Skip to content

Siradin Rayuwa 1 | Babi Na Biyar

3
(19)

<< Previous

Sannu-sannu yake takun shi mai karfi irin na mahaifin shi, bai san dakin da take kwana a gidan ba, amma zuciyarsa ke ba shi tana kicin din ta.

Gidan Bello Makarfi na garin Abuja irin tafkeken gidan nan ne (family house) da wani sai ya yi wata bai ga dan uwansa ba, in har ba shi ya neme shi ba, don haka ba wanda ya san Al’ameen na zuwa kicin, in ma da wanda ya sani yake kuma kallonsa da duk wani takunsa to Dela ce, shugabar ma’aikatan gidan.

Duk wani shige da ficen Al’ameen a kan idonta ne, tana kuma leken duk abin da ke faruwa cikin kicin din ta labulen dakinta sai dai ba ta iya jin abinda suke cewa.

Ile kuwa tsammaninsa ya zama gaskiya, sai ya ganta kwance bisa tabarmarta, ta kifa wani littafi a fuskarta tamkar tana barci, sai in mutum ya lura ne sosai zai gane ba barcin take ba, ta dai yi karatun ta gaji ne ta afka kogon tunani; deep in thought. Ya tsaya bisan ta ya yi murmushi ya ce,

“Halimah yau in na ce da ke Assalamu alaikum za ki amsa?”

Ta zare littafin daga fuskarta, kana ta mike zaune cikin nutsuwa, muryarsa ta gane amma shi bata gane shi ba kasancewar ba kasafai take fuskantar mutane da daddare ba, ta zauna sosai kawai bata ce komai ba. Ya ja kujerar robarta kwaya daya tal da ke cikin kicin din da take zama don yin ‘yan yanke-yanke ya zauna idanun shi a kanta, ya lura idanunta sun yi jazur, tamkar an watsa masu barkono duk sai ta sake ba shi tausayi, ya sadda kai yana duban yatsan kafarsa, a tsammanin shi kukan tuna iyayenta ta yi shi ne har suka yi hakan.

Bai sani ba, littafin take so ta karanta ba ta iya bambance rubutun da ke ciki, domin tana da lalura a ido, shine har suka yi hakan. A ransa ko ji yake kamar ya tsinewa wannan baban nata.

Ya dago ya sake duban ta, ta yi shiru, ta dage kai sama tana kallon ceiling tamkar mai son irga adadin taurarin da ke can saman sa.

Ya ce, “Kin san ko karfe nawa yanzun ki ke zaune still a kicin?”

A nan ne ta yi masa magana ta ce,

“Yanzu zan tashi dama.”

Ya ce, ‘Halimah, idanun ki sun yi ja kwarai, what are you crying for? (Me ki ke wa kuka).”

Ta ce, “Ni fa ba sunana Halima ba, haka kawai ka lika min wani Halima, kai na lika ma sunan wani duk da ban san sunan ka ba?”

Ya murmusa kadan don ya lura son jin sunan nasa ke cin ran ta ya ce, “To ya sunan ki?”

Ta yi shiru ta kyale shi sai da ya sake maimaita tambayarsa nan ma ta yi shiru, ya ce, ‘O.K, as long as you wish (zuwa san da ki ka ga dama), ki gaya min sunan naki, zan kira ki Halimahhhh, in ya so ran da ki ka yi niyyar gaya min sai na kira ki da sunan naki.”

Ta ce, ‘Sunana mutum mana.”

Ya ce, ‘Of course, we are all humans, (Dukkannin mu mutane ne), amma akwai wani suna kebantacce ga mai shi, wanda za a kira sa da shi ya amsa. Kin ga kenan tunda kowa mutum ne, in aka kira kowa da hakan ba za a bambance da wa ake ba. Kin ga kamar ni sunana Al’ameen amma mutum ne?”

Yadda ya maida kansa wani yaro shi ma kamar ta ya bata dariya, haka maganar shi ta matukar bata dariya sai ka ce wani malamin Hausa, sai ta saki wani lallausar murmushi da ta dade rabon ta da yi tun kafin barin Faisal kasar Nigeria. Bai taba ganin ta yi murmsuhi ba, ashe kyawun ta ma na cikin murmushinta ne?

