Skip to content
Part 9 of 10 in the Series Sharri Kare Ne by Rukayya Ibrahim Lawal

RATA

RUWA YA ƘAREWA ƊAN KADA.

A lokacin ne na juya kallona gare ta, kamar ta san me nake tunani sai ji na yi ta ce “Dare ya yi sosai ko? To ya kamata mu haƙura mu kwanta domin dai gobe sammako zan yi.” Ba ta jira jin me zan ce ba ta miƙe tsaye tana mai janyo zanin shimfiɗar tamu da na fahimci gyara take so ta yi mana.

A lokacin ne na miƙe tsaye cike da kasala sam ba na jin ƙwari ko kaɗan a jikina. Ban furta komai ba na fara takawa langwai-langwai na nufi hanyar fita, muryarta na ji ta baƙunci kunnuwana.

“Ina kuma za ki je a tsakiyar daren nan?” Na dakata gami da juyowa kamar ba zan yi magana ba sai kuma na ce da ita.”Alwala zan yi ina dawowa.”


Ban jira na ji amsar da za ta bayar ba na yi gaba na ci gaba da tafiya har zuwa lokacin da na fice a daƙin zuwa farfajiya gidanmu.

Duk da akwai wutar lantarki a lokacin ba ta zamo hanyar da za ta kawar da duhu ba sakamakon al’adar gidanmu ba a kunna wuta da dare duk kashe makunnai ake, hakan ya saka ni amfani da ƙaramar wayar da ke hannuna wajen samar da hasken da zai mini jagoranci.

Wanda a cikinsa idanuna suka mini tozali da ɗakin Ummana da ke a rufe, ban yi mamaki ba domin duk zafi duk sanyi a dare za ka iske ɗakin ne a rufe.
Zuciyata na ji tana kwaɗaita mini na je na ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, sai dai tunanin bai yi nisa ba ya rasa matsugunni a kwanyata, domin dai na sani yanzu ba lokacin da ya dace ba ne, ballantana kuma da a yanzu na riga na san duk inda take tana fama da azabtuwa gangar jiki da zuciya a dalili abin da na aikata da ba su taɓa zato ba, haka kuma ba ta fatar yin tozali da ni kamar yadda nake muradin yi da ita.

Da wannan tunanin na ƙarasa wurin ma’ajiyar ruwa ta gidan don aiwatar da abin da ya fito da ni. Can bayan wasu daƙiƙu na shiga ɗakin na samu Nuriyyah har ta kammala gyaran ta kwanta a gefe ɗaya, da alama bacci ya yi awon gaba da ita. Don haka sai na shimfiɗa sallayata na tada sallar nafila.

Bayan kammalawa na ɗaga hannuwana sama cike da damuwa na fara kai kukana a wurin mahaliccina faɗar na ke, “Ya Sarkin da ba ya bacci bare gyangyaɗi wanda jinSa ya wadaci sauraren kukan halittunSa na saman tudu da na cikin kwari, wanda cikin isa da buwayarSa yake iya share kukan dukkanin halittunSa in ma rayayyu ko yasassu, ina kawo kukana a gare ka, Ka yaye mini wannan iftila’in da ya faɗa mini, Ka sanyaya zuciyar mahaifana su yarda da wannan a matsayin ƙaddara kuma su taya ni rungumar ta…” Ina zuwa nan kukan da nake ƙoƙarin dannewa ya ci ƙarfina, sai kawai na shafa addu’ar ba don ta ƙare ba na bar saura a gurbin zuciyata wanda mahaliccin wannan zuciyar ya fi ni sanin me ke ɓoye a cikinta.

Na share hawayena tare da miƙewa na je na kwanta a gefe ɗaya, kamar daga sama na jiyo muryarta tana faɗar “Ya zancen Amir kuwa? Barazanarki ta yi tasiri a kansa? Me kike shirya masa a gaba?” Na yi murmushin yaƙe da hausawa kan ce ya fi kuka ciwo yayin da na juyo na fuskance ta da fuskata da ta kasa ɓoye mamaki na ce,
“Da ma wai ba ki yi bacci ba?”
Ta gyaɗa mini kai ba tare da ta yi magana ba, sai ni ce na ci gaba da cewa,

“Damuwar da nake ciki a yanzu ba ta ba ni damar tunawa da shi ba duk da shi ne silar ta. Ban shirya komai a gaba ba, amma nan bada jimawa ba za ki ga tasirin da barazanata za ta yi, ke dai ki zuba ido.”

