Skip to content
Part 6 of 10 in the Series Sharri Kare Ne by Rukayya Ibrahim Lawal

DASHI

Tawa Ta Same NI

Tun bayan amso sakamakon bogi da na yi, sai hakan ya yi tasirin kore zargi da umma ke yi a kaina. Na samu sauƙin zazzaɓin da nake, amma akwai ciwo da nake yi lokaci zuwa lokaci hakan kuma ina fama da yawan kasala, da bacci tare da zaɓen abinci.

Ina samun kulawa sosai daga Abbana da Mahaifiyata wanda suka kasa fahimtar ainahin abin da yake damuna. Sosai suke kula da ni tamkar ‘yar tsanar da aka ƙera da zallar zinare.

A safiyar yau na tashi da wani irin yanayi maras daɗi, ina kwance a kan katifa idanuna a buɗe cike da tunanin yadda nake cikin hatsari na ɓoye abin da watarana tilas zai fallasu. Muryar Umma na ji tana ambaton sunana, amma sai na yi mirsisi na ƙi amsawa, ba wai don na raina ta ba ne ko ba ta da darajar da zan amsa mata kawai wani baƙon yanayi na fargaba ne na ji ya riske ni a lokacin da na ji muryar tata.

Kwatsam! Na ji shigowar ta ɗakin a lokacin idanuna suka gane mini wata mata sanye da shigar fararen kaya da ke tsaye a bayanta, sai na ji gabana ya yanke ya faɗi ras!

“Kin gan ta nan kullum jiya iyau, koyaushe tana kwance kamar ruwa.” Umma ta faɗa a lokacin da matar ta bi ni da wani irin kallo da har sai da na tsargu. Ta tako a hankali zuwa kusa da ni tana ƙoƙarin zaunawa.

“Sannu ya jikin?” Matar ta faɗa yayin da ta ci gaba da bi na da kallo kwatankwacin kallon da mutum ke yi wa mutumin da yake zargi. Ban iya amsawa ba sai raka ta da ido da nake yi tare da gyaɗa mata kai sama alamun amsa wa.
Ta sauke jakar da ke rataye a kafaɗarta kafin ta sake kallona ido cikin ido.
“Me kike ji yanzu haka?” Nan ma ban iya yin magana ba, sai janye idona daga nata da na yi ina duban gefe.

Ganin ba zan tamka ta ba sai ta mayar da duban ta ga ummana ta ce “Hajiya shin kun taɓa kai ta asibiti kafin yanzu?”
“I, ta je har ma ta karɓo takardar sakamako.” Umma ta amsa cike da ƙarfin gwuiwa.
“Ok ko za ki iya ɗauko sakamakon na gani?” Umma ta amsa da I a lokacin da take ƙoƙarin juyawa zuwa waje.

Har za ta fice daga ɗakin matar da nake kyautata zaton likita ce ta dakatar da ita ta hanyar sake tambayar ta, “Shin tana da aure?”
Umma ta girgiza kai don tabbatar da amsar da za ta bayar tun kafin bakinta ya furta. “A’a budurwa ce, dududu shekarunta 16 ne.”

Bayan ficewar mahaifiyata matar ta sauke jakar da ke rataye a kafaɗarta ta shiga ciro kayan aikinta da ke cikin jakar tana ajiye su a ƙasa. Wani abu mai kamar akwati na ga ta ɗauko da ban san ko miye ba, sannan ta nufo ni ta shiga yi mini gwaje-gwaje yayin da zuciyata ke barazanar fasa ƙirjina ta fito.

Kafin ka ce me Umma ta dawo ɗauke da takardar ta miƙa wa likitar. Ta karɓa tana gyara zaman gilashinta. Karɓar takardar ta yi ta gyara zaman farin gilashinta ta shiga yawo da idanunta a kan takardar kafin daga bisani ta ɗago ta kalle ni cike da tuhuma sannan ta naɗe takardar,
“Za ki iya zuwa ki yo fitsari a nan?” Ta tambaya tana miƙa mini wata ƙaramar roba da ta ɗauko cıkın tarkacen da ta ajiye. Ban yi magana ba gudun kar a kama ni sai kawai na ari ɗabiar ƙadangarwa na gyaɗa mata kai alamar a’a.
Umma ce ta yi karaf ta ce “Likita bari na taimaka mata.”
Tana rufe baki ta miƙar da ni ta saƙala kafaɗata a cikin tata ta riƙe da kyau sannan ta ja ni muka fara takawa a hankali. Da mun yi taku biyu ana uku sai na naɗe ƙafa ina yunƙurin faɗuwa da gangan, ita kuma umma sai ta yi hanzari ta tallafe ni da hannuwanta ta sake miƙar da ni. Na yi hakan kusan sau uku a dabarance duk don ta haƙura da rakiyar ta yarda ba zan iya ba, amma a ƙarshe dai duk haƙa ta ba ta cimma ruwa ba don sai da ta yi nasarar kai ni ƙofar banɗakin sannan ta tura ni ciki ta tsaya a waje.

