Skip to content

Siradin Rayuwa 1 | Babi Na Sha Biyu

3.3
(18)

<< Previous

Cikin ‘ya’yan Hajiya Nafi kaf, Aminu ne ya debo halin ta na keta da kekasashshiyar zuciya. Da ta lura shi ne kadai mai taya ta kishin su Saratu, mai kuma son duk abin da take so, duk yaranta sun tare a gindin Anti Saratu sai ta shiga zuga shi ya ki Saratu karama, ya kuma dinga gana mata azaba a boye. Dama kuma duk cikin yaran gidan kaf ba maras kirki irin Aminu, amma Daddyn bai ganewa, wannan ya samo asali ne da kasancewar Aminu lumbu-lumbu wutar kaikai, sunkuru macijin sari ka noke, a fuska Musa a zuci Fir’auna, don a fuska mutumin kirki ne.

Daddy na son Aminu ne saboda hazakar sa wanda kullum cikin dauko kyaututtuka yake a makaranta, bai taba yin na biyu ba a gaba dayan shekarun sa na sakandire. Hakan nan Aminu na da shiga ran iyaye da sauran jama’ar duniya ma baki daya. Shi kan sa ya san shi kyakkyawa ne, wannan na sa shi kara homa cikin tsararrakin shi duk da haka yana masifar gudun bacin ran Daddynsu.

Shekarun Intisar uku cif, amma hikima da basirarta sun fi karfin shekarun ta, ko kadan ba ta da wayo sai dauke abinda duk aka koyar da ita nan take, don haka Aunty Saratu ta tuntubi Daddy da shawarar ya dace a sanya ta ajin rainon yara.

A lokacin an yi posting din Daddyn jihar Lagos dukkan su sun tare a sabon gidan su da ke Victoria Island, wani azababben gini da Daddyn ya yi shekaru yana zubawa kamar ba ba za a mutu ba. Faisal ne ya kawo shawarar a kai baby Intisar Links International School, makarantar rainon yara da wata Baturiya mutuniyar Russia ta zo ta bude a Lagos. Satin baby kwata-kwata hudu a Links shugabar makarantar ta zo ta samu Daddy a ofis, bayan sun gaisa ta ce ita shugabar makarantar da yarinyar shi Saratu ke karatu ne, ya ce, ‘O.k, Links ko?”

Amma can a karkashin zuciyar shi cike yake da tunanin ko laifin me? Saratu ‘yar shekaru uku da doriya kacal a duniya ta yi? Matar ta ce,

“Wato abin da ya kawo ni shi ne in shawarce ka, gaskiya basira irin ta yarinyar ku ya wuce nursery, don haka na kawo ma shawarar in da hali kawai a kai ta (primary 2) a Turkish da aka bude kwanan nan, sai dai makarantar akwai tsada, amma I’m sure, Saratu za ta sami sound background (tushe na kyakkyawan ilimi) a gaba.”

A nan ne Daddyn ya ja numfashi ya kuma saki murmushin jin dadi,

“Ku kai Saratu duk makarantar da ku ke ganin ta dace da ita. Kada ku dama da kudi, daga naira daya har million zan biya, ni dai burina kasar mu ta amfana da ilimin ‘ya’yana.”

Baby Intisar na aji uku a Turkish, amma fasaharta da kwazon ta kan ba malamanta tsoro. Ba ta da magana ko kadan sai tsabar karatu a cikin kanta tamkar wadda ake wankewa kwakwalwa da ruwan zam-zam. Kyawun ta kadai ya isa yasa mutum ya so ko da ya ki Allah. Sai kuma aka yi sa’a ya hadu da ‘yar gayun uwa; Aunty Saratu kullum cikin wanki da gyaran sumar Intisar take da mayuka masu kyau da tsada, don haka ne kullum za ka ga kan yarinyar yana wani sheki da kamshi, baki sidik kuma a kanannade (curl). Fara ce sol, siraran labban ta jazur da su, hancin ta matsakaici tamkar ansa ruler an ja shi an daidai ta shi a tsakanin idanunta.

Wasu irin lumsassun idanu kullum kamar tana jin barci, fasalin su na ‘ya’yan itacen Almond (Almond eyes). Akwai tawwadar Allah a gefen hancinta na dama. Shape din fuskar ta oval (Tamkar zanen kwai), akwai gazar-gazar gashin gira, yalwatacciyar suma ta Fulanin usli, ga kyawawan yatsun kafa da hannu Tubarkallah.

