KWASTA.
Abin Mamaki Agwagwa Da Ƙin Ruwa.
Ta sake sauke ajiyar zuciya sa’annan ta ce,
“A shekaru huɗu baya tun lokacin ina jss2 a makaranta aka saya mini waya a gida, kasancewa ta ‘yar gatan iyayena kamar yadda kika sani. An saya mini ita ne don yin harkokin karatu da wasanni (Games) kuma hakan ya yi mini daɗi sosai.
Haka kurum watarana na yi karambanin ɗaukar ta zuwa makaranta ba tare da sanin yan gidanmu ba, a lokacin ina GDSS Bakari Dukku.
Bayan an buga tara ɗalibai duk suka watse zuwa sabgogin gabansu ya rage daga ni sai Zarah Nura a ajin, bayan na dudduba na tabbatar mu biyu ne jal a ajin kuma akwai tazara tsakanin inda nake zaune da inda take kawai sai na fiddo sabuwar wayata ina buga game ai kuwa tana ganin wayar ta baro inda take zaune ta dawo inda nake ta zauna kusa da ni tana faɗar “kawo na tura miki abubuwa.” Ban musa ba na miƙa mata wayar.
Ita ma ta ɗauko tata da take ɓoye a jaka ta tura mini bidiyoyi na comedy da littafai, ni dai da ido kawai nake raka ta har lokacin da ta gama ta miƙo mini wayar.
Ina buɗewa na ga labarai sai na tambaye ta, me zan yi da waɗannan kuma miye amfanin su? A nan ta kwaɗaita mini cewa na fara karatun littafai za su nishaɗantar da ni kuma zan ƙara samun gogewa ta fannin rayuwa.
Ban yi mata gardama ba don kuwa idan ba zan manta ba ina jin wani azanci da hausawa kan ce mutum ba ya ƙin ta mutane wai an ce da ɓarawo gudu. Don haka ni ma sai na ɗauki shawarar tata.
Ashe wannan shi ne kuskure mafi girma da na tafka a cikin rayuwata a lokacin wanda illar hakan ba ta bayyana ba sai da tafiya ta yi nisa.”
Tana zuwa nan a zancenta ta sauke ajiyar zuciya tare da cire hijabin da ke jikinta ta ajiye shi gefe sa’annan ta gincira tana murmurshin da ya fi kama da na takaici sannan ta ɗora da faɗar,
“Bayan komawa ta gida ko uniform ban cire ba abinci kaɗai na ci na ƙule a ɗakina na shiga kallon sabbin comedies (bidiyoyin nishaɗi) da ke wayata, tun kan na ƙarasa na farko zancenta ya dawo a massarrafar sautukana.
“Ki karanta labaran nan za ki samu nishaɗi sosai fiye da waɗannan comedies ɗin kuma za ki ƙara samun gogewa ta fannin rayuwa.”
Zumbur na miƙe zaune daga kwanciyar da na yi ina jin zaƙuwa da son sanin keke ciki, na shiga lalubo su, ina zuwa kan wani littafi wanda shi ne na farko da sunanshi ya fi tafiya da ni na yi hanzarin buɗe shi.
Na sake maimaita karanta sunan littafin a bayyane Motar Haya.” Na yi jim ina son gano ma’anar wannan suna da kuma inda labarin ya dosa kafin na karanta.
A iya sanina dai motar haya na nufin motar kasuwa wacce kowa zai iya hawa ya sauka kuma ya biya kuɗin ladar aikin sauke shi da aka yi, kenan miye alaƙar labarin da sunansa?
‘To ko motar tijararru ce?’ na tambayi hakan a zuciyata ɗayar sashen zuciyar ya ce da ni ‘me kike ci na baka na zuba? Karanta ki ji mana ai ɗanɗane ya zarce ganin ido.’ Ba tare da na musawa zuciyar da ta shawarce nin ba na fara karantawa.
Duk da cewa a lokacin ina aji biyu ne kacal amma na samu tushiyar karatu mai kyau tun daga nursery wanda hakan ya saka zan iya yin kowanne irin karatun hausa ba tare da wata matsala ba, sai dai ‘yan kalmomin da ba za a rasa ba da suke yi mini gardama a lokacin.
Tun a tashin farko na motar labarin na fara cin karo da ababen da suka fi ƙarfin ƙwaƙwalwata, amma son sanin ma’anar sunan labarin ya sa na nutsu sosai a cikin labarin.
