Shekara kamar kwana.
Baby Intisar ta zana Common Entrance Exam dinta ranar Asabar. A ranar ne kuma Najib da Faisal suka sami admission a jami’ar Ilorin (Unilorin) inda dukkaninsu za su karanci fanni daya wato Engineering sai dai Faisal na Chemical, Najib na Electrical, Yasir da Bello ba su samu first choice din su ba, wato Ilorin din sai second din, shi Yasir OAU (Obafemi Awolowo Unibersity), sun dauke shi sai dai a maimakon course din Banking and Finance, da ya nema Entrepreneurial Studies suka ba shi.
Bello kuwa LASU sun ba shi kwas din da yake so Marketing, don shi rago ne, ya fadi dama bai son karatu mai wahala. Haka Nasir ya samu Jami’ar Abuja inda zai karanci Pol. Science, Faruk yana ajin karshe a sakandire yayin da ‘yan biyun gidan Furkan da Idris ke ajin SS II, shi ko auta Khalil ranar da Intissar ta zana Common Entrance (jarrabawar shiga sakandire) ranar ne ya zana Placement wato jarrabawar gama karamar sakandire.
*****
Intissar ‘yar shekaru takwas da haihuwa, a yau tunani goma da ashirin ya dame ta, ba ma yau kadai ba, tun ranar da aka fara shirye-shiryen tafiyar su Riyadh ita da Khalil wanda makarantar su Turkish ta nema masu da kanta saboda hazakar su, a karatu a yau, babu irin ‘ya’yan gidan Bello Makarfi.
*****
Dakin ta na jikin na Anti Saratu, dan karami ne da ke zagaye da fararen labulaye. Tun daga kofa za ka ji kana nitsewa cikin lallausan chinese carpet da ya malale dakin, dan karamin gadon ta na silber cike yake da taron teddy bears din ta wadanda su ne abokan rayuwar Baby Intisar a kullum, barci ko zuwa anguwa baya raba ta da su. Katifar gadon ta ruwa ce duk gidan ba mai irin ta sai ita ‘yar lelen Daddy, akwai tebir da take hawa karatu da bed side lamp bisan shi.
A kullum dakin Intisar cikin raba yake, ga wani sassanyan kamshi na air freshner din raspberry, da Anti ke sawa a kai akai. Akwai tangamemen hotanta window size da ta dauka cikin snow wato kankarar Switzerland sanye da thick coat baka doguwa har gwiwa da farar doguwar safa, sai takalmin shiga kankara baki da farar hular sanyi da ta rufe har kunnuwanta ruf rungume da teddin ta, sai murmushi take kai ka ce kafafun nan ba su taba taka kasar Nigeria ba. Sun je ne Arm-forces Remembrance Day da ake yi a can duk shekara da Daddy da Mamarta.
Ta yi tagumi kamar wata babba ta zubawa kifayen da ke gudu zuwa can karkashin ruwa a akwatin talibijin ‘yar karama da ke aiki a dakin, rungume da teddin ta da take kira ‘Lulu’ daga can bayan ta aka lallaba aka cire mata gilass kallo ya koma dusu-dusu. Ta kumbura suntum ta bi shi suka soma tsere cikin dakin tana korafin “Ba ni gilass dina Ya Faisal, ka ga bana so.”
Matsanancin tausayi ta ba shi har bai san yadda zai kwantanta ba, ya yi dariya ya maida mata, kamar kullum sai ta kara kyau, ta yi ajiyar zuciya ta soma jifan sa da teddin daya bayan daya yana karewa da hannunsa yana cewa,
“Haba baby na, wai ke ba ki san wasa ba ne? Allah na rike Lulu ba zan baki ba sai na yi flushing din ta tabi tutu (kashi).”
Anty ce ta raba fadan da kyar, ya fiddo sabon Math-set daga aljihun wandon jeans da ke jikin shi ya cilla mata, nan suka koma shirin su. To kusan kullum haka suke, ita Baby ba abinda ta tsana irin a cire mata glass lokacin barci bai yi ba, shi ko ya dage sai ta cire ta dinga hutawa, me ya yi zafi?
