Hamida ta bi shi suka tsaya gaban motarsa ya ce “Lagos zan tafi, kwanaki uku zan yi. Mahaifina zai zo gobe har sadakinki zai bayar, ba na son mu’amalarki da wannan gayen.”
Wal ta yi mishi da idanuwanta jin abin da ya faɗi kan ya Aliyunta.
Haɗa rai ya yi “Haka na ce ba na so.”
Kuɗi ya miƙo mata a karan farko da ya yi hakan, ta ɗan noƙe ya ce “Meye haka? Ta karɓa tare da godiya, ya faɗa motarsa ta mishi addu’ar sauka lafiya sai da ya ɗaga ta koma ciki
Ba ta ga Walida ba Innawuro ta ce mata ba su daɗe da fita ba ita da wata ƙawar Aina, kuɗaɗen hannunta ta nuna ma Innawuro ta ce “Ni ma kin ga waɗanda ya ajiye mini, Umma ma yanzu ta fita da waɗanda ya ba ta.” Hamida ta ce “Bari in kai wa Gwoggo nawa.” Don tana tuna mitar Gwoggon kullum kan rashin alherin Abdurrashid.
Innawuro ta ce “Ba laifi.” Sai ta fita a ɗakin, Gwoggo kawai ta samu ta fito wanka “Ya tafi? Gwoggon ta soma tambayarta kai ta ɗaga sai ta miƙa mata kuɗin, ƙamshin da ta ji kuɗin suna yi ya sa ta gane daga inda suka fito “Wai su ƙanƙamo yau an ɓanɓaru kenan? Ta janyo jakarta ta saka su.
Hamida ta ɗan jima wurin ta, suna maganar bikin kafin ta fito.
Ranar gidan ya cika tam ba masaka tsinke baki na nesa duk sun iso. Hakanan Hamida ta daure ta kwana gidan zaman ƙunshin Amina ita da Walida. Tun wayewar garin ɗaurin aure su Malam suke ta sa yaran gidan maza share ko’ina na gidan don taran baƙi, suka ba za tabarmi a zaure da ƙofar gida.
Ƙarfe goma na safiya tsadaddun motoci guda uku suka tsaya a ƙofar gidan Marigayi Malam Muntarin Adamawa.
Jama’ar da suka fara taruwa sai kallon motocin suke suna tunanin mijin Aina ne ya iso da jama’arsa, sanin babban mutum ne.
Saɓanin haka wasu manyan mutanen ne suka fito tare suke da Malam Buhari mijin Gwoggo Indo, shi ya isa da sauri inda Malam da yan’uwansa suke ya gaya musu isowar mahaifin mai son Hamida. Su Malam suka isa don taran su, sai dai me? Haɗa idon Malam da Engineer Shehu Bello zura ma juna ido suka yi kafin Engineer ya ce Abdurrashidu! Malam ma ya ce Shehu! Sai suka isa gaban juna suka rungume juna kafin Malam ya cire shi jikinsa “Ashe da ma kafin in mutu zan sake ganin ka Shehu? Hannun Engineer Malam din ya kama suka yi cikin gida har dakinsa, suka bar sauran jama’a cike da mamaki.
Ƙannen Malam iyayen su Hamida su suka yi wa jama’ar da Engineer ya zo da su maraba suka ba su wurin zama.
Suna zama dakin Malam ya shiga ƙwallawa Innawuro kira, ta iso a kiɗime ya nuna mata Engineer “Yau addu’ata ta amsu Innawuro da nake yi, idan Shehu na raye Allah ya haɗa duskokinmu kafin ya amshi raina.” Innawuro ta fara gaida Engineer ba don ta tuna kamannin sa ba sai dai sunansa da ba zai taɓa ɓace mata ba.
Sun gama gaisawa ta fita ta bar su suna labarin bayan rabuwa.
Malam da Engineer abokai ne na ƙut da ƙut a garin su Adamawa, gidajen su maƙotan juna ne tare a ka haife su aka goya su, akwai wata irin shaƙuwa da ƙauna mai ban mamaki a tsakanin su.
Gidan su Engineer ana karatun boko ya yin da Malam Muntari bai yadda da wannan aƙida ba, sun rungumi karatun Muhammadiya.
Bayan ƙare karatun sakandiren Engineer ya samu Scholarship daga gwamnatin tarayya zuwa turai karatu, saboda hazaƙarsa.
Zuwan shi na farko da ya dawo hutu ya samu abokinsa Abdurarrashidu mahaifinsa ya yi masa aure da Innawuro, dawowarsa ta biyu kuma labarai biyu ya samu marasa daɗi a rayuwarsa mutuwar mahaifinsa, da kuma tashin Malam Muntari da iyalansa, wanda ko labarin wanda ya san inda suka nufa bai samu ba. Haka ya koma inda ya fito cikin ɗinbin baƙin ciki.
