Skip to content
Part 7 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Tafe yake a mota zuciyarsa na faman tafasa da kuna, tunda yake ba a taba humiliating (Cin mutuncin) shi irin yau ba, ba a taba yi masa wulakanci irin na yau ba. Don haka maimakon sautin Khusairi kira’ar Mahmood Khaleel yake bi cikin Suratul Ma’idah. A ran shi kamar ya yi zagi, sai dai dadin kira’ar da yake sauraro na sanyaya masa zuciya, ya ce,

‘Ihsan din me har da za a daga wa mutum hankali kan auren ta? Ita nan har wata mace ce da za a tada hakarkari a dagawa mutum murya a kan ta mts! In da sun san a yanzu babu wani gurbi da yake jin zai iya jogana son wata diya mace a zuciyarsa, bayan HA-LI-MAH, da ba su yi masa wannan jan ran ba, da ba su yi masa wannan wulakancin ba, in ba don ma Hajiya da ta hankado shi ba zai zo ne? Ya yi kwafa shi daya ya ce,

“Allah za su sha mamaki.”

Daga nan harkokin sa ya wuce, ya duba ginunnukan shi ya ga yadda ake aiki tukuru cikin fasaha da kwarewa irin ta Malam Bature, abin ya burge sa, haka tsakanin shi da hukumar lafiya komai na tafiya daidai, ya biya ‘Sahad Stores’ da ke kan titin Benghazi Street ya yi wa Halimarshi sayayya masu firgitarwa duk na kayan ciye-ciye da lashe-lashe, mayukan gyaran kai da shampoos, dryer  zuwa sauran tarkacen kayan gyaran gashi, haka ya ciko mata kit da kayan shafa duk set din neutrogena collection kamar wani mai hada lefe, ya san da kyar ne za ta yi amfani da su, ba burinsa kenan ba, illa ya ga dan murmushin ta mai gigita shi.

Haka ya koma boutikue na kayan kanti ya saya mata riguna da skirt zuwa dogayen riguna (Designers) masu karshen tsadar. Gaban sa baya ko dar na za a iya tambayarta ina ta samu? Idanuwan shi sun makance cikin wata irin soyayya mai gigitarwa, tunanin shi ya gushe, ita kawai yake gani a gabansa.

Ya riga ya shirya tunkarar kowa da maganarta, auren ta zai yi cikin watannan da son ran wani ko babu he did not care (Bai dame shi ba).

A dai kamfanin ta kicin ya same ta tana yankan danyar kubewa da Hajiya ta ce a yi wa Daddy da busasshen kifi da daddare, ‘yar zulunbuwar rigarta ta sha wanki da omon Aerial ta yi fes. Nadadden gashin kanta a cure wuri guda kamar gammo as usual (kamar kullum), duk da wahala da ta tsotse ta ta kuma kwalmade ta still ita kyakkyawa ce kullum kuma kamar ana kara mata kyau ne.

Ya hade hannuwan shi bisa kirjin shi bayan ya aje ledojin da ke hannunsa bisa marbles, duk wani acting din ta cikin yauki na halitta sha’awa yake ba shi, haka duk wani motsin ta burge shi yake, ya ce, “Ha-li-mah.” Da muryar da ke dauke da sakonni da dama.

Ba shakka gangar jiki da ruhin ta duka sun amshi sakon da ke tattare cikin muryar Al’ameen, sai ta yi murmushin da yake son gani, ba kuma tare da ta dube shi ba ta ce,

“Ni fa na gaya ma Al’ameen ba sunana Halimah ba, ka daina ce min Halimah.’

Ta kasan idanun ta ta dube shi don ita yanzun wata masifar kunyar shi take ji, tun maganr su ta daren jiya. Aminu ya kasa magana, tuni ya bushe a tsaye, ji yake kamar ya jawo ta ya rungume, amma ya yaki zuciyarsa da aikata hakan. Tunda yake, bai taba jin wanda ya furta kalmomin nan uku sak, Al-A-Min, ya yi mai dadi ya kuma iya fadi tamkar ita ba.

Sai ya zari mayafin daya cikin dogayen rigunan da ya saya mata ya karasa ya nannada mata aka, still ba ta dube shi ba ta ce, ‘Shukran.’ Wato na gode.

Ya ce, ‘Yunwa nake ji sosai, tun safe ban ci komai ba, na fito bikon matata ga shi ba su ba ni ba, ni kuma don haushi na ki cin abincin su, don Allah ko kin yi ragowar na rana ki sammun?’