Ina gama faɗa na yi hanzarin juyawa tare da rufe idanuna gam don hana mata damar ci gaba da zancen da ta soma. Ina jin lokacin da ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi da ban san dalilin hakan ba.

Zuciyata a cike take da fargaba da tunanin makomar rayuwata a kwanakin da nake fuskanta, don sanin da na yi cewa iyayena sun ankara da halin da nake ciki. Na sani kuma hukuncin da zai biyo baya ba zai yi mini daɗi ba. Na ji ma ina saƙa da warwara tare da hasashen abin da zai faru a gobena kafin bacci ɓarawo ya yi nasarar sace ni.

Firgigit na farka sakamakon jin da na yi ana bubbuga kafaɗata da ɗan ƙarfi. Na yamutsa fuska tare da fara mutsittsike ido sannan na juyo don ganin wanda ke son takura duniyar mafarkina, duk da cewa ya ceto ni ne daga barazanar da Amir yake yi mini a cikin mafarkin. Idanuna suka sauka a kan Nuriyyah da fuskarta ke ɗigar da ruwa. Ta ce da ni “Ki tashi an yi asuba fa.”

“Wai har gari ya waye?” Na faɗa cikin hamma ina mamakin yadda daren ya gajerce mini. Kodayake idan na tuna cewa ban kwanta da wuri ba sakamakon jerangiyar tunani da na jima ina yi zan fahimci cewa bai kamata na ji mamakin ba. Ganin ta tada sallah ba tare da ta kula ni ba ya saka ni ma na miƙe ina mai jin yadda Nuriyyah take ƙara birge ni saboda tsananin riƙon ibadarta.

Lokuta da dama na kan yi mamakin yadda tasirin ibadar bai hana mata faɗawa shagaltar rayuwa ba. Sai dai idan na tuna cewa duk ɗanAdam ajizi ne kuma kowa da irin ƙaddararsa sai na sassauta mamakina da tunanin cewa igiyar ƙaddararta ce ta yi mata ɗaurin talala.

Bayan na idar da sallar ne muka miƙa zuwa ɗakin Umma don kwasar gaisuwa. Mun tarar da ita zaune a kan sallaya tana lazimi, hannunta ɗaya tana riƙe da babbar wayarta tana faman rubutu muka gaida ita. Sai dai ga mamakina ba ta ko kalli sashen da nake ba, ta dai amsa gaisuwar a taƙaice. Muka sake haɗa baki da Nuriyyah wurin faɗar “Umma ya jikin?”

“Jiki da sauki Nuriyyah.” Ta amsa tana fuskantar Nuriyyah da ke tsugunne a gefena, ni kuma ban samu daraja koda irin ta guntun kashi ba a wurinta, don shi za a kalle shi koda kuwa irin kallon hadarin kaji ne amma ni ban samu wannan albarkar ba. Tana gama amsa gaisuwar ma ta miƙe zuwa cikin uwar ɗakanta ta bar mu a wurin sororo. Sai a lokacin na tabbatar da cewa mage ma ta fini ƙima a idonta, kuma tabbas ruwa ya ƙarewa ɗan kada bai gama wanka ba.

Jiki ba ƙwari na miƙe muka shiga aika-aikacen gida har zuwa lokacin da hantsi ya dubi ludayi Umma ba ta fito ba, yanayin jikina ba walwala na ci gaba da taya Nuriyyah aikin haɗa abincin karin kumallo da take yi, da ke mun samu duk wani abun buƙata a wurin da nasan ake ajiyewa. Na juyo zan fito daga madafar kenan na ji an warce filas (flask) ɗin ruwan zafin da yake hannuna, cikin rashin sa’a filas ɗin ya suɓuce ya tarwatse a ƙasa tamkar mataccen kasko.

A gigice na ƙwala razananniyar ƙara sakamakon ruwan zafin da ya wanke mini ƙafafuwa gabaɗaya. Na buga tsalle, ƙarin rashin sa’ar da na yi ban dire ba sai a kan fasasun kwalaben filas ɗin. A take wasu suka nutse mini a tafin ƙafa na runtse ido a gigice ina ihun neman agaji.

A daidai lokacin na jiyo muryar Nuriyyah da na baro a ɗaki tana nufo inda nake yayin da take faɗar “Umma me ya same ta?” Sai a lokacin na buɗe idanuna da suke a rufe na dire su fes a kansu.