Allah Sarki, ita ta san me take gani, dusu-dusu yana-yana, Ubangiji Allah kada ka taba dora mana matsala a ido, domin wani abu ne da idan babu shi rayuwa take zamowa mara amfani.
Ya zauna bisa lallausan carpet din ta, hannuwan shi bisa gadon da take zaune yayin da ya zuba mata ido yana murmushi, ta yi filla-filla da math-set din tana dubawa da dukkan attention dinta, ina ruwan sarauniyar lissafi ya ce a ransa, amma a fili sai ya ce, “Ke kam kina jin dadin ki Intisar.”
Cikin halin ko’in kula ta ce, ‘Dadin me?” ba tareda ta dauke kanta daga math-set din ba.
Ya ce, ‘Ga ki nan kuwa, ba abinda ya dame ki, daga Antin ki sai teddin ki, muku yanzu karatu muke mai matukar wahala, karatun akwai wahala sosai.’
Ta tura dan bakin ta gaba, wanda ke kara mata kyau da yarinta,
“Bacin nima Daddy ya ce za a kai ni wani garin, kuma idan na tafi shi kenan na daina ganin ka da Mamana, kuma kasan Khalil cin zali na yake amma wai tare za mu tafin?”
Faisal ya juya hular kaboyi da ke kan shi baya ya ce,
“Ai in kun je ya ga ba ku da kowa ba zai doke ki ba, sai dai ma in ya ga ‘ya’yan Larabawan sun dake ki ya rama miki, kin san shi ba daga nan ba wajen karfi ba irin ki ba ne da kowane banza da ko wane hofi yake kayar da ke.”
Ta tura mai baki gaba tabbacin ya kular da ita, ya kyalkyale da dariya, amma ita yanzun ba wannan ne a gabanta ba, ta kuma cewa,
‘Shi kenan na daina ganin ka Ya Faisal?”
Sai hawaye a guje wani na bin wani, ya ce, ‘Oh! No Intisar, duk shekara za ku zo hutu gida, mu ma kuma za mu ke zuwa musamman muna duba ku, Riyadh gari ne mai dadi, you’ll enjoy it in a little while (Za ki ji dadin zama cikin ta cikin dan lokaci). Ya yi mata murmushinsa mai kyau, ya daga mata gira cikin tsokana ya ce,
‘Ba ki yarda ba ne?”
Ta girgiza kai bata ce komai ba,
“So what do you have to worry about (Me kuma zai dame ki)?”
A daidai lokacin da Anti ta dawo rike da kofin da ake kira mug cike da madarar shanu fresh milk ta nufi bakinta da shi amma sai ta ture, Faisal ya yi kiran ta da hannuwan shi ya ce “Come on beautiful baby!”
Sai ta mike cike da yauki da yangarta ta nufe shi, kafin ta karasa gare shi ya yi mata nuni da Anty Saratu da ke tsaye ta harde hannuwanta a kirji rike da kofin madara tana murmushi, sai dai da gani na rashin jin dadi ne, yau ta ba Babyn ta madara ta ture, ya ce,
‘‘Maman?” Bayan ya dan fiddo ido kadan alamar mamaki, sai ta karasa da gudu ta amshi kofin a hannunta ta kafa kai ta shanye, ta rungume kugun Aunty Saratu ta yi ajiyar zuciya ta ce,
“Mamar mu ki yi hakuri, tafiya ne bana son in yi in bar ki.”
Tana shafa kwantanccen gashin kanta ta ce, ‘Na hakura baby na, nima ina jin tafiyar nan ta ki har cikin raina. To amma ina so ki yi ilimi ingantacce wanda zan dinga alfahari da ke Saratu.’
Ta ce, “I promised you Maman, I’Il try my best to make you proud. (Na yi miki akawari Mamana, zan yi iya kokarina in ga kin yi alfahari da ni).”
Faisal ya sasa masu tafi mai karfi wanda ya janyo hankalin Daddy da ke dakin Antin shi ma ya zo, gaba daya suka taru suna lallashin ta sai da ta tabbatar masu ba ta tare da damuwa, sannan suma suka ji dadi. Intisar kenan.”