Ba ta san san da ta tuntsire da dariya ba, yadda ya karya murya ya rausayar da kai sai ya tuna mata da Patch Adams, jarumin fim din America na fim din (Brilliant) sai ta girgiza kai ta ce,

“Ko ka san Patch Adams?”

Ya ce, “Humour is the best medicine, shin ke kin amince cewa humor is the best medicine? (Ban dariya shi ne babban maganina kowacce cuta).”

Suka koma tattaunawa a kan fim din inda ya lura ita dai tana son fim din sosai. Ta ce,

“Me yasa suka hana ka matarka?”

Ya zuba uban tagumi abin dariya hannuwan sa a kan freezer ya ce,

“Oho! Masu, Kiristoci ne sai ana hakuri.”

Da haka ta ja bakinta ta tsuke, ta jawo babban food flask na Daddy ne da ta je daukowa domin wankewa ta taras ko budawa ba a yi ba, niyyar ta in anjima ta ci idan Hajiya ba ta nema ba, a nutse ta dauki babban plate ta juye abin da ke ciki, farfesun kayan cikin rago ne irin mai sa yawun mutum tsinkewar nan tun bai sa a bakinsa ba, sai farar macaroni a babban flask din, ta bude wani fadi ka mutu, wani abincin Larabawa ne shartoum da ake yi da naman kaza, kwai da waken gongoni, ga kuma farfesun kifi ragon ruwa fari sol da shi, ta hada duk a katon tray ta dora mai akan freezer inda yake jingine a jiki ta ce,

“Ko za ka iya cin wannan Al’ameen kafin in kammala tuwon dare?”

Ya dube ta cikin ido da idanun shi masu kama da an diga masu silver saboda sheki, ta kawar da kanta da sauri domin ba ta iya jure kallon nan nasa ta ce, “Ka ci kafin in kammala wannan, Al’ameen ka fiya kallon mutum Allah.”

Ya yi murmushi mai fidda sauti, ya dubi abincin ya ce,

“Yanzu duk ke ki ka sarrafa wannan Halimah, a ina ki ka san Shartoum?”

Ta wani irin juyo ta dube shi a ranta ko cewa take,

“har ni za a tambaya abincin Larabawa?”

Ta ce, “Allah ka rage kallo, domin haramun ne.”

Ya sake murmusawa a karo na biyu ya ce,

“In banda Halima ba mutumin da ya ishe ni kallo.”

Ta dan juya kadan ta ce, ‘Ah! Matarka fa?”

Ya ce, ‘Ihsan sunanta.’

Ta ce, “Ni ai ba sunan ta na ce ka gaya min ba, cewa na yi ita ma haka ka ke takura mata da kallo?”

Ya kai lomar farko na macaroni cikin bakinsa, dandanon girkin da komai ya yi masa dadi har kunnuwansa sai da suka motsa ya ce,

“To wai ke, ina gamin ki da matata ne, are u jealous?”  Ma’ana kina kishi?

Ta juye kubewar da ta kammala yankawa cikin tafasasshen ruwan miya mai rai da motsi da ta hada ta ce, “Wa, ni?”

Ya ce, “Yes, ke Halimah.”

“A kan me ka ce haka?”

“A kan na ga kin damu da ita, ita ba ta ma san ki ba.”

Ta zobara baki gaba yadda takema Faisal in ya ba ta haushi ta ce,

“Na yi zaton sai ana son mutum ake kishin sa?”

Al’ameen ko ya nuna damuwa da shaguben ta, sai zuba abincin shi yake cikin tumbinsa santin dadi na dibar kununwansa, ya ce,

“Oho! Haka nima na ji?” Su duka ba su san sanda suka sa dariya ba.

Ya ce, ‘Zan tafi Niger yanzun nan sai wurin jibi zan dawo, na zo miki sallama ne, ga kaya ki yi amfani da su kafin in dawo in gayawa mutanen gidan nan bukata ta ta auren ki halimah. Ina fata ko me za a yi miki, Halima za ki kasance a baya na?”

Ya kafe ta da ido, ta yi shiru ba tare da ta juyo ba, amma ta yi sanyi da juya miyar da take yi. Anya za ta iya aure ba da yardar iyayenta ba? Duk ko da yadda take jin Al’ameen a zuciyarta, ruhin ta da kasusuwa, bargo da gangar jikin ta gaba daya?

