Skip to content
Part 9 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Hamida ta cigaba da karatunta suna tare da Walida wadda yanzu ta zama ‘yar gida a gidan Gwoggo Indo.

Kafin sati ya ƙare za ta biyo Hamida sau biyu wani satin ma sau uku.

Da suka samu hutun second term Gwoggo ta je da ita Daura suka yi kwana biyu suka dawo Aina dai har yanzu tana nan, Alh Ma’aruf ya ɗauke ƙafarsa ba kuma wayarsa in ta kira shi ma ba zai dauka ba, ita da Gwoggo suna cikin tashin hankali.

Wani yammaci Hamida ta shigo daga makarantar Islamiya Gwoggo ta samu zaune a falo kusa da ita ta zauna bayan ta amsa sallamarta “Yawwa Gwoggo, an ce a kawo kuɗin sauka dubu 20 sai kaji biyu sai kudin unifoam dubu b… Da sauri Gwoggo ta katse ta “Duk ni kaɗai wannan dogon lissafin? To tun wuri gara ma ki sani wancan mai son naki da ba ya ɓanɓaruwa shi zai yi komai, ki ma gaya masa, in kuma ba haka ba kina kallo yan ajin naku za su yi saukar su bar ki.” Kuka Hamida ta sanya, Gwoggo ta ce “Allah na gama magana kowane irin kuka za ki yi.”

A haka Aina ta shigo ta same su a komai za ka same ta bayan Hamida amma yau ta ce Gwoggo na da gaskiya Hamida ta tambaye shi kawai.
Kuka Hamida ta daɗa rushewa da shi.

Ranar ko abincin dare ba ta ci ba Aina da ta ga ta ƙi barci sai kuka take ta janyo ta tana rarrashi “Shi ya dace ya yi miki Hamida, Gwoggo gaskiya take fada miki.

Gara tun yanzu ya saba da hidimarki ba komai ya rungume hannu, share hawayenki kin ji yar ƙanwata?

Ta gyaɗa kai sai ta share hawayen ta ce ta je ta wanko fuskarta sai da ta wanke ta dawo ta kwanta lamo tana tuna tsawon watanni biyu kenan tana fama da karatu don son da take ta yi na ɗaya a jarabawar saukar su.

Da safe ba walwala ta tashi, haka ta shirya ta tafi makaranta.

Ko a makarantar ma hakanan take sukuku sai tambayarta abin da ya same ta Walida ke yi sai ta ce ba komai.

Da suka tashi maimakon Malam Adamu da ya saba zuwa daukar ta yau saɓaninsa Abdurrashid da kansa ta gani tsaye jikin motar ko da ta doshi motar tana takawa a hankali kamar wadda ƙwai ya fashe mawa.

Tana isa inda yake ta ce “Ina wuni? Sai ka saurara da kyau za ka ji me ta ce, shi ma ban da ita yake kallo ganin ganin sauyin yanayinta da ba zai gane ta yi magana ba.

Ya zagaya ya shiga ita ma ta buɗe ta shiga bai ko dubi inda take ba har sai da suka hau titi.

‘Me ya same ki? Ta girgiza kai “Ba komai.” “Ba wasa nake miki ba fa.” ya faɗi a ɗan hasale. Ta buɗe baki ta yi magana sai kuka kallon ta yake ta yi sai da ya ga ba ta da niyyar shiru ya ce “Ya isa ki yi shiru, an tashi yazan amma gobe zan shigo sch din in ji abin da aka yi miki.” da sauri ta ce “Ni ba abin da aka yi mini a makaranta.” “To me ya faru? Shirun ta kuma yi tana cigaba da hawaye, ya tsaida motar gefen hanya ya kuma tsare ta sai ta fadi mishi abin da aka yi mata.

Kan ba yadda za ta yi ta ta ce mishi sauka za su yi a Islamiya, kuma Gwoggo ta ce ba za ta biya kuɗin ba sun yi yawa.

Ya tambaye ta nawa ne kudin ta fada mishi, motar kawai ya tada suka bar wurin bai kuma sake ce mata komai ba har suka isa ya sauke ta.

