Skip to content
Part 19 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Daidai lokacin da Anti ta turo kofar ta shigo dauke da jug cike da tatattun ‘ya’yan itacen tuffah da tambulan mai garai-garai. Ya mike ya karbe ta, ta tsiyaya masa ya sha suna gaisawa ta ce, “Bayerabe saukar yasuhe?”

Ya yi dariyar da ya lotsa beauty point din shi, ‘Ke ma Anty tsokanar baby za ki lankaya min?”

Ta ce, ‘ina suka yi posting din ka NYSC?”

Ya ce, ‘Ai ni na shiga uku da kasar Yarabawa, nan Ilorin din suka bar ni.”

Ta kyalkyale da dariya nan suka shiga hirar makaranta. Ya ce, ‘Aunty gobe fa Intisar za ta koma, ga bisa din ta na amso, yau ko darajar kallo ban samu daga Intisar dina ba, duba ki ga yau ko gaisuwa babu? Ni na rasa me kuma zan ce da Baby ta fahimci ba ni da laifi?”

Yanayin yadda ya yi maganar ya bala’in ba ta tausayi, ta kai idon ta ga stool din da Saratu ke zaune tana ta aikin kalbar ta.

“Wai da gaske Saratu ba ki gaishe shi ba?”

Ta saki jelar hannunta, ta juyo kadan ta cira lumsassun idanun ta a gicciye ta zube su a kan shi, cikin sassanyar muryarta ta ce,

‘Ina wuni ya Faisal?”

Ji ya yi tamkar ta ja shi da wutar lantarki, abin da bai taba ji ba a rayuwar shi. Gaba daya ya karasa kidimewa, kwayar idon shi na neman bacewa, ya yi kokarin saisaita tunanin shi ko don saboda Anti da ta kafa masu ido, cikin jarumtaka amma da kyar sautin ya fito daga makoshin sa da ya bushe rayas, ya ce, “Ba na amsawa, alhalin sai da na roka?”

Ta yi murmushi kawai cikin halin ko in kula, ta juya ta ci gaba da kalbar ta. Anti ta yi mata fada sosai amma ba ta ce ko kanzil ba. Ta samu gefen gadon Intisar din ta zauna ta ce,

‘Maganar tafiyar Intisar Riyadh a gobe, ina ganin a bar ta kawai Faisal.”

Maganar ta yi mai kama da saukar kibiya a kahon zuciyar dan adam, duk gwiwoyin sa suka yi sanyi, ya yi dagwalo abin tausayi, a ransa ko cewa yake me zai yi ya farantawa wadannan murdaddun uwa da ‘ya?

Ta ce, “Da farko dai ina son sanin inda ka samo million biyu Faisal?”

Faisal bai iya karya ba, kazalika duk ‘ya’yan Brigadier.

‘Hajiya ce ta ba ni in kai mata banki, ni kuma na ga da a kai kudi a aje a banki hakan nan kawai, ba gara na maida Baby makaranta da su ba?”

Aunty Saratu ta yi murmushi, yau kam ta kara tabbatarwa kanta Faisal yaro ne danye da gigin kuruciya ke diba,

“Yanzu saboda Allah Faisal, idan ta je banki daukar kudin ta, ta tarar baka kai ba, me mahaifiyar ka za ta dauke ka?

Mara amana. Da mai cutar mahaifiyarsa wanda ni bana maka fatan hakan. Zafin rai ba shi zai sa Saratu karasa karatu ba, komai na rayuwa yana tafiya ne da lokaci. Idan Allah ya ce iyakar abin da Saratu za ta karanta kenan a duniya babu dan adam din da ya isa ya kankare. Har yau, har gobe Faisal ba mu fidda rai da releasing din Baban ku ba. Don haka yanzu-yanzu ka je ka saida bizar nan ka mayar mata kudin ta inda ta ce. Idan fa Allah ya yi hukunci Annabi sai ceto.