Ba ta jin za ta iya zartar da wani al’amari ga rayuwar ta ba tare da sani ko amincewar wadannan iyayen nata biyu ba, ina! Balle aure dungurungum, tukunna ma shi Al’ameen waye ne? Bata da wani sani a kan shi, dabi’a, sana’a da uwa-uba asali. Ba ta san komai a kan shi ba, in ban da so makaho ne. Haka kawai fa rana daya suka ga juna, guguwar mahaukacin so ta fyade kowannensu, duk da bata jin ko barawo ne za ta fasa son shi da kaunar shi, amma aure?

Sai ta kada hafizin harshenta ta ce,

“Idan har Daddy ya amince ba?”

Ya ce, “Idan kuma aka samu akasin haka?”

Ta girgiza kai da sauri,

‘Nima ba zan amince ba!”

Ji ya yi kirjin shi yayi wani irin bugawa da karfi! Ya hadiyi wani makalallen miyau da ya tokare a makoshin sa da kyar, ya zuki iska ya fesar cikin takaici ya ce,

“Kenan you don’t love me Halimahhh?” (Ba ki so na Halima?).

Ta ce, “Sam, ba haka ba ne Al’ameen…” Ya riko hannuwan ta duka biyu cikin zafin nama a zafafe ya ce, “To yaya ne?”

Ta daga lumsassun abnormal idanunta ta dube shi, shi ma duban ta yake impatiently (A kagauce) ta ce cikin raunannar murya.

‘You said so many things to make me happy, and try your best to make things work out okey for me. If I could describe your kindness, I would be describing an angel. If I should describe your love, I would be describing my whole heart. U are a gift Al’Ameen, from Glorious God to me, you are an angel! How could I say I don’t luv U (Ta yaya zan ce ba na son ka?)

Illa iyaka ana son duk abinda dan adam zai gabatar, ya yi kokari kada ya saurari ra’ayin shi, ya saurari ra’ayin na gaba da shi.

Ka ga kaman shi Daddy ya girma har ya kusa tsufa, ya yi edperiencing wasu al’amura na rayuwa, musamman auren da aka gina a kan soyayya, wanda mu da muke kasa da shi ba mu yi ba.”

Al’ameen duk da cewa maganar ta ta farko ta yi mai dadi, ta kuma wanke shakkun da ke zuciyarsa, amma ya kasa fahimtar ko me take nufi da wannan murdaddiyar magana? Bai san san da ya ce,

‘Shin me ye tsakanin ki da Daddyn gidan nan?”

Anan ne ta fuskanci shirmen da take shirin tafkawa, da sauri ta ce

“Babu, sam babu, illa a dan zamana tare da su na fahimci cewa shi mutum ne irin sauran mazan jiya masu kaifin tunani da hangen nesa.”

Ya ce, “To magananniya, kina ganin wrong choice (Zaben tumun dare) za ki yi wa rayuwarki kenan a hada rayuwa da Aminu?”

Ta ce, “Kash! Ana baka kana kin amsa, na riga na amince da Al’ameen-Al’ameen ne100%, illa just what my sociology told me, ka yi hakuri a bar maganar sai ka dawo din?”

To Al’ameen ya tafi Niamey da kwarin gwiwa da dukkan goyon baya na zuciyarsa kan amincewa da yarinyar da ko sunan ta bai sani ba, dari bisa dari zuciyarsa ta amince da ita. Ya lura bayan nutsuwa, yarinyar mai hankali ce da sanin abinda take yi uwa-uba kyakkyawan tunani da hangen nesa she leave no stone unturned tamkar ba karamar yarinya da ba ta kai shekaru ashirin ba.

Hakan nan akwai wannan kalmar ‘class’  a tare da ita ba daya take da sauran matan da ya sani ba wannan daban ce, ta san mutuncin kanta, ta san baiwar da Allah ya yi mata na ‘ya mace mai darajjah. Duk rudewar da mata ke yi a kan shi a Miami, ita ba ta yi surprised! (Don Allah mata mu dinga jan mutuncin mu a komai).

Ya yi duk abin da zai yi a Yamai cikin kwanaki uku rak ya turo kayan shi ta jirgin ruwa. Ranar da zai dawo ya shiga kasuwa a Yamai don bude ido kawai, ba abinda ya dauki hankalin shi irin kayayyakin matan su da ya tabbatar za su yi kyau da Halimar shi tun da itama tana yanayi da su, ya ciko akwatuna masu kyau da kayan matan Zindar, Niamey, Maradi da Damagaram da niyyar in sun yi aure da Halimar shi zai bata ta dinga yi mai kwalliya yana ganin ta kamar ‘yanmatan Niger. Hatta necklaces da duwarwatsun adon su ya saya mata, su wannan da niyyar su zai ba ta a matsayin tsaraba da zarar ya koma.