“Ban sani ba Nuriyyah, ko da ma kin ba ni gadinta ne?” Umma ta faɗa a fusace tana wurga mata harara kafin ta yi fuu ta bar wajen fuskarta a haɗe tamkar ba ta taɓa sanin an halicci wata aba mai sunan dariya ba. A daidai lokacin da za ta shige Abba ya nufo wurin da nake zaune ina hawaye yana faɗar “Subhanallah! Nuriyyah me ya samu ƙawar taki? Tun daga banɗaki nake jiyo ihunta.”

“Da alama ruwan zafi ne ya ƙona ta sai kwalba da ta taka.” Ya iso da hanzari ya kama ƙafar tawa yana yunƙurin cire mini kwalaben da suka nutse a ƙafar tawa ba tare da ya kalle ni ba. Bayan wani dogon lokaci ya kammala cirewar tare da miƙewa yana faɗar
“Allah Ya koro sauƙi, ki raka ta ɗaki Nuriyyah and kuma ku bar aikin haka ummanku za ta ƙarasa.” Daga haka ya wuce har zuwa lokacin bai yarda ya kalle ni ba ko sau ɗaya, da alama shi ma zuciyarsa tana cike da jin haushina, kuma ya tsani ganin fuskata duk da ban ga laifinsa ba don kuwa komai ya samu shamuwa watan bakwai ne ya ja mata.

Ban san lokacin da hawaye ya ɓalle daga ƙoramar idanuna ba, kawai na jiyo saukar ambaliyar ruwan hawayen a kan tudun kumatuna.

Nuriyyah ce ta kama ni muka koma ɗaki tare da shafe mini hawayen da ke malale a farantin fuskata da tafukan hannayenta. Ta zaunar da ni a kan katifa tana faɗar “Ki yi haƙuri Noorhan komai zai wuce kamar ba a yi ba, da sannu umma za ta fahimci cewa ƙaddara tana kan kowa ta sassauta miki hukunci…” Tana zuwa nan na ji ta katse zaren zancenta duk da na san ba a nan ya kamata saƙar zancen ta ƙare ba. Hakan ne ya saka na ɗago kumburarriyar fuskata da har a lokacin ba ta gama sacewa ba na kalli saitin ƙofa inda na ga idanunta na kalla.

Umma ce take shigowa riƙe da kofi guda ɗaya wanda yake cike da ruwan zafi, hannunta ɗaya yana riƙe da biredi rabin leda ta ajiye a gaban Nuriyyah tana faɗar.

“Nuriyyah yarinyar kirki karɓi wannan ki karya, da alama kina son tafiya gida da wuri.” Girgiza kai sama ta yi alamar eh sannan ta ce, “I umma, amma kuma…” Sai kuma ta yi shiru tana sunkuyar da kai tare da sosa shi.
“Amma me Nur?” Kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ƙara yin ƙasa da kai tana faɗar, “Am umma da ma zan ce ne ina na Noorhan?” Ta ƙarashe zancen tana wasa da ‘yan yatsun ƙafarta. Ni kuma sai raka su nake da ido ba damar yin magana. Umman ta ja gajeren tsaki ta juya yayin da take faɗar “Au! Da ma da wata halittar a nan kenan? To ai sai ki ba ta naki ke da kika damu da cinta, amma ni ba zan ciyar da wanda ya kasance ɗan kuka ba…”

Daga haka ta fice. A take hawayen da nake ƙoƙarin tsayarwa ya sake ɓalle mini, cikin wani irin yanayi nake bin bayan ummar tawa ta kallo. Ƙawar tawa ce ta lallashe ni sannan ta miƙo mini kofin tea ɗin tana faɗar “Karɓi wannan ki shanye…” Murya ƙasa-ƙasa na ce “ke fa?”

“Ni ai yanzu gida zani ke kuma idan ba ki sha wannan ba ba na tunanin za ki samu madadinsa.” Da kamar zan musa sai kuma zuciyata ta gasgata zancenta don haka a kunyace na karɓe kofin na ci gaba da tallafawa ‘ya’yan hanjina da suka fara naɗewa. Bayan ta tabbatar na gama karyawa sai ta miƙe ta zura hijabinta tare da saɓar jakarta har ta yi mini sallama da nufin zuwa gida sai kuma na ga ta dawo ɗakin bayan daƙiƙa huɗu.