Shi ma ta fannin Abdurrashidu ya yi iya na shi ƙoƙarin wurin zuwa Adamawa ko Allah zai sa ya dace da zuwan Shehu amma bai dace ba, don mahaifiyar Shehu ta rasu tun yana ƙarami, matar mahaifinsa mutumniyar Adamawa ce kuma ta koma garin su tun ƙare takabarta, Shehu shi da yayarsa su kaɗai ne wurin mahaifinsu yayar tashi tana aure a birnin Kano. Kuma shi ba su taba ziyartar ta da Shehu ba. Hakanan ya dangana don dole sai dai zuciyarsa kullum ba ta huta ba wurin tuna Shehu da addu’ar Allah ya haɗa fuskonkinsu.
“Ya aka yi ka gane gidana bayan tsawon shekarun da na ɗauka ina neman ka?
Engineer ya gyara zama kan tabarma “Danka na zo nema wa aure a gidanka.”
Malam ya dafe baki “Allah mai iko, kar dai yaro Abdurrashid wanda ya zo jiya da ganin farko da na yi masa ya kwanta a zuciyata na wajenka ne? ya ɗaga kai “Shi kadai Allah ya mallaka min na sanya mishi sunanka.” Nan suka yi ta al’ajabi da ƙaddarar su ta zam iri daya, kowannen su ɗa guda Allah ya ba shi, duk da shi Malam Innawuro ta yiyyi ba rai, shi kuma Engineer sau daya Haj Mariya ta yi ba rai. Engineer ya kwance ma Malam tafiyar Abdurrashid, da gudun da yake yi kafin ya dawo Hamida ta suɓuce masa. Malam ya yi murmushi “A yau zan ɗaura auren ɗana da ɗiyar ɗan’uwana, in ya so ka tafi da ita.” Engineer ya ce “Ma sha Allahu, haka da sauri? Ya ce “Don in tabbatar maka da farin cikin da nake ciki yau” Engineer ma murmushin ya yi “Ba ka kai ni farin ciki ba, don rana ba ta taɓa fitowa ta faɗi ba tare da na tuna ka ba, yau rana ce mai muhimmanci a gare ni.”
Malam ya leƙa ya ce a kira mishi yan’uwansa, da suka zo Baban Laila da ke bi masa shi kaɗai ya shaida Engineer. An zauna tare da ba su tarihin abin da ya shige kowa sai tu’ajjibi yake, kafin ya dubi yan’uwan nasa “Nawa ne sadakin Hamida? Ina nema wa ɗana aurenta a ɗaura duka tare da sauran yan’uwanta.” Jin sun yi shiru ya dubi Baban Amina “Kai ne waliyyin Hamida nawa ne sadakinta? Ya ce “Dubu ɗari.” Kowa ya ce Ma sha Allah, Allah ya tabbatar da alheri Engineer ya ce Bari ya fita ya shaida ma jama’ar da ya zo da su abin da kenan. Ko da ya shaida musu dakin Malam ya koma a ka bar su su kaɗai suna cigaba da ganawa, sai da aka kira sallar Azahar suka fito don zuwa masallaci da suka dawo aka fara haramar ɗaurin aure, Brigadier da jama’arsa sun ƙaraso don a Katsina suka kwana, haka fannin angon Amina gabadaya layin ya ɗinke da motoci da jama’a.
Na Aina aka fara ɗaurawa daga ita ce babba sai Amina na Hamida ne ƙarshe sai sannan labari ya kai wa mata a cikin gida an daura har da Hamida kowa sai mamaki yake daga nan labarai mabanbanta suka yi ta zagayawa ana faɗin dalilin faruwar hakan.
Sai dai cikin masu mamakin ban da Innawuro don Malam ya yi mata bayani a hannunta ma ya karɓi kuɗin da ya biya sadakin na shanunsa da ya saida da ƙaramar sallah.
Ba wanda ya kai Gwoggo Indo murna yau yayanta sun yi aure kuma irin mazan da take so su samu suka aura masu hannu da shuni.
Hamida ba ta da labari har sai da suka dawo gidan ta ji har da ita take ta sa kuka ta ƙi yin shiru har sai da aka kira Gwoggo Indo hannunta ta kama zuwa sasan su Hamidar don ba mutane suka haɗu ita da Innawuro suna rarrashin ta, har Innawuro na cewa ko ba ta son sa ne? Malam ya aiko kiran Innawuro ta tashi ta tafi cikin sairi sai kuma ya aiko aje mishi da Hamida.