A kullum shakuwa mai tsanani na kra shiga tsakanin ta da yaran gidan musamman Faisal da Khalil da yake kusan tsaran ta.

Rannan Antin na ofis aka sanar da ita tana da baki kafin ta yi masu izinin shigowa kasancewar ta nemi (transfer) zuwa nan Lagos, suka gaisa, sai suka ce su Malaman su Saratu ne, sun zo ne kurum su ga Mamar ta, su gaya mata Allah yai mata baiwa da ya bata ‘ya kamar Saratu.

Aunty Saratu sai ta yi dariya, wannan complain (korafi) na jama’a ba yau ta fara jin sa ba, tun ranar da ta soma fita da Saratu mutane suka gan ta. Ta tambayi sunan su, dayan ya ce suna shi Mr. Victor shi ke koyar da Saratu lissafi. Dayar Mrs. Risikat malamar Turancin su Saratu ce. Tohaka ko kanti suka shiga sai an ba baby sweets zuwa biscuits an ce da Anti Saratu ana son ‘yar ta.

Rannan Faisal ya ce, “Anti amarya ba za ki wa baby layar baki irin wanda Hajiyar mu ke mana ba in zamu shiga mutane?”

Maganar Faisal ta ba ta tsoro. Don haka a washegari Makarfi suka yi sallar Azahar ta kwashe abinda Faisal ya ce ta gayawa Baffa. Baffan ya ce, Faisal ya yi tunani, kuma tsari tun yanzu zai soma yi wa Saratu.

A wannan shekarar ne Aminu ya kammala karatun shi na sakandire a FGC Abuja, with flying colours (da sakamako mai ban mamaki). Aminu ya sha albarka a wurin Daddy, gata kuma ya karu sai abin da ya ga dama yake yi a gidan.

A falon Hajiya ake hirar wai budurwar Ya Aminun, Bose ‘yar yarbawa Aminun ya kai mata katunan happy-Xmas masu kyau. Yasir ke baiwa Hajiyar labari, ta fusata ta ce, “Kai ina ka san Bosen?”

Ya sosa keya yana dariya ya ce,

“Ki rufa min asiri Hajiya, Allah in Daddy ya ji harbe ni zai yi, kin san Allah kanwar abokina David ne, in suka zo masa visiting sai ta yi ta kawon kaya wai tana sona, ‘yar wannan General Benga Delsun abokin Daddy da suka shirya coup (juyi mulki), a shekarar baya suka fasa?”

Hajiya ta kwabe baki ta ce,

“Kai nan har ka isa yin budurwa dan nan, oh, duniya ina za ki da mu?”

Ya yi murmushin da ke lotsa gefen bakin shi na hagu (beauty point), ya kuma lotsa tsakiyar habar shi (cleave).

“Kai Hajiya, ita har ta isa in yi budurwa da ita? Ba ki gan ta ba fa baka mummuna, ga warin Yarbawa, romantic eyes din ta kawai nake so.”

Hajiya ta yi salati yayin da gaba daya yaran suka kwashe da dariya, ta ce,

“Miko min wayar can Faruk ka gani, in zane dan banzan nan.”

Ya mike yana murmushi ya ce, ‘Fada kawai ki ke Hajiya ta, amma na san ba za ki iya ba, ni din Al’ameen dan Hajiyarsa?”

Faisal ne ya shigo rike da hannun kanwarsa Intisar da ta ci ado har ta gaji, sanye take da ruwan bular riga da siket din jeans, gashin kanta an yi kananun kalba an makalkale su da kyawawan ribbons kala-kala. Faisal ya ce,

“Ya Aminu ka je in ji Daddy yana falon Anti Amarya.”

Aminu ya mike ya tura hannuwan shi aljihu, ya dube shi cikin haushi ya ce,

“Kai dai la’ananne ne, kullum kana gindin wadannan miyagun ko? Ko da yake na san ba laifin ka ba ne, ba mamaki kai ma an kai sunan ka wurin mai buzun nan na Makarfi.”

Hajiya ta tuntsire da dariya, amma su yaran hankalin- su bai kai su gane ko da wa yake ba, ya mikawa baby hannu ya ce,

“Come on beautiful baby.”  Sai ta saki hannun Faisal ta tafi gare shi cikin yaukin ta na halitta, don wannan kira ne da ba mai yi mata sai Daddyn ta, kira ne da Daddyn ta ke mata.