Ita Saratu ba wai tana jin haushin ka don ku kun koma makaranta ita bata koma ba, illa ba ku damu da ni ba da kuma tunanin me ta yi wa Hajiyar ku ta tsane ta? Wanda na gaya mata wannan tunanin ba zai amfane ta da komai ba. Don Allah kan halicci mutum ya kimsa rashin jituwa tsakanin sa da wani ba tare da wani dalili ba. Bai yiwuwa mu samu soyayyar kowa a rayuwa . Na tabbata kana kaunar mu Faisal, kauna ba kadan ba. To albarkacin kaunar nan Faisal do as I said, ma’ana yi yadda na ce.”

Sai ya mike, duk jikinsa ya yi sanyi lakwas. Ya maida passport din aljihun gaban rigar shi. Wasu hawaye suka tarar masa a kwarmin ido, amma ya yi kokarin maida su. Tausayin Aunty Saratu da Intisar ke narkar da jijiya mai bada jini a jikin sa!

*****                         

A Korea

A cikin babban birnin Seol din kasar Korea, Hajiya Hadiza ke kwance masu yawa, ta juya a hankali gami da dafe kirjinta domin samun sauki cikin sofa idanun ta a rufe, zuciyar ta cike da kuncin da ta kasa rabo da shi tsayin shekaru daga tafarfasar da zuciyar ta ke yi tamkar ta faso allon kirjin ta ta fito. Wasu irin hawaye suka biyo lallausar kumatun ta masu zafin dake kara zafin da zuciyar ta ke ciki. Cikin dan lokaci zazzabi mai zafi ya rufeta, jikinta ya rude sosai, zazzabin ne, ciwon kai ne, kirjinne duka ba wanda cikin su bai mata ligi-ligi ba, daga kwancen da ta ke ta fado kasa tana mirgin-mirgin, a sabili da wani irin zafi da tukuki da kirjinta ke yi.

Ambassador Basheer Sambo, ya fito wanka ya zuba suit bakake ya na daura ‘links’ din hannun rigar shi, cike da tunanin me ya tsayar da Haddizah?

Tunda suka yi aure kimanin shekaru goma sha biyar a baya, dai dai da rana daya bata taba barinshi da daure tie da botirin riga ba in ba da wata muhimmiyar lalura ba, sai ko yau din nan. Ya shiga danna mata kira ta intercom har ya gaji, babu Haddizah babu tattausar muryar ta.

Yana shirin fitowa ne bayan ya dauko briefcase din shi suka yi wani uban karo da babbar diyar shi Hidayah, a zahiri a firgice take, ga hawaye na zuba a idon ta, kira ta ke cikin tashin hankali “Mummy ta mutu Daddy…”

Wadannan sune kalami mafi muni da ya taba ji a rayuwar shi, suka kuma hautsina ‘ya’yan hanjin sa duka a lokaci daya. A guje ya soma hada matattakala uku-hudu har ya tadda falon shan iskar su, inda a nan ne ya baro ta tana sallar asubahi.

Rigingine ta ke kurum, babu alamun tana motsi haka babu alamun numfashi a tare da ita.Ya kai hannu cikin sanyin jiki ya juyo da fuskar ta gareshi yace “Ha-di-zah!”

Ya kira sunan yafi sau goma cikin rawar murya kakkaura, amma bata amsa ba, kamin yayi ta maza in ji mata ya fiddo wayar shi cikin aljihu ya kira likitan su, cikin mintuna ashirin likitan ya shigo. Ya jima yana aune-aunen sa a kanta yayin da uban da ‘ya’yan suka yi sukutiii… suka zubawa sarautar Allah ido, kowanne zuciyar nan ba sai an tona ba da tararradi.

Tuni Hunainah ta soma kuka, likitan ke lallashin ta yana gaya mata Maman ta ba mutuwa tayi ba, ya daura mata drip yayi mata allura guda daya yace idan ruwan ya kare zai dawo. A ranar ta sha allurai har da na jijiyoyi kamin ta soma shaida wanda yake kanta. Kwananta uku a kwance.

