Da daddare Gwoggo Indo na zaune tana cin abinci, Hamida na gefenta idonta na kan TV. Aina da ke ɗaki ta fito “Ni fa Gwoggo halin mutumin nan ya fara isa ta, wai idan yana gida ba hali in kira shi? Ni dai ban da kin matsa da tuni na kore shi.” ta zauna tana tura baki. Gwoggo ta kwantar da murya,
“Kar ki kore shi Aina ki yi hakuri, ina gaya miki yadda matar tasa ta nema ta samu muma neman za mu yi, wuyarta dai ki shiga gidan, duk masu zuwa shi kaɗai ya zo da maganar aure, Alh Uban da kika dage sai shi ina yake ya sulale, ya za a yi shi a kore shi? Ga Malam ya taso ni gaba da ki fitar da miji dan a satin nan aka kawo kudin gaisuwar Amina.”
Ido Aina ta buɗe “Amina dai za a yi wa aure? (Aminar shekara daya ta bai wa Hamida, Babanta shi ke bi wa baban Laila)
“Kwarai don haka ya ce ba za a aurar da Amina kina zaune ba, har Hamida ya ce ta samu miji har ita zai haɗa.” Tagumi Aina ta rafka kafin wayarta ta shiga ƙara, ta duba Gwoggo Indo ta ce “Waye? “Me yan canji ne.” ta bata amsa “To yi maza ki amsa ki ji da wacce ya zo.” ta yi picking yar magana kaɗan suka yi ta sauke wayar “Yana waje wai Gwoggo.” “Yawwa to ki fita ki same shi ki ma shaida mishi ya fito ni ma mijin ta cen nan ya ishe ni, ki yi duk yadda za ki ƙara sace zuciyarsa don ya ƙara mutuwa kan son ki.” ba ta yi magana ba Hamida ta duba ta ce ta dauko mata mayafi a daki da ta kawo a kafaɗa ta ajiye shi sai kallon ta Hamida ke yi shigarta ce ta koyaushe jikinta doguwar riga ce da dinkin ya matse ta dam sai ta fice.
Kallo Hamida ta cigaba da yi har goma ta wuce wani film MBC bolly wood suka sanya mai suna krish 3 ya matuƙar tafiya da ita, har lokacin Aina ba ta shigo ba. Gwoggo Indo ba ta cika doguwar hira ba amma yau ta kasa kwanciya tana jiran Aina ta ji yadda suka yi da mai yan canji, sai gyangyadi take amma ta kasa haƙura ta je ta kwanta. Malam Buhari tunda ya yi mata magana sau ɗaya ta ce Aina take jira ya koma daki ya yi kwanciyarsa. Goma da rabi Aina ta shigo motsinta ya sa Gwoggo Indo yin zumbur tana rarumo ɗankwalinta da ya zame daga kanta “Yaya Aina, an dace zai turo? Ta jera mata tanbayoyin, ba ta yi magana ba sai da ta zauna kusa da ita “Da na yi masa maganar aure cewa ya yi a halin yanzu dai ba shi da buƙatar ƙarin aure, sai dai ko nan gaba in s…
“Shi ne kuma ya gaya miki wannan maganar banzar kika tsaya sauraronsa tsawon wannan daren? ba ki yi masa wankin babban bargo kika kamo kanki ba? Aikin banza aikin wofi yau ga tsi.. Maganarta ta ta katse ya yin da suka yi ido biyu da abin da Ainar ke miko mata, kudi ne ba ma kuma Naira ba dalar America ce.
Ba ta ƙi ba miƙa nata hannun ta yi ta karɓa tana jujjuya su.
“Duk shi ya ba ki wadannan? Aina ta daga kai “Amma kuma don tsiya ya fito a yi aure sai ya ce ba haka ba?”
“Wai kuma gobe zai zo in raka shi wani taro, da ni kadai zai iya shiga wurin.”
Wani tsaki Gwoggo ta ja “Kyale dan iska ya je da matan nasa ba inda za ki. Su kuma wadannan kudi mun yagi rabon mu, ko a waya ya kira ki ki ce idan ba maganar aure zai yi ba ya manta ma ya taɓa sanin ki. Aure nake so ki yi Aina, Daura magana ta fara yawa har yau ba ki yi aure ba, duk yaran gidanmu ba wadda ta taɓa kai kamar shekarunki.”