Sai da na yi nisa sosai a cikin tafiyar sannan na fahimci inda aka dosa, na so na ajiye labarin daga lokacin, amma sai zuciya ta yi mini taurin kai ta tilasta mini ci gaba da yin nutso a cikin labarin, a lokacin ne kuma na riski baƙon yanayin da ban taɓa ji ba a rayuwata. Daga wannan ranar kuma na zagaɗe da karatun littafan batsa sama da littafaina na makaranta da a da ba abin da ya fi su muhimmanci a wurina.
Wata ranar Laraba da muka haɗu a makaranta muka sake keɓewa ni da Zarah na labarta mata yadda na ji daɗin labaran da ta tura mini, kuma na nemi ƙari, tare da sanar da ita halin da nake tsintar kaina bayan karanta su, na kuma tambaye ta sunan baƙon yanayin da nake ji.
Ta yi ‘yar dariya haɗe da wani shu’umin murmushi sannan ta ce “Sunan abin da kike ji shauƙi, da sannu za ki isa birnin da nake miki fatar zuwa.”
Ban ce da ita kanzil ba haka ban fahimci ma’anar kalamanta ba sai kawai na raka ta da gajeren murmushi. Sa’annan ne ta sake karɓar wayata ta loda mini wasu bidiyoyi kusan guda talatin.
Ta miƙo mini wayar tana murmushi, “karɓi wayar ki je ki kalli waɗannan za su rage miki shauƙi.” A lokacin har na danna wayar da nufi buɗewa na ga abin da ta turan sai sautin ƙararrawa ya daki dodon kunnena alamar an kaɗa dawowa aji don haka na yi hanzarin kashe wayar gaba ɗaya na jefa a jaka.
Bayan na koma gida ko abinci ban nema ba na sake ƙulewa cikin ɗaki na buɗe folder (ma’ajiyar abubuwa) da suke ciki. Na tsorata ainun a lokacin da na ci karo da bidiyoyin banza kala-kala, har sai da na yi saurin ɓoye wayar a ƙarƙashin filo ina waige-waige, don kuwa a firgice nake ainun, gani nake kamar wani yana tsaye a wurin yana kallona.
A lokacin da na fahimci ni kaɗai ce a ɗakin sai na manta cewa mahalliccinmu ba ya gyangyaɗi ballantana bacci, kuma yana kallon abin da nake aikatawa. Sheɗan ya ci gaba da yi mini huɗuba yana nuna mini cewar ai ba wanda ya san me nake aikatawa, hakan kuma ba laifi ba ne.
Don haka na kunna bidiyo ɗin sannan na tura hannuna da yake riƙe da wayar, ta cikin kusurwar gadon sai na zura kaina tamkar ƙadangaruwa yayin da take tsaye a bakin tukunyar ƙasa tana leƙen cikin.
Ɗaya bayan ɗaya na shiga kallon su, ina matse ƙafa gangar jikina tana amsar saƙon baƙon yanayi. A lokacin ne kuma na jiyo muryar mahaifiyata a kurkusa tana ƙwala mini kira.
Wai ashe har ta iso cikin ɗakin tana kirana ban sani ba tsabar nisa da na yi a cikin tafiyar saɓon mahalicci.
Ba shiri na sake wayar ta faɗo kan gadon kasancewar na riga na ciro hannuna daga kusurwar gadon da tuni wayar ta fashe.
Na gyara filon daidai yadda zai rufe hasken fuskar wayar ta yadda ba za ta iya hango abin da yake ciki ba.”
Nuriyyah na zuwa nan a cikin labarin ta sake ɗan tsagaita tare da muskutawa, ta zuba mini darara-dararan idanuwanta a cikin nawa, har zuwa lokacin ban ce komai ba na dai ci gaba da zuba mata kaddarar mujiyata.
Nuriyyah ta ɗora labarin da faɗar “To tun daga wannan ranar kuma na zaƙe har na fi mai kora shafawa a wannan safgar, don kuwa ba ni da wani aiki a kullum sai na karance-karancen batsa da kuma kallon irin waɗannan bidiyoyin da nufin rage zafi, zancen hardar Alqur’ani da nake yi tuni na watsar saboda na daina gane komai, na rage taya mahaifiyata aikin da na saba yi a gida, a kullum ba ni da aiki sai kallon waya har zuwa lokacin da na gama junior waec na fara makarantar da na zo na sake haɗuwa da ke bayan shafe shekaru uku ba ma tare.