Gaba daya jikinsa ya mace lis, wata irin kasala ta saukar masa wadda ta kai shi ga runtse ido da karfi kada ya yi abin da ba daidai ba.

Babu wata gaba da bata amsa kaunar yarinyar a jikinsa ba. Bai taba jin irin wannan yanayin ba a duk matan da ya taba mu’amala da su cikin duniya hatta matarsa. Wannan shi ne ake kira natural love kenan da bai taba tsintar kansa a ciki ba?

Ya sa hannu ya tallafi goshinsa ya sunkuyar da kai yana kallon kyawawan yatsun kafar ta tamkar na Balarabiya. Lokacin ne idon sa ya kai ga littafin da ta yasar a gefe guda, ya kai hannun shi ya dauka ya duba sai ya ga an rubuta Essential Biology, ya soma buda shafukan littafin anan ya ga ta yi alama a wani waje da wani dan karamin hoto daukar Saudiyyah mai dauke da fuskokin wasu kyawawan yara mata guda biyu suna kyalkyala dariya, ya jima yana kallon hoton ya ce, ‘Duk da ban sani ba, amma wannan kamar ta gaya min yaran nan kannen Halima ne?”

Ta ce, “Ko daya, makaranta kawai ta hada mu, amma mutane da dama ba sa gane hakan har Mamar su ma kamar mu daya.”

Ya aje hoton gefe daya ya ce,

“Ya sunan su?’

Ta ce, ‘Siririyar Hidayah kenan mai jikin kuma Hunainah, ni da su muna son juna sosai kuma mun shaku musamman Hunainah.”

Ya ce, “Me ki ke karantawa cikin littafin nan?”

Ya kashe wancan zancen kenan, don da alama in za a kwana ana yin sa ba za ta gaji ba, da gani ba karamar kauna take yi masu ba.

Ta dubi littafin ta ce,

“Duk gaba daya amma yanzun ba karatun nake ba.”

Kamar da wasa ya ce, 

“Yanzu idan na tambaye ki abinda ba ki zata ba cikin Biology za ki iya amsa min?”

Ta ce, ‘Na jima da barin makaranta, sai dai bana jin akwai abinda na manta, go on.”

Ya yi murmushinsa (broad smile) kamar kullum, ya gyara zama har da gyara murya ya kuma sarke kyawawan yatsunsa cikin na juna, da gani ka ga malami mai fasahar koyarwa, ya canza harshe kwata-kwata ya ce,

“Zan yi miki tambaya a cikin wannan darasin na Supporting Tissues in Plants.”

Ta yi murmushi, hakan nan ta ji ya burge ta, bata taba jin mutumin da ke karya turanci ziryan with American accent hakan ba, ko don wannan lafiyayyen turanci ai ta amsa masa tambayoyin sa itama. Ta ce,

“Kai na ke saurare.”

Ya ce, ‘supporting tissues’ nawa ne in plants?”  Ta daga yatsun ta ‘sabbab, ibham da wusda da na karshen ta ce,

“Hudu.”

Ya ce, “Lissafo man su.”

Ta ce, “Ka ga akwai turgid-parenchyma, akwai Sclerenchyma, Collenchyma da dylem.”

Ya girgiza kai ya ce,

“Wanne suna aka san dylem tissue da shi bayan dylem?”

Ta ce, “Ana kiransa wood (Katako).”

Ya ce, ‘Ta yaya dylem ke ba da support din shi ga plants?”

Ta ce, “Dylem yana bada support din shi ta hanyar bai wa tsirrai suffa ne.”

Ya ce, ‘Shi kuma parenchyma fa?”

Ta daga kai sama ta ce, “Shi parenchyma sai a yayin da vocoules ke cike da sap ya ke bada karfi ga plants, ya kuma kare su daga barin karyewa da wuri.”