Na bi ta da kallon mamaki, kafin na samu damar yin magana har ta riga ni da faɗar “Na je ne wurin Abba na roƙi alfarmar idan masu chemist sun buɗe ya raka ki don a duba miki ciwonki. To ya kawo uzurin fita aiki saboda haka ba ni da wani zaɓin da yafi na zauna a nan har zuwa lokacin da za su fito sai na raka ki…”

Na ci gaba da kallonta da idanuna da suka gama tara ruwa suka yi narau-narau na ce “Amma ƙawata ya kamata ki je gida da wuri…” Ta ɗora yatsarta a kan laɓɓanta sannan ta fitar da wannan sautin “Shit!” Sai ta matso ta saka tafukanta a cikin nawa tana faɗar “Kora ta kike yi ne?”

Na girgiza kai da hanzari sai ta yi ɗan murmushi “To idan ban tsaya na taimake ki a yanzu ba wa kike tunanin zai taimaka miki? Sanin kanki ne Umma ba za ta taɓa raka ki neman lafiya ba a yanzu.”

Na yi hanzarin rungume ta ina hawaye tare da faɗar “Na gode kawata, tabbas kin cancanci a kira ki da Aminiya.”

A haka muka wanzu muna jiran sakwanni su ci gaba da bugawa zuwa daƙiƙu yayin da daƙiƙu suka ci gaba da tsere don ba da awanni. Bayan cikar sakwanni dubu bakwai da ɗari biyu da suka ba da awanni biyu cur. Muka fice daga gidan zuwa shagon magani ba tare da neman izinin umma ba, duk da tana zaune a wurin sana’arta sai ta yi halin ko in kula da mu don kuwa ba ta nemi jin inda muka nufa ba, mu ma kuma ba mu sanar mata ba, cikin tallafawar gaɓoɓin Nuriyyah na samu taka ƙafafun da dabara har muka isa shagon maganin. An ba ni duk wani taimako da ya dace don tallafawa raunukan su samu tsanewa da wuri sai muka dawo gidan, inda a nan ne kuma ta yi mini sallama ta tafi gidansu.

Bayan fitar ta yanayin da ta same ni a ciki ya sake yi mini dirar mikiya ganin na zama mara amfani a cikin gidan, ba ni da banbanci da jiƙaƙiyar takarda. Gidan da a da nake samun farinciki yayin da na kasance a cikinsa ya zame mini tamkar gidan kunama saboda matsatsi da rashin damar motsawa ko nan da can.

Duniyar ta zame mini irin ta kwaɗon da ya tsinci kansa a ruwan zafi. ‘da alama wannan nadamar ce za ta ci gaba da bibiyar rayuwata har zuwa lokacin da zan kwanta dama, ga shi ba ni da damar fita ko nan da can saboda tsoron abin da zai je ya dawo. A kan tilas na zaɓi sabuwar rayuwar ƙuncin gidanmu da ta aure ni a kan rayuwar ‘yancin da ke jirana a waje.

Can bayan wasu awanni na jiyo muryar Abba yana waya,
“Yaya ban san me zan ce da su ba, amma ina ga ba wannan ne lokacin da ya dace ba, da sun bari har a zo ɗaura auren idan Allah ya nufa zai yiwu.”

Ban san me yayan nasa ya faɗa masa ba amma ina da tabbacin halin nasa na saurin ɗaukar zafi ya nuna masa tare da zazzaga masa ruwan masifa ba tare da saurarar dalilinsa na ƙin amincewar ba, saboda na jiyo shi yana magana cikin ladabi da rage murya.
“Allah Ya huci zuciyarka yaya yanzu zan shirya tarbar tasu, sai ka zo.” Ina kallonsa ya kashe wayar da yanayin damuwa, ni kuma na ci gaba da gyara shimfiɗata da nake ƙoƙarin yi a tsakar gidan. Don kuwa a yanzu ba ni da wani aikin yi a gidan da ya wuce kwanciya da zama, umma ta tsame ni daga cikin sabgogin gidan gabaɗaya da alama ko aiki ba ta so na taya ta da na yi wani yunƙuri na yin wani abu take dakatar da ni, abinci ma Abba ne yake jin tausayina ya ɗibo mini sannan ya kawo mini har cikin ɗaki, idan kuma ba ya nan na fita da kaina zuwa madafar idan na gani na ɗauka na ci, idan kuma ban gani ba na haƙura.

A ɗan tsakanin jiya da yau na fuskanci hantara da tozarci daga mahaifiyar tawa. Ina nan zaune na ga iyayen nawa sun tunkaro ni lokaci ɗaya kowannen su fuskarsa a tamke tamkar shuwagabannin ‘yan wuta.

Na tsorata da yanayin su duk da ban san me suke son amayarwa ba amma na san akwai sauran rina a kaba.

<< Sharri Kare Ne 8Sharri Kare Ne 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×