Skip to content
Part 32 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Ga ƙamshi mai tsayawa a rai da ba ta tarar yaushe ya kamata ta sanya, koyaushe cikin sa take. Kenan duk namijin da ya shaƙa zai zame masa fitina duk da dai a ƙarshen zamanin nan da muke mai hijab ma yan iskan maza ba su bar ta ba don ko ƙawarta da lacturer su ya yi ma maganar banza kullum cikin hijab take.

“Zan shiga Islamiyya.” Ta faɗi kamar mai magana da wani “Zan ƙarar da rayuwata wurin bauta ma Ubangijina.”

Sai kuma ta dafe kai don sabon tunanin da ya shige ta ba abin da ke samun ta a rayuwarta ta tsaya ta fuskanci Ubangiji ta yi addu’a, dubi duk wannan bala’i da ya same ta daidai da rana ɗaya ba ta taɓa dagewa da sallar dare ba kan Allah ya kawo mata ɗauki ba.

Shigowar mahaifiyarta daga Islamiyya ya katse mata tunanin, lafiya ta shiga tambayar ta ganin fuskarta yau cikin damuwar da kwana biyu suka daina ganin ta cikin ta.

Ta ce “Ba komai.” Zama ta yi ta yi ta gaya kalaman kwantar da hankali da imani da ƙaddara tare da jaddada mata ta yi ta addu’a ba abin da ya gagari Allah.

Buɗe bakin Hamida ta ce “Zan shiga Islamiyyarku Umma.”

Kai ta girgiza “Ba za a yi haka ba ki riƙa fita ba iznin mijinki,ki dai bari har Allah ya kawo daidatawar ki da mijinki kika koma ɗakinki sai ki shiga.”

Ta gyaɗa kai”In sha Allah zan shiga Umma.” Sun daɗe har sai da Innawuro ta aiko ta zo ta ci kwaɗon zogale da ta ce tana so ta miƙe sai ta bar sashen.

Watanta guda sai ga Gwoggo Indo ta zo duba ta bayan ta tafi sai ga kiran Momi Binta sai faɗa take mata tana tambayar Hamida me ya haɗa su da Abdurrashid da har ta taho ba su sanar mata ba? Ta kasa magana.

Kwana biyu tsakani sai ga Momin da Aunty Safiya sun ce Daada ta zo su taho tare to kwana biyu ciwon ƙafa ya sanya ta gaba ga hawan jininta ya tashi.

Sun zauna da iyayen Hamida aka gaya musu matsalar da aka samu suma jimamin suka shiga tare da bayar da haƙuri kan matakin da Abdurrashid ya ɗauka tare da neman a ba su Hamida su tafi tare, su ma haƙurin suka ba su tare da yi musu godiya amma sun ce su bari har Abdurrashid ɗin ya zo da kanshi, wanda suka faɗi baya ma ƙasar, sai yamma suka bar ƙasar.

Su Hanan da Mimi sun zo mata suka kwana guda suka koma.

Wata da suka yi karatu tare mutumniyar Kaduna da ke saye da sayarwa na yadikan hijabai da ɗinkakku da safuna masu kyau ta yi wa magana tana son ɗinkakkun hijabai ne nuna mata ta yi ta zaɓi kala-kala da safuna ta zaɓi irin ɗinkin da za a yi mata ta bayar aka sanya a mota Hamida ta aiki ƙanenta ya amso mata, ta yi alƙawarin canza shigar ta za ta koma rufe jikinta kamar yadda musulunci ya yi umarni duk da ba inda take zuwa sai awon ciki da ta fara zuwa Asibitin da suka je aka tabbatar mata tana da ciki.

Watarana daga wurin awon ta wuce gidan yar’uwarta Amina, wadda yanzu yaranta hudu.
Mimmiƙe ƙafafu ta yi a tsakar ɗakin Aminar suna hira tana kallon Aminar tana haɗa garuka da su gumba su tsimi za ta sha. Ta jinjina kai “Kuna ƙoƙarin shan magani Amina, ni kam sai ta ƙure nake rufe ido ba kuma kowanne ba.”

Aminar ta kai bakinta sai da ta sha ta sauke kofin, “Shan na dole ne Hamida, ni ma kin san ba son magani nake ba.”

Hamida ta ce, “Kamar ya dole? Ta ƙara kai kofin sai da ta sauke ta ce “To in ba ka gyaran ba akwai matsala, musamman mu masu kishiya.”

Hamida ta yi murmushi “To ai sai in ji ana ta yi wa masu saidawar tsira a ce ki gama kashe kuɗaɗenki duk daɗin da namiji zai ji bai hana ya nuna miki shi ɗin namiji ne. Wai duk masu sayarwar ma yawancin su ba su da aure in yana da amfani da ba a sake su ba.”

