Skip to content

Siradin Rayuwa 1 | Babi Na Goma

3.6
(24)

<< Previous

Ya saki layin unguwar Sarki, ya dauki wanda zai kai shi Gwaman Road GRA.

Ya tsaya a gida mai lamba dari da hamsin mai dauke da rufin jan kwano na zamani. Sojoji biyar ne suka bude kofar gate din cikin zafin nama yayin da direba Sam ke sulala motar mazaunin ta a hankali, tun kafin ta ida tsayawa sun bude murfin motar Oga ya fito cikin kakkarfan takun shi rungume da bebi.

Cikin su ba wanda ya furta ko umh, illa idanun Sam direba da ke cike da gulma nata walainiya cikin na abokan aikin shi. Ai kuwa Oga na matsawa ya shiga tsurkun ta masu.

“May be Oga gone crazy, ya tsinto baby a daji.”

Hajiya Nafi, ita ce uwar gidan Brigadier, gajera ce kyakkyawa mai masifar kibar hutu. Ta kawata hakoran ta biyu da hakoran Makkah na gwal masu sheki tana da yalwar idanu manya. Hutun da take ciki shi ke boye zahirin shekarun ta, amma a kalla ba a kasara ba ta baiwa talatin da takwas baya. Sanye take cikin shudiyar atamfa Super mai zanen ruwan hodar furanni da ratsin kore kadan.

Cikin sassarfa take ratsa falullukan da za su sada ta da sassan magidan da ke ta ruda ta da kira ta intercom. Mai aikinta Asbi ta tsayar da ita tana cewa.

‘Hajiya, na fa gama aikina na yau zan bulla gidan wannan ‘yar in mata sallama, kin san hutu na gobe ne zai fara ko kina da sako Sokoto? Don ni wannan hutun kusan don ke na yi shi, don kuwa na ji labarin zuwan wani sabon hatsabibin boka a Talata-Mafara, an ce aikin sa kamar yankar reza.”

Hajiya ta ce, “Ke da Allah rabu da ni, irin wannan kira na Brigadier mai barazanar fasa dodon kunne kamar an ce na yi cikin ‘ya mace?”

Asbi ta yi guda ta yi dariya ta ce, “Ai kiran ma alheri ne, kuma sai mai matsayi ake kiran, kin ji a kira wannan funkason ne?

‘Ya mace kuwa sha Allahu kin haifa kin gama don yadda Malam Arzai ya ce ba ta isa ta aje kwai a gidan nan ba, hakan ne ba kuskure.

Tun da ta ki fita don sharri, asiri da makirci ai ta fita don rashin haihuwa, kinibbbiyar yarinya kawai sai kafirar kissa kamar Bakatsina. Ai yadda ta zo ita daya haka za ta sa kafa ta fita salin-alin, sha kurumin ki Hajiya Nafi, gagara gasar mata uwar gidan Brigadier, ke daya rai da ajali, uwargida kan gidan in kin so gida ya zauna lafiya, in kin bijire gida ya hautsine, Maman Aminu mai tumbin gwal ki ba ni doller.”

Hajiya ta yi dariya, irin wannan washin na su Asbi da ire-iren su ba karamin kai yake fasa mata ba. Ta sosa keya ta gyara daurin dankwalin ta ta ci gaba da taka matattakalar da za ta sada ta da sashin maigidan tana cewa,

‘Duk kin bi kin cika ni da washin ki da bai karewa, kin hana ni amsa kiran maigidan. Jira ni in sauko komai ki ke so zan ba ki Asbi na.”

Sai safa da marwa yake a kayataccen falon rugnume da jaririn da ke ta tsala kukan wahala da yunwa, yana hura masa iska cikin kunne shi bai yarda ba lallashi yake, falon cike yake da duk wani nau’in kayan jin dadin rayuwa na zamani. Hajiya Nafi ta ja da baya.

“Subhanallah! Ran ka ya dade ina ka samo baby?”

Ya ce, ‘Samu wuri ki zauna tukunna, ai maganar ba ta ja da baya ba ce.”

“Dole in ja da baya, na san ina ka dauko shi?”