Rannan da daddare sai ta ji ta narke cikin laima, ta yi salati ta runtse ido, babu ko tantama, dan yaron cikin da take dauke da shi ne, ya fice.

Sakamakon binciken kwararren likita Norman, Hajiya Hadiza jinin ta ya hau sosai sabida wani damuwa da ta sama ranta tun da dadewa. Ambassada ya kama kai, “hypertension, Haddizar? Shin me ke damun Hadiza? Meye matsalan ta a rayuwa?

Duk wani so, duk wata kauna ya mallaka mata ita da ‘ya’yan ta. Bai taba barin su cikin bacin rai ba dai-dai da rana daya sai ko cikin ajizanci irin na dan adam. Bai yi zaton akwai wani buri da take da shi ba kuma bayan wannan. Ba abinda ya gaza yi masu a rayuwa, to shin ta ina ya kuskurota da har ta ke neman rugurguza masu kyakkyawar rayuwar da suke ciki? Me ke damun ta, da ke neman ya cuce shi? Dan cikin da ya ke begen ta haife mashi da namiji, ta bari ya bi rariya a hofi da tunanin da ya ke ganin na banza ne.

Satinta kwata-kwata daya a kwance, amma in kaga muguwar ramar da ta yi tsammani za kai shekararta guda tana jinya. Tayi duhu, idanun ta sun fada sosai kullum kuma bata umh bata umh-umh ko sannu su kai mata bata amsawa sai dai ta bisu da na mujiya kawai. Ambasada ya shiga matumkar damuwa kazalika ‘ya’yan ta ko makaranta sun kasa zuwa. Koda ta sami sauki ma jiya I yau, kullum tana kwance kawai (flat) tana kallon (ceiling) ita kadai tasan me ta ke sakawa tana kuncewa a zuciyar nan tata tamkar bata taba gamuwa da wani abu wai shi farin ciki ba a gabadayan tsayin rayuwar ta. Duk kuwa da kakkausan gargadin da likitanta ya yi mata na nesantar tunanin da take yawan yi don tserar da lafiyarta daga kamuwa da ciwon zuciya.

A yau ma kamar kullum, ya dawo daga ofis ya taddata rigingine hawaye na bi ta gefen  kuncinta, wani haushi ya kama shi amma ganin ‘ya’yan sun tasa ta a gaba suma kukan suke, an rasa mai lallashin wani, ya ji babu dadi. Dukkan jikin sa ba lakka, ya zame ya zauna gefen ta dai dai saitin kanta cikin rarraunar murya yace “Hadizah, in kina kaunar Ubangijin da ya halicceki, ki gaya mana me ke damun ki? Ki tuna fa daga ni har ‘ya’yan ki, muna da hakki mai girma a kanki da ya zamo dole mu san damuwar ki. In kina ganin bana iya magance maki ita, akalla babu abinda kudi basa yi a duniya, ni kuwa in har kudi zasu yi min maganin wannan damuwar da kike ciki, ban ga amfanin su gareni ba.

Duk fa wani hakilo da na ke yi a duniya domin dauwamar farin cikin ku ne, da kokari na na cika alkawarin dana dauka akan ku ke da Hajjo. Idan kuma ni ke bata maki ki gaya mun don in gyara, don shi dan Adam har kullum ai ajizi ne?”

Hadizah ta girgiza kai alamun ko daya babu cikin abubuwan da ya lissafa. Ya ce “to ko zaman kasarnan ne baki so mu nemi sauyin aiki?” Nan ma Hadiza tace “lala” yace “kenan aure na ne ya ishe ki, ko kuma kin gaji da zama da ni sabida wani illa ko nakasu da nike da shi, wanda ni din ban sani ba, kike kuma jin nauyin ki gaya mani? Idan haka ne ki fada mun man, ni har kullum Bashir mai kaunar ki ne da farin ciki da duk abinda kike so, zan iya sauwake maki domin farin cikin ki, ni da ‘ya’yan ki mu dauki danganar rashin ki, in har hakan zai maido maki da rayuwar ki ta  baya…” sai ya fiddo biron shi daga aljihun gaban rigar shi, ya ja littafi ya yagi takarda, ya aza biro kamar mai shirin yin rubutu.

