Skip to content
Part 7 of 10 in the Series Sharri Kare Ne by Rukayya Ibrahim Lawal

KWAIBA

Mai Rabon Shan Duka

Haka kuwa aka yi don kuwa ban saduda ba a ranar har sai da na cika burina.

A mafi akasarin lokuta samari ne ake yi wa shaidar yaudara, su ne idan suna da wata mummuna manufa a kan yarinya za su shiga su fita har sai sun cimma burinsu na raba ta da mutuncinta. Amma a wancan lokacin idan ban manta ba ni ce na yi ruwa na yi tsaki, na ƙulle Amir da baƙin zaren kissa da makirci irin na mata har sai da na yi nasarar raba shi da tarbiyyar da iyayensa suka ɗora shi a kai ya cika mini burina.

Shau! Na ji saukar dorina mai zafi a jikina, wanda hakan ya tilasta durowa ta daga gajimaren tunanin da nake yawo a kai ba shiri. Na cira kaina da ya yi mini nauyi na sauke dubana ga fuskar umma wacce ta dawo ɗakin a fusace, kuma ita ce take ci gaba da jibga ta tana maimaita tambayarta.
Duk da cewa ina tsananin jin raɗaɗin dukan, gashi na galabaita ta yadda ko yatsana ba na son ɗagawa, amma hakan bai saka na ji cewa akwai wata azaba a doron ƙasa wacce za ta saka ni fallasa sirrina ba.

“Don ubanki ki yi magana.” Ta faɗa cikin ƙaraji tare da sake ɗaga hannu da nufin sauke mini dorinar a karo na barkatai.

Na runtse idanuna gam ina jiran jin saukar ta a jikina, sai kuma na ji shiru har bayan shuɗewar wasu ‘yan sakanni, hakan ce ta saka na buɗe idon nawa don ganin abin da ya dakatar da ita daga cika muradinta.
Buɗewar ke da wuya ganina ya sauka kan hannun Abba da ya riƙe dorinar yana girgiza mata kai. “Ki ƙyale ta Fauziyya kada a yi biyu babu.” Ya faɗa da wata iriyar muryar kamar mai shirin yin kuka.

“Amma malam ba ka ga abin kunyar da ta ja mana ba, yanzu ina take so mu…” Tana zuwa iya nan ta dafe ƙirjinta idanunta suka birkice sai kawai mu ka ga ta faɗi ƙasa sharaf kamar tsohuwar katanga.

“Fauziyya! Fauziyya!! Ki tashi.” Ya ci gaba da girgiza ta yana ƙwala kiran sunanta amma shiru ba alamar za ta ko motsa ballantana ta tashin kamar yadda ya umurta. Cike da damuwar da ta yashe dukkan nutsuwarsa ya miƙe ya je waje, bayan daƙiƙa ɗaya ya dawo ɗakin da kofi cike da ruwa ya kwarara mata a jiki.

Sai dai ba ko alamun za ta motsa hakan ya bayyanar da firgici a kan fuskarsa, ya sake fita waje a ruɗe.
Bayan ficewar shi ne ta sauke doguwar ajiyar zuciya tare da buɗe magananta tana kallon sama, ba ta motsa ba har lokacin sai hawaye dake bin kumatunta waɗanda ke alamta cewa akwai wata damuwa da ke cin zuciyarta a lokacin.

Koda ya dawo ya tarar ta dawo daga gajeruwar sumar da ta yi, don haka ya taimaka mata ta miƙe suka bar ɗakin.

A ranar dai haka na shafe wuni a kwance, har dare ko ƙadangare bai leƙo ɗakin da nake kwance ba, ballantana na saka ran za a tarairaye ni kamar yadda aka saba.

Da na ji ɗan ƙarfin jikina sai na yunƙura na ɗauko waya na kira aminiyata wacce muke kashewa mu binne ba tare da sanin kowa ba a wasu lokutan. Duk da kowa ya shede ta da tsinannen surutu da har ake yi mata laƙabi da ganga ba kya sirri, amma ni ita ɗin ce kaɗai abokiyar sirrin nawa, a mafi akasarin lokuta ina zargin kaina da yin batan basira wai roƙon Allah da goge. Sai dai duk da haka na kasa janye amincewata a gare ta da har zan ƙwace makullan sirrina da ke hannunta.

Bayan ta ɗaga wayar take cewa da ni “Lafiya kika kira ni a daren nan? Tsaya ma me ya hana ki dawowa makaranta bayan kin san jiya aka koma?” Ta jero mini tambayoyin da zan iya cewa a lokacin ba su da alaƙa da abin da nake son ji. “Don Allah ki zo yanzu Nuriyyah ina da buƙatar ganin ki.” Na faɗa da raunanniyar murya.