Aunty Saratu, Faisal da Daddy su ne ‘yan rakiyar Saratu da Khalil makaranta. Kingston College, makaranta ce ta kimiyyah zallah a Riyadh (Capital din Saudi-arabia). Ba a hutu sai karshen shekara kadai, ta hada dalibai daga ko’ina cikin duniya musamman ‘ya’yan Larabawan Morocco, Pakistan, Egypt, Istanbul, da Syria. Ba kowa suke dauka ba, duk kudin ka kuwa sai ka ci interview din su. To Saratu da Khalil sun ci har sun side a darussan lissafi da Ingilishi. Ilmul-Kimiya’i wato (Science) shi suke koyar da daliban su zallah tun daga ajin su na karamar sakandire. An sa Khalil aji daya na babbar sakandire (SS), ita kuma Intisar aji daya na karamar sakandie (JSS).
Tana sanye da riga da wandon Pakistan ruwan madara (milk colour), ta yane kan ta da siririn mayafin kayan, ta zuba yatsun ta duka biyu a baki tana tsotso kamar kullum, kafar ta sanye cikin wani rufaffen takalmi baki kirar Andalus.
Tana kallon Faisal, Daddy da Mamar ta suna fita daga harabar makarantar cikin (Tadi) din da ta kawo su suna ta daga masu hannu. Sai ta ji wasu dumammun hawaye (warm tears) na zirarowa ta karkashin gilashin ta suna diga kan takalmin ta.
Tsakanin Antin ta da Ya Faisal bata san wa ta fi kewa ba.
Rayuwarta A Riyadh
Saratu Bello Makarfi, yarinya ce daga cikin irin yaran nan da ake kira gifted wato ‘yan baiwa. Hakika Allah ya yi mata baiwa a ilimin Chemistry, fasahar ta tafi karfi a nan. A duk san da suke practical lokacin da ta isa babbar sakandire, akwai wani malamin su Balaraben Turkiya wai shi Dr. Alhassan a duk lokacin da take leke cikin ‘microscope’ da ‘stethscope’ sai ya ce, ‘Saratu is doing research to improve the quality of our lives. Ma’ana (Saratu na yin bincike domin gyara karkon rayuwar mu).“
A duk san da ya fadi hakan ji take kanta ya kumbura, burin ta ya karu kan son gyara rayuwar al’ummah!
Tun a shekararta ta farko a makarantar sunan ta ya yi tambari a set din su, ta yi sadikai (abokanai) da dama, ‘ya’yan Larabawa bila-adadin saboda farin jinin ta da shiga rai. Harshen ta ya juye da larabci ziryan. Larabci na hakika kuwa ba kala daya ba, ba kala biyu ba, tun daga na Hijaz, Maghrib, Yemen, kudanci da arewacin Istanbul babu wanda ba ta yarawa saboda cakudo da mu’amala da jinsi-jinsin dalibai ‘yan asalin kasashen.
A shekarar ne kuma aka bata Nakeebatul-fasl wato (class monitress), shugabar ajin su saboda duk tafi ‘yan ajin focusing a hankali a hankali malaman su ke gane hakan don a komai ita ce a kan gaba.
Uniform din su farar shirt ce sol da bakin tie, hade da bakin skirt sai farin ribbon da bakin sandal kirar Turkey. Ba kasafai suke haduwa da Khalil ba da ke bangaren maza in ba wani taro na makarantar ya hada su ba kamar quizzes ko debates da makarantar ke shiryawa a kai akai.
A shekarar ne ko kusan karshen shekarar aka kawo wasu yara mata guda biyu daga France, hostel din da take, daya a saman gadon ta daya a gefen gadon ta ke da ganin su kin ga half-cast wato ruwa biyu, suna magana da harshen Faransanci a junansu, maimakon Larabcin Saudiyyah da ya fi yawa a makarantar.
Yara ne da ko za ta girme su da kadan ne, kyawawa amma farin su mai duhu ne, hakan nan ba su da yawan gashi cancan, wanda ke nuna ‘yan asalin Ifrikiyyah fatar jikin su da irin maganar su shi ke nuna girman Faransa ne ko kuma dai sun zauna a France na lokaci mai tsawo.