Har zuwa lokacin ban daina ɗabi’ar kallace-kallacen ba, duk da rashin mai tura mini a kusa sai na fara zuwa website ina kallar su a online tunda yake na riga na zama addicted da wannan ɗabi’ar.
Sannu-sannu na fuskanci ƙarfin ganina ya fara raguwa, abin da nake iya hango shi a nesa a da sai ya zamana a lokacin bana iya hango shi sai ya matso kusa da ni, daidai da kallon tv wannan idan zan yi sai na zo kusa da screen ɗinsa sosai sa’annan nake iya karanta tittle na fim da ganin fuskar jaruman wasar da kyau.
Sannu ba ta hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba, watanni kaɗan gaba na fuskanci matsalar ido da nake fama da ita tana ƙara tsananta a take na tuna wani posting da na taɓa cin karo da shi yana yawo a media game da views na malaman addini da suke cewa kallon tsiraici yana rage ingancin gani idan aka yi wasa ma za a iya rasa ganin gaba ɗaya, shi ya sanya za mu ga ƙadangarun bariki da yawa a ƙarshen rayuwarsu basa mutuwa da idanu.
Dam! Ƙirjina ya yi mummunar faɗuwa, a lokacin na ƙudurce a raina lallai sai na yi duk yadda zan yi na samu ganin likita don duba wannan matsalar tawa duk da cewa ina sane da cewa iyayena irin mutanen nan ne da ba su yarda da yawan zuwa asibiti da bincike-bincike ba musanman Abbanmu, da a ce bai yi boko ba sai mu yi tunanin rashin wayewa ce ta janyo hakan…”
Dakata kaɗan Nuriyyah! Kina nufin duk da kasancewar Abba (Nurse) malamin jinya, amma bai yi imani da yawan zuwa asibiti don binciken lafiya ba?” Na tambaye ta da yanayin mamaki a fuskata.
Ta miƙe daga kishingiɗar da ta yi tana ‘yar dariya ta ce “ƙwarai kuwa, duk da na fara wani hasashe a kansa game da wannan al’amari.” Na gyara kwanciyata tare da janye idona a cikin nata na ce “Ikon Allah! Wannan shi ne abin mamaki agwagwa da ƙin ruwa.”
Ta sake yin ‘yar dariya “ba za ki tambaye ni hasashena a kansa ba?”
Na yi murmurshi domin har na fara mantawa da yanayin damuwar da nake ciki daga zuwanta zuwa yanzu na ce da ita “Ai za ki iya faɗan koda ban tambaye ki ba.”
“A hasashena ko na ce hasashen yaran gidanmu, Abbanmu ba ya son duk wata lalura da za ta taɓa lafiyar aljihunsa, haka ba ya maraba da duk wani al’amarin da zai saka aljihunsa ya yi zafi shi ya saka duk irin waɗannan al’amurran ba ya bayar da goyon bayan wanzar da su a cikin iyalinsa sai ta kama dole.
Ni kaɗai ce nake iya cin abin hannunsa kasancewa ta ‘yar da yafi so, ni ma ba koyaushe yake iya nunan soyayya da aljihunsa ba.”
“Hmm!” Na sauke ajiyar zuciya ina fuskantar ta “Kina da gaskiya kin san a wannan zamanin akwai kalolin iyaye maza da basa iya sauke haƙƙin iyalansu duka saboda yanayi na matsin rayuwa da ake ciki, sukan saki ragamar kula da gida a hannun iyaye mata, duk da sun fi kowa sanin cewa mata suna da rauni haka ma haƙƙin ciyarwa ba a wuyan matan ya rataya ba, amma a haka suka sakar musu ɗawainiyar ci, sha da tufatar da yaransu, shi ya sa tarbiyyar yaran zamani ta ɓalɓalce saboda ba haɗakar mahaifi da mahaifiya wurin gyaran tarbiyyar, Allah dai ya kawo mana mafita. Ƙarasa mini labarinki.”
Ta amsa da amin sannan ta gyara zamanta tare da jingina bayanta a jikin bango ta ɗora labarin da faɗar “to a wannan lokacin ne na yi iya ƙoƙarina wurin fahimtar da Abbanmu matsalar idanu da muhimmancin binciken lafiyarsu. Da ƙyar na ciyo kansa ya amince zai ba ni ‘yan wasu kuɗi sai dai ya faɗa mini ba zai kai ni asibiti ba sai dai na je da kaina.