“Ƙarfe takwas da rabi ta gota fa, ki yi mini uzuri zuwa safe sai na zo.” Ta furta murya ƙasa-ƙasa kamar mai raɗa. Na runtse ido hawaye na ci gaba da tsere a kumatuna na ce da ita,
“Shi ke nan Nuriyyah, bari har zuwa lokacin da za a kawar da gawata sai ki zo. Ina ji a jikina ba lallai na wuce yau a raye ba.” Murya a dabarce ta ce “Subhanallah! Wannan furucin haka Noor, Noor me ke faruwa? Kodayake bari gani nan, gani nan zuwa kawai.”

Ko kyawawan mintuna talatin ba a rufa ba na jiyo muryar ta tana gaisawa da su Abba, hakan nan na ji wani ɗigon sanyi na sauka a zuciyata.
Kafin na yi wani yunƙuri na jiyo sallamar ta a ƙofar ɗakin, na ware manyan idanuwana na zubawa firgitacciyar fuskarta idanu lokacin da take yunƙurin afkowa cikin ɗakin.
Na yi nasarar gane yanayin fuskarta ne dalilin wadataccen hasken wutar lantarki da ya mamaye ilahirin ɗakin.

“Sannu Noor, ya jikin?” Ta faɗa tana ƙara gudun fankar ɗakin, hasashena ya ba ni cewar ganin yadda nake ta haɗa gumi kamar wacce ta haɗiye kunama. Tana gama ƙarawar ta ƙaraso inda nake ta zube kan gefen katifar da nake takure a kai. “Subhanallahi! Noor meke damun ki ne haka? Dukan alamu sun nuna kina cikin damuwa bayan cutar gangar jiki, ga kuma jikinki a farfashe, meke faruwa ne?”
Na ja jiki ina matsowa kusa da ita ina ta faman sauke ajiyar zuciya, “Nuriyyah ina cikin matsananciyar damuwa, su Abba sun gano ƙwayar sirrin da muke ta ƙoƙarin binnewa tun kafin ta tsiro.” Da ƙarfi ta dafe kirjinta ta sake nannauyar ajiyar zuciya kafin daga bisani ta janye hannunta daga ƙirjin, ta sauyawa fuskarta shimfiɗa daga tausayi zuwa halin ko’in kula.
Kamar ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ce “Abin da nake guje miki kenan, amma da yake mai rabon shan duka ba ya jin kwaɓo sai kika saka auduga kika toshe kunnuwanki, yanzu wa gari ya waya?”

Na miƙe na jingina bayana a jikin bango tare da saka idanuna a cikin nata na ce “Ba wai na ƙi shawararki ba ne, na yi biyayya ne ga ubangijin talikai, shin da umurnin shi da naki wanne ya fi cancanta na bi?”

Ta yi kasaƙe tare da sunne kanta ƙasa. Na yi wani busasshen murmushi mai ciwo kafin na sake cewa, “Bayan kin ɗau zafi da ni na koma asibiti don na nemo wa kaina mafita, sai na ci karo da wata baiwar Allah, da ta yi mini nasiha, ta janyo ni daga hanyar halaka ta ɗora ni a ta shiriya duk da cewa idanuna bai taɓa tozali da ita ba. Na ji a raina matar kirki ce kuma zan yi duk yadda zan yi don haɗuwa da ita domin ina buƙatar sauran bayanai daga bakinta.” Daga nan ne kuma na shiga labarta mata duk yadda muka yi da aljanar murya.

Bayan na kammala ba ta labarin ta yi ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya kafin ta riƙo hannayena biyu a cikin nata ta ce “Tabbas kin fi ni gaskiya, kuma ina tare da ke ɗari bisa ɗari. Ni kaina bai kamata a ce na manta illar yin hakan ba, ko don tawa illar da abin ya haifar mini ba ta kai haka ba ne ya saka na manta?”

Na kalle ta irin kallon da alƙali yake yi wa shaida yayin da ya dakata daga bada amsar abin da ake buƙata ba tare da zancen ya ƙare ba. Da alama kuma kallon ya tasirantu wurin fahimtar da ita manufata saboda ji da na yi ta ci gaba da cewa, “labarin yana buƙatar lokaci, sai dai muna da isasshen lokaci zuwa safe idan ba zan takura miki ba.”
Tana rufe bakinta ta ɗauki wayarta ta kira yayarta Mariya ta sanar mata cewa za ta kwana a gidanmu ta faɗawa ummansu. Jin hakan ya saka ni jindaɗi ko ba komai za ta rage mini kewar da ke addaba ta a wunin ranar.

