DUHU
Tsugune Bata Ƙare Ba
Na ci gaba da bin ta ita kuma tana ƙara sauri, amma duk da haka ban fasa ƙudurina na ƙoƙarin ganin na riske ta ba.
A haka muna tafe har ya rage saura ƙiris na tardo ta kwatsam! Sai ga wasu mata kamar su goma sun zo wucewa ta gabana wanda hakan ne ya samar da shamaki tsakaninmu. Daga nan kuma sai na neme ta sama da ƙasa na rasa ta tamkar wacce ta yi layar zana.
Turus na ja na tsaya ina waige-waige zuciyata cike da fargaba yayin da nake ƙara jaddadawa zuciyata cewar aljana ce. Tamkar saukar aradu na fara jiyo muryar da tsoronta ya ɗarsu a zuciyata.
“Hmmm! Noorhan kenan, kin cika kafiya. Zai fi miki kyau ki daina ƙoƙarin bibiya ta domin ba zan ba ki damar ganina ba, sai dai yana da kyau na share miki tantamarki.”
A kiɗime na fara nufar inda sautin muryar ke fitowa ba tare da lura da gargaɗin da take yi mini na in daina bibiyarta ba, sai dai ban yi nisa ba na ja na tsaya sakamakon jin muryar ta canza muhalli.
“Ki kalli gabanki na tabbata za ki hango wata bishiyar mangwaro ki ƙarasa wurin za ki riski wata farar ambulan a ƙarƙashin bishiyar ki ɗauka, akwai wasu muhimman bayanai a ciki da za su taimaka miki ki gano manufata a kan bibiyar rayuwarki. Ki koma gida kada ki cutar da yaron da ba shi da laifin tsaye balle na zaune.”
Wannan karon na razana sosai da jin yadda muryar ke yi mini siddabaru kuma nake sauraren ta tamkar a cikin iska.
Na yi kasaƙe ina kokonto shin zan aminta da ita kuwa ko kuma kawai na share na je zuwa ga abin da ya kawo ni?
Na so na share ɗin kamar yadda wani ɓangare na zuciyata ke zuga ni, amma sai ɗaya ɓangaren ya tursasa mini na fara takawa a hankali ina nufar gindin bishiyar ba don ina saka ran riskar saƙon nata ba kawai zan je ne don ganin ƙwal uwar daka.
Koda na ƙarasa kuwa sai ga abin da ta ambata saboda haka hannu na kakkarwa na ɗauka na juya a hanzarce.
Wuri na nema inda ba hayaniya sosai na zauna tare da fiddo abin da ke cikin ambulan ɗin ina ƙara dudduba cikin ambulan ɗin ko zan ga abin da ya fi wanda na gani a farko. Sai dai idan aka ɗauke wani memori sabo gal da yake ciki, ba komai a cikin ambulan ɗin.
“To me hakan ke nufi?” Na faɗa a bayyane fuska ɗauke da alamun mamaki. A take sabon tunani ya bijiro a ƙwaƙwalwata na yi saurin fiddo ƙaramar wayata daga aljihun gefen rigata na saka memorin a ciki sa’annan na kunna ta tare da sanya ji sauti (earpiece) da yake maƙale da ni kusan koyaushe.
Na ɗauka cewa wani abin ake so na kalla a ciki sai dai wani abin mamaki ba komai a ciki sai wasu sautuka (Audios) guda biyu.
Hannu na kakkarwa na kunna sauti na farko, wannan dai sababbiyar muryar ce da na fara sabawa da ita take bayani kamar haka;
“Barka da wannan lokacin ‘yar’uwa a musulunci, na sani kina da tambayoyi da dama a kaina kamar irin su wace ce ni, mutum ko Aljan? Me ya saka nake bibiyar rayuwarki? Me ya haɗa hanyata da taki ? Me ya sa nake gargaɗarki, Me ya saka na zaɓi yin amfani da murya wurin gargaɗin? sa’annan a ina na san labarinki? To ki sani ba zan samu sukunin amsa miki tambayoyinki duka ba sai ranar da Allah Ya ƙaddara haɗuwarmu da ba zan so ta kasance a nan kusa ba. Sai dai zan amsa miki wani sashe na tambayoyinki ko za ki samu salama a cikin zuciyarki.
Da farko dai ni mutum ce kamar ke, mai laifi kamar ke, wacce take cikin matsala kamar ke, sa’annan mai burin ganin ta dakatar da sauran ‘yan mata daga faɗawa tafkin nadamar da ta take ciki.”
Jin cewa ita mutum ce ya sama mini salamar da ta yi mini fatar samu, hakan ne ma ya ba ni damar ci gaba da sauraren muryar tata a nutse.
“Ina yi miki gargaɗi ne ganin kin biyo hanyar da nake kai kuma wacce na san ba za ta ɓulle da ke ba. Ina so na dakatar da ke daga sake aikata kuskure bayan wanda kika riga kika tafka a baya.