“Allah ne ya ba ni, kuma ina so kwatankwacin su Aminu, ina fata za ki ji kai, ki amshi amanar da Allah ya danka mana? Ki rike tamkar su Khalil, Nafisa, ina neman hadin kan ku kamar kullum?”

A wannan karon kam kallon shi take tamkar ta ga mahaukaci sabon kamu.

‘Daddyn su Khalil anya ka san abin da ka ke fada kuwa? Dan tsuntuwa, in rike? Ni?”

Ya juyo gaba daya da murmushin da ya san ya kan kwantar mata da hankali, domin a da ya juya mata baya ne, sanin kan shi ne ita rudaddiya ce don haka baya son ganin rudanin da fuskarta ke ciki. Ya dube ta cikin ido ya ce, ‘I know, u’ll be shocked, amma kin sani, da dai na kowa ne kuma amana a wurin mu iyaye, ban so ki ki fahimtar abin da nake nufi da gangan, wato mu yi taimakon ceton rai don Allah, ba tare da tunanin abin da gaba za ta haifar ba.”

Hajiya Nafi ta gama harzuka ta tabbatar shi mutum ne kaifi daya, tunda ya ce hakan mai raba shi da wannan jaririn da take gani shege ne sai Allah. Ta sake ja baya.

“Wallahi dan tsuntuwa ba a gida na ba, ba dai cikin tsarkakakken zuri’a ta ba. Haka kawai, muna da ‘ya’ya ba rasawa muka yi ba, daidai har goma, ka dauko mana dan tsuntuwa? Wa ya sani ma ko uwarsa shegensa ta yi ta yar don gudun abin kunya shi nemu za ka kwaso mana?”

A lokuta da dama Hajiya Nafi kan mance zuciya irin ta tsohon sojan, tsawa ya daka mata mai gigitarwa ya ce, ‘Get out! Stupid, idiot.”

Kafin ta farga kuma har ya rigata fita daga dakin, shi da ya ce ta fita, ta yi tsaki ta yarfar da hannuwa cikin kakabin yau ita Brigadier ke kira idiot abin da bai taba yi ba, shekaru daidai har ashirin da biyar sai yau a kan wannan tsintattar magen, wannan ya kara mata tsana da tsangwamar jaririn da ba ta ma san ko wane jinsi ba ne a rai.

Lallai in ta bar jaririn nan tare da shi tana shirin ganin wulakanci da tashin hankali, don shi in ya so abu ya so shi kenan, haka in ya ki shi ko duniya za ta taru a kan shi ba zai so shi ba.

“Haka kawai ina zaman – zamana a kwaso min jidali, ai sai ka kaiwa munafukar matar ka tunda dama da ita ku ke kulle-kullen munafurcin ku, sai yau don rana ta baci za a kira ni? In ma kai ka yi shegensa aka kawo ma ai in ta yi wari ma ji.” Ta yi waje fuuuu! Kamar guguwa tana kwalawa ‘yar koren ta Asbi kira.

Kishingide take cikin (3 seater) tana nazarin jaridar TIME takun shi kadai ta ji bisa marble din da ke shimfide a gidan ta san cewa shi ne, kasancewar shi, maigidan ta, Brigadier Bello Makarfi, mutum ne mai takin kansa. Duk da ya kwana biyu, kakkarfan mutum ne mai tsari, ga masifar saukin kai, musamman a cikin iyalinsa.

Ta aje numfashi da jaridar gaba daya ta maida hankalin ta ga kofar shigowa, Sanye take cikin jajayen English wears riga da siket na zaman gida, a kunnen ta jan dankunne ne na barima dan mitsitsi, ta matse gashin kanta cikin jan hair-bound sai kamshin turaren ta Sandara ke tashi a falon. Saratu Sani Makarfi kenan.

Ta mike cikin zumudi ta amshi babyn,

“Ikon Allah, Baban su Khalil baby daga ina?”

Ta kai duban ta gare shi, kyawawan idanun ta na masu bidar bayani, ‘yan bakaken lebban ta makale da lallausan murmushi.

“Allah ne Ya ba ki, short and simple.”  Ta fadada murmushin ta zuwa dariya-dariya.

“Kada ka zolaye ni da abinda har abada ba zan samu ba.”