Dole ƙanwar na ƙi ta saka na yo na bada cike da fargabar abin da zai biyo baya. Haka ta sake riƙe ni muka koma ɗakin inda likita ke dakon jiran dawowarmu.

“Yawwa likita ga shi.” Umma ta faɗa tana miƙa mata robar, bayan ta amsa ne Umman ta fara kiciniyar kwantar da ni a kan katifar.
A kan idonaclikitar ta ɗauko wani farin abu mai kama da tsinke a cikin kayan aikin nata sannan ta jefa shi a cikin fitsarin nawa. Bayan kamar sakanni biyar ta saka hannunta mai sanye da gloves ta cire shi tana bin wani ɓangare nashi da wani irin kallo sai girgiza kai take. Ba tare da ta ce uffan ba ta cire gloves din hannunta ta ajiye a ƙasa alamar ta gama aiki da shi sannan ta fara tattare kayan aikinta ta mayar a jaka fuskarta ɗauke da yanayin damuwa.
Wani kallo ta jefa mini tana faɗar “Allah Ya sawwaƙe.”
Sannan ta fita waje ba tare da ce wa ummana ci kanki ba, ganin haka ya sa Umma ta bi bayanta a hanzarce tana tambayar ta ba’asi,
“Likita ya za ki tafi ba ki faɗa mini abin da yake damun ta ba?” Numfashina ya ɗauke na wucin gadi a lokacin da na jiyo tambayar daga bakin Ummata.

‘Shi kenan tawa ta same ni kura da hatsin gandu, yau fa tusa tana neman ƙurewa bodari.’ Na faɗa a zuciyata cike da tashin hankalin sanin amsar da likitar za ta ba ta idan har ta kasance mai gaskiya da tsare amanar aikinta. Na jima ina jin masu azanci na cewa ramin ƙarya ƙurarre ne amma ban kawo cewa maƙurar nawa ramin za a cimma ta da wuri haka ba sai ga shi ruwa ya ƙare wa ɗankada.
“Sai haƙuri malama, ‘yarki tana ɗauke da juna biyu har na tsawon watanni biyu da sati biyu….”

“Ci me?” Na jiyo muryarta ta faɗa da ƙarfi cikin alamar razana. Duk da bana kallon fuskarta a lokacin na tabbatar tana cikin tsananin tashin hankali da kaɗuwa.

“Ki ga ciki a kanki, ba dai a kan ‘yata ba.” Na jiyo muryar fusataccen Abbana tana doso kunnena, bisa ga dukkanin alamu yanzu yake shigowa gidan. ‘Ya zan yi da rayuwata? Ina zan saka kaina? Me zan faɗa a matsayin hujjar da zan kare kaina?’ Na tabbatar suna gamawa da likitar kaina za su juyo.

Ina jiyo likitar tana tabbatar musu da furucinta tana mai ƙarawa da faɗar “Sai haƙuri ɗan yau ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba, sau da yawa albasa ba ta yin halin ruwa, don kuwa da za ta yi da ba ta yi yaji ba. Amma idan ba ku yarda da bincikena ba za ku iya kai ta asibiti a bincika muku, Allah ya sawwaƙa.” Tun daga nan ban sake jin muryarta ba, hakan ya tabbatar mini ficewa ta yi daga gidan bayan ta gama faɗa.

“Ko ba a tona ba, shirwa ta san abin da ke cikin ɗan tsako. Da ma tun farko na hasaso hakan a farkon fara ciwonta, amma ka ce baƙin furuci nake yi wa ‘yarka.” Umma ta faɗa da raunanniyar murya kafin ta ɗan tsagaita sannan tal ɗora da faɗar “Na shiga uku ni Fauziyya idan wannan zancen ya tabbata ina za mu kai wannan abin kunyar?”