Ki sani ba a gyara kuskure da kuskure, yunƙurin zubar da cikin da aka same shi a kan kuskure ba zai gyara wancan kuskuren ba face ya ƙara damalmala al’amarin.
Wataƙila kina da tunani irin na mutanen da ke tunanin cewa don an zubar da ciki a watanni uku na farkon samuwar shi ba laifi ba ne tun da ba a rigaya an busa masa rai ba. Sai dai ina son ki sani zubar da cikin wata bakwai da na wata uku dukkanin su laifi ne bambancin da yake tsakanin su kaɗan ne. Idan kika zubar bayan busa masa rai kin aikata kisan kai kuma zunubi ne mai girma. Abin da kike ƙoƙarin yi ma laifi ne sai dai bai kai girman wancan ba.
Na zaɓi yi miki gargaɗi da murya ne domin na lura ita aba ce mafi girma da sauƙin sarrafawa yayin aikata gyara ko yin ɓarna a kan yi saurin cin nasara idan aka yi amfani da ita.
Bugu da ƙari haɗuwarmu za ta iya cutar da ke a wannan yanayin da kike ciki, shi ya sa ba zan yarda mu haɗu ba. Ba zan ba ki mummunan tarihina a yanzu ba, sai wani jiƙon ki huta lafiya.”
A sanyaye nake ƙara kallon wayar tamkar ina ganin mai maganar a ciki. ‘To ita kuwa wannan wane iftila’in ta faɗa? Mene ne sila?’ Kawai sai na ji na ƙagu da son jin waɗannan amsoshin da ba ni da su shi ya sa a ƙagauce na kunna sauti na biyun ko zan riske su a ciki.
A nan kuma ga abin da take cewa “Noorhan ki sani ina jin ki kamar ‘yar’uwata ta jini shi ya sa ba zan juri ganin kin faɗa a halaka ba. Ke yarinya ce da shekarunki ba su haura sha shida ba a rayuwa. Tsakanina da ke akwai ratar shekaru shida, na fi ki hankali da sanin abu mai cutarwa. Kada ki bari ƙawa ta taɓar da makomar ki, a irin wannan lokacin bai kamata gurɓataccen tunani ya shigo ƙwaƙwalwarki ba, istiqfari ya kamata ki runguma ki ƙasƙantar da kanki a wurin mahalicci ki nemi gafarar shi sa’annan ki nemi mafita daga gare shi. Haƙiƙa shi kaɗai yake da iko da ‘yancin ba ki mafita wacce ba za ta cutar da ke ba.
Na sani kina jin raɗaɗin abin kuma kina jin zafin cutarwar da waɗannan marubutan suka yi miki, amma ki sani kan su suka yi wa domin shi alhaki kwuikwuyo ne watarana zai komawa wanda ya aike shi. Ki ci gaba da yi musu fatan shiriya sa’annan ki daina taya ɓera ɓari, ki gargaɗi waɗan da kika ga suna yi ta hakan ne kaɗai za ki samu mafita kuma ki rabauta da ladar yin hani da mummuna.
Ina son ki ɗaukar mini alƙawarin daga yau ba za ki sake rungumar waɗannan littafan da sunan karantawa ba, a maimakon hakan ki nemo Hisnul Muslim da Alqur’ani ki runguma kuma ki kyautata tubanki, ina da kyakkyawan yaƙinin idan kika yi haka Allah zai ba ki mafita cikin sauƙi.
Kada ki sake zuwa wannan asibitin da wannan manufar na roƙe ki da girman sarki mai shimfiɗa mulki. Ki huta lafiya.”
Sautin yana zuwa iya nan na ji tsit alamar ɗaukar ta zo ƙarshe a sanyaye na miƙe na bar wajen ina maimaita faɗar “Astaqfurullah wa atubu ilaihi!”
“Sannu da zuwa Dr Saif likitan mata, gwani na gwanaye.”
Na jiyo sautin muryar wata matashiya tana faɗa cikin sauti mai nuna kambamawa. Cikin hanzari na ɗago don yin tozali da likitan da nake kyautata zaton shi na shafe tsawon mako ɗaya ina mararin ganin shi domin ya kauda damuwata.
Matashi ne a zubi da tsarin halitta guntu ne lukuti fari a kalar fata. Na ƙura masa ido a lokacin da yake zabgawa matashiyar murmushi ba tare da ya ce da ita kanzil ba ya fara tafiya zuwa cikin ginin da ke gaban shi cike da takun ƙasaita, da alama Allah a wadata shi da alfahari.
Ni da nake yi masa neman ruwan jallon sahara kuma na zo nan da nufin ganin shi domin ya kwantar da cikin jikina har sai bayan na yi aure sa’annan a tada shi na haife shi a gidan mijina sai ga shi na kasa taɓuka komai a lokacin da yake tsaye a gabana.