Ya dube ta, thoroughly ya ce, “Fata, rubi nawa ce a jikin dan adam?”

Ta ce, ‘Uku.”

Ya ce, “Wannan dabbar kadangare a wane aji yake?”

Ta ce, ‘Reptile ne.”

Ya ce, “Kada fa?”

Ta ce, ‘Ai shi ma haka.”

Ya rike baki ya ce, “Gaya min sunayen cuttutukan hanta guda biyu.”

Ta ce, ‘Akwai cirrhorses, akwai kuma dirrhorses.”  Ya ce, ‘Tumatur, a cikin fruits din mu a wanne aji yake?”

Ta yi murmushin raini ga tambayar ta ce, ‘Berry, of course?.”

Ya ce, ‘To mango fa?”

Ta ce, “Drupe.”

Ya aje wadannan kananun tambayoyin a gefe, ya kara sarke hannun shi cikin yatsun shi ya ce,

“Me yasa fatar tsoffi ke tattarewa?”

Ta ce, ‘Saboda jini baya gudu a jikin su?’

Ya ce, ‘Yes, ta wacce hanya kyankyaso ke numfashi?”

Ta ce, “Tracheal system.”

Ya dan kalmashe murya tabbacin zai kure ta anan ya ce, ‘Gaya min in zaki iya chemical formula na magnesium sulphate?”

Ta daga kai sama, tamkar mai karantowa a ceiling, ba tare da ta sauke kannata ba ta ce,

‘Na sani, MgSO4.”

Ya ce, ‘Na water fa?”

Ta ce, ‘ana kiran sa H20.”

Sai ya yi shiru yana duban ta. Allah kadai ya san me yake tunani, ba zai wuce yara irin su ake nema ruwa a jallo domin farfado da harkar lafiya a Nigeria ba, amma wai uban ta ya sai da ta? Kai ba zai taba yarda da wannan karyar ba, koma dai ya take ne ya amince da abinda zuciyar shi da gangar jikin shi ke so ba tun yau ba, a tun ranar da ya soma dora idanun shi a kanta, ya amince zai taimake ta da dukkan karfinsa, zuciyarsa, lafiyarsa da abin da ya mallaka in har suna taimakawa.

Baya bukatar tambayarta makarantar da ta yi, ya tabbata koma ina ce to ba ta kananan mutane ba ce ba, ba kuma ta dakikan dalibai ba.

Ya dago sannu a hankali ya dube ta, cikin wani sabon sauyi a tattare da shi da muryar shi gaba daya ya ce,

“Kin ki gaya min gaskiyar labarin ki, kin ki gaya min ko ke wace ce? Amma Halimah ko ya ki ke, ko ke wace ce am sorry to say… I’m in love, shin za ki iya aure na?”

Ko motsi ta kasa, babu wanda ya taba yi mata magana da irin wannan muryar mai kashe duk wata gaba mai motsi a jikin dan adam. Ba ta taba jin wani abu wai shi emotional disturbance ba sai yau. Bata taba jin ta takura a gaban namiji ba sai ko yau a gaban Al’ameen Bello.

Tamkar an daure mata harshe da baki mai motsi ya fidda sauti ko kafafun ta ta kasa motsawa, son shi ke kara shiga kowanne lungu da kowanne sako na gangar jiki da tsokar zuciya kwaya daya da ta mallaka cikin tsakiyar kirjinta, ba tun yau ba, tun ranar da ta fara ganinsa. (A irin wannan yanayin ne ake cutar  yara mata, musamman a shekaru irin nata (teenage).

To amma Al’ameen ya amincewa kansa son Allah yake mata, babu wani tunani na banza ko kankani game da ita a tare da shi. He loves her because he loves her kawai.

Ya tabbata itama ta ji son sa tun daga kokon rai har kwakwalwar ta ita ma, amma so yake yi ta fada masa da bakinta ta amince, don baya so ya takura ta, natural love yake nema don ya tsani love out of pity kamar irin nashi da Ihsan kenan, wanda yake jin dadin bangare guda takurar daya bangaren.