Har zuwa lokacin ban sake jiyo muryar Abba ba wataƙila mamaki ya dasƙarar da shi ya kasa motsa laɓɓansa. Kafin na yi wani motsin kirki na ji durowar umma a cikin ɗakin tamkar wacce aka harbo da kibiya ta damƙi kwalar rigata.

“Ke Noorhan don ubanki faɗa mini inda kika samo wannan abin.”

Ta shiga jijjiga ni, tana jibga ta da zagina, gabadaya idonta ya gama rufewa tsabagen takaicin da take ciki.

Duk wannan abin da ake Abbana ya kasa shigowa ɗakin ballanta ya fanshe ni, da alama na shayar da shi giyar mamaki mai matuƙar bugarwa wacce ta gusar da masa hankali daga tunanin illar da ke cikin jibga ta da take yi ballantana har ya yi yunƙurin hana ta.

Duka na take ba ji ba gani ga shi ba ni da kuzarin kare hare-harenta don haka na sallama a raina ina faɗar
‘Komai ta fanjama-fanjam, kushewar baɗi dai sai baɗi.’

“Don ubanki ba za ki faɗa mini gidan uban da kika samo wannan abin ba?” Ta faɗa cikin tsawa tare da miƙar da ni tsaye ta sharara mini wani uban mari har sai da na ga taurarin wuya suna giftawa a idona, gilasan idanuna suka daina aiki na wasu ‘yan sakanni kafin su dawo bakin aiki.

“Ba za ki faɗa mini uban da ya yi miki ciki ba?” Ta sake tambaya sai dai ba alamar zan bada amsa don na riga na ƙeƙashe ido cewar komai zai faru sai dai ya faru amma duk rintsi ba zan bari su san wannan sirrin ba.

Ba wai ina fatar rufawa Amir asiri ba ne sai dai ina ƙoƙarin ramawa kura aniyarta ne, idan har suka gano Amir ne ba zan samu damar ɗaukar fansa da kyau ba don kuwa duk abin da zan yi zai tafi a banza ne girman ƙashi ba tsoka.

A haka Umma ta ci gaba da lakaɗa mini na jaki har lokacin da Allah Ya gajishe ta hankaɗe ni na yi baya kamar zan ki fa sai aka yi Sa’a bangon ɗakin ya tallafe Ni. Ita kuwa ta yarfe hannu cikin rashin damuwa da hakan ta fice daga ɗakin tana hawaye.

Ina ganin ficewarta na zame daga jikin bangon na kwanta kan katifa ina sauraren yadda raɗaɗin dukan yake ratsa sassan jikina ga azabar ciwon da ya ƙara tsanantar mini lokaci ɗaya da ma tun safiyar yau na tashi da laulayin.

‘Duk wannan abin ni na ja wa kaina shi.’ na faɗa a zuci ina jeranta sauke ajiyar zuciya. A take na hau gajimaren tunanin ranar farko da na janyo Amir muka faɗa tafkin sabon Allah.

Wataranar Asabar ce na shirya tsaf a cikin uniform ɗina na islamiyya sai fara’a nake zubawa, laɓɓana sun sha man leɓe sun yi luf abin su, siririyar baƙar fuskar nan tawa ta ji hoda ta yi fayau da ita, na zizara wani kwalli na musamman da na saya wai shi (bita-zai-zai/ ido ka idona) a cikin manyan idanuwana.

Sai da na je daidai kan kwanar da za mu haɗu na janyo kwalbar fitanannen turaren da na yi cuku-cukun saya saboda wannan ranar na bulbula shi a jikina. Idan ka ji yadda ƙamshi ke tashi a jikina sai ka rantse ɓarin turare aka yi a wurin.

Ban fi mintuna goma da tsayuwa a wurin ba Amir ya faka dalleliyar baƙar motarsa ƙirar marcedec benx, ba jira na buɗe murfin gidan gaba na afka ciki a hanzarce gudun kada wani ma ya gan ni. Bai tsaya wata-wata ba ya tada motar yana sakar mini lallausan murmushin da ya ƙara rikita ni ya sake dulmiyar da ni a kogin shauƙin don shi.