Sai da daddare ta kwanta ta shige cikin bargo bayan ta yi addu’o’in da take yi ta shafe jikinta, amma barcin ya ki zuwa, tana ta tunanin wadannan yaran da ta ji sun shiga ranta farat daya tana kuma tsoron ta kula su su yi mata wulakanci don da alamun su ‘yan jin kai ne sai me? Kawai ta ji sun juye harshe zuwa zallar Hausa kamar jakan Kano, ta ji ta saman gadonta ta ce,
‘Hunainah kin yi barci ne?”
Ta ce, ‘A’a, Allah na kasa barci Yaya Hidayah, wannan Balarabiyar ta kasan gadon ki kawai, haka kawai na ji ina kaunar ta don kamannin su da Mamin mu in kin lura har ya yi yawa. Amma kalli ko kallo ba mu ishe ta ba, ko ta gane mu ba Larabawan ba ne oho.”
Wadda aka kira Hidayar ta cafe, ‘Kamar kin san abin da zan ce miki kenan. Amma Allah ya kai mu gobe duk inda Larabci yake zan koye shi a gobe dole mu zama kawayen ta Allah….”
Dariyar da take ta faman babboyewa ce ta kubuce, ta rasa dalilin da yasa mutane da dama basa gane ita Bahaushiya ce a makarantar, don su ba su san ma wata kabila wai ita Hausa ba, hatta malamanta sunanta ne kurum yake fallasa ta domin sukan ji shi banbarakwai har ba su iya fadi dai-dai, su kan tambaye ta nationality dinta a kullum amsar ta ita ce,
“Ana Nigery (ni ‘yar Nigeria ce).” Daga haka ba ta kara komai a kai.
Dariyar ta tasa duk suka tsorata suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su ta ce da su, ‘Ma’ana Arabi, (Ma’ana ni ba Balarabiya ba ce), nima Bahausa ce kamar ku, ku sauko mu yi hira.”
Duk suka dirgo gadon ta suka dubi juna, sai kuma suka tuntsire da dariyar gane ashe dukkan su tushen su daya.
“Sunana Saratu Bello, na zo daga Nigeria.”
Hidayah ta ce, “Muma duk ‘yan Nigeria ne. Amma an haife mu a France. Sunana Hidayah Bashir Sambo kanwata Hunainah. Baban mu ke aiki anan sai kuma aka cilla mu Russia, daga baya ne aka turo mu nan, nan din ma an ce ba da dadewa ba ne za mu tashi, saboda aikin da zai yi anan temporary ne. Sunan garin mu Shanono a cikin Kano, ke kuma ya sunan garin ku?”
“Mu a Kaduna muke, daga baya kuma muka koma Lagos yanzu duk gidan mu suna can Lagos.”
“Mu ma muna zuwa Lagos wata unguwa Bictoria Island akwai antin mu Hajjo mu kan je hutu wurin ta.”
‘To ai mu anan arear ma gidan mu yake, in kin wuce gidan Major General Shitu Allazi.”
Karamar wato Hunainah da ta zuba mata ido kawai tunda suka fara surutun su ta ce,
“Allah kamar ki daya da Mamar mu, end of the year, wato karshen shekara za a kai mu gida hutu, za ki bi mu Maman mu ta gan ki?”
‘Idan school ta amince min sai mu je mana kafin mu tafi gida, amma akwai yayana Khalil yana bangaren maza sai dai in tare za mu je?”
Gaba daya suka hada baki suka ce,
‘Ba sai mu je taren ba?.”
Daga ranar fa kawance ya kullu, inda duk ki ka ga Intissar kya ga Hidayah da Hunainah, dakin cin abinci, wajen daukar darasi, dakin karatu da wajen wasannin motsa jiki duk tare suke zuwa. Su ci mai kyau su sha mai kyau su zauna a mai kyau, kada ki so ki ga yadda suke wani irin girma cikin shekara guda kacal.kamar kajin gidan gona.
Ga Hidayah da shegen tonon fada da ‘ya’yan mutane sai su taru su shigar mata wani lokacin kuma ta zame ta bar su a ciki don duk ta fi su wayo, ba ‘ya’yan Larabawan kadai ba har ‘ya’yan manyan Saudiyyah yaran nan ba sa kyalewa kamar kasar ta uban su ce. Hakan nan kowacce na ji da basira da kwakwalwar da Allah ya hore mata komai su ne higher ita Hidayah a fannin sport ta fi kauri kasancewar ta doguwa sosai.