Na kuwa amince da hakan, a wannan satin na karɓi ‘yan kuɗi daga hannunsa a wata ranar Laraba na nufi Almanzoor Hospital da ke Igbo quarters duk da ina sane da cewa (Commercial hospital) asibitin kuɗi ce kuma abubuwa za su ɗan yi tsada a can to amma na yi amanna da cewa zan fi samun ingantaccen rahoto game da lafiyata a kan asibitin gwamnati,
Kamar dai yadda hasashen mafi yawan yan ƙasa yake saboda tunanin ba a wadata asibitocin gwamnati da ingantattun kayan aiki da ƙwararrin ma’aikata ba. Sanin kanki ne kuma duk wanda yake da yadda zai yi ba zai kai kansa inda yake tunanin rayuwarsa za ta iya shiga hatsari saboda rashin kula daga ma’aikatan gun ba.”
Na ɗan muskuta daga kwancen da nake sannan na tari numfashinta da faɗar, “yanzu ke ƙawata a tunaninki laifin na iya ma’aikatan wurin ne? Ina kika bar masu ba su damar yin aikin? Ina nufin waɗanda ke ɗaukar matasan aiki? Ke dai kawai a rufe tutu a ci tuwo. Mu yi fatar Allah ya gyara mana al’ummar ƙasarmu baki ɗaya.”
Ina kashe saƙar zaren labarin na ƙulla sabuwa ta hanyar faɗar, “to bayan layi ya zo kaina na shiga ofishin likitan, a nan ya yi mini wasu ‘yan tambayoyi game da ganina. Na yi masa duk irin bayanan da na yi miki ɗazu. Likitan mai suna Zaidu Hassan kamar yadda na gani rubuce a allon shaida da ke kafe a gaban teburinsa, ya yi wasu ‘yan rubuce-rubuce a kan farar takadar da ke gabansa kana ya fuskance ni sosai ya ce da ni, “kada ki damu matsalarki ba wata doguwa ba ce, zan dai ɗora ki a shawarwari.” A ɗan ruɗe na ce da shi “Dr da ka taimaka ka faɗaɗa mini bayanin abin da ka gano a kan matsalata.”
“Shi kenan, kina ji at scientifically akwai wasu jijiyoyin ƙwaƙwalwa da suke da connection da idanun ɗanAdam, akwai wani yanayi da yake kasancewa idan ɗanAdam ya yawaita kallon hasken screen na tv, laptop, waya ko ma farar takarda da makamantan su wannan hasken yana affecting eyes sosai kuma ya kan janyo (Vision problem) matsalar ragwantar maganan ɗanAdam, gilashin idanunsa zai rage inganci sai ya zamana ganin nasa yana raguwa har za a iya kai matakin da zai iya daina ganin gaba ɗaya idan ba a dakatar da matsalar ba.”
Na tsorata sosai a lokacin fuskata ta bayyanar da wani yanayi irin yanayin fuskar ɓeran da ya ji shi damƙe a hannun mage har ma ta fara kai masa cisga.
A wannan lokacin kamar dai wannan ɓeran na kasance a cikin neman mafita da gaggawa da za ta ceto idanuna daga salwanta.
Na miƙe na fara zarya a ofishin ƙwaƙwalwata cunkushe da tunanin mafita.
Cikin tausayawa ya ce da ni “nemi wuri ki zauna ‘yan mata kwantar da hankali, kowacce matsala akwai hanyoyin magance ta, ballantana ke da kike da sauran dama ta dakatar da faruwar matsalar.”
Ban bijirewa umurninsa ba na zauna domin har ƙafafuwan nawa sun fara barazanar kada ni. Ya tsare ni da idanu yana mai ci gaba da yin bayaninsa “Ina mai shawartarki da ki rage kallon haske, kuma ki daina kallon batsa idan har kina yi domin yana janyo matsololi masu yawa..”
Na zazzaro ido ina kallonsa cike da fargabar yadda aka yi yasan halin da nake ciki. Ya ɗan muskuta kafin ya ci gaba “I’m sorry ba wai ina nufin kina kalla ba ne, ina yi miki hannunka mai sanda ne domin a wannan zamani nasan matasa da yawa da suka faɗa matsala dalilin wannan aikin.”