Wata zuciyar na umurta ta da na yi fatali da shawarar aljanar murya na bi shi ciki don fitar da kaina daga ƙangin da nake ciki. Wata zuciyar kuma tana faɗa mini cewa na yi fatali da son zuciya na bi shawarar aljanar murya.
‘Kenan wace shawara zan ɗauka a cikin biyun nan?’
Take a wurin na ajiye wasi-wasi na ɗauki shawara ta biyu, sai dai yin hakan ya saka wata sabuwar damuwar ta kunno a rayuwata. ‘Me zan faɗawa Umma idan ta tambaye ni shaidar gwajin da aka yi mini? Lallai tsugunne ba ta ƙare ba wai an sai da kare an sayi biri.’
Wannan tambayar da ta zo kaina ce ta saka ni a ruɗani sai dai nan ma ba a wani jima ba dabara ta faɗo mini na nufi wani sashe cikin asibitin.
Da akwai wata nurse da na sani da muke ƙawance a manhajar WhatsApp da take aikin asibitin ita na nema ta taimaka mini ta haɗa ni da Dr Ziyad.
Isar mu ofishin kedawuya ta yi masa bayani na a taƙaice sannan ta juya ta fice daga ofishin a ɗarare, ina lura da yanayinta kamar tana tsoron shi. Ban kawo komai a raina ba na fuskance shi cikin girmamawa na gaida shi.
Da ƙyar ya iya amsa wa da “Lafiya Ƙalau, meke tafe da ke?”
“Ranka Ya daɗe ina neman wata alfarma daga gare ka.”
Likitan da ya tsare ni da manyan idanuwansa tun shigowa ta yana faman lashe laɓɓa kamar tsohon maye ya ƙara yi mini ƙuri da idanunsa da suka fara sauya kala ya yi murmurshi mai sauti,
“Yawwa kyakkyawa ina sauraren ki.”
Kallon da yake yi mini ya saka na tsargu sosai don haka na sunkuyar da kaina ina faɗar
“Ina neman alfarmar ka yi mini takardar gwajin ƙarya da take tabbatar da ina ɗauke da cutar maleria.”
“Ni kuma me za ki ba ni a madadin wannan ‘yanmata?” Na jiyo muryarsa tana faɗa cikin wani irin yanayi. Na ɗago kaina ina satar kallon shi da faɗar
“Ranka Ya daɗe ba ni da abin ba ka, ka taimake ni saboda Allah.” Na faɗa ina ƙara marairaicewa wai ko ya ji tausayi na.
“Ke ko kike da abin bayarwa mafi girma da daraja. Idan kin shirya bayarwar ni ma a shirye nake da yin wannan aikin duk da ya saɓa dokar aikinmu.” A raina na ce ‘Wannan fa dattijon biri ne da alama.’ A zahiri kuwa tausa murya na ƙara yi ina faɗar
“Ban gane ba me zan ba ka?”
“Kanki za ki ba ni ‘yammata, na san kin fahimci yaren ai ko?”
Sai da ƙirjina ya buga da ƙarfi tsoro ya sake ratsa ni, yanzun kan na sakankanci a raina na faɗo hannun dattijon banza, ma sani kuma abin da yake so ba zai taɓa samu daga gare ni ba a halin nadamar da nake ciki.
Sai dai ina da yaƙinin idan na nuna ƙin amincewa ba zai yi mini abin da nake so ba, don haka cike da iya taku irin na ƙwararren ɗan wasa na ƙaƙalo murmurshi na yi masa ina faɗar
“Wannan ba matsala ba ce sai dai ina tsoron na cutar da kai. Kaina ba ya da girman da zai iya dakon haƙƙinka.”
Jin hakan ya saka shi tambayar abin da nake nufi, na sake yin murmurshi ina faɗar
“Duk da cewa a yanzu ba ni da kuɗi har gara ka yi mini aikin a bashi na biya ka da kuɗi a kan na yi maka sakayya da cutar Ƙanjamau.”
A zabure ya miƙe yana ƙara yi mini ƙuri da ido, fuskarsa ta bayyanar da tsantsan tashin hankali wanda nake kyautata zaton jin na ambaci cutar ƙanjamau ne ya haddasa masa hakan.
Can bayan wasu daƙiƙu ya saisaita nutsuwarsa yana sauke huci a jejjere sannan ya ce “Shi ke nan zan yi miki amma bisa yarjejeniyar za ki biya ni naira dubu ashirin bayan cikar wata ɗaya. Kada ki yi tunanin don ban san ki ba za ki iya guduwa, idan ina bin bashi komai ƙanƙantar shi ba matakin da bana iya ɗauka don karɓar haƙƙina. Haka ko cikin ƙasa kika ɓuya sai na zaƙulo ki na ɗauki mataki a kanki, kin amince?” Ya ƙarasa zancen yana murtuƙe fuskar tamkar bai taɓa dariya ba.
Jin ma yi shiru na tsayin sakanni ya saka shi cewa “Ki yi tunani sosai kafin ki amsa tambayata.”