Ya tsaya a wani kantin turare ya saya wa Hajiyar shi saitin Givenchy (for women) da take amfani. A ranar ya sauka a Abuja.

Masu aikin fenti ya tarar suna ta yi a kowanne sako a gidan. Khaleel ke gaya masa wai Aunty Saratu ce za ta dawo sati mai zuwa. Har ran shi ya ji dadi, amma sai me?

Ya shiga sashin Hajiyar domin ya sanar da ita dawowarsa, ya kuma bata tsarabar ‘givenchy’n da yayo mata, ya ji shi a kulle gam da mukulli. Ya kwalawa Furkan kira ya ce,

“Kai Hajiya ta je anguwa ne?”

Furkan ya ce cikin rashin jin dadin al’amarin “Ya Aminu rabu da Hajiyar mu kawai, wallahi tana bin shawarar su Anty Suwaiba ne kawai, suna kai ta su baro. Yanzun wai ta koma Kaduna saboda Daddy ya ce da ita Maman Intisar za ta dawo, ba ka ga irin zagin da ta yi wa Daddy ba a gabanmu har mu da muka goya masa baya.”

Al’ameen ya rasa me ma zai ce? Ba tun yau ba wasu halayen na Hajiyar shi ke ba shi kunya da takaici ba, yanzu da girman ta a ce ta yi yaji ai ba karamin abin kunya ba ne a garesu, bai taba ganin mace mai kishin kishiya irin ta ba, wanda a shekarun ta ya isa a ce ta bari, ta kame girman ta, amma ashe wasa farin girki? Ko zama bai yi ba a lokacin ya zari mota ya nufo Kaduna cikin unguwar Kabala Custain, ainahin gidan kakanin su na wajen uwa.

Tun daga get maigadi yake sanar da shi duk gidan babu kowa sun tafi hutu Dubai har Hajiyar.

Ya girgiza kai a daren ya dawo Abuja, amma bai koma gidan su ba, gidan sa da Daddy ya ara masa wanda cikin ‘yan kwanakin babu abin da ba a zuba a ciki ba na jin dadin rayuwa, sai su da suka ki zaman gidan, anan ya kwana.

Ya kira Hajiyarsa a washe gari, yana ba ta hakuri ta dawo ko don darajar su, amma sai ta sa masa kuka wai su da uban su so suke su taru su kashe ta. Ya ce, “Amma dai Hajiya ko za ki Dubai ba yanzu ne ya dace ba, sai a ce bakin ciki ya kore ki, ai kamata ya yi ki bari sai ta dawo tukun duk in da za ki sai ki je.      Ya ya za ai mu kashe ki da bakin cikin mu bayan ke ce wadda ba mu da ya ita a duniya? Ki yi hakuri ki dawo don Allah.”

Ta ce, “In dai ni ce uwar ka Aminu, to ba kai ba Saratu ko ta shigo gidan, in har kana son in dawo.”

Ya ce ya amince, amma fa in har ta dawo din. Ban da abin Hajiya shi ina ma ya zauna a gidan balle ya shiga harkar su (sai ka ce wani lokacin kuruciya). Shi dai har ga Allah lallaba ta yake yadda take so don kar ta zubar da kimar ta a idon mutane, tunda kowa ya ji ba ta gidan ya san me ta yi wa tafiyar, shi kuma ba zai so zubewar mutuncin uwarsa a idon kowa ba duk lalacewar ta kuwa, duk da cewa ita din halin ta sai ita.

Karfe goma na safe, ya shirya cikin danyen boyel navy green, haka motar da ya hau a yau ‘Kia’ ce, lemon green, koren takalmin fata ne a kafar shi kirar Italy. Daman Al’ameen ba dai iya cool dressing ba, ya yi amfani da farin mudubin ido don ado kawai, ya nufo gidan su cike da nishadi.

Ya saki kan motar a shararren titin Atiku Abubakar, har ya tadda katafaren gidan su yana bin sautin Alicia Keys, iskar damuna na kara armasa masa hantsin tare da gudanar masa da wani bakon nishadi, in da duk ya motsa kamshin turarrukan sa Ultraviolet da Vanderbilt da yake yawan amfani ke tashi. Al’ameen kenan.

