Skip to content
Part 3 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Makarfi

Hakan nan yana son ya je ya gaida surukan shi a Garki, ya yi masu wata kyauta mai daraja ba don komai ba sai don neman albarka, duk da hararar gefen idon da ya ga ana yi masa duk da cewa he did not care, wai sai ya shiga yi wa kansa dariya, da ya ce zai kai wa iyayen Ihsan abu don neman albarka. To albarkar Kiristin zai nema?

Ya yi saurin cewa a’a na uban da yake Musulmi, kuma mutumin kirki a bakin kowa.

Akwai kuma muhimman kayayyakin su da suka taho da su musamman motocin su zai je port da airport ya fitar da su. Ya san idan ya fita yau sai Allah, don haka akwai bukatar ya yi kyakkyawan break-fast da abinci mai nauyi don shi ba ya jure yunwa sam.

Kafarsa ko takalmi babu yana tafe yana magana da Ihsan din shi tana gaya masa yadda ta yi missing din shi ne a daren jiya, tana kuma tambayarsa ko how much did he missed her?  Sai ya kada harshe ya ce, “Wai ke Ihsan kin yi murna da ganin Ann, da ki ka dame ni da mu zo ki gani? Ni ko sai na ga you are not happy as I am, don ni jiya har sha biyun dare ina tare da Hajiyana, muna hirar da for so long ba mu samu mun yi ba. Ina na tuna da wata soyayyar ki can?”

Ta ce, “Ya yi kyau, ai ni dama kullum mantawa nake ni ke son Al’ameen, ni na damu da shi, ni kadai ke kaunar shi, amma duk kokarina bana burge shi, so ka yi hakuri.”

Da haka ta katse layin, ko ba ta fada ba ya san ranta ya baci, shi ko sai ya yi murmushi ya ce, “Allah Sarki, nima ina son ki, damu ne ba na so, ko karyawa ban yi ba.” Sai ya bai wa kansa dariya a karo na biyu, lallai kam duk girman mutum a gaban iyayensa ashe yaro yake komawa, ko kuma don ya dade baya tare da su ne? Oho. Yadda kyawawan fararen kafafunsa ke mannewa bisa marbles ma kadai abin sha’awa ne, to haka his gait, his geniusness and his coolness ke da daukar hankali.

Wata yarinya ce fara, irin farin nan da ke da jaja-jaja wanda Bahaushen tsantsa baya mallakarsa, doguwa sambaleliya tamkar kirar matan Seirraleone. Fuskar ta oval shape, mai wadace da kayataccen dogon karan hanci, tamkar ansa ruler, an ja shi an daidaita shi a tsakanin idanun ta. Idanuwan ta kadai sun isa su sa mutum ya so ta ko da ya ki Allah (Almond-Eyes). Girar idonta gazar-gazar kuma kakkaura siririya, bakinta dan surut jazur da shi mai matukar daukar hankali, yatsun ta na kafa da hannu zara-zara masu matukar taushi da kyan tsari, tamkar ba na ‘yar aiki ba.

Sumar kanta yalwatacciya ta Fulanin usli nannade take kamar gammo duk ta wani irin mummurde alamun rabon da a taje ta har an manta, sanye take cikin wata zulumbuwar riga ja mara ado wadda a kullum suke cikin dattin kitchen, duk inda kyakkyawar mace mai fasali take to wannan yarinya ta isa har ta wuce. A ransa ya ce, ‘Kai Allah ya yi halitta tamkar Hurul’eeni???”

Ya yi sallama har sau uku, amma yarinyar a zuci ta amsa ko dagowa ba ta yi ba balle ta ga waye mai sallamar, illa zuciyar ta cike da jin dadin yau an yi mata sallama sabanin da da duka ko zagi ke mata sallama.

Hakan nan wannan wata murya ce da ake kira ‘husky” da ba duk maza Allah ya mallakawa ba sai ko wadanda suka amsa sunansu ba ‘muna-maza’ ba. Murya ce mai shigen ta Ya Faisal, sai dai wannan akwai alamun sense of humour wato raha tamkar ta Daddy, ba ta raba daya biyun Yasir ko Nasir ne oho, ita yanzu ko a lahira ta ga ‘ya’yan Hajiya ba ta fatan Allah ya ba ta ikon kula su.

To Al’ameen sai ya dauka ko ba ta ji ne kwata-kwata, ya kai hannu ya kwankwasa lockers din kichin din da karfi, ta dago a dan razane. Ta so ganin mamallakin wannan murya mai sanyawa mace kasala ba tare da ta ga mamallakinta ba, ta so ganin mamallakin wannan ni’imtaccen kamshi da ba ta taba ji ba a rayuwarta, sai suka yi ido biyu da mutumin da ba ta sani ba ba ta taba gani ba.