So kawai yake ta ce ta amince, shi kuwa ko sama da kasa za ta hade sai ya aure ta ko da Hajiya za ta ki amincewa.

Ya dago fuskarta, ta rintse idon ta da karfi, ya ce, ‘No, magana za ki min Halimah idanun ki widely opened (a bude tangararas) cewa kin amince ki aure ni?”

Baki daya jikinta rawa yake, ta tabbata ba ta da mafita ban da ta ce ta amince din. Yadda numfashin su ke dukan na juna bata taba zama kusa da wani namiji so closed hakan ba, hakan kuma ba karamin sauyi ya kawo a gangar jikinta da ma bugun zuciyarta ba, don haka ta bude idanun ta da suka yi jawur tun tuni ta ce ta amince.

Suka yi wa juna lallausan murmushi a tare. Sai da ya ga shigar ta dakin da suke kwana ya sake yin murmushin, ya juya. Yau kam ya yi barci mai kyau cikin kwanciyar hankali irin wanda bai samu yi ba a tun ranar da ya baro Miami. Baya ko tunanin gagarumar rigimar da yake shirin tayarwa.

Washe gari da safe ya je gaida Hajiyarshi take nuna mai bacin ranta na kin zuwan shi Garki wurin su Ihsan ta ce, “Wannan ai rashin mutunci ne Aminu, jiya Daddy ya je ofishin Babanta sun gaisa ya ce abin da ka yi ya bata masu rai duka, yaya muna cikin gari daya amma a ce gaisuwa wannan ta gagara balle tahowa da itan bayan ba abin da ba a kammala a gidan ba, wannan ai wulakanci ne.”

Ya shiga ba Hajiyar shi hakuri yana gaya mata matsalolin da ya kashe wadanda suka hana shi samun lokacin kansa, amma ta ki sauraron shi ya ce, ‘Ita ma Ihsan din ta sani saboda transfer din aiyukan su duka amma yanzu da ya karya kumallo (breakfast) can zai fara zuwa kafin ko’ina.

Ina! Hajiya ta ki ta ce yanzu-yanzun ya tashi ya tafi ya ci abincin a waje, har tankado keyarsa ta yi daga kofar dakinta, sai ya yi murmushi ya lalubi ‘yan mukullayen motarshi ya tabbatar suna nan cikin aljihun shi sai ya fita. Zuciyarsa cike fal da jin haushin rashin ganin kyakkyawar fuskar Halimar shi a safiyar.

Tafiya yake sannu-sannu bisa kyawawan titunan birnin Tarayya marasa tudu balle gargada. Dressing din da ya yi a yau ya burge kwarai, ga wani dan siririn farin gilashi da ya manna tamkar Ba’indiyen nan Bobby Doel, kira’ar (Khusairi) yake bi cike da nishadi, ya san yau zai gamu da fushin Ihsan din shi da ke ba shi dariya, don da an dan kissing din ta shi kenan ya kare, ko ko don tana son shi ne? Bai sani ba.

Yana bin adireshin da ke jikin katin bai sha wuyar gane gidan ba, tun daga gate ya tabbatar su Ihsan kam ana ji da naira. Maigadi ya yi mai iso Ihsan ta ba shi izini ya kai shi can babban falon saukar bakin babanta. Ta samu Ann tana waya ta ce, ‘Kin ji Al’ameen ko sai yau ya waiwaye ni?”

Ann din ta rufe wayar ta ta dauki malafarta ta kifa a ka, ta ce,

“Fara bashi abinci tukunna, don daga ji sammako ya doko kada ya ce muna tsiya.”

Ta yi dariya ta ce, “Kai Ann, ba ki da dama. Amma ai ko kofar gidan mu mutum ya kalla ya san ko jikokin-jikokinmu, su da tsiya sai da su ji ana labarinta.”

