Wannan labarin na gaske ne, kuma ya faru ne a cikin wannan zamanin na mu labarin MARYAMA, da mijinta SULAIMAN, sai labarin IBRAHIM matarsa HAJARA, idan yazo daidai da labarinka kayi haƙuri arashi ne.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Katsina.
Ƙaramar hukumar Daura, unguwar Dole.
Zaune take da tsohon cikinta, ta haɗa uban tagumi tana tunanin halin da ta tsinci kanta tun daga farkon rayuwarta har zuwa yanzu da take cikin tashin hankali na rayuwa, kuka sosai take yi don tunda cikinta ya shiga na haihuwa take cikin tashin hankali, don tana masifar cin abinci sosai amman kuma babu halin hakan saboda babu, ayanzu ma haka tana zaune ne bayan ta kankare ƙanzon tukunya taci, wanda ya yi baƙi sosai saboda ƙonewar tukunyar ta yi amman duk da haka sai da ta kankari ƙanzon sosai taci don tsabar yunwar da take ji.
tana cikin kukan Baba hari ta fito, ta banka mata harara sannan ta fara zage zage tana ce wa” aikin banza aikin hofi tsabar ci kamar aljana shi ne kika koma cin ƙanzo? to wallahi ta Allah ba taki ba kuma wallahi duk wanda ya zagi ɗana akan baya baki Allah ya isa ban yafe ba, ciki kuwa har da waɗannan fulanin iyayen na ki marasa mutunci, waɗanda basu san annabi ya faku ba”. Ta faɗi hakan tana sanya koɗaɗɗan mayafinta alamar ce wa unguwa zata tafi, Maryam ta bita da kallo zuciyarta na kai kawo a iya tsahon watanni goman da tayi da Baba hari ta gano munanan halayenta, waɗanda suke sanyata shiga ruɗu ako da yaushe, tunaninta ɗaya ashe dama Baba harin muguwa ce, ta dinga yiwa iyayenta daɗin baki akan idan har ta auri ɗanta ba ita babu wata damuwa, ashe daman mayaudariya ce? tabbas Baba hari ta cika muguwar baiwa, don kuwa ba zata taɓa gamawa da duniya lafiya ba.
Har tayi gaba sai kuma ta dawo baya, cike da tsana ta ta kalle ni sannan ta ce” yauwa ki tashi ki bar wannan munafuncin ki haɗa waɗancan kayan wanke wanken ki wankesu tas tas, sannan idan kin gama ki duba ɗakina na haɗa kayan wanki kije ki wankemin su tas, saura kuma na dawo in iske bakiyi ba wallahi na lahira sai ya fiki jin daɗi, banza me kama da aljanu”.
Kasa ɗago ido na yi na kalle ta, maganganunta na dukan zuciyata sosai na share hawaye na sannan na ce” Baba baki bada omon wankin ba, kada ki tafi na manta ban tambayeki ba”.
Da baya ta dawo ta tsaya tana kallona, sannan ta kawomin duka da sauri na kauce ina jifanta da wani irin kallo na haushin rayuwar dana zaɓawa kai na, cike da masifa ta ce” shegiyar yarinya wannan idan ke mayya ce kika kama mutum wallahi sai kin cinyesa tas tas, in banda mugun hali ai kinsan hanyar shagon na mamajo ko? ba acan ne kike amsowa sulaimanu bashi ba? To n saboda rashin mutunci da mugun hali irin na fulani shi ne za kice babu omo? Ai kinsan hanyar shagon kije ki amso ki wankemin kayana tas kafin kuma in dawo ki hau juyamin waɗannan mayun idanuwan na ki”.
Kallo na bita dashi, na tashi ahankali saboda nauyin da jiki na ya yimin, na kalli kayan wanke wanken da suke wajen, Allah ya taimakeni ban faɗa kan wuƙar dana gani ba, da tuni ta daɗe da hudamin naman jikina, ina kuka na haɗa uban kayan na fara wankewa alhali kuma ba ni kaɗai ce agidan ba, aƙwai ƴammata huɗu agabanta waɗanda bata aurar ba, dama kuma Sulaiman mijina shi ne babban ɗanta wanda ahalin yanzu shi ne ya ke kula da duk wata ɗawainiyarsu, wataran ya samu aci wataran kuma ya dawo haka kowa ya zauna da yunwa.
Ina cikin wanke wanken sai ga Saddiqa ta shigo, tana ta waƙe waƙenta ko kallon inda nake bata yi ba ballantana in sanya ran yin sallama, daman kuma ɗabi’ar Saddiqa ce shigowa gida ba tare da sallama ba.
Ina kallonta ta shiga ɗaki ta ɗakko goga ta fito, tana zuwa ta cillamin ita dai dai kan cikina, na firgita na tashi da saurin gaske ina haki na ce” haba Saddiqa ya zaki zo ki ƙwaɗamin guga? me nayi miki”??.
kallona tayi galala sannan ta ce” oh! baki ma san me zaki yi da gugar ba? Ni kike tambaya abinda za kiyi da guga? to uwarki da ubanki za kiyi dasu”.