Da yamma lis kuma sai ga shi gidan Gwoggo, ta waya kamar yadda ya saba ya shaida mata isowarsa. Ta ce ya shigo.

Gwoggon kawai ya samu a falo sai da suka gaisa ta shiga ƙwala kiran sunan Hamida da yake yau ɗin Alhamis ce ba Islamiya kafin fitowar Hamida ta ce “Fushin take har yanzu kenan? Sai ta yi shiru don son jin me Abdurrashid zai ce, jin bai ce komai ba sai ta cigaba “Don na ce ba zan biya kudin sauka ba ta faɗa maka shi ne take fushi.”
Shi dai ko dagowa bai ba sai wayarsa yake faman dannawa.

Hamida ta fito cikin nutsuwa baƙar jallabiya ce jikinta sai hijab ƙarami shi ma baƙi ta zauna Gwoggo ta mike ta bar musu falon, gaishe shi ta yi suka zauna shiru kafin ya mike ya bar gidan.
Gwoggo ta dawo falon tana tambayar Hamida ya yi mata zancen kudin saukar? Hamida ta girgiza kai ta zabga ƙwafa “Duk da gaya mishi da na yi da kaina?

Nan ta yi ta faɗa har Aina ta dawo
ta ji abin da kenan, hakuri ta yi ta ba Gwoggo.

Ranar Asabar da Hamida ta je Islamiya malaminsu mai kula da hidimar sauka ya kira ta ya bata unifoam da sauran abubuwan da aka bai wa masu saukan. Ta koma gida tana ta murna ta gaya wa Gwoggo da Aina baki Gwoggo ta taɓe ta ce hala shi ya biya.

Suna ta shirin sauka har lokacin ya gabato Ahmad mijin Laila shi ya kawo abincin da za a ci da abin sha wurin saukar Laila ta yo mata memo mai dauke da kyakkyawan hoton Hamida.
Aina ce ta yi mata dinki wanda za ta sanya ranar sauka.

Har ana gobe saukar Abdurrashid bai kawo komai ba, Gwoggo ta yi mita har Allah gajiyar da ita.

Sai dare Hamida na wanke lallen da aka yi mata ya kira waya yana waje Gwoggo ta buntsura baki.
Hamida ta shida nuƙu-nuƙu Aina ta ce jiranki fa ake Hamida. Ta ce “Ban yi wanka ba Aunty Aina Aina.”

Dan murmushi Ainar ta yi tana duban ta wata yar ƙaramar riga ce jikinta sai bakin dogon wando kanta sabon kitso ne da aka yarfa mata a yammacin yau. “Ai ya san hidima ake, sanya hijab din Islamiyarki daga dogo ne.” ta wuce ɗakinsu don ɗauko hijabin Laila da ke zaune wurin ko tari ba ta yi ba, nan za ta kwana saboda bikin saukar.
Yan daura mutum uku suka zo da ta shiga saida ta ɗebi abin da aka yi na rabo ta zuba cikin leda sai ta boye a hijab dinta ta fito, jikin mota ta same shi tsaye yana kallon ƙofar gidan har ta iso inda yake yana kallonta ta gaishe shi ya taka zuwa wurin boot ya buɗe ledoji ya yi ta cirowa sai da ya gama ya rufe boot din ya bude kofar baya ya ciro wani kwali “Zo mu gani za ki iya dauka.” ta karaso gabansa sai da ta ajiye ledar hannunta sai ta karɓi kwalin “Ki kai ciki sai ki samo mai taya ki ku kwashe waɗannan. Kai ta ɗaga sai ta yi godiya ta juya ciki ta ajiye kwalin ta dawo ta dauki ta ta ledar ta buɗe front seat ta ajiye mishi ya bude ya shiga ta ce mishi sai da safe sai da ya bar wurin ta soma tattara ledojin tana kaiwa ciki.
Gwoggo da Aina ke ta buɗewa, shi ma ya yo mata calendar da memo da jaka masu dauke da sunanta sai dai ba hotonta. Sai alƙur’ani hizif bi biyu sune cikin kwali. Sai kaya kala biyar masu matuƙar kyau da tsada.