Babu abinda ya firgita ta kamar kwarjini da cikar zati irin na Al’ameen wanda hakan ya janyo mata gigicewa tare da mance abinda take yi, wani matsanancin tsoronsa ne ya kama ta, tsammani take Hajiya ce ta turo shi ya sa mata shocking din da ta ce za ta sanya mata in ba ta kammalawa bakonta karin kumallo da wuri ba a safiyar yau.

Tuni ta karasa rudewa ta rikirkice ta soma matso kwallah ta ci gaba da firar jibgin dankalin turawan da ke gabanta fiye da bokiti guda tana ferewa da dukkan karfinta da iyakacin saurin da za ta iya sai shap! Ta zaftare tsokar dan yatsan ta jini ya soma fita a guje, amma ba ta kula ba sam, aikin ta ta dage da yi. Aminu ya kama kai, ya karaso gabanta ya rusuna ya kama hannun ta mai rike da wukar ya ce, ‘Ke ba kya ganin kin yanke ne?”

Maimakon ta bari, sai ma ta kara daukar dankalin da ya subuce a lokaci guda kuma tana kici-kicin kwace hannunta daga hannunsa ya ce, “Ki yi hakuri in tsayar miki da jinin?”

Ta dago a hankali ta dube shi, to shi ma din kallon ta yake, suka yi wa juna kuri da ido; wani chemistry  ya shiga aiki cikin ‘yan mintocin da ba su gaza uku ba, ita ta fara kawar da kai, ya mike ya fita da sauri yayin da ita kuma ta yi jigum ta na duban yatsanta da ke ta bulbular da jini ta ce a ranta wannan wane irin mutum ne he is so caring.

Ya dawo rike da dan karamin First-aid bod cikin nutsuwa ya wanke mata yatsan da ruwan hydrogen tas babu ko kwayar jini, ya shafa iodine don azabar shi sai tasa kuka, yasa plasta karama ya nade yatsan, ya tsani ya ga mace tana kuka. Ya sarke yatsun su cikin na juna ya ce cikin tattausar muryar shi.

‘Ki yi hakuri, duk ni na jawo miki, don haka tafi daki, ni zan karasa miki.”

Ta share hawayen ta da gefen rigar ta iodine na mata radadi da zugi, amma tausassan yatsun Al’ameen sun tsare komai. Da ya ga ta yi shiru da kukan da take sai ya zare hannunsa ya shiga aikin dankalin nan tukuru cikin dan lokaci ya gama ya zuba a katoton fraying fan da ke tafasar da mai ya soye shi tas, haka ya shiga hada kowanne kwai da dan uwansa ji ka ke kas! Sai ya juye cikin babbar silver nan da nan ya soye shi fes. Tuni ta kammala ragowar kananan aiyukan kamar su zuba ruwan zafi a filas da jera komai bisa faranti.

Ya dauki plate mai tsabta, ya debi abinda zai yi masa ya dau cokali fork ya aza bisa ya juya ya fita, har ya kai bakin kofa sai ya dawo ya dube ta ya ce“Ke daga yau in kin gan ni kar ki sake firgita, don bana satar yara, hakan nan al’adana ne shiga kicin, don haka in ki ka sake yankewa ba ruwana.”

Bai fita ba sai da ya bi Hajiya sassan ta suka gaisa, Daddyn bai fito ba don haka ya zauna zaman jiransa a falon gidan har ya gama. Shi ya sauke Daddyn a ofis yau kana ya wuce ya kama harkokin gabansa zuciyarsa cike fal da tausayin ‘yar aikin Hajiya, ya yi mamakin yadda kyakkyawar yarinya kamar ta da daga gani ta fito ne daga gidan hutu ke aikin wahala irin wannan.

Idanuwanta kadai sun ishi kowanne irin namiji yanga da ita a matsayin mata. Ya alkawartawa ransa matsar ta ya ji dalilinta na wannan aikin wahalar duk da ya lura yarinyar ba ta son magana da kowa to shi dole ta yi masa.

A Makarfi gidan Baffansu ya tadda kannensa su Najib sun zo suma, nan gidan Baffan ya kaure da murnar ganin Ya Aminu. Ya dade rike da kyakkyawar babyn ta Zarah, yana kallon ikon Allah don kamar su da Faisal har ya yi yawa (Zahara ce autarsu ‘yar amaryar babansu da ya saki). Ya ce, “Anty ko za ki ba Ihsan rikon Zarah don Allah.”

Shi Al’ameen bai da masaniyar rabuwar Antin da Daddyn shi ya dauka wankan jegon dai take kamar yadda Hajiyar su ta gaya masa, sai ta murmusa ta ce, ‘Ban ga Ihsan ba, amma tunda na san a America aka aurota ba za ta so rikon dan da ba nata ba.”