Ta rungume babin a kirjinta idanunta suka ciko da kwallah, ya janyo ta gare shi ya ce,

‘Na taba yi miki wasa kwatankwacin wannan?” Ta girgiza kai da sauri.

‘To I mean what I said (Ina nufin abin da na ce).

“In kuwa haka ne sai in ce Allah ya biya ka da Aljannar Firdausi Baban su Khalil, very cute baby girl, (kyakkyawar jaririya). Don Allah Daddyn daga ina?”

“Daddy ko Darling?”

Ta yi murmushi ta ce, “To Darling din, Allah ji nake kaunar ta na karuwa a raina, har bana jin zan iya baiwa uwar ta, ka taimaka ka karba min riko baban su Khalil.’

Ta kwantar da kanta bisa kafadun shi kamar ta saki kuka, ya janye zuwa ga kan wayarsa da ke ta faman tsuwwa ya amsa ya ce,

“Hello.”

‘Wato Daddy ka mance da mu a school ko ka ce da Sam ya zo ya dauko mu ko?” Faisal ya ce.

“Kuma ka san yunwa ta matsa min amma ba ka damu ba ko….” Cewar Najib.

“To da ka je Kanon, ka sayo min Gurasar?” Yasir ya tambaya.

“Wai me ya same ka ne Daddyn mu? Muna ta Magana ka yi shiru. Ko Hajiyar mu ta sake bata maka rai? Faruk ya dora na shi tambaya.

“U keep silent Daddy, what’s the matter (Ka yi shiru me ke faruwa)? Inji Furkan.

“Wai ma tukunna ka bawa bindigata bullets din da na ce ka sa mata kafin in dawo?” Bello (Daddy) ya ce.

Ya yi murmushi cikin rashin gajiyawa da jerin gwanon tambayoyin su, don in akwai abin da ya saba da shi to wannan ne.

“To shin nawa zan fara amsawa ne my cuties, irin wannan tambaya haka, yaushe ku ka koma ‘yan jarida daga sojojin da na sani?”

Gaba daya suka rude, kasancewar duk suna jin sa a tare, shi ma hakan handsfree.

“Nawa-nawa za ka fara amsawa Daddy.”

“To ku yi mun uzuri my dear soldiers, Antin ku ce ‘in labour’, so ku bari in ji da zuwan our newly born baby.”

“Eho!!! Daddy Anti amarya haihuwa za ta yi? Amman mace za a haifo mana ko?”

“Ga Sam nan na turo shi ya dawo da ku in kun zo kun gani.”

Ya rufe wayar ya dubi Saratu da ke ta faman lallashin baby ya bude mata hannuwan shi duka, ta tafi da sassarfa sai kuma ta kara da gudu-gudu ta shige, ya maida ya rufe su ruf, ita da babin ya shiga rada mata cikin kunnuwanta.

“A kullum shi yasa nake dada son ki Saratu, duk abin da ni ke so kina so. In an batamin sai ki shayar da ni farin cikin da ke mantar da ni ni tsoho ne. Allah ya yi miki albarka ya kuma sakawa Baffa Sani da ya yi tunanin hada mu aure da alkhairin duniya da lahira. Wannan yarinya Allah ne ya ba mu.”

Ya kwashe duk yadda ya tsinto babin gaba daya ya fada mata har yadda su ka yi da Hajiya kafin ya shigo sashin ta ya fada mata bai rage komai ba. Ta yi salati ta kara kankame jaririyar gaba daya ta ce, “Amman Hajiya ta yi wauta, da ai na kowa ne, kuma ba ka san wanne ne zai ji kan ka ba. Ni kam Allah bai nufe ni da haihuwa ba da kai Baban su Khalil, amma na gode masa da ya kawon ta inda ban tsammani ba.

Na yi alkawarin rike yarinayr nan tsakanina da Mahaliccina ba kuma zan taba nuna mata ba ni na haife ta ba.

Abin yi yanzu shi ne ka je ka rufe bakin wanda duk ya san al’amarin don gujewa bacin rai a gaba, sai in ce Ubangiji Allah ya taya mu riko da amana.”

Ya yi mata kyakkyawar sumba ta nuna kauna da yarda, hadi da godiya mai tarin yawa. Ko a yanzu kimar amaryar shi Saratu ya dadu a idanun shi, hakan nan ya kara ba ta wani matsayi na musamman a zuciyar shi.