Tana tsugune gaban shi nasiha yake mata da ba su labarin abin da ya shude har ya ja ya ɗaura aurenta yau daga zuwa neman aure. Ya ba Innawuro sadakinta ya ce ta ba ta sannan aka shigo mishi da Aina da Amina aka kira duka iyayen su kowa ya yi musu nasiha aka ba kowacce sadakinta har aka gama kowa ya kama gabansa hamida ta koma ɗakin Innawuro kuka take.
Bayan magrin ana ta tafiya kai Amina ɗakinta don Aina sai gobe Hamida kuma an ce sai an yi shawara. Innawuro ta tayar da Hamida da ke kwance rub da ciki ta mika mata furar da ta dama mata amsa ta yi don ba ta ga alamar wasa ba, ta sha ta miƙa mata ta ce ta ƙara ta ƙara ta ajiye kofin ƙasa, kuɗin sadakinta ta miƙo mata “Na cire dubu ashirin zan saya miki yar tinkiya a yi miki kiwo. Sauran kuma ki riƙe a hannunki idan akwai abin da za ki saya sai ki saya.” Amsa ta yi ta koma ta kwanta.
Sai da aka kira Innawuro kai amarya Hamida ta sulale zuwa sasan su, ta taki sa’a Innarta ba ta je kai amaryar ba don ƙaramin ɗanta da ya wuni da zazzaɓi. Gaban ta ta tsuguna ta saki kuka yi ta yi kamar ba za ta tanka mata ba karshe dai ta ce “Ki yi shiru ki yi haƙuri, ‘ya mace haka ta gada. Ta jima tana mata nasiha game da zaman aure sai da Hamida ta ji ta yi shiru ta ciro kudin sadakinta ta ajiye ma uwar “Ki yi amfani da su Umma.” Za ta yi magana suka ji motsi saurin juyawa ta yi daga ɓangaren Hamida Babanta ne zama ya yi shi ma nasihar ya yi ta yi mata ji ta yi kamar ta kwana wurin su amma sai Babanta ya ce ta tashi ta je ta kwanta.
Da ta kwantan ta daɗe bacci bai ɗauke ta ba tana jin kamar mafarki wai yau ta zama matar aure.
Walida ta bi jama’ar da suka zo wa Gwoggo Indo ta koma Kano don wani hali da ta shiga jin an ɗaura auren Hamida da Abdurrashid.
Ƙarfe takwas na dare a ɗakin Hotel Abdurrashid ne ke zaune da laptop dinsa akan cinyarsa sai dai sam ya gaza cigaba da aikin da yake yi kafin labarin ɗaura mishi aure a yau ya riske shi.
Dakin ba wadataccen haske TV da ke ta aiki hasken da ke fitowa cikinta shi ya haskaka dakin. Ya sa hannuwansa ya rafsa tagumi kafin ya mike ya cire rigar da ke jikinsa, ya matsa ya ƙara gudun fanka wayarsa da ta dauki ƙara ya sa ya kai idonsa inda take, Momi Binta ce mai bi ma mahaifiyarsa sai dai har ta yi ta yanke bai daga ba don ya san zancen ne dai da Aunty Karima ta kira ta gaya mishi ya dagula lissafinsa ita ma shi za ta jaddada masa. Gabadaya yau wayarsa a rufe ta wuni sai yanzu da ya dawo masaukinsa ya yi wanka shi ne ya kunna ta, kamar kuma ana jiran ya yi hakan Aunty Karima ta kira shi bakinta har kunne tana yi mishi albishir.
Ya za a yi su yi masa haka? Yake ta rayawa a ransa, abokansa ma suka ga wannan yar jaririyar da ya ba shekaru sun kai sha biyu a ce ita ce matarsa ai dariya za su yi masa a bar shi yadda ya tsara, lokacin da zai dawo ta zama cikakkiyar budurwa.
Har wayar ta tsinke sai kuma ga kiran Aunty Safiya haka suka yi ta kira bi da bi kamar jan carbi ba tare da ya amsa ko ɗaya ba sai da Daada ta kira ita kam ya san idan bai ɗaga ba hankalinta zai mugun tashi ne ta yi tunanin wani abu ne ya same shi.
Ya kai hannu ya dauko ta sai ya yi picking ita ma murna take ta yi da wannan rana da Allah ya gwada mata ya zama cikakken mutum. Sauraren ta kawai take har ta ƙare ta ce “Miskili ka fi mahaukaci ban haushi, ranar auren naka ma ba za ka yi magana ba? Ya ce kanshi ke ciwo. Sai kuma hankalinta ya tashi ta shiga jimami tare da jaddada mishi ya sha magani , jin yadda ta tashi hankalinta ya sa ya kwantar mata da hankali ya lallaɓa ta ta ƙyale shi ya kwanta tare da rasa tunanin da zai yi.