Kwanci tashi ba wuya gurin Allah kuma dama masu iya magana suka ce wai shekara kwana ce. Yau ga ranar tafiyar su hutu ta zo, an jinkirta tafiyar ‘yan Nigeria saboda babu jirgin su zuwa washe gari. Da taimamkon Dr. Alhassan kasancewar shi mutumin Intissar aka bar su bin su Hunainah da kuma kasancewar gidan gidan Jakadan kasarsu ne, ita da Khalil suka bi direban su Hidayah da cewar mota za ta je har can washe gari ta dauke su zuwa airport.
Gidan su Hidayah na Shari’ Palastine ne a cikin birnin Riyadh. Tun daga gate Saratu ta tabbatar su ‘yan gata ne, amma gatan da ta ga ana gwadawa su Hidayah ya dame nasu ya shanye.
Har a jikin kofar shiga falon gidan an mammanna card na Larabci da Turanci da Faransanci, masu dauke da rubutun “U’re highly welcome kids.” Wani kuma an rubuta “Marhaban bikum ya bunayyah.”
Ta yi tsaye hannu a haba tana kallon Mamar su Hunainah na katantanwa (juyi) da su a tsakiyar falo tamkar ta maishe su ciki ta sake haifo su don kauna, shekara guda ba ta gan su ba. A ranta ta ce, “Nima dai insha Allah gobe I yanzu ina jikin Antina, nima ina jin dumin Mama na.”
Ba ta ankara ba ta ji Mamar su Hunainah ta rungumeta ta baya, ta sumbaci kuncin ta na dama wani dadi ya ratsa ta irin wanda bata taba ji a duniya ba, ita ma ta maida mata da irin hakan, gaisuwar garin kenan “Marhaban bi kum asdi’ka’l’ wato barkan ku da zuwa abokan mu.
“Ya Rabbi!” Haka ta fadi tana ja da baya. Wannan kama da yawa take tamkar ta yi kaki ta tofar. Tunaninnika daban-daban take sakawa tana warwarewa a ran ta amma ta rasa na kamawa. Su ko su Hunainah sai dariya suke abin su suna kyakyatawa suna fadin dama sun kawo Saddikar su ne (kawar su) Inteesar don ita ma Maman ta ji irin mamakin da suka ji da ganin Saratu.
Jikin ta ya yi sanyi kalau, tuni ta jike kashirban da gumi. Tasa masu aikinta suka yi entertaning ’ya’yan ta da bakin su domin ta nemi duk wani tunani da kuzari da ke tare da ita ta rasa.
Su kan su masu aikin da suka dubi Intisar, suka kuma dubi tangamemen hoton uwargijiyar su da ke kafe a falon sai suka ce ‘Subhana Rabbiyallazi iza ya kulu li shai’in kun fa ya kun.” Ma’ana tsarki ya tabbata ga Ubangijin da in ya ce kasance, sai ya kasance. Domin wannan kama da yawa take.
Ambassador Bashir Sambo, shi ne mahaifinsu, baya gari a wannan lokacin. Duk kokarin Haj. Hadiza na neman layin shi abin ya ci tura a wannan daren, duka wayoyinshi a rufe, kamar ta dora hannu ta ce Wayyo Allah! Jikin ta har wani irin rawa da kyarma yake.
Ita kanta ta kasa tantance me ke damun ta game da bakuwar ‘ya’yanta? Haka ta kwana cikin zullumi da ci da zuci, wani abin takaici kuma da sassafe sai ga motar Kingston College a kofar gidansu ta zo tafiya da su airport tana kwance a daki wani matsiyacin zazzabi ya rufe ta, Khalil ya ja hannun kanwar shi ko wanka ma ba su yi ba balle karin kumallo suka shiga motar suka tafi. Karfe goma na safe suna cikin jirgin Mea International wanda zai sada su da kasar su ta haihuwa, Nigeria.
Mun gode
Thanks
Thanks alot
Badamuwa
Thanks so much
Muna godiya
Intisaar ta zo gida