Amina ta gyara zama “I ba abin da ba a faɗi amma ni wurina yana da amfani, kin ga kafin ayi min amarya basu dame ni ba Baban Amar yana yin aure ya daina nema na a shimfiɗa sai mu yi wata ni dai sai dai in ji mata na hirar abin nan don ni har manta ma ina da miji nake, sai ya zam ririta ni da yake da abubuwan buƙata da yake mana ni da yayana ya rage hakanan dai nake zaune duk wani farin ciki na shi ya mayar da shi wurin amarya, na tashi haiƙan ina amfani da magungunan nan ashe kuma sanyi ya yi min mugun kamu hakan ya hana ni gane amfanin abin da nake shan, na gaji na watsar na ci-gaba da zaman haƙuri.

Ana nan sai Allah ya haɗa ni da wata mai sayar da magungunan mata da ƙyar ta sani na ɗauki wani ta ce in gwada, na dai karɓa na biya ta na zo na ajiye ya yi wata uku da safe ban koma ta kanshi ba sai watarana na ɗauko shi na yi amfani da shi a ranar na ga abin mamaki don gaba ɗaya susucewa ya yi, in taƙaice miki magani ya yi daga nan bunu-bunu mutum na manne da ni, abubuwan cikin gida da duk ya maƙale hannunsa duk ya saki ya dawo yana mini hira da da ta soma gagara tsakaninmu.

Zai yi ma yarana hidimar duk da ta kama, tun daga nan na kama matar nan na riƙe da ta samu masu kyau za ta kawo min. Amir (Yaronta na farko) da ya ga matar ta shigo sai ya yi ta jin haushi wai in ta kwashe kuɗina ina ba ta, a raina sai in ce yaro har kai wannan matar tana ma amfani.

Wato ni Hamida abin da na fahimta game da waɗannan magungunan, ba wai za ka mallaki namiji ba ne ko ya yi ta kwasar abin duniya yana ba ka, a’a za ka tsira dai da ƙimarka, Hamida ta gyaɗa kai “Na gamsu da bayanan ki, ni ma ban da ban iya sha da na saya.”

Ta ce “Ai akwai masu daɗi irin su zuma da gumba, za ki iya ci.”

Ta ce “Sai na tashi amfani da su zan sa ki saya min, ke ma zan ba ki nawa da nake amfani da su.”

Wayar Hamida da aka shiga kira ta katse su Hamida ta ɗaga kiran tana murmushi ganin sunan ya Aliyu ne kan screen ɗin ta ce “Ya Aliyu, yayana ni kaɗai.”

Murmushi ya yi mai sauti har ta ji “Yanzu dai kina ina? Innawuro ta kira ni hankali tashe wai har yanzu ba ki dawo ba.”

Murmushi ta yi “Ita Innawuron? Sai dai in ta soma ruɗewa amma na gaya mata zan shiga gidan Amina, in gaishe ta ta samu miscarrige ka sani.”

Kai ya gyaɗa kamar tana kallon sa “Zan zo in kai ki gida.”

Ta ce “To ya Aliyu.”

Ta ajiye wayar suka ci gaba da hirar su har ya kira ta ya shaida mata isowar sa, hijab ɗinta ta janyo dogo har ƙasa ta sanya Safa sai ta miƙe Amina ta biyo ta don mata rakiya sai da suka zo zaure Hamida ta tsaya ta buɗe jakarta kuɗi ta ciro masu kauri ta kama hannun Amina ta damƙa mata Aminar tana meye haka ta ce “A sayi kayan gyara a ƙara gyarawa Baban su Amir.”

Suka yi dariya ta ce “Ya za a yi in amshi kuɗinki ke da kike zaune? Murmushi ta yi don ta san ba ta da matsalar kuɗi duk wata sai Abdurrashid ya turo mata kuɗaɗen da ya saba ba ta.

Ta ce “Kar ki damu ina da kuɗi.” Ta kaɗa kai “To na gode sosai.”

Suka isa inda ya ajiye motar Amina ta gaishe shi sai suka wuce.

Yammacin wata Laraba ta fito wanka ko da zaman ta gaban mirror sai ta samu kanta da son yin kwalliya wacce tun da ta zo ba ta yin ta, ta murza hoda ta gyara girarta ta goga wet lips sai ta sanya turare.

Jin ƙamshin ya tuna mata da rayuwarta da Abdurrashid hannayenta ta haɗe ta shiga tumani, ta jima kafin ta miƙe ta nemi kayan da za ta sanya cikin ya fara fitowa duk da ya sa ta yi ƙiba jikinta ya kuma yin lukwi-lukwi ta dai yi kyau irin na mata masu ciki.

Wata doguwar riga ta zura ta wani yadi mai taushi, sai ta sanya hijab takalmi flat da jakarsa.
Ta fito Inna Innawuro na zaune a falo tana kallon shirin Kwana casain da ake gabatarwa ganin ta da hijab ya sa ta ce “Ina kuma za ki? Ta ɗan zauna hannun kujera “Ka ji Innawuro sai ka ce wadda ke fita kullum, ya Aliyu zan dubo.”