Ban ce komai ba sai sunkuyar da kaina da na yi tamkar wacce ta yi gulma aka kama ta, ya ci gaba da cewa
“Kallon batsa da kike gani yana haifar da matsololi da yawa a cikin ire-iren matsalolin da yake haifarwa akwai ɗabi’ar masturbation (Istimna’i) wacce take da wuyar dainawa, wadda wannan ɗabi’ar haramun ce ko a addinance, tana janyo lack of satisfaction (Rashin Gamsuwa)wanda ya fi damun ma’aurata, yana haifar da Hyper-multi sensory stimulation (yawan sha’awa da ƙarancinta) akwai abin da ake ce da shi Always want more (wato mutum ya ji kullum yana son daɗa kallarsa), Akwai Decrease in memories Capabilities (Daƙushe wasu daga cikin ayyukan da ƙwaƙwalwa ke yi, akwai Lose of interest in any other activity (Rashin sha’awa ko maida hankali a kan sauran abubuwa na rayuwa, sa’annan akwai Lack of concentration (Rashin maida hankali a kan abu) da ita kanta vision problem da kike fama da ita, though ba iya wadannan kaɗai ba ne matsalolin yana affecting both physical and mental health.”
Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya zare gilashin idanunsa ya ce “Ki yi haƙuri ƙanwata, na san kamar za ki ga na cika ki da surutu ko kuma ki yi zargin ina tuhumarki ne, amma sam ba haka ba ne kawai yana da kyau ne ki san waɗannan abubuwan don tsare lafiyarki ya fi komai muhimmanci a rayuwarki da za ki lura.
Yanzu zan aike ki wurin wani a nan asibitin ki kai masa wannan, ya miƙo mini wata takarda mai ɗan faɗi sannan ya ce
“Za su auna idanun sai a yi miki medicated glass Allah Ya ƙara lafiya.”
Na karɓa ina faɗin amin, sannan na ja ƙafafuwana simi-simi na bar office ɗin ina saƙe-saƙe a raina, ‘ba shakka ƙawa ta kai ni kwazazzaɓon nadama ta baro ni.’ na faɗa a raina, sannan na je na cika umurninsa bayan wani lokaci na je na karɓo medicated glass ɗina sannan na ƙudurce a raina zan daina waɗannan ayyukan da ba su ƙare ni da komai ba sai gadar mini da cutuka, amma ina! Na riga na yi mugun sabo da waɗannan ɗabi’un tamkar yadda maciyi goro ba ya iya dainawa.
Da ƙyar da addu’a na samu na daina karatun novels ɗin, kuma na daina kallace-kallacen sai dai fa an kashe maciji ne ba a sare kai ba, na bar waccan ɓarnar na faɗa wacce ta fi ta, a zahiri iyayena natsattsiyar halitta suke gani amma a baɗini ina da samarin rage zafi duk da ni ba mazinaciya ba ce.”
Tana zuwa nan a zancenta ta sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan ta ce “Wannan shi ne taƙaitaccen labarina, don haka ina mai shawartarki da ki jure ki rungumi ƙaddararki da hannu biyu, ganin abin da ya faru da ke ya zama izina gare ni, in sha Allah daga yanzun nan da muke magana da ke na ajiye duk wani shashanci da nake yi, zan yi istigfari na tuba, tubar da ba komawa saɓon Allah daga baya.”
Da rawar murya ta ke zancen tana zuwa ƙarshe ta fashe da kuka tare da rungume ni tsam a jikinta cikin muryar kuka ta ce. “Ki yafe mini kuskurena na shirin ɗora ki hanyar sabon Allah da n so yi. Ki yafe mini Noory.”
Ni ma na rushe da kuka cike da rauni nake faɗar “tabbas gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, mu yi haƙuri da ƙaddara ƙawata.”
Kuka muke yi sosai daga ni har ita ba mai rarrashin wani, mun ji ma sosai a haka kafin daga bisani ta tsagaita kukanta tana bubbuga bayana, alamar rarrashi ta kasa furta koda harafi ɗaya ne.
Zuwa lokacin jiyojin kaina sun yi rudu-rudu sai harbawa suke, jin kaina yana barazanar rabewa gida biyu ya sanya na fara lallasar zuciyata, a hankali kukan ya tafi na sake ta ina share hawayena da gefen kallabina.
Koda ta ji jikinta ya samu ‘yanci sai ta lalibo wayarta ta danna makunnarta a lokacin da take mayar da ajiyar zuciya.
Idanuna suka sauka a kan manyan lambobin da ke saman fuskar wayar waɗanda ke nuni da lokaci 2:00am na gani. Lalle ashe mun jima muna zantawa ni da ƙawata.
Share & Comment.