“Sweet kin haɗu da yawa fa, duk da a cikin uniform kike.” Na mayar masa da martanin murmushi mai gusar da hankali tare da maƙale murya a karo na farko a rayuwata da na fara amfani da mayaudariyar murya don cim ma manufata na ce,

“Ka fi ni haɗuwa ai darling baby, kamar ma ka zame mini tv na yi ta kallon ka ina nishaɗi.”
Ya ƙara wadata fuskarsa da murmushi hankalinsa na kan hanya ya ce “Na yi fatar a ce ni tv ne kuma ina da farin jini irin nashi ko don waɗannan kyawawan idanun su kasance a kaina kodayaushe.”

Ya ɗan tsagaita kafin ya waigo ya jefa mini wani irin kallon da na kasa fassara ma’anarsa, yana ƙara baje hanci. “Turaren nan naki ya yi yawa sweet, ba ya hau miki kai ne?” Ya jefo mini tambayar cikin kasalalliyar murya.
Murmushi da ke fuskata na ƙara faɗaɗawa kafin na fara magana cikin shagwaɓaɓɓiyar murya a daidai lokacin da ya kawar da kansa ya mayar da hankali ga tuƙin da yake.

“Ba ya yi Darling baby, saboda kai fa na saka ƙamshin bai maka ba ne?”

Bai iya yin magana ba a lokacin sai gyaɗa kai da ya yi yana sauke ajiyar zuciya, ina lura da yadda yanayinsa ya fara sauyawa.

Can bayan wasu daƙiƙu ya sake sauke ajiyar zuciya kana ya ce “Yanzu ina muka nufa? Mi ye dalilin wannan fitowar tamu? Me kike son faɗa mini da ƙofar gidanku ta yi kaɗan da saurarar shi har sai kin saci hanya?”

Na aro salo irin na ‘yan bariki na juyo kacokan tare da matso fuskata kusa da shi ina faɗar,
“Ka adana duk waɗannan tambayoyin naka zuwa nan da wasu ‘yan daƙiƙu. Yanzu ka fara sama mana wuri mara hayaniya da za mu zauna mu yi zancen.”

“Ok mu je park?” Ya tambaya har lokacin idanunsa na kan titi yana kula da motsin ababen hawan da yake tafiya a tsakankani da bayansu.

“A’a sweet wurin zai yi hayaniya, me zai hana mu je otel ko wani wuri makamancin wannan?”

Kiit! Na ji ya taka wani wawan birki a tsakiyar titin sannan ya juyo da maɗaukakin mamaki a fuskarsa yana bi na da kallon mamaki, da ƙyar ya motsa laɓɓansa ya ce da ni,
“Idan kunne na ba zagi yake ba na ji kamar kin ambaci otel ko?” Na gyaɗa kai ina yi masa fari da ido a ƙoƙarina na kwatanta yadda jaruman littafan da nake karantawa suke yi don jan ra’ayin mazaje.

“Kin fara tsorata ni Sweet.” Ya yi maganar a lokacin da kunnuwanmu suka fara tsinkayo mana horns na motocin da ke bayanmu, alamar mun tare musu hanya suna so mu matsa su wuce.

“Kai dai mu je kawai da sannu zan cire maka duk wani tsoro da fargaba da kake ji a kaina.”
Ban jira ya yi magana ba na sake cewa “Ka ga ma har kaina ya fara ciwo saboda ‘yar wannan hayaniyar.”

Ina gama faɗa na langaɓar da kaina a kan kafaɗarsa tare da rufe idanuna, na sake matsawa na shige jikinsa sosai. Shi kuma jiki a sanyaye ya tada motar ya fara tafiya saboda yawaitar horn da ake masa.

“Meye haka ne Sweet? Ɗaga ni mana.”
Idona a rufen na ce da shi “Ba ka ji ba na ce kaina ke ciwo, ka bar ni na samu sassauci Please.”

Ina jin lokacin da ya ƙara gudun motar sai dai koda wasa ban buɗe idanun nawa ba ballantana na ba shi damar sake yin tambaya, hakan nan kuma ban ɗaga shi ba kamar yadda ya buƙata, a maimakon haka ma sai ƙara lafewa da na yi luf.

A nan na yi amfani da duk wasu dabaru da ƙadangarun bariki da sauran taurarin cikin labaran suke yi don farauto abin harinsu.
A lokacin na ƙudurce cewa komai zai faru a ranar ba zan bar shi ba har sai na ɗanɗani abin da jaruman sukan ji don kuwa komai zaƙin maƙunshin gishiri, gishirin ya fi shi.

SHARE it pls

<< Sharri Kare Ne 5Sharri Kare Ne 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×