Gwoggo sai aka shiga murna, Hamida dai wucewa ta yi ta juye ruwan wankanta ta yo wankan ta fito ta yi sallah mai kawai ta shafa ta goga Sure sai ta kwanta tana jiyo hirar su Gwoggo har lokacin da yan Daura.

Da safe da wuri Hamida ta wuce makaranta.
Ita da sauran yan ajin su suna cike da farin ciki a yau, sun sanya kayan sauka an jera su a inda za su zauna, aka soma shirye-shirye.

A wurin da manyan baƙi suke zaune ta hango Abdurrashid zaune kallo daya ta yi masa ta kauda idonta, ya yi kyau ƙwarai cikin wani lallausan yadi fari ga hula ya ajiye a sha tara ya yi mata kyau fiye da koyaushe.

Shi a ka kira ya ba maza shahadarsu, mata kuma wadda ta wakilci matar gwamna ta raba musu.
Hamida ba ta samu cikar burinta ba ta yi na daya, ta dai zo ta biyu namiji ne ya yi na daya. Baki har kunne su Gwoggo da aka kira Hamida aka ba ta kyautar wadda ta zo na biyu.

Daf da tashi aka shiga rabon abinci da drinks wasu jama’a masu kaya iri daya su ashirin suka shiga cikin filin suna raba take away cikin wata leda ledar na dauke da sunan Hamida sai da suka koma gida suka tabbatar da zarginsu kan Abdurrashid ne ya yi hakan don ya aika ma Hamida ta raba wa mutane.

Pepper chicken ne a ciki wani kuma dambun nama irin mai kamar audugar nan sai drinks.
Taro ya yi kyau jama’a kowa ya ci ya sha ya an tashi lafiya zuwa magrib yan Daura kuma sai washegari suka ɗauki hanya.

Wannan hidima da Abdurrashid ya yi ta ɗan wanke shi wurin Gwoggo duk da ba haka taso ba wasu manyan kudi ta so ya miƙo ya ce a yi hidimar.

Wannan kenan. Sati guda kacal da ƙare bikin saukar suka wayi gari da labarin rasuwar mahaifiyar Aina asubar fari suka bar garin Kano zuwa Daura Aina na ta sharɓar kuka Hamida na taya ta Gwoggon ma hawaye take ta zubarwa.

Sun samu gida cike ba masaka tsinke ba su iske gawar ba an tafi kai ta, faɗuwa Aina ta yi tana ta rusa kuka da ta sanya jama’a da dama zubar da hawaye.

A daren ranar an gama sallar magarib Gwoggo ta kira Hamida ta miƙa mata wayarta Abdurrashid ke kira ta karba sai ta bar wurin.

Wani lungu can bayan ɗakuna da ba mutane ta lafe sai dai akwai hasken lantarki sai ga kiran shi ya shigo ta ɗaga da sallama bai saurari gaisuwar da take masa ba ya ce “Me ya faru na ji a ka ce an ga kun shiga mota da sassafe? Sai da ta kalli gefe da gefen da take sai ta rage murya “Maman Aunty Aina ce ta rasu. Ya yi addu’ar Allah ya ji ƙanta sai ya ce ta kai ma Gwoggo wayar zai kira ya yi mata gaisuwa.

Ranar da aka yi uku aka aiki Hamida da Amina su amso waina a wani gida bayan layin su. Haka suka gifta taron mazan da suka yi dandazo a ƙofar gidan.

