranta bai yi ba don haka ta tuhume ni dalilin hakan.
A gajarce na karanta mata uzurin da ya maido ni gida sannan na shige ɗaki na yi kwanciyata cike da fargaba da tunanin me zai je ya dawo. Ina jiyo muryarta daga waje tana faɗar
“Bari Malam ya dawo ya karɓo miki magani a kyamis ɗin Balarabe, amma wannan ciwon naki ya fara tsorata ni.”
Na lumshe idanu kawai ina sauraren sautin bugawar zuciyata abin ya zame mini gaba kura baya sayaki na rasa ya zan yi da wannan ƙaddarar.
“Allah Ya Yi mini sakayya.” Na furta a hankali.
*****
Wajajen ƙarfe takwas na dare ina kwance a ɗaki duk da tsananin zafin da ake ga shi ba wutar nepa, amma ba ni da damar fitowa waje shan iska kasancewar ƙaryar da na yi wa zazzaɓi ba za ta ba ni wannan damar ba.
Kamar daga sama na jiyo muryar ummata tana faɗar “Yawwa Malam don Allah gama cin abincin nan ka raka mini Noory kyamis a yi mata allura, ciwon nan nata ya fara firgita ni. A kwana biyun nan duk ta ƙwarjame ta yi haske fayau ga yawan amaye-amaye kamar mai sabon ciki.”
‘Daram dam!’ sautin bugawar ƙirjina kenan yayin da kalamanta suka daki dodon kunnena.
“Na shiga ukuna ni Noorhan!” Na furta da siririyar murya. Ina sauke kalamaina na jiyo tashin murya Abbana cikin sauti mai kaushi da amo sosai.
“Habah Fauziyya! Ko kusa ban kawo zan ji wannan mummunan furucin daga bakinki ba. Fatan banza kike yi wa tilon ‘yarki?”
“A’a Malam ba abin da nake nufi ba kenan alamomin ne duk…” Ya tari hanzarinta da faɗar
“Na ɗauka ko a bakin wani kika ji wannan za ki ƙaryata kuma sai inda ƙarfinki ya ƙare, kasancewar ni da ke ne muka rene ta kuma muka san irin tarbiyyar da muka ba ta. Duk da ba a yabon ɗan kuturu sai ya shekara goma da yatsa, amma ni dai zuciyata ta aminta da yarinyata ɗari bisa ɗari, al’umma ma suna yi mata kyakkyawan zato. Saboda haka ki kiyaye furucinki ke uwa ce bakinki tamkar lalle yake ga ‘ya’yanki.” Ya karasa zancen da sigar nasiha.
Ban samu damar jiyo amsar da ta ba shi ba kasancewar ina daga ciki ne, mai yiwuwa kuma ta tausasa harshe ne wanda hakan ya kasance ɗabi’ar mai laifin da yake son yin rarrashi.
Ban san ya aka fara ba kawai na ji hawaye na sauka a kan tagwayen kumatuna. Na dai san cewa hawaye ne na tausayin mahaifina da irin amincewar da ya yi mini ba tare da sanin cewa tuni na rina halayena daga farare zuwa baƙaƙe ba.
Ina tausaya masa a ranar da shukar da na yi a ɓoye za ta tsiro ta fitar da mummunan iri ban san wane irin hali zai shiga ba.
‘Tun wuri ya kamata na yi wa tufkar hanci.’ Na raya a zuciyata tare da lallaɓawa na miƙe jiki ba ƙwari na janyo jakar makarantata da ban ko waiwaye ta ba tun dawowa ta sai a lokacin. Na ciro ƙaramar wayata da layina yake ciki na dannawa Nuriyyah kira sai dai wannan karon wayar a rufe take.
‘To me ya faru da ita ne? Ita da duk yanayin da ake ciki ba ta kashe waya? Ko dai cajin wayar ne ya yi ƙasa?’ Na jerowa kaina ‘yan ukun tambayoyin da ba ni da mai amsa mini su ga shi ana hutun boko balle na ce za mu haɗu a makaranta na rarrashe ta ta ba ni mafita. Na mayar da wayar tare da kwanciya bayan na yanke shawara da zuciyata cewa gobe idan jikina ya yi kyau zan fita nemawa kaina mafita.
Sai dai a tsakiyar dare zazzaɓi mai zafi ya rufe ni, wanda nake kyautata zaton na maleria ne. Kasancewar yadda sauraye ke cin kasuwarsu a ɗakina ga shi ban damu da kunna musu magani ba da yake ba na jin cizon su a fatata sai dai su yi mini illa ta hanyar saka ni zazzaɓi. Umma na yawan yi mini faɗa a kan kunna maganin ko kuma na shiga net, amma da ke ba sa damuna sai na yi biris ba tare da tunanin afkuwar illar hakan da ake guje mini ba.