Ya duba kicin bai gan ta ba, ya leka dakin da suke kwana nan ma ba ta nan, ya leka dakin Dela babu alamar ta, gabansa yayi mugun faduwa, sai ya tsaya a kofar kicin din cikin zakuwa rike da ‘yan makullan shi yana zuba idon ganin ta inda za ta bullo. Zuciyarsa fes, take a yau domin hakika ta azabtu da rashin ganin Halimarsa for long four days (Tsayin kwanaki hudu).

Daga can lambun gidan ta bullo rike da ribdediyar goba koriya shar da za ta hadawa Daddy guava juice sai ta ga bakon da bata zata ba, tsaye kofar ofishin ta. Ta saki baki galala! Da gani na jin dadi ne ta ce,

“Lah! Al’ameen saukar yaushe?”

Idanun su ke kallon juna tamkar sun hadiye junan su don so da kauna. Ita kanta ta yi kyau a yau, domin ta yi wanka kenan ta sanya daya cikinr iguna da skirt din da ya sayo mata kalar su black and pure white, sai doka kamshin brut (body spray) take, hakan nan curarren gashin ta mai kama da gammo yau ya sha wanki ya ga mayuka kala-kala da ya shekara bai gani ba sai sheki yake a cikin sassanyan hantsin na Litinin. Ta yi mai tufka daya kwal murtukekiya jelar sai yawo take a gadon bayan ta, she look so cute kwarai cikin kayan.

Ita kanta ba ta san nishadin me ta tashi da shi a yau ba? Haka kawai tun da Dela ta ce da ita Hajiya ta yi balaguro Kaduna ta tashi ta fetse kwalliya, ashe rabon gwarzon masoya Al’ameen ce. Ya bude mata dukkan hannuwan shi amma sai ta noke ta cilla mai katuwar gobar da ke hannun ta, ya mika dogon hannunsa ya janyo jelar gashinta da karfi, don zafi ba ta san sanda ta fada jikin shi ta yi maza kuma ta ture shi ta ce (Dela da ke makale jikin kofar dakin ta, tana leken su, ta daura hannuwan ta a ka ta ce, “Na shiga uku ni Dela, kar dai yarinyar nan ba ta san Aminu ba?

Za a aikata da na sani! Ko da yake duk laifin uwarsa ne…ikin ta babu inda baya rawa saboda kaduwa, yau kam ta yi dana sanin sa masu idon da ta yi, da bata ganowa kanta wannan kayan takaici ba, wai an ce ka bar abin da ba ruwanka izuwa abinda bai shafe ka ba, sa-ido sana’ar banza).

Sai ta ja bargo har kanta ta kudunduna tana rawar dari. Ta ce cikin fushi, “Aminu, ba na so, kada ka sake, wannan haramun ne, idan kuma ka ki zan gaya wa matar ka ta ja ma kunne.”

Ya tuntsire da dariya ya ce, ‘Ita har ta isa?”

Ta gyada kai, ‘Har ta yi yawa.” Ya tura hannun shi a aljihun shi ya ce, ‘Zo ki ji?’

Ta harare shi cikin haushi ta ce,

“Ba’a zuwa.”

Ya mannawa wani gefen daban ido ya ce (ba tareda ya dauke idonsa daga gefen da ya mannawa idon ba),

“Ashe kadangaru ma na son kafar fararen mata? Dubi yadda yake lasar farar kafar ki cike da so da kauna.”

Haba! Da ta daka wani tsalle, sai gata makalkale jikin Al’ameen tana ihun rokon sa, “Don Allah cire min shi, don girman Allah! Sai hawaye sharrr! Jikinta na kyarma. Ya fiddo hannun shi daga aljihu rike da necklaces da zobba, abin hannu da kafa na duwarwatsun matan Niger da ya sayo a Niamey, ya russuna ya daura mata a kafa, ya daura mata a hannu, ya mike ya daura mata a wuya. Ya bula hancin ta da kwambalelen abin hancin su mai kama da awarwaro, sai da ta feso wasu hawaye don azaba, amma ta yi kyau! Ta yi kyan har ta gaji!!

Ta bishi da ido galala! Kana hannayen ta da ke cikin nashi. Da jikin sa data makale. Ta sauke idon ta ga kafafun ta, wani hawayen ya zubo.

Ya kai hannun ya shafo hawayen yana murmushi ya ce,

“Haba Halimah! Ya ya ki ke min asarar hawaye a kan kadangare? Ba kadangare ba, ko Zaki bai isa ya taba ki ina gani in kyale shi ba, sai dai ko ni ko shi. I luv u Halimah!”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.2 / 5. Rating: 20

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 6Siradin Rayuwa 8 >>

5 thoughts on “Siradin Rayuwa 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×