Bata san yaushe ne ta samu kanta a gabansa ba tana magiyar kada ya rubuta, da wanne zata ji? Haka Hidayah da Hunainah sun rirrike hannun shi tamau da suka fuskanci aika-aikar da yake shirin yi wadda ko giyar wake ya sha yasan shima ba zai fara ba, komai rintsi. Suka ce “Daddy in ka saki Mamar mu Allah muma bazamu zauna da kai ba” yace “to ya kuke son in mata? Hidayah-Hunainah Mamin ku bata kauna ta.

Baka taba boyewa wanda kake kauna damuwar ka ko ta mecece balle mijin ka, abokin rayuwar ka na har abada! Ku duba ku ga cikin da muke neman samuwar shi shekara goma da doriya, ta bari ya salwanta a banza, ba ruwan ta da mu balle damuwar da muma zamu iya kasancewa a dalilin tata damuwar, a dalilin rashin walwalarta garemu, shin wannnan shine zaman iyali na hakika da suka fahimci juna suka kuma yarda da junan su? No matter what ke damuna, ba zan taba boyewa mahaifiyarku ba…”

Ya mike ya bar su nan ya fice. Hajiya kuka ‘ya’yan ta kuka. Tun da suke, basu taba fadawa halin kunci irin na yau ba. Gabadayan rayuwar su cikin farin ciki da fahimtar juna ne eben once, yaran nan basu taba ganin wani sabani makamancin wannan ya faru tsakanin iyayen su ba balle har a kai ga musayen ra’ayi ko tankiya. A ko’ina, Ambassador Bashir da Hadizah, masu nuna suna kaunar junan su ne.

Amma a yau wai za’a rubutawa Maman su saki? Hidayah da Hunainah, cewa sukai a ran su kada Allah ya kuma nuna masu wata rana makamanciyar wannan. A fili kuwa rokon Mamin su suke ta gaya masu me ke damun ta????

Tushen Labarin

Suna na na asali Hadiza-Kubra, amma a rugar mu DIJE a ke kira na. Ni mutuniyar wani kauye ce wai shi Shanono, karamar hukuma ce a cikin birin kano Nijeriya. Koda yake asalin mu ba Kanawa bane matafiyan fulanin daji ne.

        Mun billo daga wani jeji a yankin Adamawa muka dira a Gongola, muka dawo Dukku ta Gombe, muka sake tashi muka koma zama a Alkaleri ta Bauchi. A kan hanyar mu ta isowa Medile daga Yako, mahaifinmu wanda shine shugaban ayarinmu ya mutu, sai kanin sa Baffa Lalajo shi ke kula da mu kuma shi aka nadawa rawanin mahaifin mu.

         Bayan rasuwar sa ne muka lula cikin nahiyar Kano, a wani jeji bayan garin Shanono muka kafa bukkoki, muka saki dabbobinmu muka yi zaman mu anan cikin kwanciyar hankali. A can duk aka haife mu ni da kanwata Hajjo, da Baffa ya mutu ya bar Innar mu da tsohon cikin ta, kushewar ‘yan uwa da kakannin mu har yanzu suna can.

Malam Ibrahim sarkin noma shine Sarkin Noman kauyen Shanono, mutum ne mai arzikin gaske, a garin Shanono bakidaya, babu wanda ya kai shi nome amfanin gona mai yawa, ya mallaki tafka-tafkan gonaki sama da goma ya kuma fi duk manoman garin samun amfanin gona mai albarka. Dabbobi garke-garke da gidajen gona da wannan mutum ya mallaka har ba zasu lissafu ba, a takaice abinda za’a ce shine duk fadin garin babu wanda ya kai shi arziki.

Abin tausayi da wannan bawan Allah shine bai taba haihuwa ba, har shekarun girma suka riske shi. Shekarun su ashirin cif da matar shi ta ladan noma Shatu amma ko batan wata bata taba yi ba.