Daidai nan suka yi ido biyu da Hamida Gwoggo ta riƙe baki “Ba ki kwanta ba Hamida? Ta ɗaga mata kai sai ta mike “Wani film nake kallo Gwoggo ya ma kare yanzu.”
“To kashe kayan kallon.” ta kashe ta wuce ciki ta bar Gwoggo da Aina suna neman mafita, don ita ma Ainar hankalinta ya koma kan ta yi aure har an fara maganar auren ƙannen bayanta, yaran gidansu ba su wuce sha bakwai an kauda su, ko Laila da Gwoggo Indo ta riƙe Sakandire kawai ta ƙare aka yi mata aure ita ce dai da alhazan birni suka yi mata caa! Tun zamowarta budurwa shi kenan ita da Gwoggo sai suka yi fatali da zancen aure, maimakon auren magana ta yi wa Ahmad mijin Laila ya samo wa Aina makaranta. NCE aka samu tun kuma da ta fara karatun idanuwanta suka ƙara budewa, duk kuma da matsin lambar da suke fuskanta daga Malam Aina ta fito da miji, Gwoggo Indo na cewa karatu take don Allah ya yi haƙuri ta ƙarasa daga ta fara. Duk da ba son karatun bokon yake ba ta sani hakanan ya hakura.
Maza suna kashe mata kudi suna shan soyayyarsu ta shan minti, Gwoggo na sane amma tsabar son abin duniya ya sa ba ta tsawata mata. Da ta kammala karatun kuma duk wanda ta nemi ya fito ba ya fitowa sun fi son su yi ta soyayyar su a haka, Alh Maaruf shi ya zo da batun aure sai aka yi rashin sa’a mugun shakkar matarsa yake yi shi kuma.
Ranar dai haka suka kwana Aina da Gwoggo ba daɗi.
Washegari ta kama Alhamis ba Islamiya Aina ta ce wa Hamida da La’asar za su fita a gyara musu kai ta ce “To.” Don haka ƙarfe hudu da rabi suka fito cikin shiri Aina riga da skirt ta sanya na Less sun kamata kamar ma da ƙyar take numfashi ta jefa gyalenta a kafaɗa. Hamida ma riga da skirt din ne sun yi cif a jikinta sai bakin gyale da bakin takalmi bayan ta murza farar hoda Aina ta sanya ta ta shafa jambaki ai kuwa ba karamin kyau ta yi ba ta daura mata dankwali tulin gashin ta ma da ya fito ta gefe da gefe bayan ta kama mata shi da ribbom ba ƙaramin kyau ya ƙara mata ba shi ma
Suka fito suna ƙamshi mai sanyi.
Gwoggo Indo ta fita unguwa.
Sun yi nisa da tafiya har sun kusa Gate don fita inda za a su samu adaidaita sahu wata mota ta tsaya ba su shaida wanda ke ciki ba har saida suka dubi mazaunin direba Abdurrashid ne baƙar shirt ce jikinsa da ta yi matukar amsarsa “Ina za ku? Ya fadi cikin rashin sakin fuska Aina ta fara gaishe shi sai ta amsa mishi tambayarsa “Za mu je wurin gyaran gashi ne.” “Ku shiga mu je ya furta ba tare da ya dube su ba Aina ta bude kofar baya ta shiga Hamida ta mara mata baya sai dai kallon da Ainar ta jefa mata ya katse hanzarinta ya sa ta tsayawa, jin su shiru ya sa shi waiwayowa don ganin halin da suke ciki “Shiga mana.” Aina ta ce ma Hamida sai dai ba ta motsa ba ta sake cewa “Me kike yi haka ne Hamida?
Ya ce “No bar ta ta zauna nan din.” har ajiyar zuciya Hamida ta fidda ta shiga ta zauna gefen Aina.
Ya zuge gilasan motar wadanda suke masu duhu ne sai ya tashi motar.
Aina na ta jira ya tambaye su inda za su gyaran kan sai ta ji shiru, wani ƙayataccen wuri ya kai su can kusa da Zoo road ya ce su fito.
Ya mika wa Hamida Atm ya fada mata pin din ya ce su biya idan an gama masu.
Suka shiga ciki ya kwantar da kujerar yana sauraron kiɗan da ya sa a motar.
Aina ganin banza ce ta faɗi ya sa ta ce bari su bi ta da yakushi, bayan gyaran gashin ta ce a wanke musu ƙafa, ta kuma jidi maya mayai na kai da na jiki duk a ka cire a kudaden Abdurrashid.