Wasa-wasa sai da na kwashe kusan sati ɗaya ba na fita ko nan da can. Kowanne kalar abinci ba ya zama a cikina sai ruwan tea shi ma rabi ke zama rabi zan dawo da shi ta hanyar amayo shi. An yi mini allurai har da ƙarin ruwa amma sai dai a ce da sauƙi don ko iya zazzaɓin ne ya sauka amma laulayi sai abin da ya ci gaba.
A daren Laraba Umma ta riske ni a ɗaki tare da zama kusa da ni tana cewa
“Gaskiya Noory ba zan zuba miki ido ina ci gaba da kallon ki a haka ba. Dole za ki daure gobe mu je na raka ki asibiti a duba mini lafiyarki, don wannan shan maganin ba ƙa’ida ina ga tsugunne ba za ta ƙare ba.”
Na langaɓar da kai tare da tausa murya ba tare da na kalle ta ba don bana son ta fahimci damuwar da nake ɓoyewa na ce da ita, “Umma da kin haƙura da zancen asibitin nan ai na ji sauƙi.”
Na ƙarfafa jikina na tashi zaune ina ci gaba da faɗar “Kin gani na ma samu ƙarfi gobe ni zan miki kunun siyarwar.” Na ƙarashe faɗe ina ‘yar dariyar ƙarfin hali.
Ta kalle ni tare da girgiza kai tana faɗar “Aa Noory duk wayonki fa sai mun je asibitin nan gobe. Ban san mene ne ya janyo ƙiyayya tsakaninki da asibiti ba. Ki kwantar da hankalinki ‘yan gwaje-gwaje kawai za a miki. Ita asibiti da kike gani wuri ne na bankaɗo ɓoyayyin cutuka sannan wurin yaƙar su daga gangar jikin ɗanAdam.”
Ta ƙarasa da sigar lallashi ganin ta kafe na ce a raina ‘Wannan shi ne Gaba kogin ruwa baya na wuta duk wanda na ce zan faɗa a cikin su zan iya hallaka.’ A fili kuwa cewa na yi “Shi ke nan Umma ke ki zauna ki yi sana’arki zan kira Nuriyyah ta raka ni asibitin gobe.”
Da wannan na samu na shafa mata maiƙo a baki ta yarda da wannan shawarar da na kawo don ceton kaina ita kuma take kallon don na tausaya mata na kawo.
Washegari tun ƙarfe tara da rabi na safe na shirya cikin doguwar riga baƙa da farin hijabi iya gwuiwa, na fito na same ta a waje tana fama da kwastamominta na ce,
“Umma ki ba ni kuɗin abin hawar mun yi magana da Nuriyyah zan same ta a gidansu sai ta raka ni.”
Sanin cewa can yafi kusa da asibitin ya saka ta amince ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Buɗe ƙaramin bokitin da take adana kuɗin sana’arta ta yi ta zaro wata tsohuwar ɗari biyu cukurkuɗaɗiya ta miƙo mini da faɗar “Allah ya tsare ya bada sa’a.” Na amsa da amin lokacin da nake tunkarar ƙofar fita daga gidan.
Har na kai ƙofa na jiyo muryarta tana faɗar, “Za ki iya tafiya ke kaɗai kuwa Noory?”
Na gyaɗa mata kai ina ba ta tabbacin na ji ƙwari sosai, sannan na ci gaba da tafiya a ƙarfafe don kawai ta aminta da furucina.
Ko da na fita daga unguwarmu ban zame ko’ina ba sai asibitin don kuwa ina ganin tsayawa neman taimakon Nuriyyah wani ƙarin ɓata lokacin ne, musamman a irin wannan lokacin da kwaɓa ta take gaf da yin ruwa.
Ranar ma kamar satin da ya gabata na fara yin nisa a cikin asibitin kamar daga sama na sake jiyo murya mai gargaɗi tana faɗar,
“Me ya saka ne kunnuwanki na ƙashi ne Noorhan? Ina mai tabbatar miki za ki yi nadama idan ba ki janye ƙudirin…”
Wannan karon tun kafin muryar ta ƙarasa furucinta na waigo a hanzarce na kalli ɓangaren da nake jiyo muryar. A lokacin na yi sa’ar ganin wata mata mai sanye da hijabi baƙi ta juya a gaggauce tana tafiya.
A take zuciyata ta ɗarsa mini cewa na bi bayanta mai yiwuwa ita ce mai wannan gargaɗin don kuwa ita kaɗai ta bayyanar da yanayin da ya ba ni kafar zargi ba ko shakka idan ma ba ita ce mai aljanar murya ba to akwai abin da take ɓoyewa, don haka ban tsaya ɓata lokaci ba na bi bayanta a sukwane sai zabga sauri take kamar wacce za ta bar ƙasar ni kuma ban haƙura da bin ta a uzurce ba.
Ummu Inteesar ce
More comments more typing…..
Share it pls