Ya yi murmushi ya ce, “Amma za ki ba Intisar?”

Ta ce, ‘Idan mijin da ta aura na kirki ne ba?”

Da haka ta kashe zancen, ta lura Al’ameen bako ne kawai daga Miami, bi ma’ana bai san komai ba cikin al’amuran da suka faru cikin rayuwarsu.

Ba yadda Al’ameen bai yi da ‘yan uwansa sa ba kan su tafi Abuja tare, amma sun kiya wai a cewar su tafiyar dare za su yi wa Enugu.

Abinda ya lura dukkanin su bakin su daya har Antin suna boye masa wani muhimmin abin da ke damun su ba sa so ya sani, ko ma meye. ai in ta yi wari zai ji ne tunda yana nan a kasar ba inda za shi. Ya kyale su da alkawarin har Enugu zai kai masu Ihsan.

Wurin karfe goma na dare ya koma gida, a daidai lokacin Daddy na kokarin hawa sama shi kuma yana kokarin sauka, sai suka yi kacibus, dukkanin su suka yi wa juna murmushi mai cike da kauna irin ta da da mahaifi.

Daddyn ya ce, “Ina ka yi ne Aminu tun safe ko gama hutawa ba ka yi ba?”

Ya ce, “Masu cinikin fili man ke ta min yawo da hankali, amma yanzu mun daidaita da wani a Addis-Ababa Crescent.”

Daddy ya ce,

“Abin da nake gani ya fi kawai ku yi amfani da gidana da ke ‘Colorado Close’, don ba mutunci ba ne abar yarinya a gidan su har sai an gama ginin, gobe in Allah ya kai mu za ni mu gana da shi Dr. Argungu, don dama mun san juna sai dai ban taba tsammanin za ka hadu da ‘yarsa ba ma balle har mu zama daya.”

Ya dan murmushi kadan, don ya lura su dai su Daddy suna son auren nan nasa ko don cikin samarin ‘ya’yansu kaf babu wanda ya yi auren fari ne? Bai sani ba. Daddyn ya kuma cewa, ‘Mun daidaita da kamfanin Julius Berger da za su yi ma ginin tun safe in ka samu filin?”

Ya ce, ‘A’a a sallame su kawai don tuni na yi magana ta komfuta da kamfanin da ke yi min gini a Miami, ina son aikin su sosai, za su zo su cikin dan lokaci kankani za su zuba komai.”

Ya ce, “Babu damuwa, duk yadda ka ke son haka za a yi.”

Al’ameen har ya juya ya dawo yana sosa kai ya ce, “Af Daddy, na je fa Makarfi?”

Ya dawo shi ma da dukkan attention dinsa gare sa cikin sanyin jiki ya ce, “Yaya ka baro su, suna lafiya ko?”

Ya ce, “Kowa lafiya, Zahrah ta yi girma da wayo sosai, shin sai yaushe za su dawo ne?’

Daddyn ya lura sam Al’amin bai san ya rabu da Aunty Saratu ba, ga shi shi kan sa a lokacin babu abin da ke damunsa kaman, shin wai ma ya a kai ya saki Saratu? Me ta yi masa? Iyaka tunaninsa ba ya ce ba, bai sani ba. Kuma wai har Intissar ta tafi, amma ya kasa wani abu a kai? Ya ce cikin jin nauyi.

“Al’ameen na fa rabu da Saratu, amma gobe insha Allah ka raka ni biko, shi kenan? Allah ni kaina bana ce ga actual sabanin da ya faru ba, wanda kwata-kwata bai taba faruwa ba.”

Al’ameen ya yi shiru ba don komai ba sai don tausayin mahaifin shi da ya lullube shi, ya san irin wannan nadamar, ai shi zai gayawa kowa nadama mara amfani, to amma me yasa Hajiya ta boye masa komai? Ba mamaki don ba ta son duk wani abu da ya shafi Saratu, ta kuma san a wannan lokacin ba zai goyi baya ba, to ko Intisar da ke Riyadh ta san wannan?

Ya ce, ‘Ba komai Dady, haka Allah ya tsara, amma insha Allah komai zai daidaita, don ni Aunty Saratu ba ta min komai ba, heart and soul  (Baka da zuci) kamar da, sannan in na sami lokaci zan je Riyadh in ga Saratu karama (Intisar).”

Daddyn ya ce, “Au! Ta koma makarantar ne?”

Ya ce, “Hakan dai aka ce da ni”

“In za ka din, sai ka yi min magana mu tafi tare, rabon da in sa Saratu a idona tun ranar da Saratu babba ta bar gidan nan.”