“Ni za ni in biyewa shirmen su Furkan, sai ku je Mother’s Delight ki hado mata duk abin da za ta bukata. Daga naira daya zuwa million na yarje miki Saratu ki je ki hado a kawo min bill din.’

Ta yi murmushin da ya fidda siririyar wushiryar ta,

“Har yanzu ban ji sunan Baby na ba?”

“Ai yanka za ai Saratu sati mai zuwa idan Allah ya kai mu, haihuwa fa muka yi, kuma haihuwar ma na ‘ya mace da muke mafarkin samu a gidan nan, kenan dole a yi shagali ko don rufe bakin mutane?”

Ta yi ‘yar dariyar ta mai ban sha’awa ta ce,

“To ai kowa ya san ba ni da ciki, the worst part din ma yadda ku kai da Hajiyar su Aminu, yi tunani?”

Ya yi dan jim,

“Idan har za ta dagawa mutane hankali ne kan abin da aka yi domin neman mafificin lada a wurin Ubangiji, wallahi sai dai ta bar gidan nan, don ba ta isa ta sani ko ta hana ni ba.”

Ta girgiza kai ta yi daki rungume da babyn ta da ta samu barci.

*****

“Magana ce nake so mu yi?”

‘Ba ni da lokaci.”

“To ki aro, ki karkade kunnuwan ki ki ji ni. Dukkanin mu ba yaro a nan, kuma na yi zaton shekarun ki da tunanin ki ya isa ki zama mutum, amma kina halin dabbobi.”

Ta gwalo ido cikin mamaki, “Yau ni ka ke kira dabba Baban su Khalil, a kan tsintacciyar ‘yar ka?”

‘Ni ban ce miki dabba ba, na ce ne kina irin halin su na rashin tunani. To ki ji ba da wai ba, ranar da duk ki ka bude baki ki ka furtawa wani yarinyar nan ba ‘yata ba ce, tsinto ta na yi, babu igiyar aure ko daya a tsakanin mu.”

Ta fashe da kuka,

“Au! Ci min mutunci za a yi saboda ka je ta tsafe ka shi ne za a tozarta ni? Ba ka cewa ka sake nin kai tsaye?”

Ya juya zai fita ta sha gaban sa fuskar nan jage-jage da hawaye, “Na ji ba zan fada ba, amma ina fada ma gaskiya, ba ruwana da yarinyar nan, na tsane ta, Allah tun ranar da ka kawo ta, na fada na kara.”

‘Wannan kuma matsalar ki ce, gafara nan ban hanya in wuce tun ban babballa ki ba.”

‘Ai ban gama ba ne, mijin karuwa, kada shegiyar ‘yar ku ta sake ta shiga sabgar halatattun ‘ya’yana.” Ya nuna ta da dan manunin sa ya ce,

“Nafisa, ke Nafisa ki fitar min a ido in rufe. In ki ka kara kira min mata karuwa, za ki dandana kudar ki, karuwanci har aka fi ki? Ko ba kina karuwancin na aure ki ba?

‘Ya’ya kuwa ‘ya’yana ne babu fitinanniyar da ta isa ta raba mini kan su. Kin san tsintsiya ko? To haka zan maida su. Ki kiyaye zugugun bakin nan naki.”

To kwana biyu dai suna badakala da yin ta ba dadi da maigidan. Ta dai tabbatar Brigadier gab yake da ya guntile tsohon auren su a kan shegiyar jaririyar shi. Yinin ranar zungur kukan bakin ciki ta wuni yi musamman da ya kori ‘yar koren ta Asbi ya ce kuma ko gaisuwa ta sake yi da matar shi sai ya harbe ta ya ba ungulu naman ta, don ya lura sun kukkulla munafurcin su da suka saba. Sam direba da sauran sojojin da ke aiki a karkashin sa duk ya tura su Lagos ya dauko wasu sababbi daga Porthacourt. Brigadier Bello Makarfi kenan, namiji saura mazan jiya, hadari sa gaban ka, guguwa mai fyade wanda ta so, sojan arewa mai watsa shashashai. Wannan ne kirarin sa.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

3 thoughts on “Siradin Rayuwa 1 | Babi Na Goma”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×