Skip to content
Part 1 of 2 in the Series Shaukin So by Wasilu Kano

Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga wanda ya halicce mu domin mu bauta masa, sannan mu yi koyi a bisa tafarki madaidaici da bin sunnar Manzon Allah (S.A.W).

Mu alfahari da kasancewarmu Musulmai, kuma al’ummar Annabin da babu kamarsa a rayuwarmu baki ɗaya. Allah ya sa ya ceto mu a ranar gobe ƙiyama.

Ina alfahari da iyayena bisa kyakkyawar rayuwar da suka bani tun ina ɗan ƙarami har izuwa yanzu dana mallaki hankalin kaina.

*****

A zahirin gaskiya ita ta daban ce 

A wajen nuna kulawa fitacciya ce 

A bangaren ƙauna ita gwana ce

A dukkanin ilimi kuwa an yi dace

A fannin iya girki kuwa ta yi fice

A yanzu sauran mata sun fece !

A soyayya ita ɗin jaruma ce

A rayuwa ita amintacciya ce

A bayyane ita mai godiya ce

A fili ita ɗin kyakkyawa ce !

Ga fa’a da da’a
Ga sana’a da sa’a
Ga tarbiyya da biyayya
Ga soyayya babu ƙiyayya

Bata nuna ƙasƙanci
Bata yin sakarci
Bata izgilanci ko zalunci

Sai nuna karamci
Sannan babu shashanci
Sai dai tsantsar mutunci…

Shaukin So 2 >>

1 thought on “Shaukin So 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×