Ya kalli Hajiya suka kifta ido, (za a yi mugunta kenan), ya dauke ta cancaras kamar ya dau kofin shayi, Hajiyar na cewa,

“Kai dai Yayan kobo ne, kawo min babyn nan, kai Faisal je ka ce masa yana zuwa.”

Ya juya jikinsa a sanyaye cike da rashin jin dadin barin baby tare da su, don azaba tun tana rarrafe Aminu ke gana mata kala-kala, amma ta ki ta gane ta guje shi, sam-sam ba ta da wayo, yanzu ne za a mata abu yanzun ne za ta manta in har ba karatu ba ne.

Aminu ya yi hanyar kicin din Hajiya dauke da baby a kafadun shi ya fiddo markadadden tattasai danye cikin firji ya cika kofi ya bude bakinta ya shiga dura mata bayan ya daura ta a saman deep freezer din tana ihu tana zillo, hawaye ya hade da majina shi ko cewa yake.

“Sha maza beautiful baby, ko kya koyi magana, pepper soup ne.” Sai da ya dure mata tattasan nan duk a cikinta, ya cika ruwan kankara a cup ya sake dura mata, ya wanke mata baki tas, ya sake ta a kasa sai ta fadi talau, ya yi dariya ya kama gabansa.

Faisal ya koma daukar baby, ba kowa a falon sai Hajiyar, ya ce, “Hajiya ina kanwata?”

Ta ce cikin halin ko in kula,

“Nan na ga ta yi hanyar kicin.”

Duk da shekarun Faisal a lokacin ya san mahaifiyarsa bata kaunar Intissar yadda ba ta kaunar mutuwar ta. Ya kan tambayi kansa ko me yarinya karama kamar wannan ke mata? A guje yake kiran Intisar har kicin, abin tausayi, sai ya gan ta kwance bisa tiles din kicin din idanun ta a rufe tana fidda wani irin miyau tsinkakke, ba alamun barci take ko idon ta biyu sai wani irin nannauyan numfashi take a wahale, ya sungume ta ya sa a bayan shi yana gudu har yana faduwa ya nufi sashin Anti Amarya.

Yana kuka yace, ‘Anti Intisar ta mutu! Ban san me ta ci a kicin din Hajiya ba.”

Antin ta amsheta ta tabbatar ba mutuwa ta yi ba, sai dai jikin ta da ya yi wani irin jagab, kamar an yi mata duka. Ta yafa mayafi ta fito ta kira direba ya  kai su wani private hospital nan kusa da su.

To likita ya yi wa baby allura ta amayar da tattasai tsurar sa, ya basu gado don ta huta, nan Daddyn ya isko su Aminu na biye da shi, ya tambayi abinda ya faru da Saratun, Antyn na share hawayen da suka cika mata ido ta ce,

‘Oho ni na kasa gane wannan abu! Na ke jin firji ta bude ta sha ruwa kuma ta sha tattasai? Amma a shekarun baby duk da ba ta magana da kowa, ya isa a ce ta san ruwa wallahi, koma wa ya ba ta ai Allah yana gani.”

Aminu ya kau da kai, shi ko Daddy bai ce komai ba, don bai san ma me zai ce din ba. Ya tabbata duk cikin ‘ya’yansa babu mai kin Saratu sai ko uwar su, ita din ma yanzu ba ta nunawa, abin da ya dauka kawai ko dai baby ta dauka lemu ne kawai. Wannan ta wuce.

Rannan direban yara bai zo ba har bakwai da rabi ga shi ranar Litinin ce, Hajiya ta iske Daddy tana ta fada wai Emma bai zo ba yara duk sun matsu su tafi kar a duke su, to saboda baya son mitar ta ya kira Aminu ta wayar hannun shi ya ce ya kai yara makaranta.

Sauran yara na baya, Khalil da Intisar na gaba, kan ka ce me ye wannan fada ya kaure tsakanin Khalil da Intisar wai sai ya biya ta littafin ta da ya cika da zanen biro. Aminu ya cire lafiyayyen hannun shi ji ka ke kau! Ya wanke ta da marin da ba a taba yi mata ba, ya ce,

“Ko uwar ki ba ta isa ta yi surutu ina tuki ba.”