To amma ita kanta Ihsan ta san wannan ba halin Al’ameen din ta ne ba, rainawa mutane kura, ta dai fada ne kawai don ta ga Ann da alama ran ta ya baci da Al’ameen sosai. Ta koma kicin ta bawa yaron su Ike umarnin abinda zai kai masa matsayin karin kumallo (American breakfast) kamar yadda ya fi so a kullum. Daga nan toilet ta yi ta fesa wanka na musamman ta zuba fararen undies kafin ta daura wani masifaffen tattausan lesi cotton fari sol, mai adon kala-kalar duwarwatsu.

Wannan less da shi da babu duk daya don manyan hudojin da ke jikinsa sun wuce misali amma kudi na gugar wuri har naira dubu saba’in kudin mu na nan gida Nijeriya ta saye shi a London, ba don komai ba sai don Al’ameen mutum ne mai son farin abu, ya sha gaya mata in ba farar kwalliya ta yi ba, ba ta burge shi, kuma ya kan so ta don farin ta ba don kyan ta ba.

To wannan ne dalilin da yasa ta sanya shi, haka ko ‘yanmatan Al’ameen jar fata sun fi yawa don dai Allah ya so ta da shi ne kawai duk da yake ita din ma fara ce, amma fari ne na jin dadi ba na halitta ba. To wannan na daga dalilin da yasa ta fiye farar kwalliya don ta lura Aminu fa sai da lallami ake samun shi.

Tun can ba ta daura dankwali bare yau da kwalliyar ta musamman ce. Hakika ta azabtu da rashin ganinsa na ‘yan kwanakin nan, domin ba su taba kaiwa tsawon wannan lokacin ba sa tare ba, tun auren su, ko ofis tana like da kayan ta saboda nurses masu yi masa kallon da bai gamsar da ita ba. Ihsan kenan.

Takalmi flat fari sol dan Thailand ta zura kafafun ta dan dagwas, turare mai suna turare ita kan ta ba ta san kala nawa ta fesa ba, musamman collection na Calvin Klein da Dior, ta yadda har ba za ka tantance kamshin wane turare take ba, wannan duk yana daga cikin koyarwar Al’ameen Bello, domin shi mutum ne mai masifar son kamshi, baya jin kyashin saya masu turare ko na nawa ne.

Musamman zai je Paris don kurum ya sayo masu turare, wadannan na daga cikin dalilan da suka sa har kullum take son shi, take kuma kara kaunarsa a kowanne dakika, domin hakika shi din special ne, haka komai nasa na musamman din ne.

Tun haduwar su bata kara duban wani da namiji a duniya da sunan so ba, shi kadai take so, shi kadai take sha’awa, shi kadai ke burge ta, hakan nan shi kadai ne namijin da zai iya yi mata kowanne irin wulakanci ta shanye. Dr. Ihsan kenan.

Cikin takun kasaita ta wuce Ann ta ce,

“Ba za ki je ku gaisa ba Ann?”

Ann din ta dube ta sama zuwa kasa ta ga yadda ta wani hade kamr mai shirin zuwa dinar babbar aminiya, wani haushi ya kama ta don ita so take ta kashe auren kowa ya huta, don ba ta ga yaron da ya isa ya wulakanta gudan jinin ta ta kyale ba komai tashen nairarsa kuwa, kuma ko dan uban waye shi balle wani shirmen banza likitan kwakwalwa, amma ba ta son ta bata farin cikin Ihsan, don ta lura still tana son mijinta sai ta bi ta da siyasa.

Ta juyar da kai kawai ta ce,

“Ki je kawai ki ji wadda ya zo da ita, zan zo in raina ya yi sanyi, don har yanzu raina a bace yake. Kin kuma sanni ban iya boye bacin raina ba.”

Ta kadai kai ta fita fuskar nan ba annuri sam, ta shiga taka matattakalar da za ta sada ta da falon, kasancewar ainahin ginin falon bakin Dr. Argungu a kasan gidan yake tamkar ka shiga rijiya ne ka tadda sabuwar duniya. Ta sa kai ba ko sallama.

Aminun shima daman ya cika fam, da shanya shin da aka yi fiye da awa biyu kamar wani mai neman aiki a bankin su?

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

6 thoughts on “Siradin Rayuwa 1 | Babi Na Biyar”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×