Ta faɗi hakan cike da tsiwa, tana riƙe da ɗan siririn ƙugunta.
Sosai haushi ya kamani, ai ban san lokacin da na shaƙota ba na kama dukanta na yi mata lilis sannan na jefa mata gugar na koma kan aikin da nakeyi ina haki, daman gashi babu kowa agidan daga ni sai ita, saboda haka babu me taimakonta daman Baba Hari ke ɗaure mata gaba, yau kuma babu ita shiyasa nayi amfani da damata na doki bakin da ya ke zagina”.
Tayi kukan sosai ta gama, sannan ta tashi da sauri ko mayafi babu ta fice na kalleta na ce”oho dai wallahi ko Baba Hari don surukatace shiyasa nake ɗaga mata ƙafa, wallahi da bata isa ta zage ni ba don ba a zagin iyayena a wanye lafiya”.
Ina gama wanke-wanken, naji gaba ɗaya ƙuguna ya riƙe na tashi ahankali na koma ɗaki, tuni wani zazzafan zzzaɓi ya rufeni na shiga ɗaki na lulluɓa har da ɗan hawayena tsabar azabar dake nuƙurƙusar jikina.
Daidai lokacin na jiyo hayaniya atsakar gidan, idanuwana a lumshe ina jiyo jarabar Baba Hari atsakar gida, amman ban san me take ce wa ba saboda halin da nake ciki, sai ji na yi ta shigo har ɗakina ta ɗaga labule cike da masifa ta fara bala’i.
“Ke ƴar gidan uban waye da zaki dakar min ƴa? Tsabar rashin mutunci har da ji mata ciwo? to wallahi ba tsohon ciki ba Allah yasa haihuwa kike sai dai ki mutu ki dawo amman sai saddiqa ta rama dukanta”.
Gabaɗaya naji sunyo kai na ita da Saddiqan.
*****
Abuja
Wuse Road.
Wani katafaren gida na hango, wanda ya haɗu ta ko’ina tun daga kan gate ɗin gidan zuwa cikin gidan abin atsaya akalla ne, kusan gate biyar ne kafin zaka shiga gidan me matuƙar kyau tamkar a cartoons.
Wasu motocine suka jeru a ƙofar gidan tamkar masu kai amarya motocin suna da kyau sosai tamkar ka sace su, dukkanin motocin baƙaƙe ne wuluƙ har wani shining suke, guda ɗaya daga cikinsu ita ce fara ƙal me ƙirar honda, sai dai yanayin yadda motar take kaɗai ya isa ya tabbatar maka duk mamallakin wannan motar mutum ne me tsananin kuɗi, saboda salo da zubin motar abin a yabawa waɗanda suka yi tane da kuma wanda ya siye ta, don ba ƙarya motar ta haɗu ajin ƙarshe.
Da sauri sojojin suka buɗe ƙaton kyakkyawan gate ɗin, sannan suka koma gefe suka sandare suna gaida uban gidansu yadda kasan anan aka haliccesu.
Sannu sannu motocin ke tafiya tamkar basa son zuwa inda aka tanada don su kaɗai, da sauri na sauran motocin suka fito, sojoji ne masu jini ajika suka fito don buɗewa ogansu me gayya me aiki wato ADMIRAL IBRAHIM KHALIL.
dda hanzari suka buɗemin murfin kyakkyawar motar, cike da kuzari da karsashi ya fito daga cikin ƙasaitacciyar motar ta shi.
Masha Allah fisha’atillah, saboda Admirah kyakkyawa ne ajin farko, sai dai ba fari bane zaka iya kiransa da Black American, saboda yanayin fatarsa ɗaya ce dasu dogone sosai kuma ƙaƙƙarfa, yana da dogon saje wanda ya ke zagaye da doguwar fuskarsa me tsananin kyau da dogon hancinsa, wanda ya ƙawata halittarsa ƙwarai sannan kuma yana da dimples me matuƙar kyau don ya lotsa sosai tamkar ka sanya ɗan yatsansa aciki saboda zurmawa.
Cike da karsashi ya fara tafiyarsa me matuƙar ɗaukar hankali, idan ya sanya ƙafarsa yana tafiya har wani taku za kaji yana yi tamkar zaki ko kuma giwa don wajen har amsa kira ya ke.
Fuskar nan a matuƙar tamke tamkar hadarin gabas, wanda ya turniƙe gabas da yamma kudu da kuma arewa, idonsa sanye da baƙin glass tamkar wanda ya shirya rashin mutunci.
Tana sanye cikin doguwar rigar barci, ta sanya wayarta agaba tana tiƙar rawar justin biba tamkar dai yadda ya ke yi ɗin, rawa take bilhaƙƙi tamkar yadda ƴammatan tiktock sukeyi awannan zamanin.
Sosai gabansa ya yi mummunan bugawa ganin matarsa Hajara kafe agaban waya tana tirƙar rawa babu kunya babu kuma tsoron Allah da gaske take rawarta.
Ckin takun da bai fi ɗaya zuwa biyu ba ya cafko hannunta, sai gata a faffaɗan ƙirjinsa gabanta ya shiga dukan uku uku, shikkenan ta mutu ta lalace…
07068606171