Daga baya ne ya shiga neman auren karamar yarinya budurwa, tare da Addu’ar Allah ya sa karshen wahalar sa ta zo na samun Magaji daga gareta, wanda ya ke kwana rokon Allah ya bashi kamin ya dauki ran sa.

Shekaruna goma sha hudu Baffa na ya ce ya ba sarkin noman Shanono aure na. Na yi kuka nayi bakin cikin kiyayyar auren tsoho sa’an Baffa na kaman in mutu, amma sai Baffa ya daga ni ya jefa a katuwar tukunya, ya zane da tsabga, sai da ya yi mun tabban da har abada ba zasu goge a gadon bayana ba kana ya kyale ni, ya kuma ce idan na sake tada hankalina kan auren sarkin noma sai ya  kore ni daga rugar mu, mahaifiyata da Yafendo na babu yadda suka iya, haka suka wanke ni suka ba sarkin noma. Sarkin Noma ya dauki son duniya ya dora a kaina, wannan ne ya sayo mun bakin jini a wajen kishiya ta, Shatu, kullum cikin yadar mun da magana ta ke kan yarinya ta dani na auri tsoho sabida tsabar kwadayin abin duniya, na juye kan tsoho kinibabbiya, har sai da ta kai ko tsakar gidan bana iya fitowa in har ba Sarkin Noma na gidan ba, bana umh bana umh-umh kullum sai sakar auduga.

Ba sai na fadi ba ku ma shaida ne a kan irin kyawun da Allah yai min, kyawun da akan ce duka rugar mu babu kama na. Da na lura Shatu ba kishiyar kirki bace sai na shiga yiwa kaina addu’o’in tsari daga sharrin ta, tare da yin taka-tsan-tsan cikin duk wasu al’amurana da ita.

A zamana na shekara guda kacal da Sarkin Noma na fahimci shi mutumin kirki ne, mai alheri mai saukin kai da taimakon talakawa, duk garin kowa na kaunar shi da girmamashi suna kuma taya shi Addu’ar Allah  ya cika mishi dadadden burin rayuwar shi kamin mutuwar sa. A hankali-a hankali sai na ji nima ina kaunar shi sabida kyawawan halayen sa.

Shatu kan ce ta san na zo ne in haihu da Sarkin Noma, in kashe shi in kwashe dukiyar sa in gudu, to kuwa na haihun ta gani, domin ita tana cikin sahun matan nan da ake kira (juya).

Yafendo na da dangina da ke ruga kan ziyarce ni lokaci-lokaci. Shekara ta daya a gidan Sarkin Noma sai ga ciki ya billo, amma da ya ke ni doguwa ce babu wanda ya farga har sai da ya shiga wata bakwai, ni kuma dama ba baki ne da ni ba balle in fadiwa wani. Ko shi kansa Sarkin Noma bai kawo a ransa wai ciki ne da ni ba duk da kibar da na yi, to abu ne da duk an fidda rai.

Rannan Aliero (Yafendon mu) ta zo duba ni kamar yadda ta saba, na tashi don in debo mata ruwa a randa  sai cewa tayi

“yaki Dije, ikon Allah, ashe juna biyu gareki baki fadi mun ba? Ke dai Aradun Allah zurfin cikin ki wataran sai ya kahe ki” nace “juna biyu? Yafendo me ar juna biyu?” tayi tsaki ta fito soro ta tadda Sarkin Noma, tace zasu dauke ni rainon ciki, ba kuma zan dawo ba sai na haihu. Farin ciki a wajen Sarkin Noma kema kin san fada ma bata baki ne. Ya daga hannu yayi godiya ga Allah ya shiga rabar da dabbobin shi da kadarorin shi masu yawa sadakah, ya kuma kara kyautatawa Malaman da ke taya shi rokon Allah kan su kara dagewa da Addu’ar Allah ya sauki Dije lafiya.

<< Siradin Rayuwa 18Siradin Rayuwa 20 >>

6 thoughts on “Siradin Rayuwa 19”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×