“Ahh!” Na yi dogon nishi ina dafe cikina da nake jin ‘ya’yan hanjina da suke ciki suna ƙullewa. Nasan hakan bai rasa nasaba da wunin da na shafe ina jan hanji. “Meke faruwa?” Ta tambaya tana kafe ni da ido. Na girgiza mata kai ina murmushin yaƙe, “Uhm! Ba komai ƙawa yunwa kawai nake ji, da yake tun safe rabon ‘yan hanjina da karɓar baƙuncin abinci.” Ta ɗan haɗe fuska kaɗan sannan ta miƙe tsaye, “Gaskiya ba ki da kirki shi ne kika tsorata ni? Me ya saka ma kika kai har wannan lokacin ba ki saka wani abu a cikinki ba alhali kina zaune a cikin gida? Bari na je wurin Umma na karɓo miki.” Ta rufe tambayoyinta da bayani.
Na gyaɗa kai tare da rufe idanuna da na ji ƙwalla ta fara taruwa a cikin su na ce da ita, “Kada ki je. Mu ba su lokaci nasan yau a fusace suke da ni.” Ina gama faɗa na buɗe idanun lokacin ne kuma na ga ta cika umurnina ta hanyar juyowa ta dawo tana yunƙurin zama yayin da take faɗar “kin zo da magana abar dubawa. Bari na buɗe shagon tafi da gidanka ɗina na gani ko za a samo miki abin taɓawa.” Ina jin haka na ƙure ta da ido, kafin ma na samu damar yin tambaya na ga ta buɗe ‘yar madaidaiciyar jakar tata ta shiga buɗe mazugan tsakiyar jakar tare da tura hannunta can ciki tana lalube.

“Ahaf! Ni nasan ba a rasa nono a ruga, duk da ba ni da yaƙinin na ajiye abin da ake nema.” Ta ciro ledar madara biyu da ta bornvita ɗaya ta ajiye a kan katifar sannan ta ci gaba da lalube-labube. Can ta ɗago ta zuba ƙwayar idanunta a cikin nawa da da ma can suna kanta ta ce “Ayyah! Kin ga an yi rashin sa’a ba sukari, za ki iya sha a haka kuwa? Don na ga dare ya fara nisa ba lallai a samu shaguna a buɗe ba yanzu.” Na ɗaga kai ina faɗar “I, da babu ai gara ba daɗi.” Ta sake yin murmurshi wanda zai fi kama da murmurshin tausayawa sannan ta miƙe ta nufi ƙofa. “Bari na nemo miki kofi da cokali.” Daga haka ba ta ƙara cewa komai ba ta fice. Bayan daƙiƙu ta dawo ɗakin ta zauna ta haɗa mini tea ɗin.

An yi sa’a wannan karon tea ɗin ya zauna a cikina dalilin da ya saka kuzarin jikina ya ƙaru, na tashi zaune daidai ina fuskantar ta. “Yanzu na samu nutsuwar da massarafan jina za su iya tace bayananki su tura saƙo ga sashi na musamman da ke ƙwaƙwalwata wanda yake taskace abubuwa.”


Ta sake yin murmurshi a karo na barkatai sannan ta gyara zamanta ta fara da faɗar “ni ma kamar dai ke, son zuciya ya tasirantu wurin jefa ni a matsala, duk da masu ji da ganina ba za su iya fahimto matsalar kai tsaye ba, koda sun fahimto nasan za a ɗorawa ƙaddara ne, bayan cewa ba ruwan ƙaddara a cikin wannan lamari. Idan ko har za a iya kiran shi da ƙaddara to ni ce na ƙaddara wa kaina faruwar ƙaddarar.” Na bi ta da wani irin birkitaccen kallo saboda na kasa gane inda kalamanta suka dosa. Ba ta jira jin ta bakina ba ta ɗora zancenta da faɗar, “matsalar ido da nake fama da ita da kuruciyata ni na siyawa kaina ita da kuɗaɗena kuma da lokacina.”

Ta ɗan tsagaita tana sauke huci yayin da laɓɓanta ke motsi alamar tana son furta wani abu mai nauyi. Na kafe ta da kadarar mujiyata a zuciyata na ce ‘Kodayake komai son rai ne yin ƙawa da makauniya amma nasan dai ruwa ba ya tsami banza.’

SHARE it

<< Sharri Kare Ne 6Sharri Kare Ne 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.