Ta gigice ta sa kuka da karfin gaske, ya ce, ‘Lalala! Ki yi min shiru, shegiyi mai zakin muryar tsiya.” Ba ta yi shirun ba sai ma kara tsananta kukan ta har da ihu, ya kai hannun shi na dama ya ciro ta daga mazaunin ta, na hagun kuwa yana murza steering wheel cikin gwaninta, ya tura ta inda yasa kafafun shi, idan ya taka totur ita ma ya taka ta, duk yaran suka yi tsit kamar ruwa ya cinye su cikin kaduwa.

Faisal kuwa da ba zai iya jurewa ba tuni ya soma yi wa Ya Aminun kuka ya daga Intisar kar ta mutu, sai da suka zo makarantar ya kashe motar, ya juyo ya dube su ya fiddo manyan idanun shi ya ce, ‘In ji wani mai tsautsayi cikin ku ya ce na mari Intisar ko na yi mata wani abu, uhn, sai na babballa yaro, ya kuma yi kwanan store Bismillah.”

Yana fadi yana hada kan Faisal da Bello yana gwarawa don wai su ne manyan munafukai, gaba daya suka sa kuka har wadanda ba a daka ba, ya ce, ‘To ku yi shiru, ai in ba ku fada ba ba zan saku a store ba.”

Duk suka yi shiru, ya ciro ta fuskar nan ta yi suntum da kuka ya zaunar ta cinyar Faisal ya ce, ‘Lashe hawayen ki I said!” Da sauri ta sa harshe tana zukewa. Ya bude masu kofa suka fice, ita ko baby kafa yasa ya cillo ta ya ja motar shi ya tafi.

Ranar wata Alhamis Malamin Islamiyyar su ya zo, duk suka fice har sun fara daukar darasi, ita ko baby ta make a bakin kofa ba ta tafi ba tana so su gama ficewa ta sha majinar ta ta koshi tukun, ta yi can hanyar baskwata ta soma fyace majinar a hannun ta tana lashewa tana kuma zakulo tasono tana dannawa a baki kamar an ce da ita juya can, sai ta hangi Aminu tsaye jikin balcony (baranda) yana zukar sigari abin shi yana danna waya, ta saki baki galala! Don ta sha jin Daddy yana yi wa su Faisal hudubar cewa duk mai shan sigari dan iska ne, kuma cikin su duk wanda ya sha sigari ba shi ba shi. Jikinta ya yi sanyi lumus, yau ga dan iska ta gani a zahiri.

Jikin shi ne ya ba shi wata kila ana kallon shi ya juyo da sauri suka hada ido, ta juya za ta gudu kafin ta yi taku uku ya danko ta ya ce,

‘Wai ke munafuka ko, au majinar taki ki ka zo sha to yau kuwa za ki dandana kudar ki, kin zo ganina ina shan rothman ko?’

Cikin kuka ta ce, ‘Allah ni majina na zo sha.” Iyakar firgita ta firgita da shi ya kama kunnuwanta ya murde da karfi ya manna mata wani azababben mintsini a wuya ta kara tsananta kukanta, ya ce,

‘Ina shan rothman?”

Cikin gigicewa Ta ce, ‘Eh.’ Ya shiga daldalle mata baki da yatsun shi biyu, da karfi ta ce, ‘A’a, ban gani ba Ya Aminu.”

Ya sassauta rikon da ya yi mata ya ce,

‘Daga yau na sake ganin ki kina lasar majinar nan sai na yanke hancin kowa ya huta, kazamar banza mai shan majina. Wane yaro ki ka gani yana shan majina a gidan nan ko don ke uwarki ‘yar kauye ce, za ku taru ku mayar mana da gida matattarar ‘yan kauye.’

Ta ce, ‘Allah ba zan sake ba.” Ya sake cewa, ‘Kin gan ni ina shan Rothman?”

Ta ce, ‘Allah ban gani ba.”

Muryar ta har ba ta fita saboda kuka da razana. Ya yi murmushi ya sakar mata kunnen ya ce, ‘Tafi wurin malam.”