Baki ta riƙe “Yau kaɗai da bai shigo ba za ki duba shi son yawo dai.”

Ta langaɓe kai “Kai Innawuro ina nake zuwa? Ya Aliyu fa ya ce yau ko fita bai ba ciwon kai ya matsa mishi.”

Tausayi ta ji ta ba ta ta ce “Shi kenan, ke da wa za ki? Ta ce “Keke napep yara za su samo min.”.
Ta fita falon Innawuro ta bi ta da kallo.

Sasan su Aina ta fara shiga ta yi wa matar Baban Aina barka don Ainar ta haihu ta samu ya mace, da ta fito na su Laila ta shiga akwai yaron da ke kwance yana fama da gaida, nasu sasan ta shiga ƙarshe ta samu Innarta na girkin abincin dare, nan ta zauna suna hira har aka aka samo mata mai napep ta fita suka tafi.

*****

A falo ta samu Aliyun yana zaune ta zauna tana duban shi yana mata murmushi “Sannu ya Aliyu.”
Ta faɗi tana langaɓe kai, Asabe da ke kallon su tana goge goge daga nesa takaici ya rufe ta.

Hamida ta zame hijab ɗin jikinta don wani zafi da take ji “Asabe ba ki ga zuwan Hamida ba? Aliyu da ya san da wanzuwar ta a wurin ya faɗi

“Ki ba ta ruwa.” Ya kuma faɗi yana waiwayawa inda take ta tako zuwa tsakiyar falon ko da Hamida take da aure sai ta yi ta ganin za ta iya zama kishiyarta, yanzu zaman da suka yi wuri ɗaya wata dacewa take ganin sun yi, da ƙyar ta iya cewa Hamida Sannu da zuwa. Ita kam ta gaishe ta cikin fara’a da tambayar ta yara ta ce suna Islamiyya.

Sun ci gaba da hirar su har aka kusa kiran magrib ta ce za ta koma gida, ya ce a’a ta bari ya yi sallah sai su tafi tare.

Ko da Hamida ta yi alwala ba ta ga fuskar shigar ma Asabe ɗaki ba, sai ta yi sallar a falo nan saman carpet tare da yarinyar Aliyun mai sunan Innawuro, wadda take goyo kuma sunan Hamida ya sanya mata, tana idarwa Asabe ta zo kusa da ita “Ba wai mutum ya baro ɗakinsa ba yana bin gidajen mazan mutane.”

Da mamaki Hamida ta ɗago “Aunty Asabe ban gane me kike cewa ba? Gaba ɗaya ta taso “Ina nufin mutum ya fita hanyar mijina.”

Ta buɗe baki za ta yi magana Aliyu ya shigo ganin Asabe tsaye kan Hamida ya ce “Lafiya.”

Asabe ba ta tanka ba sai wata cika take Hamida ta ƙirƙiri murmushi “Ba komai ya Aliyu.”

Ta miƙe, ya ce “Mu je ko.”

Yarinyar ta ce “Zan bi ki gidan Innawuro Aunty Hamida.” Ta ce “Gobe akwai Sch maama.” Ta ciro kuɗi “Ku yi break ke da su Baffa, gobe a Sch.”

Ta bi bayan Aliyu.

Sun bar gidan har ya hau titi yake ce mata “Aure zan ƙara Hamida.” Gabanta ta ji ya faɗi don tuna fargabar da ke cikin cewa za a wa mutum kishiya “Kai Ya Aliyu me Aunty Asabe ta yi za a yi mata kishiya? Ta gefen ido ya yi mata wani irin kallo “Sai ta yi wani abu zan ƙara aure? Ina da buƙatar hakan ne, a cikin garin Katsina yarinyar take.

Ina so a yi da zarar ta ƙare karatu.”

Hamida ta jinjina kai “Karatu take kenan? Ya ce “Ƙwarai ɗaliba a jami’ar Umaru Yar’adua University karatun digiri take tana shekarar ƙarshe.

Ajiyar zuciya Hamida ta fidda tuna Anisa da zaman da take da ba ta san makomarta ba. Ta ce “Allah ya tabbatar da alheri.” Murmushin da ba koyaushe yake yi ba ya yi ya ce “Amin.”

Suna isa ɗaki ta shige ta bar su suna maganar dawowar su Malam gobe, duk kuma yadda Innawuro ta so ta ci abinci ƙin ci ta yi sai hura ta sha ta kwanta.

Ta daɗe tana zubar da hawaye, abin har ya kai a fara tozarta ta? Sai da ta ji kanta ya fara ciwo ta ba kanta baki ta yi barci.

Da safe da ciwon kan ta tashi ta ce ma Innawuro za ta asibiti don ba ranar awonta ba ce. Sai da ta karya ta shirya ta tafi, napep ta hau tana kuma wucewa motar Abdurrashid na tsayawa ƙofar gidan.

<< Shirin Allah 31Shirin Allah 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×