Da wannan Al’ameen ya kwanta, al’amura, ya rasa da wanne ma zai fara, tabbas ran Hajiya zai sosu in ta ji har da shi aka je mata bikon kishiya, bikon ma na mutanen da ta ki jini fiye da mutuwarta, to amma wannan ba zai hana shi gyara sunnah ba. Shi kawai hakan nan ya ke kaunar Anty Saratun saboda yakanar ta da abin da ya yi masu na rashin kyautawa can baya, amma ba ta damu ba, ba ta kullace shi ba, kai ko a fuska ba ta taba nuna masa ta san abin da yake ciki ba. Uwa-uba karin zuri’arsu daga gare ta.

Hajiya wata irin halittar Allah ce, ba a iya mata. Dole ya raka Daddy. Sai ko tunanin murdaddiyar ‘yar aikin Hajiya, da son jin labarin ta da son sanin dalilinta na wannan aikatau din ya fi kowanne tunani mamayar 70% cikin kalbin shi. Amma dare ya yi nisa, yana kuma da muhimmin signing din takardu domin karbar licence daga hukumar lafiya ta kasa a goben haka ma zai raka Daddy Makarfi duka a goben in Allah ya yarda. Ya so kwarai ya ga yarinyar a yau, to amma da safe ma tana firgita in ta ga mutane bare da daddare?

Haka ya kwana da sake-sake, shi kam zuciyarsa ta amince mai da ya taimaki kyakkyawar ‘yar aikin nan ta samu rayuwa mai kyau, don yana ganin idan ta ci gaba da irin wannan aikatau din mai matukar wahala (for her age), za ta yi asarar kuruciyar ta ne yarinyar ta da ita.

Washe gari ta na goge-gogen kicin wurin karfe tara na safe, kasancewar a yau ta kammala komai da wuri ba kamar jiya ba, sauri take ta je ta huta sakamakon danyatsan ta da ke mata zugi, ga kuma menstrual pain (ciwon mara) da take fama da shi, don ma ta samu yanzun ya dan lafa, amma jiya kwana ta yi tana kuka, saboda azabar sa da radadin da danyatsan ke mata, ba wai don aikin ya kare ba, tunda kuwa nan da awa daya za ta soma aikin abincin rana.

Al’ameen ya kwankwasa lockers din kicin din da yatsun sa biyu a hanzarce ta juyo sai ya sakar mata murmushi mai nuna sannu, ya ce, ‘Na ga ba kya amsa sallama, shi ne na ce bari in miki ta bature, watakila ke din Baturiya ce, ban sani ba?”

Ba ta amsa ba, illa juyawa ta ci gaba da cleaning din ta tukuru, da gani ka san aiki ne da ya riga ya zame mata jiki, a ranta ko cewa take kai wannan mutum yana son matsanta wa rayuwata. Why?

Ya tura hannuwan shi cikin aljihun wandon basachi da ke jikinsa yana kallon ta kurum, duk wani motsin ta a kan idonsa ne, nutsuwarta da yaukin ta a komai yana burge sa har bai san adadin mintocin da ya bata a hakan ba can ya ce, ‘Wai ke ba kya magana ne?”

Nan ma ba amsa tamkar da dutse yake magana, ta koma ga juye snacks da ta kammala a cikin babbar roba a ranta ko cewa take wai wannan ina ruwansa da ni ne? A kan me ya damu da ita da zai ce lallai sai ta yi masa magana yana bin ta bashi ne? Ita fa duk wani da ya shafi Hajiya ba ta son gani, amma a zahiri ta rasa me yasa ba ta ko iya hada ido da wannan bako ko iya dubansa. Kwarjnin shi na da ban tsoro, shi kadai amma duk ya cika kicin din.

Ta sha ganin maza masu kyau da cikar halitta a cikin duniya da nan cikin gidansu, amma ba ta taba ganin mai kyau tsararre da ilhama kamar wannan bakon ba, to amma an gaya masa ko mutuwa ta yi ta dawo za ta yi wa jinin Hajiyar gidan nan magana? Ba ta ankara ba hakan nan ko a tunanin ta ba ta kawo zai shigo cikin kicin din ba, ya doso ta cikin daure fuska tamkar bai taba dariya ba tunda uwarsa ta haife sa, ta yi kamar ba ta gan shi ba ta juya ta ci gaba da aikinta, sai ya fizge robobin ya kifar da duk abin da ke ciki a dandaryar kasa ya yi wurgi da robar, ya kuma bi su yana takewa daya bayan daya yana rugurguza su yadda ba za su moru ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.4 / 5. Rating: 50

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 2Siradin Rayuwa 4 >>

13 thoughts on “Siradin Rayuwa 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×