An gama musu yamma ta yi sosai Aina ta ce su tafi su samu shatar Adaidaita sahu sai dai suna fitowa suka yi tozali da motar Abdurrashid wurinta suka nufa Aina ta ƙwanƙwasa glass ɗin ya sauke idonsa a kansu bai yi magana ba Aina ta bude suka shiga ya ja, a hanya ya tsaya ya yi sallar magarib don haka duhu ya shigo san da suka shiga gida.
Gwoggo Indo sai murna baki ya ƙi rufuwa jin Aina ta ce tare suka fita da Abdurrashid, ita ta bude ledar da Aina ta zubo mayukan tana cewa “Iya wannan ledar kawai ba ta yi kadan ba? Aina ta yi murmushi “Ita din ma ba shi ya bamu ba.”
Ta kwashe yadda aka yi ta labarta mata
Ta ɗan yi shiru kafin ta ce “Zuwa yanzu na yi tunanin ya soma jiƙa mu da Naira Aina, amma ko kwabo, gidansu kuma gida ne na kyauta indai ka shiga ba ka fitowa hannu biyu.
Aina dai ta dauki ledar ta wuce ciki, da ma Hamida tun shigowar su ba ta zauna ba cikin ta wuce don yin sallar magarib, ta bar Gwoggo Indo da tunanin Allah ya sa Abdurrashid ba hannun jarirai yake da shi ba.
Karshe dai ta watsar ta ce koma dai meye gidan arziki ne, kuma abin alfahari ne a ce yarta ta yi aure a gidan.
Ranar Monday Abdurrashid ya turo a ka kai Hamida makaranta a ka yi mata komai har unifoam aka ba ta da littattafai.
Dan aiken ya shaida wa Gwoggo Indo duk safiya zai riƙa zuwa don kai ta makaranta. Ranar kowa ya ga cikakkar fara’ar Hamida.
Tun daga ranar ta fara zuwa makaranta mai suna *AHLAN Internatonal School* babbar makaranta ce ta yayan masu hannu da shuni da masu riƙe da madafun iko, idan ta dawo ta wuce Islamiya.
Abdurrashid ya kan zo daga lokaci zuwa lokaci.
Tana matukar ganin girmansa saboda makaranta da ya sanya ta, ba ta damu da mitar da Gwoggo ke faman yi na ba shi da alheri kullum sai dai ya zo ya kakkaɓe rigarsa ya tafi.
Tana mayar da hankali sosai musamman da ya zam ba a hausa a makarantar sai dai turanci, ita kuma ba ta iya ba, ranar Alhamis da juma’a tana tsayawa lesson da Abdurrashid ya sanya ake mata har Asabar da lahadi take zuwa tana yi mata da yake tana so ba ta dau lokaci ba ta fara ganewa, ba ta shiga sabgar mutane tana matukar kama kanta duk da su mutanen suna son yin mu’amala da ita, saboda burge mutane da take yi.
Yarinya guda ta fi shige mata kuma dole sai da Hamida ta saba da ita duk inda ta sanya kafa nan yarinyar mai suna Walida za ta mayar da ta ta.
Walida irin yaran nan ne masu ɗan banzan rawar kai da son a ce su ɗin wasu ne, irin labaran da take ba Hamida na arziƙin iyayenta Hamida jinta kawai take don ita ba ta ga abin da ya dame ta da arzikin su ko rashin sa ba, har sai wata rana da aka kwana biyu ba ta zo ba sai Hamida duk ta ji ba ta ji dadi ba an bayar da sanarwar ba ta da lafiya, lambar wayar Walidar da ta ba Hamida ta ba Malam Adamu direban da ke kai ta makaranta ta ce don Allah za su biya ta gaishe da ƙawarta ba ta da lafiya. Mamanta ce ta dauki wayar ita kuma ta yi ta musu kwatance har suka gano gidan, wani tsukakke ne a ɗan dinshe, mai dakuna uku ta gaishe ta sannan suka tafi gida.
Bayan ta dawo makaranta ta ce ma Hamida gidan da suka zo gidan kakanninta ne nan kakarta ke ruƙonta wadda Hamida ta gani, ita mamanta na Hotoro.
Sai da tafiya ta yi nisa tsakaninsu ta gane nan ɗin dai shi ne gidansu, matar da ta gani ita ce mahaifiyarta, yayarta ce ke aure Hotoro mijin yayar shi ya sanya su makaranta mai tsada ita da kannenta.