Ƙatuwar cooler ce suka kamo shaƙe da wainar suna tafe suna hutawa dan Hamida da ke ta koken nauyi, sun shiga layinsu har sun kusa gida Hamida ta hango Abdurrashid na nufo su wata kunya da mamaki suka rufe ta ajiye hannun coller da take riƙe da shi ta yi Amina da ba ta san dalilin ajiyewarta ba ta shiga sababi “Ke dai wallahi ragguwa ce, tafiya ba tafiya ba sai ki ajiye to sai yaushe za mu kai? Hamida dai da ta sadda kai ƙasa ba ta ce mata komai ba har ya ƙaraso inda suke Amina ta jingina da motarsa tana cigaba da sababinta Hamida ta taɓa ta don ta yi shiru amma kamar tana daɗa zuga ta, har ya kama murfin motar Hamida ta matsa kusa da shi tana mishi gaisuwa, Amina sai ta yi sansarai tana tunanin ina kuma Hamida ta san wannan ɗan gayun?

“Ina kika je? Ya tambayi Hamida ta ƙara ƙanƙame hannuwanta cikin farin gyalen da ta yafa ta ce “An aike mu ne.” ya kaɗa kai “Ya yi kyau, ku je ku kai aiken ni zan wuce.”

Ta yi saurin kallonsa ganin shi ɗin ma ita yake kallo sai ta yi saurin maida idonta gefe suka yi ido huɗu da Amina da mamaki ya sandarar a tsaye, ta galla wa Aminar harara “Ba ka shiga ciki ba wurin su Gwoggo.” Ta faɗa a hankali “Yadda ƙofar gidan nan ke cike na san cikin ma cike yake da mata, ki gaishe su.

Ya faɗa motarsa ta matsa jikinta Amina ma ta matsa sai da ya tashe ta ta kama hannun coller “Kama mu je malama. Ta ce wa Amina “Wai ina kika san wannan ɗan gayun saurayin?

Dan Allah Amina ki kama, kin san dai jiran mu ake.” ba ta kama ba sai da Hamida ta yi mata alƙawarin za ta sanar da ita waye Abdurrashid.
Suka tafi Hamida na mata mitar ta ga mutum ta kasa gaishe shi.

Kama bakinta ta yi ba ta gaya wa kowa zancen zuwan Abdurrashid ba har sai ranar da aka yi bakwai tana ta haɗa musu kayan su gwoggo na zaune tana halin nata mita “Shi yanzu yana son ki
Hamida, amma a yi mana mutuwa sai dai ta waya zai yi mana gaisuwa? Hamida ta ba ta amsa ba tare da ta juyo ba “Ya fa zo Gwoggo.”

Cikin mamaki Gwoggo Indo ta ce “Kamar ya ya zo? Ni ina ina da ban gan shi ba? A hankali Hamida ta kwance mata yadda aka yi taɓe baki ta yi “Shi dai ba wani, don kar ya yi alheri ya sa ya ƙi shigiwa, ko ya aka yi ma ya san nan din?

Shigowar wani yaro na sasan su Laila ya sa su bin shi da kallo suna amsa sallamar da ya yi.
Sai da ya gaida Gwoggo ya shaida mata Malam na kira ta mike ta bi bayansa suka fita, Hamida ta sauke ajiyar zuciya sai ta cigaba da harhaɗa kayan.

Gwoggo ta jima kafin ta dawo Malam dai ya hana komawar su a yau ya ce yana son ganawa da Gwoggo idan yan gaisuwa sun gama komawa gidajensu.

don haka sai da suka kwana goma duk da damun da Abdurrashid ke ma Hamida ta waya sun je sun zauna ta manta da karatunta.

Malam ya tara meeting gabadayansu kan Aina ta fito da miji ya sanya ranar Amina kuma tare zai musu dan haka ko Aina ta fito da miji ko shi zai nemi ko ma waye ya ba shi a Daura.

Sai Hamida Alh Mustafa ya yo aike ita ɗin ma ba zai bari ta kai shekarun Aina zaune ba gara ya yi mata auren.

Sun baro garin hankalin su a matukar tashe Gwoggo da Aina Gwoggo ta sha alwashin ba za ta taɓa bari a aura ma Aina kowane kwashe kwashe ba a Daura kamar yadda ba za ta taɓa bari Hamida ta auri Mustafa ba. Watan ƙaramar sallah Malam ya sanya bikin Amina ga shi saura sati biyu kwata kwata a fara azumi.

<< Shirin Allah 8Shirin Allah 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×