Ai tun kafin ya karasa rufe bakinsa har ta kusa kaiwa, ya yi dariya ya shige cikin gida yana baiwa Hajiya labari, a fusace ta ce,

“NI da Allah rabu da ni, tun yaushe na hana ka shan tabar nan, in ba zaka bari don komai ba ai ka bari don lafiyarka, tunda aka fara haka wata ran ai Daddyn da kanshi zai kamaka, na kuma tabbatar maka duk ranar da hakan ta faru ba kai kadai ba har ni uwarka sai mun kasa kurbar ruwa a gidan nan, me ye amfanin taba ga rayuwar dan Musulmi ban da cutarwa, wallahi ko bayan raina ka kara shan taba ban yafe maka ba!.”

Yasa hannu ya dafe kai ya ce, “Haba my dear Mum, ki ji tausayina, ki janye wannan furucin naki a kaina, Aminun ki ne fa, insha Allah daga yau na daina amma ki sa mun albarka.”

Ta yi murmushi ta ce,

“Ai don ka san lagona ne, to Allah ya yi maka albarka.”

Aminu ke koya masu assignment amma baby tana kwance jikin Mamarta ta ki tashi, ta dube ta, ‘Baby yau ba ki da assignment ne?’

Ta ce, ‘Eh.’ A dan tsorace don ba ta saba karya ba. Antin ta lura karatun ne yau ba ta so, ta ji ba dadi a ranta, ta shiga daki ta bude jakar ta ta fiddo littafin Maths din ta da yake shi aka fi ba su aikin gida, ta ga aiki na jiya da na yau duk ba ta yi ba, ta fito rike da littafin a hannunta ta ce,

“Babyna, me yasa yau ki ka yi min karya?”

Duk ta dabarbarce, umh, ita kadai ta san azabar da Ya Aminu ke gana mata wajen koyar da karatun nan, duk magana daya ya falla mata ‘ya’yan carbin karfe wai ta fiya jakanci, bayan kuma har ga Allah tafi Khalil fahimtar karatun, amma shi baya dukan shi,ta yi shiru ba ta ce komai ba sai da ta kara tambayarta a karo na biyu, sannan ta ce,

“Ki yi hakuri Mamana, cikina ne yake ciwo.”

Ta ce, ‘To ba sai ki fada min baby na in ba ki magani, sai ki yi shiru ki zauna ciki yana ciwo? Abinci ma ba ki ci sosai ba ya za ai ciki ba zai ciwo ba, tashi maza ki ci sausage rolls din ki ne na yi miki ki tafi wurin Ya Aminu karatu, ko kina son gobe Anti Magret ta buge ki?”

Ta girgiza kai, ba da son ranta ba ta ci kadan ta dan kurbi ruwa ta dau littafin ta da fensir ta tafi babban falo inda ake karatun.

Abin da ta fara ji da shigar ta shi ne.

“Kin yi latti, kazama mai shan majina, kneel down”. Ta shagwargwabe fuska tana duban Faisal tamkar mai neman taimako, ya rausayar mata da kai shi ma kamar ya yi kukan alamar su duka zai doke su. Ya ce cikin tsawar da ta sa ta sakin dan fitsarin da ya fara tarar mata.

“Ur hands up, ur kneels down?”  Wato ta tsugunna a kan gwiwoyinta ta daga hannuwanta sama, ta yi yadda ya ce don tsira da lafiyar ta, amma duk da hakan ba ta tsiran ba, ya tsula mata carbi ya ce in ta yi kuka mai sauti sai ya ci uwar ta, ta kunshe baki, kuka kamar ya kashe ta, duk yaran jikin su ya soma rawa, don idan ya soma dukan mutum daya to kowa ma sai abin ya shafe shi, suka ci gaba da karatun a haka duk suna tsorace da shi, sai da ya ga dama ya ce ta zo ta zauna ta yi nata.

Yana nuna mata tana shan tsala, to kuka bai bar ta ta gane komai ba, sai ya zuba mata rankwashi kwaf, a tsakiyar ka ya ce,

“Uwar ki ne ta ce da ke tara a tara da daya sha biyar (9 +1 = 15)?” Ta nutsu, ta hada daidai, ya ce “To ko ke fa, daga yau ki ka sake kuskuren lamba ko daya ba zan gyara miki ba sai dai in dura miki fitsarin Bombino.” (Bombino sunan karen da yake kiwo kenan). Da haka karatun ya kare. 

Next >>

How many stars will you give this story?

Click to rate it!

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Share the story on social media.

3 thoughts on “Siradin Rayuwa 1 | Babi Na Sha Biyu”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.